KUSANCI PAGE 6
KUSANCI
NA
HAJ HABIBA ABUBAKAR IMAM
(Mrs Aliyu mayere)
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
......Page 6
A cikin hakane wata ranar Laraba wacce Bakil bazai taɓa mantawa da ita ba. Bayan tashin su da ga office Mustapha ya dubi Bakil, yace "mutumina yau fa ba da mota nazo office ba, ", yadan dube shi yace "me ya sami motar ta ka?", Mustapha yace "Ai tun jiya da muka tashi aiki, gareji na wuce na ba da ta a duba min saboda na ji duk ta canja, sai yanzu nake son na je garejin idan angama gyaran sai na dakko ta", Bakil yace "Ah to ai babu damuwa muje kawai na saukeka". Tare suka jera da Mustapha har inda ya aje motar tasa , daganan suka tafi.
Cikin rashin Sa'a sunje sun tadda ba'a gama gyaran motar ba, saboda abinda za'a canja babu sai an kawo zai kuma iya kaiwa gobe ko ma jibi. Suna komawa cikin mota kafin Bakil ya tada motar, Mustapha ya dube shi yace, "Gashi ina da uzurin da zanyi da mota da yammacin nan", Bakil ya dube shi yace "A'a to baga tawa motar ba, ai zaka iya yin amfani da ita, ina zaka je?". Ya ɗan yi murmushi yace "Ina son na je na dakko A'isha ne, a gidan abokin mahaifina, ta je duba matarsa ne da ba ta jindadi"
Bakil yasan A'isha domin ya sha raka Mustapha wajenta zance, domin ita Mustapha zai aura nan da watanni biyu masu zuwa. Bakil yace "Bakomai, muje mu dakkota mana mu Kaita gidan", Mustapha yace cikin fara'a gami da zolaya "kaga abokin rufin asiri, gaskiya Nagode", dariya kawai ya yi yaja motar suka tafi.
Tun da suka fara shiga unguwar, Mustapha ya fara magana yana nuna jerin gidajen dake bangaren hannunsa na hagu , "kaga duk gidajen nan na mutumin da za muje gidan sa ne yanzu, kudi gare shi sosai fa".Bakil yace "duka waɗannan rukunin gidajen kana nufin duk na shi ne", yace "Kwarai kuwa , Allah ya hore masa gaskiya, kuma Alhamdulillah ya na buda ma Alhajina sosai domin ya na samu a karkashinsa, ga taimako, in dai kana neman taimako kaje wajensa wahalarta ka haɗu da shi kawai, matarsa babbar aminiyar mahaifiyar A'isha ce, ina yawan kawo A'isha gidan, tunda tasan alakata da gidan yasa ko aikenta akayi gidan ni takan kira na kaita".
Bakil ya jinjina kai yace "Lalle wannan bawan Allah ya jidadi da duk da tarin dukiyar sa bai sa ya dauki bak'ar dabi'a ya sama kansa ba, gashi ya na samun kyakkyawar shaida tun a duniya", Mustapha yayi murmushi yace "sosai kuwa, gaskiya ya samu shaida, mutum ne me Dattaku, domin duk cikin abokan hulɗar mahaifina na fi jindadin zuwa gidansa,da kuma mu'amala da shi", ya muskuta ya zaro wayarsa yana faɗin "bana son takura maka , mun fito wajen aiki ya kamata na Barka ka huta, bari na kirata kawai ta fito waje mu dauketa mu wuce, ba sai mun shiga ba", kai kawai Bakil ya gyada ba tare da yace komai ba har Mustapha ya kira A'isha su ka gama magana, ya dube shi da sauri bayan ya aje wayar , yace "wancan katon gidan me farin get nanne gidan". Bakil ya rage wuta domin sun riga sun karaso kofar gidan, daga bisani yayi parking ɗin motar suka tsaya zaman jiran fitowar A'isha.
Ba su dade da tsayawa ba, A'isha ta fito daga get din gidan tare da yarinyar gidan. Yarinyar na sako kafa wajen gidan, Bakil ya ji gefen zuciyarsa ya fara bugawa irin bugawar da takan yi a duk lokacin da ya tuna yarinyar da ta zamo masa tamkar jarabawa. Ya kai hannu a hankali ya dafe gefen kirjinsa gami da lumshe idanunsa. Ya na jin wani irin rikicewar jiki, da azaftuwar ruhi,
Mustapha ya buɗe kofar motar ya fito cike da fara'a yana kallonsu yace "Jawaheer rakiya har kofar gida". Jawaheer ta yi murmushi tace "To tace ba zaka shigo ba kana sauri shi yasa nace bari na fito mu gaisa". A gaggauce Bakil ya buɗe idanunsa Yana waigen inda yaji Muryar tana fitowa, Mustapha ya yi murmushi yace "Aiko kin kyauta, ya jama'ar gidan? Dafatan Haj ta samu sauki, don ban so na shiga na gaisheta yanzu zata ce saboda A'isha na shigo", Jawaheer ta yi murmushi tace "Ai ta samu sauki sosai", Mustapha yace "In sha Allah zan zo takanas na gaisheta", tace "To Allah ya ba da iko",
Cikin zafin nama Bakil ya buɗe kofar motar ya fito , gaba ɗaya jin kafafunsa yayi sun kasa daukarsa da sauri ya dafa motar yana kokarin tsaida ganinsa akan jawaheer. A'isha na yi masa magana sam bai ma san abinda take cewa ba
Jawaheer ta tsaida idanunta akansa, bugun zuciyarta ya karu, shin waye take gani kamar mutumin da ya taimaka mata ya gyara mata mota?, Mutumin da ya jefata a wani mawuyacin hali wanda bata taɓa shiga irinsa ba, wanda tsawon lokacin da aka ɗauka da haduwarsa kusan kullum sai ta yi tunaninsa. Ta Matso suna kallon kallo, itace ta katse shirun nasu, da cewa "kamar na sanka", Mustapha ya waiga yana kallon Bakil, sai yanzu ya lura da halin da ya ke ciki, ya yi saurin riko hannunsa ya danna da karfi wanda hakanne ya dawo da Bakil cikin hayyacinsa.
A'isha tace "A'ina kika san shi, abokin Mustapha ne, wajen aikin su ɗaya", jawaheer ta ƙara cewa "Da gaske nake kamar mun taba haduwa da shi", tana saka kalmar kamar ne saboda bata son Bakil ya gane cewa ya samu wani matsayi a wajenta, yadda daga haduwa daya har zata gane shi.
Bakil ya ce cikin ƙoƙarin daidaita muryarsa , har yanzu hannunsa ɗaya na dafe da gefen zuciyarsa. "Ba kama bane , mun taba haduwa a lokacin da motarku ta samu matsala kin dawo daga makaranta". Jawaheer tasan hakan bata da buƙatar a tunatar da ita., tayi murmushi wanda gaba ɗaya ya ƙara narkar da zuciyar Bakil tace "kwarai hakane, na fa gode sosai da abinda kayi mana a ranar". Tuni Mustapha ya fahimci komai , zuciyarsa ta cika da farinciki matuka, ya jidadin yadda shine ya zama silar haduwar Bakil da jawaheer, ko ba komai a yau ya kawo karshen damuwar da Bakil yake cikin tsawon lokaci.
Bakil ya yi murmushi yace"haba babu komai ai, ya makaranta ?", Tace "Alhamdulillah ". Gaba dayansu sun tsaya sun ɗan taɓa hira, daga bisani Mustapha ya bukaci su tafi, ba don komai ba sai don yadda ya ga sam Bakil ya kasa samun sakewa ya kasa samun nutsuwa. Duk a gigice yake, duk hirar da suke yi bai iya cewa komai sai kallon Jawaheer kawai yake, duk motsin da take akan idonsa take yi.
Haka zalika har suka aje A'isha a gida, Bakil bai fahimci a wane hali yake ciki ba shi kansa.domin kuwa tun a kofar gidan su jawaheer Mustapha ya karbi tukin, bayan mota Bakil ya koma ya zauna , A'isha na gaba Mustapha na tuka motar har gidan su A'isha, Mustapha bai tsaya hira da A'isha ba suna ajeta ya ja motar suka tafi saboda ya kosa ya samu kebewa da Bakil domin tattauna al'amarin."
"jawaheer itace yarinyar da kake so ko?, Itace wacce kake addu'ar Allah ya haɗa ka da ita ko?" Tambayar da Mustapha yayi masa kenan. Ido jajir Bakil ya dago ya dube shi yace, "itace Mustapha, itace, yau ka taimake ni ka fitar da ni daga cikin kunci da tashin hankalin da nake ciki, Nagode Mustapha Nagode, don yau a dalilinka Allah ya haɗa ni da ita kaine sila".
Cike da jindadi Mustapha yace "Alhamdulillah , sai fatan Allah ya haɗa zuciyoyinku, duk da na lura da wani abu wanda kai ba ka lura da shi ba , don a lokacin sam na fahimci baka cikin hayyacinka", Bakil ya yi saurin cewa "me ka lura da shi, don Allah Mustapha?". Ya dan yi murmushi yace "na lura da irin kallon da jawaheer take maka tamkar itama tana cikin halin da kake ciki, idanunta sun kasa boye sakonnin da suke son isarwa", sosai Bakil ya ji wani irin dad'i ya bakunci zuciyarsa , ya shiga murmushi yana faɗin "Allah ya tabbatar da abinda ka faɗa Mustapha, yanzu ya za'ayi ba zan iya kara daukar wani lokaci ba, ba tare da na gabatar da kaina ga Jawaheer ba". Mustapha ya numfasa yace "ina ganin soyayya iri iri amma ban taɓa ganin irin taka soyayyar ba, don soyayyar jawaheer a zuciyarka ta zafafa kwarai , tabbas idan aka samu matsala ba zaka iya jurewa ba, don haka zanyi duk yadda zanyi domin ganin na kusanta ku". Bakil yace "nagode Mustapha ".
Mustapha ya ɗan dube shi yace "kuma kayi matukar Sa'a domin gidan Alh Nuraddeen canji basu da matsala, masu kuɗi ne na hakika amma basa wulakanta mutane musamman talaka kamar yadda na gaya maka dazu, zan iya rantse maka cewar babu wani mutum da Alh Nuraddeen canji yake mutuntawa sama da talaka , yana da karamci kwarai, ina tabbatar maka a irin kyakkyawan halayenka da nagartarka babu yadda za'a yi ya ki ka, kuma ita kanta jawaheer din bana zaton zaka samu damuwa ta ɓangaren ta". Bakil yace "Allah ya tabbatar da duk abinda ka faɗa, jin halayen mahaifanta ya ƙara min sonta da kaunarta kwarai, kai Mustapha ni fa bansan wane irin so nake ma jawaheer ba, zan iya jure komai saboda ita". Mustapha yace"Na tabbatar da hakan, in sha Allah kuma sai inda karfina ya ƙare akan soyayyar ku". Sosai Bakil ya yi ma Mustapha godiya.
Tun kafin Bakil ya aje Mustapha a gida , Mustaphan ya kira A'isha yace ta Turo masa number jawaheer Bakil ne ke buƙata, sai da ta gama zolayar Bakil da nuna masa tuni tasan ya fada soyayyar jawaheer tun daga lokacin da suke gaisawa, sannan dai daga bisani ta turawa Mustapha number shi kuma ya turama Bakil, sai da Mustapha ya sauka sannan Bakil ya amshi tukin zuwa gidansa ransa fari tas, zuciyarsa kamar gonar auduga, fatansa ɗaya Allah ya sa ya samu karɓuwa a wajen jawaheer.
Ilai kuwa addu'ar sa ta karbu domin lokacin da ya fara kiran ta a waya, ya gaya mata waye shi, ya yi mamakin yadda ta karɓe shi , sosai ta nuna masa mutunci da karamci, tun daga lokacin kuma da ya kirata zata ɗauka cikin mutunci. Yawan kiranta da ya ke yi nan da nan suka fara sabawa, idan ya yi jinkirin kiranta har damuwa take shiga, dole takansa idan ya yi jinkirin kira ita takan kira su gaisa.shakuwa sosai ta fara shiga tsakaninsu, wani lokacin kuma da A'isha suke kamun kafa su Kaita gidan su jawaheer don kawai Bakil ya samu kebewa da jawaheer, a dalilin hakan Bakil ya sha haduwa da Alh Nuraddeen canji, ya kuma tabbatar da abinda Mustapha ya gaya masa na karancim Alh Nuraddeen canji domin yadda yake karbar su, yake kuma sakin jiki da su, su yi hira. Abu daya kuma Bakil ya lura da shi, shine yadda Alh Nuraddeen canji ya ke nuna yana kaunarsa tun haduwarsu ta farko, shi kansa Bakil din aranar da ya fara haduwa da Alh Nuraddeen canji har cikin ransa ya ji wani irin son sa da girmamawa me yawa a ransa, lokaci ɗaya kuma fuskarsa yana matuƙar yi masa kama da wata fuska da ya rasa inda yasan fuskar, sai dai yasan duniya da fadi wani zai iya yi maka kama da wani.
Sai dai abu ɗaya ya sani zai kuma ba da shaida akai shine mutuncin Alh Nuraddeen canji ya wuce duk inda ake tsammani.
Sai da Bakil ya tabbatar ya gama gina kansa a wajen Jawaheer sannan ya gabatar da kansa a gareta a matsayin masoyi, bai yi mamakin yadda Jawaheer ta yi na'am da shi ba, ta aminta da soyayyar sa , gami da tabbatar masa da cewa bata taba yin soyayya ba, bata san yadda ake yi ba sai akansa. Wannan bayanin nata ya fi komai faranta ransa, ya ƙara budema jawaheer zuciyar sa domin yana jin duk duniya babu wani abu da yake so sama da jawaheer.
Bayan sun gama daidaitawa ne, Bakil ya ga muhimmancin ya je ya nemi izinin cigaba da neman ta a wajen mahaifinta, domin a kima da mutuncin Alh Nuraddeen canji yana ganin bai kamata ya cigaba da neman yarsa ba tare da ya sanar da shi ba. Mustapha ne yayi masa rakiya har wajen Alh Nuraddeen canji.
Duk da Alh Nuraddeen canji ya amshi maganar to bai hana shi jinjina lamarin ba, domin gyara zama ya yi ya dubi Bakil sosai yace "Tun ganina da kai na farko naji na aminta da kai da kuma tarbiyyar ka gami da nutsuwarka,yanzu kuma da ka zo min da wannan maganar sai na ji ina yi ma jawaheer sha'awar samunka a matsayin miji, duk da kwata kwata babu maganar auren jawaheer a yanzu, saboda ina da buri akan ta, ina kuma son burina ya cika kafin na aurar da ita".
Yadan ƙara gyara zamansa, sannan ya cigaba da cewa "Tun farko ina da burin a cikin yarana mata na sami wacce zata yi aikin asibiti musamman aikin jinya wato ( nurse), Allah bai cika min wannan burin ba a wajen ya ta ta farko ba, saboda wasu dalilai, shi yasa nake son na cika wannan burin nawa akan jawaheer, domin su ke nan min su biyu mata nake da su sai yayan Jawaheer na miji ɗaya yana India can yake karatu sai sauran yan'uwansu maza guda uku, don haka idan har jawaheer tana sonka ni zan baka aurenta,". Ya tsaida idanunsa akan Bakil wanda yake ganin asalin murna da jindadi a fuskarsa.
Ya jinjina kai ya cigaba da magana "Amma a bisa sharadi ɗaya ", Bakil ya yi sauri dago kai suka haɗa ido da Mustapha fuskarsa ta nuna alamun tsoro, Mustapha ya gyada masa kai alamar karfafa guiwa .
Alh Nuraddeen canji ya ce "Sharadin shine, bazan baka aurenta ba har sai ta kammala makaranta , ta zama cikakkiyar malamar jinya, kuma kada ka manta a yanzu jawaheer tana a ji biyar ne na babbar Sakandire, sai ta gama sannan ta gama school of nursing, alokacinne Zan iya yi mata aure, sannan kuma zan zauna da ita na tambaye ta idan itama ta aminta da kai shikenan ".
Ya dago yana kallonsa , sannan ya yi masa tambayar "kaji abinda nace , shin zaka iya zama ka jira ta,". Ba tare da wani dogon tunani ba Bakil yace"zan iya zama na jirata Abbu , ko da shekara dari ne balle shekara biyar, zan jirata ".
Alh Nuraddeen canji ya lumshe ido ya bude, karo da dama kenan da yaji Bakil ya ƙara mallakar duk wata yardar shi , ya dube shi sosai yace "Ni kuma nayi maka alkawarin zan aura maka jawaheer,ko da ace tsawon rayuwa zaisa ta canja ra'ayi babu wanda ya isa ya hana aurenku sai dai idan dayan ku ya bar gidan duniya, amma tabbas in dai nine na haifi jawaheer bata da wani miji bayan kai". Wannan magana ta Alh Nuruddeen canji ta fi komai faranta ran Bakil domin ji yayi kamar an jefa shi a cikin aljanna. Har wani mirgina kai yake yana cike da farinciki mara misaltuwa. Sosai ya dinga yi masa godiya Mustapha na taya shi. Mutuncin Alh Nuruddeen canji ya ƙara ƙaruwa a wajensa jinsa yake kamar shi ya kawo shi duniya. Ita kanta Jawaheer da Bakil yayi mata bayanin yadda su kayi da Alh Nuruddeen canji mamaki tayi sosai, domin tace ba ta taɓa tsammanin zai yarda ba, saboda kullum yana nuna mata muhimmanci karatunta, yana kuma nuna mata baya son ta fara yin soyayya don ba kowa bane zai iya jiranta har burinsa ya cika a kanta.
Wannan al'amarin shine asalin kara dankon soyayyar Jawaheer da Bakil, gami da cigaba da hulɗar zumunci da gidansu Jawaheer, ya dauki Haj zulaiha tamkar mama mahaifiyarsa, sau da yawa daga office gidansu yake wucewa yaje ya ci abinci, ya zama ɗan gida sosai. Domin ita kanta Haj zulaiha ta aminta da shi da duk halayensa, sosai take yi ma yarta fatan samun Bakil a matsayin mijin aurenta.
Bakil ya jima bai je Ɗandume ba, sai dai sako da yake turawa a kai akai na abinda za'a ci da sauran bukatun yau da kullum na can babban gidansu. Sosai yake jindadin zaman Kaduna saboda yana kusa da abinda yafi so.
Amma dole yasan akwai nauyin iyaye da yan'uwa a kansa da uwa uba kakarsa, duk da yana waya da ita, ta kuma san cewa ya hadu da Jawaheer, Amma duk da haka wannan juma'ar Ɗandume ya tattara ya wuce can yake son yayi hutun karshen makonsa, don haka ya gaya ma Jawaheer zai tafi Katsina ba zata gan shi ba sai bayan ya dawo.
Ranar juma'ar tun kafin su tashi aiki, Bakil ya wuce Ɗandume. Hankali kwance cikin daɗin rai da farinciki.Domin ji yake tamkar ya gama sam
un dukkan farincikin rayuwa.
Ku dakace ni
Daga taskar ✍️
Yar Gidan Imam