Page 16
by @farnanahhh
Ana gama sallar Isha an fito daga masallaci Mallam Kabiru ya wuce gidan Mallam Musa domin neman auren Maryam
Yana zuwa yayi sa’a shima ya dawo daga masallaci suka gaisa, Mallam Kabiru yace “dama wata muhimmiyar magana ce ta kawoni” Mallam Musa yace “to bari a dauko tabarma” yace “ai inaga nan ma yayi” Mallam Musa yace “A’a baza’ayi haka ba, bari naje na kawo” yaje ya dauko tabarma ya shimfida musu suka zauna
Suna zaunawa Baban sufyan yace “dama nazo ne akan Maryam” Baban Maryam yace “toh Allah yasa ba wani abu tayi ba” yace “A’a bakomai, nazo ne nemawa Sufyan aurenta” Baban Maryam yayi ajiyar zuciya yace “to Maryam dai wani yazo sun sasanta kuma na bashi izinin ya turo iyayenshi” Yace “Allah sarki, Mallam ba matsala Allah yasa hakan yafi zama Alkhairi” yace “Ameen Mallam nagode” sukayi sallama shi ya wuce shi kuma ya shiga gida
Yana shiga ya tarar Maryam da Mamanta suna zaune a tsakar gida, suka gaidashi suna mishi barka da dawowa, Ya zauna yana gayawa mama Mallam kabiru yazo nemawa Sufyanu auren Maryam, Mama tace “Allah sarki, ni dama Nace anya ba wani abu tsakaninsu Ashe akwai, amma Mallam me kace mishi” Baba yace “ce mishi nayi akwai Wanda na bashi izinin ya turo iyayenshi" Mama tace "aikam gwara da ka sanar mishi, Allah ya bashi wata" Baba yace "Ameen" Maryam dai tana jinsu ta tashi ta koma dakinta
tana shiga sai kuka ta fara, a ranta tace dama sufyan yana sonta amma ya kasa gaya mata gashi wani ya rigashi, ita dai harga Allah da Baba zai ce ta zaba a cikinsu sufyan zata zaba amma tasan aikin gama ya gama, haka ta cigaba da kuka har ta gaji, tana tunani sai ga kiran Junaid, ta gaishe shi ya amsa, yace "ya naji muryarki haka kamar kina cikin damuwa" tace "Aa bakomai inajin ciwon kai ne" yace "Subhanallah ko nazo aje asibiti" tace "Asibiti kuma, ai nasha magani nasan da nayi bacci InshaAllah zai daina" yace "to Allah ya baki lafiya, bari na barki ki huta" tace "Ameen nagode" sukayi sallama ta aje wayar ta kwanta
_____________________________
Abba yana komawa gida ya sanarwa Umma yadda sukayi, Umma tace “ai kaga yaci riba ni nasan yana son yarinyar nan amma wannan nauyin bakin nashi ya hana shi ya gaya mata gashi an riga shi, Allah ya zaba mishi tagari” Abba yace “Ameen, sai ki sanar mishi idan ya shigo” Umma tace “to InshaAllah” ta kawowa Abba abincin shi
Sufyan ya dawo shi da Ameer sukayi sallama, Umma ta fito ta amsa musu suka gaidata, Ameer yace “Umma ni Yunwa nakeji” Umma tace “to sarkin ci gaje chan Hajara ta zuba maka” ya amsa da to ya wuce, Sufyan yace “Sannu da gida Umma” tace “yawwa muje dakinka zanyi magana da kai” Yace “to Umma” sukaje dakin sun zauna Umma ta gaya mishi yanda Abba ya gaya mata, Sufyan yace “Allah yasa hakan ne mafi Alkhairi” Umma tace “Ameen” ta tashi ta fita, tana fita yayi ajiyar zuciya
_______________________________
Bazla tana kwance a dakinta tayi shirin bacci, wayarta ta fara ringing tana dubawa taga kamal ne da tayi kamar kar ta daga sai kuma ta daga, da sallama a bakinta, ya amsa yace “Ina kika shige haka, ko kuma tunanin ne har yau baki gama ba” tace “ba inda na shige ina nan, kaine dai ka buya” yace “a’a fa, nayi ta kiran wayarki kashe, har Nace Anya lafiya, da gobe ma zanzo” tace “Allah sarki” a taqaice don batason magana, yace “to yanzu dai ka kira naji me kika yanke” tace “Ka kusa jin abunda na yake kar ka damu” yace “to shikenan” tace “to zanyi bacci” sukayi sallama ta rufe idonta don tyi bacci
_______________________________
Washe gari
Misalin qarfe 11:47am Mamie tace “Haule jeki dakin Yasmeen ki kira mun ita tun dazu nake jiranta tazo ta kai saqon nan tayi zamanta, Haule tace “to hajiya” ta tashi taje dakin tayi sallama ta shiga, ta sameta kwance tana danna waya, Yasmeen ta amsa sallamar tace “menene Haule” tace “dama hajiya ce tace tana jiranki” tace “to gani nan zuwa” haule ta juya ta fita ta sanarwa Mamie tace tana zuwa
Ta tashi ta shiga toilet tayi wanka tazo ta gyara fuskarta ta dauko atampa riga da skirt mai launin purple da green sai ratsin peach a ciki, dinkin ya matuqar yin kyau ta saka tayi kyau sosai ta dauko gyalenta da jaka peach ta saka da takalmi ta fito
Mamie tace “sannu, tun dazu nake jiranki kizo ki kai saqon nan amma kinje kinyi zamanki” tace “sorry Mamie gani yanzu na fito, bani in tafi” Mamie ta bata saqon a cikin wata baqar leda, Yasmeen tace “Mamie aramin motanki naje da ita” Mamie tace “me yaci taki motar” tace “Don Allah Mamie na” tace “jeki dauko kije ki kai” tace “nagode” taje ta dauko ta kama hanya taje inda aka aiketa
_____________________________
Junaid ya kira Maryam suka gaisa yace “ya ciwon kan” tace “Alhamdulillah naji sauqi” yace “MashaAllah, Allah ya qara sauqi” tace “Ameen, ya Ashraf” yace “Ashraf yana lafiya, yana wurin Ammah” tace “ina gaidasu” yace “zasuji InshaAllah” suka danyi hira daga nan sukayi sallama
Yana kashe wayar ya tashi ya shirya ya fita, yaje gidan kawun shi ya sanar mishi maganar Maryam, yaji dadi sosai yace “to zan sanar da sauran sai a saka lokaci muje gidansu yarinyar, zan sanar maka idan zamuje din” Junaid yace “nagode sosai kawu” sukayi sallama ya wuce
Daga nan ya tafi gidan Ammah, ya gaya mata yadda sukayi da kawu tace “to Allah ya nuna mana, Idan sunje ma banaso a saka lokacin da nisa” Junaid yace “Nima dai banaso a saka lokacin sosai saboda akwai tafiyar da zanyi, kafin nayi tafiyar nakeso ayi” Ammah tace “Allah ya tabbatar mana da Alkhairi” ya amsa da Ameen
_____________________________
Abie yana gama shiri zai fita yacewa Ammi “Yanzu daga nan zanje wurin Alhaji Abdullahi yasan abunda ake ciki” Ammi tace “to Allah ya tsare” ya amsa da Ameen
Yana hanya ya sanar mishi gashi zaizo, yana isa Alhaji Abdullahi da kanshi ya fito ya mishi iso, suka zauna mommy tace “bari a kawo maka abun tabawa” yace “Aa Alhamdulillah a qoshe nake” tace “to shikenan” ta wuce ciki
Abie yace “dama nazo ne akan batun Kamal da Bazla ne” daddy yace “to inajinka” Abie yace “gaya maka ne banyi ba, tun lokacin da aka fara maganar nan yarinyar nan ta nuna bataso, Nace mata tabbas sai anyi, bazan iya hanawa yaron wajenka auren ‘yata ba, shine ta bar gidan ba Wanda ya sani Ashe daura taje wurin Umma, Umma ta kirani tace tunda bata so a bar maganar, Nace mata shikenan” Daddy yace “amma kuwa baka kyauta min ba, tunda bataso ai sai a gayamishi ya haqura, ai ba wani abu bane gaskiya baka kyautamin ba” Abie dai baice komai ba daddy ya qara da cewa “ai da ka gayamin tun farko bata so meye a ciki, yanzu da ta tafi in da bataje daura din ba taje wani wurin ai kaga ba’aci riba ba, don haka zan sanar mishi ya bar maganar” Abie yace “Nagode Alhaji Abdullahi” sukayi sallama
Daddy ya kira Kamal ya sanar mishi, yace “kaje ka nemo wata yarinyar, wannan Allah yayi ba matar ka bace” Kamal ya kalli daddy har zaiyi magana kuma ya fasa, sai kawai yace “to daddy nagode” ya tashi ya fita bai koma part din shi ba ya ja motar shi ya bar gidan
________________________________
Yasmeen da taje gidan kawunta kai saqon bata bar gidan ba sai kusan 8:23pm, ta fito tana driving cikin natsuwa tazo wucewa wani layi, layin ba mutane sosaii sai ta hangi wani a tsaye sanye da face mask ya juya bayanshi, mutanen da ke zagaye dashi kuma kowanne da makami a jikinshi, gabanta yana ta faduwa tana Addu’a, tazo zata bi daidai inda fuskar mutumin ke kallo, shi kuma sai ya juya zaiyi magana da na bayanshi, ta wuce dai a ranta tana saqesaqe
________________________