2
by @mommuhseen
🅿️........2
"Yallab'ai kamar yadda kaji d'in dai hakan ce zata kasance Insha Allahu, zan baka mamaki kuma zan fitar dakai kunya, zan yi maka abunda kowa yake ganin bazai yuwu ba to ni zan sa ya yuwun kuma ya tabbata, Ai *ABU ZAYYAD* ba aljani bane kuma ba mala'ika bane, ba da har kowa xai kasa daukar case d'in sa, idan na kintata daidai mutum biyar ana ba wannan case d'in suna gazawa su dawo ba tare da abunda ake so ba, ban dauki hakan a komi ba face gazawa da sakaci da rashin d'aukar aikin su da muhimmanci, yallab'ai ba kuranta kaina nake ba ina mai tabbatar maka ni zan cika wannan aikin da kowa ya kasa, kowa yake tsoron sa"
Duk wad'anda suke cikin office din kallon sa suke, kasancewar duk manyan sa ne zaune ana son tantance wanda za'a sake d'orawa bisa wannan case mai rikitarwa, ana cikin maganar ne ya shigo don ganawa da ubangidan sa anan ya tsinto maganar data kawo sa, shine yake ganin shi zai iya.
" *ISHAQ* ba irin k'ananun case d'in da ka saba warware wa ne cikin yan kwana ki ba, karka raina wannan aikin kar kuma kaga kamar dai-dai yake da sauran aikin da ake baka, wannan criminal case ne wanda shekara goma an kasa kama mai laifin, saboda babu hujjoji babu evidence d'in da zamu kafa mu kama shi dasu, ta ko ina babu wata hanya wata uku kenan da isah ya dawo da case d'in ya kasa, kafin shi dawud ba irin wahalar da bai sha ba karshe saida yai jinyar wata shidda saboda had'arin daya samu, kuma bai samu komi ba kafin dawud da Isah akwai mutum uku duk sun kasa taya kake tunanin kaida kazo jiya-jiya zaka iya wannan aikin, I'm sorry ba raina k'ok'arin ka nayi ba Ishaq, ina ganin gangancin kane kawai, da kuma wasa da rayuwar ka kai bak'one da aikin nan akan wad'anda muke saka ran zasu iya aikin.
dududu baka wuce shekara hud'u da fara aikin nan akan dai masu shekara goma ko sama da haka kai karami ne ina ganin kayi hakuri kawai"
Runtse idon sa yayi da ya gama jin dogon sharhin ogan nashi, wanda duk ciki baiji kwak'k'waran hujjan da zata hana abashi wannan aikin ba, d'aya daga cikin manyan da ake tattaunawar dashi yace, "Ishaq kayi hakuri idan hali ya bada zamu sake neman ka akan hakan, tunda har ka nuna kana so kuma zaka iya ai wannan duk mai sauk'i ne, zamu fara tuntub'ar wad'anda muke ganin zasu iya d'in komi kenan zamu had'u da kai"
Lumshe idonsa yayi sannan cikin girmamawa yai musu sallama ya fita daga cikin dakin taron da suke meeting din, nashi office din ya nufa ransa duk a b'ace ba kwad'ayin kud'in da zai samu yake yi ba, yana son ya zama abun alfaharin su na cewar an kawo karshen wannan tantirin mutumen daya hana ma kowa zaman lafiya, tattara kayayyakin sa yake don daman ya tashi tafiyar ce bai ba sai yanzu.
**********
"What's wrong with u jelly?"
Sake lumewa nayi cikin kujerar ina lumshe idona abubuwa biyu ne suka saka ni shiga wannan yana yin, na farko na gaji sosai zaman class ba karamin gajiyar dani yake ba awannin sunyi tsawo amman ban isa na furta ba yayah baya wasa da harkar karatuna, ni kuma gani ba wani son shi nake ba inayi ne kawai don fari cikin sa, na biyu kuma wani uncle d'inmu dayai mugun takura ma rayuwata da kallo, yana shiga sabgata duk sadda zai magana sunana ne bakin sa kamar shi ya rad'a mun shi, raina yana b'aci bana son irin haka...............jelly ba magana nake miki ba"
Firgigi na d'ago ina kallon sa da lulu eye's d'ina tubarkalla kamar kwai gasu farare, gyara zamana nayi sanyin AC motar na ratsani na ya mutsa fuska kad'an ina kallon sa, fuskar nan had'e ba walwala na daina kallon sa ina kallon glass din tagar motar muna ta wuce unguwanni don zuwa gida nace masa cikin muryar gajiya, "Yayah I'm very tired"
D'an huci ya fesar sannan yace, "what next?"
Jujjuya kai nake ina yamutsa fuska nace, "Yayah pls karka ce zaka dauki zafi abun bai wani tsananta ba, kawai damu na yake da kallo kuma yaita ambato sunana inyana lesson"
Fuskar nan ta sake murtikewa kamar zai maran cikin fad'a yace, "ban gaya miki duk d'an iskan daya fara matsa miki kigaya mun tun ranar farko ba? Ban gaya miki ba jelly?"
Soke kai nayi k'asa ina kwab'e fuska ina jan yatsuna nace, "duka duka fa yayah ba awuce sati daya fara haka ba kamar fa so yake yace yana so..............Aa ba haka bane"
Na canza maganar saboda yadda naga ya zazzaro mun idanun sa masha Allah kamar zasu fad'o, don ma bai tab'a duka na ba da ba shakka zai iya kai mun duka ahalin da yake ciki, kunnena ya kama cikin gargad'i da kashedi yace, "koda wasa naji wani labarin *SO* bakin ki saina k'ona bakin, understand?"
Da sauri nake d'aga kaina sannan ya saki kunnen yace, "ya sunan sa?"
Ina in ina nace, "yayah.........don.....don....Allah......."karki sake ki mun magiya"
Dole na gaya mashi sunan sa nan take wayoyin sa dake gefe saman hannun kujerar dake cikin motar yai danne dannen sa ya saka ga kunne, cikin isa da izzah yake maganar yana cewa, "bana son gobe nazo na iske shi wannan makarantar inba haka ba zakaji wani labarin ba wannan ba.........its ur own problem"
ya kashe kiran yana kallona hannuna ya rik'o cikin tattausan kallami da lallashi yace, "sorry kunnen yana zafi?"
Girgiza kai kawai nayi sannan ya d'ago hab'ata yana kallona lumshe mun ido yayi na jinjina masa kai, alamun na hakura kenan.
Har muka iso unguwar tamu ba wanda ya k'ara magana don ma mun saba yin shirun saboda nida shi duka ba masu surutu bane, har gara shi wani lokacin yana fira dani in y'an abun suna ka amman shi inba antab'o shi ba yana iya kwana da yini bai yi doguwar magana ba, duk abunda yai ma doguwar magana tabbata hak'ik'a halin nashi zayyi.
Tun daga ranar daya raboni da wanan dajin bai yi k'asa aguiwa ba wajen ganin Rayuwata tayi kyau, iyakar Rayuwar da nayi zuwa yanzu banga wani dake riritani yake tattalina ba kamar YAYA, zai iya sadaukar da koma miye inhar akai na ne muddin zanji dad'i kuma zanyi dariya,Yaya ba abunda yake so sama da ganina cikin farin ciki domin yace yadda ya ke rayuwa shi kadai baida kowa nima haka nake, shiyasa yake ji dani domin bani da kowa sai shi.
Afarkon zamana dashi yasha wuyata har bansan ya zan kwatan muku ba, komi ya kawo mun bazan ci ba sai dai naje fesa dashi zagi da duka inya nufoni ba wanda bana masa, ba irin cin kashin da ban masa amman ko ajikinsa maganar nan guda kullum ita yake gaya mun cewa.
"Rayuwarki abun tausayi ce Fatimah, komi zakiyi mani bazan rabu dake ba"
Ni kuma a wannan lokacin ba abunda na tsana sama da wadannan kalaman, dashi da kalaman nashi ji nake zan iya shek'esu amman ko ajikin sa abunda yake bai fasa ba,ko kari yake ya inganta rayuwata ya bani kyakkyawar rayuwa mai dadi, ahankali na fara hakuri ina sakin makaman fad'an nawa saboda irin kulawar da yake bani ko zuciyar fir'auna mutum garai dole watan watarana zai sadudu ya mik'a wuya.
Kan kace me! Na saki jikina dashi muyi tsere muyi wasanni duk tare, bacci ne kawai yake rabani dashi shima sai yaga nayi zai tafi nashi d'akin.
Ahankali na fara koya mun sabuwar Rayuwa irin tashi ta y'an gayu, tun daga karatu iya magana mai dad'i iya sanya kaya iya daukar wanka, bala'in son k'amshi da cima irin tasa duk abunda na zama a rayuwata ba kowa bane sila sai *YAYANA ABUN ALFAHARINA* sunan da nake kiransa dashi kenan, shi ya samun maitar son karatu don shiya koya mani har aka iya daukata makaranta, yaya bai had'ani da komai ba yana ji dani fiye da komi arayuwar sa, shiyasa nayi yawon makarantu bila adadin saboda bai daukar a tab'a mashi ni, babban abunda zai hasala shi har ya aikata mummunan abu shine namiji ya nuna yana sona, kai ko gani na yayi da namiji ranar babu zaman lafiya don yana iya kashe kwana uku baici komi ba, horon da yake ba kanshi kenan ni kuma na gwammace ni ya horani akan yadda yake azabtar da kanshi.
Ko iyayen da suka haifeni bana son su yadda nake kaunar yaya, domin su sun haifan ba don suna sona ba, shiyasa suka zabi dasu jefar dani akan su rayu tare dani, shi kuma ya raboni da dajin ya dauko ni don ya maidani mutum kamar kowa, shiyasa nake jigatuwa idan yana fushi dani.
Bai tab'a kuskuren cewa yana sona ba bana ganin alamun hakan ko afuskar shi, zallar kulawa ce kawai da mahaukacin kishin sa zasu nuna maka zahirin son da yake mani, yaya shine gatana bayan Allah duk sadda nakai goshina k'asa shikad'ai nake yima addua, domin shine na sani acikin jinsin mutane ko nace shi nafara sani.
Tunanin yar rayuwar baya da na tafi ya mantar dani isowar mu gida,na tsaya ina karema tafkeken gidan namu kallo, wanda har yau banga gida irin sa ba afad'in garin.
Bansan ta yadda zan kwatanta maku girman gidanmu ba, plat bu plat ne a cikin sa kuma komi kake so ba zaka rasa shi agidan ba inhar na more rayuwa ne, an zubar da kud'i manya manya a wannan gidan a iyakar fad'in unguwar banga gidan da yake shige da namu ba, ko a fenti balle akai ga sauran tsarin gidan, get d'in farko kanshi ba zakace k'arfe bane saboda yadda aka zuba fasaha aka tsara shi yai kyau, ga nauyi mutum guda baya iya bud'esa saboda nauyin sa, a gidan mu har club ke akwai duk daren duniya ake taruwa mata da maza ana casu, b'angaren drink kuwa babu irin kalar lemun da babu haka giya ma ba kalar wadda babu, gidan yana tara samari da y'an mata bila'adadin suna more rayuwar su, amman duk wannan shagalin da ake ko kusa da wajen ban isa naje ba don YAYAH tsaf zai b'allani akan hakan, kuma shi yana shiga don yana hud'd'a da yan mata yaya baya shan giya amman yana shan taba, arana sau d'aya yake sha yana iyakasje sati bai sha ba abunda nafi ma ganewa sai in yana cikin b'acin rai sannan yake shanta sosai,............."Tunanin me kike?"
Muryar sa ta dira cikin dodon kunnena naja ajiyar zuciya sannan nasakar masa lallausan murmushi nace, "Yaya Im tired"
School bag d'ina ya ansa ya tilla ma guard d'in dake tsaye bayan mu sannan bai tsaya wani jinkiri na ya daukan like a baby doll, sai na idasa makale sa muka nufi cikin gidan guard din na biye damu da bag dina...............