KUSANCI PAGE 7
KUSANCI
NA
HAJ HABIBA ABUBAKAR IMAM
(Mrs Aliyu mayere)
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
....... Page 7
Amma duk da haka bai isa ɗandume da wuri ba don sai gaf da magriba ya shiga Ɗandume, bayan motarsa cike yake da kayan abinci,zahiri Bakil dai danginsa sun yi dacen sa, domin dai wannan aikin gaba daya zuriar gidansu yake yi ma, don komai ya samu tun daga kan albashinsa zuwa dan kasuwancin da yake yi, duk akansu yake karewa bai da kyashin yi musu komai.
Domin yafi kowa sanin Babban gidansu yana bukatar taimako don haka duk karfin nemansa saboda su ne.kasancewar shi kaɗai ne acikin yan'uwansa Allah ya yi saurin daukakawa, shi kaɗai ne yafi karfin bukatunsa har kuma Yake yi musu nasu bukatun. Hakanne yasa Bakil ya zama tamkar kadara ne a wajen su.Domin duk a kanshi su ka dogara, ko kaɗan basa tausaya masa burinsu duk abinda suke so ya yi musu, babu tunanin ya na takura ko baya takura, Don kuwa yanayin yadda yake yi musu hidima yasa su ke yi masa kallon wani hamshakin mai kuɗi ne, su na gadara da fariya da shi, basu san zuciya ce kawai yake da ita ba, domin yadda suke kallonsa bai kai haka ba.
Duka kayan abincin da ya zo da su dakin Dada Laure aka sauke su. Bai kuma samu damar zama ba har sai da aka idar da sallar magriba, sannan ya fito, bai tsaya sasan Dada ba gudun faɗan mahaifiyarsa , kai tsaye sasan Mama ya wuce,
A kusa da ita ya zauna yana ƙoƙarin gaisheta, ta amsa cike da murnar ganinsa, domin ya jima bai zo ba sai dai waya, da kuma sako da yake turawa.
ta ƙare masa kallo, cikin yanayi na canja fuska tace "wane kaya ne akace an sauke a sasan Dada". Ya dan yi jim!, Sannan ya amsa, "Dama kayan abincin da na taho muku da su ne aka sauke acan", nan da nan fuskarta ta canja ta ƙara zuba masa ido tace , "Wai Bakil me ka ɗauke ni ne?", Cikin rashin fahimtar tambayar yace "Mama ban fahimci tambayar ba," ta ɗan sakar masa harara , sannan ta gyara zamanta tace "kawai ina mamakin yadda ka ke fifita Dada akan ni uwar da ta haifeka ne, kana bata muhimmanci fiye da yadda kake ba ni, na yi zaton zuwa yanzu zaka bani dukkan hakkina dake kanka tunda ka mallaki hankalin ka fiye da da, kasan abinda kake yi , don ba don ka ki ba da tuni ka aje ya'ya, amma har yanzu kana rage min matsayina". Bakil ya kasa cewa komai, har ta cigaba da cewa " nayi zaton duk abinda ka zo da shi , nan dakin nawa za'a kawo saboda ni ce Yakamata ace ina rabawa kowa a gidan , hakanne zai ƙara sawa su san muhimmancina , su kuma san matsayi na ya wuce inda suke tsammani". Kan Bakil ya yi masa nauyi, wannan dabi'ar ta Mama tana matukar tayar masa da hankali, son gadara da son fariyarta baya so, ya lura Kwarai, tunda ya taso ya fara kula da gidan tun kafin ya fara aiki, ɗan kasuwancin da yake yi, da shi yake taimakawa gidan, tun awannan lokacin ya fahimci Mama tayi matuƙar canjawa tana nuna ita wata ce, ko ga abokiyar zamanta Anti Amarya ta dinga cin mutuncin ta kenan a duk lokacin da ya sayi abu aka raba da ita ta dinga yi mata habaici kenan , sam ba ya jindadin hakan duk da Alh Bello Malami yana tsawata mata , amma kwata kwata ta ƙi canjawa.
Yanzu kuma bayan samun aikinsa ya fahimci kusan gaba ɗaya matan gidan wata irin sabuwar biyayya su ke yi mata .........."Agaskiya bazan yarda da wannan ba, duk abinda ka zo da shi ka kawo shi dakina ni zan raba", maganar da ta cigaba da yi ya katse masa tunaninsa, ya dubeta a sanyaye, baya son jan maganar yadda har Alh Bello Malami zai shigo ya riski maganar, don haka kawai ce mata ya yi "To shikenan In sha Allah zan ringa yin hakan, dama naga saboda Dada itace shugabar gidan shi yasa na zaɓi yin hakan , amma tunda ba kya so an bari". Kawai sai cewa tayi "shugabar gida ai nice, tunda ɗana shine yake kawo shinkafar da za'a ci, shi yake ɗaukar dawainiyar gidan, idan Dada na son ta zama shugabar gida ai sai ƴaƴanta su dinga ciyar da gidan gami da daukar nauyin bukatunsu",
gaba ɗaya Bakil bai jidadin maganar ta ba, zaiyi magana kenan Alh Bello Malami ya shigo, nan ya zube ya ƙara gaishe shi bayan gaisuwar da suka yi a kofar gida.
Ya zauna yana fadin "Ai na ɗauka kana sasan Dada ne , daga can na fito ashe kana nan, sai buhunan shinkafa da sauran kaya dana gani, Bakil wannan aika takura ma motarka sosai, kayan sunyi mata yawa". Yayi murmushi yace "Gaskiya kam ta takura sosai tayi ƙasa, dai dai inda zan wuce ba tayi guga ba" Alh Bello Malami yace "To ai Alhamdulillah tunda an iso lafiya,", ya zauna ya na faɗin "mun gode da dawainiya sosai Allah ya yi maka albarka, Bakil ka cika dan kwarai abin alfaharin ko wane iyaye", sai alokacin Mama tace "Allah ya yi maka albarka", ta dubi Alh Bello tace "Ai nayi tsammanin ma nan za'a shigo da kayan ", ya dubeta yace "da nan da wajen Dadan ai duk ɗaya ne, can nema yafi dacewa akai", addu'a Bakil yake yi sosai aransa, Allah yasa kada mama ta ƙara cewa komai. Addu'ar sa dai ta karbu domin bata kara magana ba. Dai dai lokacin Anti Amarya ta shigo ɗauke da kular abinci, cike da fara'a ta dubi Bakil tace "A bar hirar nan, ga abinci nan ka ci, kasha hanya", Bakil yana yi da Anti Amarya yana ganin girmanta, don macece me hakuri kuma me shanye duk wani batanci da mahaifiyarsa zata yi mata, don
ba don hakurin ta ba tabbas da kullum an kwashi yan kallo tsakaninta da Mama,
Cikin fara'a ya miƙa hannu ya amshi kular , yana cewa "Wa zai ki girkin Anti Amarya me dad'i, shi yasa wancan zuwan nawa, duk naji ba dad'i har na koma baki dawo ba, ya me jikin to", Anti Amarya bata damu da hararar da Mama take zuba musu ba daga ita har Bakil din, tace "Ni ma sai bayan da na dawo ake gaya min ka zo har ka koma, jikin kawu da sauki amma dai ana jin jiki, ga karfi duk ya kare Allah dai ya rufa mana asiri", ya jinjina kai yace "Allah ya bashi lafiya", da ita da Alh Bello Malami suka haɗa baki da "Amin Amin", Daga nan ta juya ta fita cikin rashin damuwa da kunkunin da Mama take yi don idan da sabo ta riga ta saba da halin Haj Hadeeza.
Duk zaman ya gunduri Bakil domin yadda Mama take ta watsa masa harara tun bayan fitar Anti Amarya, don haka ya mike da kular abincin sa ya dubi mahaifinsa yace "Alh ina sasan Dada". Nanne Mama ta dube shi tace "kada ayi kasafin kayan abincin nan sai na shigo", ya ɗan dubeta sannan yace "Toh", Alh Bello Malami ya dubeta yace "meye damuwarki da yin kasafin abinci, ina ruwanki, da zaki ce sai kin zo za'a yi Kasafi ki cire hankalin ki akan nan wajen don ba hurumin ki ba ne".
Zata yi magana kenan, maganar da ta ji sajeeda na yi daga waje ta katse ta , "yaya Bakil ina can sasan Dada inata jiranka, ka zo mu gaisa, Dada tace itama baka dawo ba tunda ka fita har yanzu "
Bakil ya ɗan yi murmushi yace "Ban koma ba , amma yanzu can zani ", tayi saurin amsar kular hannunsa tace "kawo na rike maka", ya sakar mata kular, lokaci ɗaya suka jera tare suka tafi.mama ta numfasa tace tana dawo da kallonta kan Alh Bello Malami ta na faɗin "Allah dai ya ƙara haɗa kan yaran nan", Alh Bello Malami yace "Amin, dalilin jinkirtawar mu kenan na sanar da shi abinda mu ka yanke, saboda mu na son su sami fahimtar juna a tsakanin su", ta ƙara kallonsa tace "Amma dai zaku yi masa magana kafin komawarsa, saboda wannan zaman ya isa, Bakil bai isa ya ƙara wata bakwai nan gaba ba tare da yayi aure ba, wannan sakarcin da yake yi ya isa haka, an ririta shi, anyi lallashi, anyi nasihar duk don ya fito da matar aure amma ya ki, to wannan karon tsaye tsaye za kayi masa ka runtse idonka ka tabbatar masa da cewa babu wani sauran lokaci da za'a ƙara ba shi , haka ya isa". Alh Bello Malami yace "lalle mun riga mun gama magana da su saluhu wannan karon dole Bakil ya karbi abinda muka zo masa da shi", tace "kwarai kuwa, me yake nema wanda bai samu ba,da zai zauna gotai gotai da tarin shekaru a kansa amma yaƙi aure,ko har akwai wata kamala da yake nema ne da ta wuce na ya yi aure".
Alh Bello Malami yace " komai ya zo karshe in sha Allah, domin ina da yakinin cewa babu abinda za mu kawo ma Bakil yasa kafa ya shure", ta juyar da kai gefe tace "shurewa kuwa na nawa?, da ace ya bi abinda ku ka zo masa da shi ɗin ai da tuni ya na nan da yan ya'yan sa a gabansa, amma a zauna ayi ta magana ɗaya". Alh Bello Malami ya jinjina kai yace "uzuri mu ke masa, yanzu kuma duk mun gama yi masa ko wane irin uzuri, ya zama dole ya amince da bukatar mu matuƙar ya na son zaman lafiya da mu".
Cikin jindadin maganarsa tace "Ato, abinda Yakamata kenan". haka suka ci-gaba da tattauna maganar a tsakaninsu.
Acan sasan Dada ma, Dada haka take bin Bakil da sajeeda da kallo tana jinjina abinda zai iya biyo baya, tasan tabbas wannan karon mawuyacin abu ne idan Bakil zai yi musu biyayya, domin tafi kowa sanin wacece Bakil yake so, kuma da irin yanayin soyayyar da yake mata wanda ita kanta sau tari abun yana bata tsoro, a duk sanda ta tuna ba lalle bane Bakil ya auri zabinsa takan ji zuciyarta ta yi mata nauyi, tsoro kuma ya lullube ta, domin tabbas tasan Bakil bazai juri rashin yarinyar ba, to ina mafita?. Ga son rai na damun ta , ga tunanin halin da Bakil zai iya shiga idan su ka ce zasu tankwara shi dole ya yi mu su abinda su ke so.
Amma tunaninta da ita da ƴaƴanta na na rashin son Bakil ya auri bare da zata zo ta ci arzikinsa, kila ma har ta nemi raba su da shi, shi ne dalilin da yasa su ka yanke shawarar haɗa aurensa da sajeeda. Domin a wannan rayuwar da suke ciki Bakil shi ne gatansu, shi ne sanyin idaniyarsu, don haka dole su dinga yin taka tsantsan da duk abinda ya shafe shi.
Sosai Bakil ya so sajeeda ta barsu shi da Dada don yana son ya yi mata bayanin halin da ake ciki agame da Jawaheer da irin dattakon da mahaifinta ya yi masa. Domin ya zabi kada ya gaya mata a waya sai ya zo shi da ita tukuna, domin yasan ya na da aiki a gabansa , ya kwana da sanin mawuyacin abu ne iyayensa shi, su amince da sharadin Alh Nuraddeen canji, a yadda suke uzzura masa akan yayi aure tun ba yau ba, daker su yarda tsawon shekaru biyar sannan ya yi aure.
Dadar ce yake ganin zai iya kama kafa da ita ta goya masa baya, A duk lokacin da ya bijiro masu da maganar. To ga sajeeda ta ki matsawa ko'ina sai aikin hira su ke wani yasa baki wani Dada tasa baki, duk ya kosa ta tafi, ga gajiya na damunsa, bacci yake ji sosai . Kiri kiri dai sajeeda taki tafiya, ita kanta Dada ta lura akwai abinda Bakil yake son tattaunawa da ita, idanunsa sun nuna hakan .
A dole haka Bakil ya tashi yayi sallama da Dada ya fice zuwa makwancinsa. Yana tafiya itama sajeeda ta tashi tayi mata sai da safe, ta dubeta tace "eh kya tafi mana tunda wanda kika zo domin sa ya tafi", tare murmushi sai kuma ta dawo ta zauna kusa da ita, tace "Dada, kinfi kowa sanin yaya Bakil, don Allah ki gaya min Kinga alamar shi ma ya na so na kamar yadda nake sonsa", Dada ta muskuta tace "To ni ina zan sani, tunda ba zuciyarsa zan iya shiga ba amma ni nasan Bakil bazai taba kin ki ba , tunda ke yar'uwarsa ce jininsa ce", ta danyi rau rau da idanu tace " Ni ai kinji matsalar sam bana son ya so ni don ni yar'uwarsa ce,nafi son ya so ni don yana so na kawai". Dada tace "Allah ya zabi abinda yafi alheri a tsakaninku kinji, sajeeda aini idan hakan ya kasance sai nafi kowa farinciki" , sajeeda ta saki dariya ta tashi da sauri zata fita tace "dawo ki tafi ma da Naja kularta", sajeeda ta kara kallon kular tace "dama kular Anti Amarya ce?", Ta gyada kai tace "kular tace mana, tafi mata dashi ki bata sai ki wuce sasan ku, ban son na kwana da wanke wanke a daki". Sai da sajeeda tayi jim! Tana tunanin yadda zata kaima Anti Amarya kularta tayi mata magana kuma ba tare da ummanta ta gane ba, tunda ta hana su kula Anti Amarya da shiga duk wata sabgarta..... "Ki ɗauka ki tafi mana tsayuwar me kike", Dada ta katse mata tunaninta, dole ta durkusa ta dauka ta fita. Cikin sanda ta tsaya a kofar dakin Anti Amarya tayi sallama, cikin Sa'a nan da nan ta amsa gami da fitowa , ta dan yi jim tana mamakin ganinta don tana jin rabon da sajeeda ta yi mata magana ta manta, yau din ma tana mika mata kular ta juya da sauri ta tafi ba tare da tace mata uffan ba. Anti Amarya ta bita da kallo har ta bacema ganinta, ta numfasa a zahiri idan tace bata cikin damuwa akan wannan bakin zaman da take yi a gidan nan to tayi karya, tana jin labarin kishin bal bal amma bata taba ganin irin wanda suke yi a cikin gidan ba, tana da ilimi tasan abinda ta keyi shi yasa take jinta tamkar tsirara, in da tana da halin canjawa, da ta canja abubuwa da yawa a cikin gidan, cikin sanyin jiki ta koma cikin daki.
Sajeeda na shiga falonsu, Haj Aseeya ta jawota kusa da ita cike da fara'a tace, " Har kun gama hirar?", Ta gyada kai tace "eh, ya tafi ya kwanta shi yasa ni ma na dawo". Ta tsareta da ido sosai tace, "To yaya kike ganin abubuwan", ta ɗan muskuta tace "Umma, ni har yanzu ban fahimci komai ba, a game da abinda yake ji a game da ni", tace "kuma duk abinda nace ki dinga yi kina yi masa", tace "sosai ma, ni dai bansan me yasa ba, ko da yake kinsan yaya Bakil da miskilanci, ba lalle bane ya buɗe min abinda ke cikin zuciyarsa ba lokaci ɗaya, amma koma dai menene tunda aka lasa min zuma a baki a game da aurena da yaya Bakil, to zan iya jira na kuma jure komai har zuwa lokacin da shi ma zai buɗe min asirin zuciyarsa "
Haj Aseeya ta ɗan aje numfashi sannan tace "koma dai menene gobe za'a gaya masa komai, na kuma yi imanin Bakil bai isa ya bijirewa maganar babanninsa ba, da uwa uba na mahaifiyarsa, don kinfi kowa sanin kusancina da ita yasa itama take matukar son ayi wannan haɗin , kamar yadda bani da burin da ya wuce aurenku da Bakil, saboda ni ma na dama kamar yadda Haj Hadeeza ke damawa, kamar yadda kika fi kowa sanin a yanzu Bakil shine fitilar gidan nan", sajeeda ta numfasa tace "Ni kuma umma duk bana kallon wannan, hakanan nake son yaya Bakil har cikin zuciyata, ina jin ko baida komai zan iya aurensa, balle ya fi karfin bukatunsa yana da rufin asirinsa, shi yasa tunda Abba ya gabatar min da wannan maganar na rabu da duk tarkacen samarina, " Haj Aseeya ta jinjina kai tace "Ba zaki gane komai ba yanzu sai zuwa gaba bayan kunyi aure, zaki gane aurensa wata garkuwa ce a gare ki, za kuma ki gane hujjojina da na gaya Miki yanzu gaskiya ne, don tabbas aurenku zaisa yadda ya zama ɗan lelen kowa a gidan nan , kema ki zama yar lele abin son kowa". Ta ƙara kallonta ta cigaba da cewa "waɗannan tarkacen samarin na ki kuma meye ranar su, ba su aje ba ba su ba wani ajiya ba, me suka taɓa tsinana miki idan ba shegen zuwa hira ba, babu mai iya miki kyautar kirki, ai ko babu maganar Bakil dama duk cikin su banga mijin aurenki ba, Bakil kuwa ki na ganin irin hidimar da yake yi tun kafin soyayyar taku ma ta ginu ina kuma ga soyayyar ta tabbata zuwa aurenku bansan nawa zamu samu daga baitul malinsa ba". Sosai sajeeda ke ɗaukar duk maganganun da mahaifiyarta take mata.
Haka Haj Aseeya tayi ta kawo ma sajeeda misalai har sai data gamsu aurenta da Bakil shi ne kaɗai rufin asirinta, ta kuma ji aranta zata iya yin komai don ta mallake shi .
Washegari a dakin Dada Laure Bakil ya karya, nan ma ya so yin magana da ita, amma yadda jama'a ke ta aiken kiransa yasa dole ya tashi ya tafi domin jin kokensu. Ko da ya fita kuwa da yawansu neman taimako su keyi, wanda yake da rabo ya samu, sai da ya gama sallamar mutanen lokaci daya wayarsa ta shiga kara , yana dubawa yaga kiran mahaifinsa ne, da sauri ya dauka, Alh Bello Malami yace "wai ina ka tafi ne, duk gamu a falon Dada muna son yin magana da kai", yace "ina nan wajen jama'a ne a waje , gani nan zuwa", yace "Aah ka tsaya ka gama da su tukuna sannan sai ka shigo", yace "Ai na gama da su, dama ina hanyar shigowa gidan ne", yace "to sai ka karaso din". Yana aje wayar ya kara sauri domin isa sasan Dada, domin kuwa baisan wace magana suke son su yi da shi ba.
Cikin sallama ya shiga falon Dada,inda Alh Bello Malami, Alh saluhu Malami da Alh Nasiru Malami ke zaune dukkan su akan kujera, gefensa kayan abincin da ya zo da shine da alama har sun gama rabo, kowa fuska cike da fara'a. Yana zauna wa kusa da Dada, babu girman kai babu komai duk suka yi ta masa godiya, gami da sa masa albarka, tare da nuna jindadin wannan halin nasa, wanda tun yana samun kuɗi kadan daga yar sana'ar da yake yi na wayoyi yake dawainiya da su, yanzu kuma daga fara aikin sa, su kansu ba zasu iya lissafa irin hidimar da yake musu ba, tunda ko bai zo ba sakonsa na kuɗi na tafe ko yaushe. Basu da abinda zasu ce da shi sai godiya tare da shi albarka.
Bayan duk sun gama yi masa godiyar ne, sannan Alh Bello Malami ya dube shi sosai yace , "Akwai maganar da muke son muyi da kaine Bakil". Ya dago yace cikin natsuwa "To Alh ina jinku, Allah yasa ba wani lefin nayi ba", Alh saluhu Malami ya girgiza kai yace "Ko ɗaya babu laifin da kayi, illa dai maganar da muke ta fama da kai,shekara da shekaru da kaki maida hankali akai, itace muka ga ya dace mu kawo karshen ta a yau, wato maganar aurenka", sai alokacin ya ji ya samu nutsuwa, domin kuwa yana da amsar da zai iya basu yau. Alh Nasiru Malami ya muskuta yace "Shekarunka sun fara ja Bakil, bugu da ƙari babu abinda baka da shi, domin dai akalla a yanzu nasan ba mata ɗaya ba ko mata huɗu ne zaka iya rikewa, tunda ka iya rike mana wannan bataliyar gidan, don haka ni banga dalilin da zaisa ka zauna babu aure ba, wannan sai a fara maka zargi duk da nagartar ka, domin dai shi aure daraja ne da shi",
Yana aje numfashi Alh Bello Malami ya amshe, "To mun gaji mun kai makura, don haka mun zauna mun tattauna mun kuma yanke shawarar haɗa ku aure kai da sajeeda". Gaban Bakil ya yi mummunan faduwa ya waigo ya dubi Dada wacce itama idonta ke kansa nan da nan idanunsa suka kada su kayi jawur, Alh Bello Malami yace "Ba shawara muke baka ba, ba kuma gaya maka muke ba, umarni ne muke baka".
Dada Laure ta shiga gyara zama,domin dai irin kallon da Bakil yake mata kallo ne me cike da tuhuma, ita kanta tasan a yau dai son kan su ya yi yawa, cikin ƙasa da murya tace "To ai sai ku ba shi dama, aji ta bakinsa", Alh Bello Malami yace "Haba Dada wace irin dama za'a bashi, maganar nan fa har da ke mu ka zauna mu ka tattauna mu ka yanke shawarar hakan, kin kuma san cewa maganace ta babu cewa a'a", ta girgiza kai tace "Duk da haka dai a bashi damarsa", Alh saluhu Malami yace "eh, yaya ya kamata aji abinda ke bakinsa". Alh Nasiru ya dube shi yace "Bakil muna sauraronka, me kace a game da wannan maganar*.
Bakil ya muskuta daker saboda nauyin da jikinsa ya yi domin bai taɓa zaton Dada zata yarda da wannan maganar ba bayan ita kaɗai ce tasan tsakanin sa da Jawaheer.
ya fara magana cikin wata irin murya, "Naji abinda ku kace, amma a gaskiya Alh ina da yarinyar da nake son na aura, har gidansu sun san maganar, bana son na zama daga cikin mayaudara, bayan haka kuma ina son ta matuƙar so, bana jin zan iya auren wata mace idan ba ita ba, saboda haka don Allah ku janye maganar nan". Alh Bello Malami ya fiddo idanu waje cike da fusata yace"Anki abar maganar, mun riga mun gama magana sajeeda zaka aura, domin babu yadda za'ayi mu bari ka auri wacce zata raba mu da kai, duk wannan abin alherin da kake mana ta hanaka yi, Gara ka auri yar'uwarka wacce zata ƙara kusanta mu da kai , wacce ba zata hanaka yi mana alheri ba",a gaggauce yace "itama wannan din babu abinda zata hana nayi muku, domin ba tarbiyyar gidansu bace, kuma bata neman komai a hannuna balle ta hana nayi muku don ita nayi mata, domin mahaifinta yana da kuɗi matuka, yadda ba ma zata kalli nawa kuɗin ba", Alh Nasiru Malami yace "Duk da haka mu munfi sha'awar ka auri yar'uwarka, don zamu fi samun nutsuwa", Alh saluhu Malami ya ɗan gyada kai yace "Ni ina ganin bai kamata muyi masa dole ba, idan baya son sajeeda yana kuma da wacce yake so, to abar shi ya aureta, a wane garin take?", Ya juya yana tambayar sa, yayi saurin cewa "Anan Kadunan take , anan muka haɗu", Alh Bello Malami ya dube su a fusace yace "meye na yi masa wannan tambayar, bayan ba yarda da auren za muyi ba, mu ga zabin da muka yi masa nan", Dada ta shiga rudu akan irin kallon da Bakil yake yi mata kallo ne me nuna alamun yana neman taimakon ta a wannan gaɓar Don haka ta dawo da kallonta ga ƴaƴanta, ta daure domin sosai take son ta wanke kanta a wajen Bakil, ta na son ko na Karya ne ta nuna tana goyon bayansa, tace "Kada kuce za kuyi masa dole, ku barshi ya auri wacce yake so, domin gujewa danasani, kada kuzo ku haɗa abinda zai dameku,ya damu kowa nan gaba, idan akwai rabon auren a tsakaninsu ai sai ya aureta a ta biyu, ba namiji bane", ta karasa magana ta na kallon idanun Bakil , Alh Nasiru Malami yace "Hakane Dada, kada mu takura masa, muji wacece yake so ɗin idan ya so sai aje a aje magana ayi auren don Bama son bakil ya wuce watanni biyar masu zuwa ba tare da yayi aure ba".
Nan fa gaban Bakil ya yi mummunan faduwa, wata biyar?, Shi da yake son ya yi jiran shekaru biyar, suma ɗin a kintacensa ne .
Alh Bello Malami dai ya haɗe rai , tunda anfi karfinsa, bayan sun gama magana kowa ya yarda amma ganin idanun Bakil kowa ya na son ya janye jikinsa,don kawai ka da su yi laifi a wajen Bakil ɗin .
Dada ce ta dubi Bakil tace "ka natsu kayi musu bayanin yarinyar, idan ya so sai a aje ranar da zasu je nema maka auren, kayi dai kayi auren nan kowa ya huta ya samu nutsuwa, idan ya so sajeeda sai tayi hakuri ta shiga a ta biyu".
Tsoron furta abinda dole sai ya furta Bakil yake yi, amma babu yadda zaiyi dole sai ya faɗa. Ya gyara zamansa yace "yarinyar da nake son na aura ba zai yuwu na aureta nan da watanni biyar ba?". "Saboda me?", Gaba ɗaya suka haɗa baki suka tambaya banda Alh Bello Malami.
Bakil yayi ƙasa da murya sosai yace "saboda mahaifinta ya tabbatar min da cewa ba zai yi mata aure ba sai ta kammala karatun gaba da Sakandire, shi ne a kintace na na ke hasashen sai nan da shekaru biyar, domin kuwa yanzu ko Sakandire bata gama ba, amma ya tabbatar min da cewa in dai zan iya zaman jiranta to ba ta da miji sai ni......."?.
Alh Bello Malami ya katse shi da ƙarfin murya yace "kaji maganar banza, maganar da babu hankali aciki, ka zauna ka jira yarinya har shekara biyar, saboda baka san muhimmancin lokaci ba acikin rayuwa, ka jirata shekara biyar shi ma shekara biyar ɗin a tunanin ka ne, kenan ya na ma iya fin shekara biyar ɗin kenan, lokacin shekarun ka nawa kenan a duniya?, Ka tsufa kenan",
Dada ta dube shi da sauri itama cikin canjawar fuska tace "Me kake faɗa Bakil, ai ni bansan wannan maganar ba, ta yaya zaka zauna zaman jiran shekara biyar sai kace ita kadaice mace a duniya, haba haba shekara biyar ai ba kwana biyar ba ne, a shekarunka kai yanzu ko jiran shekara ɗaya zaka iya yi ma mace ne balle wannan tarin shekaru tsababa haka". Bakil Ya juyo yasa mata ido yana neman sassauci daga gareta, ta girgiza kai tace "A'a daina min wannan kallon yau duk soyayyar da nake yi maka bazan iya goya maka baya ba, don cutar da kanka zaka yi, ni kuma duk abinda zai cutar da kai bana kaunarsa". Alh Nasiru Malami cike da mamakin Bakil yace "Aini nama rasa bakin magana, kaina ya daure kwarai, yadda duk girman ka duk wayonka ka kasa gane kora da hali gidan su yarinyar suke yi maka", Alh Saluhu Malami yace "Kwarai kuwa kawai su ce ba zasu baka auren yarsu bane, suka ki faɗa suke son su cigaba da wahalar da kai".
Alh Bello Malami yace "Aini bansan baka da wayau ba sai yau, shashancin banza da wofi, garama kabar wannan maganar tun muna shaida juna, su je su samu wani bawan ba kai ba". Duk rigar Bakil sai da ta jike da zufa, tuni ya dafe gefen kirjinsa inda zuciyarsa keta bugawa, kansa ya shiga sarawa, tabbas dama yasan sai ya samu matsala da iyayensa akan wannan maganar.
Ku dakace ni
Daga taskar ✍️
Yar Gidan Imam