3
by @mommuhseen
🅿️........3
Ransa amugun jagule haka ya iso gida kwata-kwata baiga wata hujja da zata sa ahana shi wannan case d'in ba, sani ne kawai basuyi ba shi don wannan case d'in ya shigo hannun sa ya b'ata tsawon shekara biyar yana neman aikin DSS, sai yan shekarun nan da suka wuce Allah yasa ya samu, yanzu kuma ya saka ran za'a bashi case d'in ganin mutane da dama sun kasa, shine za'a wani cemasa bazai iya ba ai akwai ma rainin wayau aciki, to ko suna so ko basu so shine zai kawo karshe *ABU ZAYYAD* insha Allahu zubewa yayi bisa lallausan gadon sa yana cusa yatsunsa cikin yalwatacciyar sumar sa, wayar sa ya lalubo yana huci ya nemo no d'in ummin sa..............
"Dan Albarka na ka dawo kenan"
Cikin shagwab'a da muryar sa daya lauya kamar wani d'an yaro yace, "ummi I need u now please come to me"
Cikin sauri tace, "ishaq lafiyar ka? Allah yasa ba wata matsala bace"
Kashe wayar yayi yana jefar da ita gefe sosai ransa yake b'ace, shi zasu raina ma wayau to wallahi muddin wannan case d'in baizo hannun sa ba bai cika Ishaq ba, zasu gane shi mai kafiya ne lamba d'aya.............Ishaq d'ina meke damunka? Baka da lafiya ne? Naji amuryar ka ba dai-dai ba"
Ta zauna gefen sa cike da rudewa tana tab'a goshin sa taji ko akwai zafi, ya rik'e hannun nata idonsa har ya canza kala saboda b'acin rai yace "Lafiya ta qalau ummi kawai raina ne ab'ace"
Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tace, "nasha gaya maka ba tun yanzu ba Ishaq in ranka ya b'aci ka ringa amaton Sunan Allah, sai ka biyewa zuciya tajefaka acikin wani hali,nidai bana so koma miye ka ringa sassautama zuciyar ka don Allah, yanzu menene ya faru?"
Dora kanshi yayi bisa cinyar ta yana kwanta wa cikin kaunar ta da begenta yace, "Ummi kinsan burina, kinsan fatana kin san irin fafutukar da nayi har na kawo iwar haka, to rana tsaka ga dama ta samu amman ana kokarin hanani wannan damar, acikin aikin Dss banda wata manufa ko buri daya wuce abani case d'in ABU ZAYYAD, Amma ummi sun hanani sunce wai duka yaushe na fara aikin wai ba irin kananun case d'in dana saba warwarewa bane cikin d'an lokaci ba, in bari aba wadanda zasu iya ummi ni na cancanci wanan aikin, dani ya dace amman ba zasu gane ba ba zasu fahimci irin kishirwar da nake ciki akan wannan case d'in ba, don haka bazan hakura ba duk ta inda zanbi saina ga anbani, ki taya ni addua ummi sannan ki fara sanar da Baffa kafin ni nafara sanar dashi"
Sumar sa take shafawa tunda ya fara maganar har ya kai aya,tayi shiru na d'an lokaci sannan taja ajiyar zuciya tace "Ishaq ka kwantar da hankalin ka, ko bakai ba ABU ZAYYAD dole za'a samu mai iya kama shi kuma zai fuskanci hukunci,akan wannan karka nemi ka rasa natsuwar ka"
"Ummi ni nake son na kama shi, ni nake son ya shigo hannu na muyi ga da ga dashi ta hannu na nake son hukuma ta hukunta shi"
"Ya isa haka, kabar tada jijiyar wuya ni bana son kana tada hankalin ka har haka, insha Allah burin ka zai cika zan samu Baffan muyi magana, tashi ka watsa ruwa bari na kawo maka abinci"
Ta zamar dashi ta fice mirginawa yayi yana rungumar filo babu abunda yake hangowa sai ranar da wannan d'an iskan zai shigo hannun sa, yaja kuta har da naushin iska (😂 yi ahankali mazaje)
*******
"Yaya ni bana son kana yima Anty Nawwara irin haka, bana jin dad'i baka ganin yadda take kula maka dani"
Ya lumshe mun idonsa cike da nuna kulawa ya shafa kaina yace, "jelly na baki ga na hanata tana baki abu mai yaji ba, baki saba da shan yaji ba har yau bana son ya cutar dake, ko rannan bakiji abunda likita yace ba tunda cikin ki baya so adaina baki"
Na d'an turo bakina gaba nace "amma ai akwai tasting mai dad'i ko"
Dungure mun kai yayi yace, "disturber girl"
Dariya nayi ina d'arewa saman wani can bed muna bakin swimming, bag d'ina na dauko ina fiddo books d'in da nake da assignment inyi, akwai babbar tap da ita nake aikin school, har computer ina da ita adakina.
zama yayi gefena saman wani bench ya na operating computer sa, na mak'alo ta wuyan sa ina kallon abunda yake, cikin kwarewa yake yin abun bansan ko me yake ba kuma ina son sani sai nace, "Yaya me kake son yi"
Cigaba da aikin yayi yace, "hacking account nake"
Ba sabon abu bane wajena na saba ji na saba gani, kuma ko kadan ban dauki haka wani laifi ba, tunda wanda yai masa shi yake mawa,ba ruwan sa dakai muddin baka shigo gonar sa ba,sai na dauki lemuna ina sha yace "ina kokarin ganin na anshe dukkan dukiyar dake hannun gwaska, ina da burin ganin bayansa kamar yadda yai sanadiyyar ganin bayan mahaifina"
Tausayin sa ya kamani nace, "Yaya meyasa tun a wancen lokacin baka gama dashi ba, ya cutar dakai ya jefaka cikin wata hark'alla da bana jin zaka iya barinta, Yaya gwaska mugune shida Billah"
Kallona yayi tare d'ago hab'ata ganin zan masa kuka, lumshe idonsa yayi yana girgiza mun kai yace "karki b'ata ranki akansu inhar kin son muga bayan su sai kin mun alk'awarin ba zaki sake zubda hawayenki akansu ba, soon insha Allah zan zube maki su gabanki"
Na lumshe idona kafin na bud'e naji tattausan lips d'insa ga nawa har saida naja ajiyar zuciya, dai-dai dawowar Anty Nawwara saurin matsawa daga jikinsa nayi saboda kallon da naga tana yi mun, hakan sabon abune a wajen mu bai tab'a yunk'urin tab'ani ba da sunan wani abu sai yau, jinai duk na rikice zuciyata tana dokawa dirar tiren da ta had'o mun wani abincin shi ya dawo dani dan guntun tunanin dana tafi, murya ta can k'asa nace "thank you Anty Nawwara"
Da ido kawai ta ansa ni naga ta rab'e zata wuce shi naga yai caraf da hannun ta, saurin barin kallon su nayi ina son maida hankalina akan aikina, amman na kasa zuciyata tun zurani take akan na kallesu ni kuma ina hanata don zan ga abunda yafi karfin kwalwata, sautin moaning d'in Anty Nawwara yasa dole na dauki bag dina na sagala sannan na dauki tiren na k'ara gaba, ban san me zuciyata take nufi ba amman tabbas inajin ciwon abun, meyasa in zai abun sa bazai kauce ma idona ba ko yana ganin har yau yarinya nake ban san komi ba, Aa bazaiyuwu ba Im 18 years old I'm matured ko yana tunanin bana jin haushi? Yana nufin bana kishin sa kamar yadda yakejin nawa kishin? Impossible..............nai wuce wata can study room d'ina duk na rikice kamar wata zararriya dana rufe idona sautin moan d'inta nakeji, kenan tana jin dad'in abunda yake mata, wow bazan dauka ba muddin Yaya yana son mu zauna lafiya dashi,ni ya hanani kula ko wane irin saurayi sannan suma samarin ya hana su kulani, ko muftahu nake magana dashi yanzu zai gigice yahau ciwo, why ni yake treating d'ina a haka?
Sosai nake jin zafi a zuciya ta ban ma tab'a samun kaina cikin tsananin kishi da jin zafin abunda yake mata ba sai yau, nasan wacece wajen sa matar sace amman don me zai ringa tab'ata gabana..................sai hawaye sharrrrrrrr kamar an kunna famfo bazan iya tuna when last time da nayi kuka irin haka ba, mantuwar ta manta har akai sallar magriba ina nan naci kuka na k'oshi assignment d'in da banyi ba kenan na wuce nayi sallah na saka ma d'akin key, na haye gado na kudun dune.
Inajin sadda yazo ya fara knocking nasan ya gama duk abunda zai daita lokacin shiyasa ya waiwaye ni, daga yadda muryar sa ke fita zai nuna maka zallar tashin hankalin da yake ciki,nai muk'us kamar banaji tun yana kirana har ya gaji ina jin sadda ya tashi hankulan ma'aikatan gidan kan neman spare key d'in dakina, kafin wani lokaci mai tsawo naji ya fara saka key yana budewa saurin saukowa nai yana bud'ewa ina banka toilet na shige saidai banyi nasarar datse kofar ba yai wani uban tsalle ya shigo, nufo ni yayi yana shashsheka na maida kaina k'asa saboda kwallar dake silalo mani, d'ago hab'ata yayi na fizge ina kauda kaina, ya sake biyo ni bangaren dana maisa fuskar na dago a zafafe bansan na sauke yatsuna biyar akan fuskar sa ba, ni kaina da nayi marin har cikin k'ok'on raina ina sauke hannuna na fashe da kuka ina durk'ushe wa k'asa na sa kaina cikin guiwata, sosai nake kukan sai ya biyo ni k'asan yana kokarin dago fuskata cikin kukan nace, "kai jani, ban tab'a tunanin zan daga hannu na doke ka ba gashi nan yau ka tunzura ni, bana......ba.....bana son abunda kake mun bana si!!!, nima fa ina zuciya a kirjina akan me zaka ringa hurting d'ina da abunda bana so? Kai ka hanani kula kowa baka son ko jariri namiji yai mgn dani why why Yaya??..............na cigaba da shashshekar kukana idonsa jajir yake kallona bakin sa ya bushe kallon juna muke ido cikin ido ga hawaye share-share,ban san sadda fuskar sa ta had'e da tawa ba yake lashe hawayen, ya dora hannuna saman kuncin sa dana marai yace cikin disashshiyar murya "please Jelly slap me again,"
Na girgiza kai ina jan majina nace, "No I can't slap u, na farkon ma zuciyata ce ta tunzura ni Im very sorry"
Girgiza kai yayi yace, "inhar baki sake marina ba hukuncin da zan ma kaina ta dalilin zubar hawayen ki yafi wannan marin zafi, oya slap me too"
Runtse idona nayi ina nadamar yin na farkon don inhar banyi wannan daya nace ba, tabbas hukuncin dazai ma kanshi saiya shafeni ahankali na daga hannun na maresa slowly, sai kawai na fada jikinsa ina kuka.
Rungumeni yayi tsam yana bubbuga bayana kafin ya d'agoni muka tashi tsaye, wajen shower ya tsayar damu sai dai naji saukar ruwanta mai sanyi ajikin mu, wata nannauyar jiyar zuciya na sauke yana yawan yi mana haka duk sadda mukai fad'a, saboda ina son ruwa yana saurin saukar da fushina, kan kace me tuni munyi sharkaf da ruwan gashina ya jike ya manne, ture hular yayi ta fad'i kasa ya ringa yawo da hannunsa cikin gashina dan danan na nemi rasa natsuwa ta, na sake rik'esa sosai Yau yaya meke damunsa akaina.
A kunnena yake rad'a mun cikin wata murya kamar ba nashi ba, "pls jelly na forgive me, I will never ever hurt u again"
Kai kawai nake d'aga wa saboda ya hana ni ma yin magana, saboda yadda yake lasar kunnen, muryata na kerma nace "ya.....yaya"
Yace, "uhmm jelly na menene"
Ina sauke ajiyar zuciya nace, "ka daina"
Hancin sa yake goga mun yace, "why?"
Ina ta jan ajiyar zuciya nace can k'asa, "inajin wani iri bazan iya cigaba da jurewa ba"
Zip d'ina ya zage ya jefar da rigar sannan ya balle bra d'in ya jawo towel ya nad'eni ciki, sannan na zare pant d'in ya dauko ni ya aje kan gado ya kashe Ac dakin, sannan ya dauko cream din da nake shafawa yace "in shafa miki"
Na girgiza kai ina turo baki murmushi yayi ina ganin yadda yake b'oye reaction d'insa kar in gani, baisan tun a toilet na gani ba.
Da kaina na shafa man sannan na saka kayan bacci, na shige bargo kissing for head dina yayi yace, "Good night jelly na"
Ina kallon sa farin ciki da zunzurutun kaunar sa suna narkar mun da zuciya,nace "sleep well my Yaya"
Saida naji karar rufe kofar sannan na sauke wata kafirar ajiyar zuciya, na sauko na koma toilet d'in saboda abune ya fito mun tsarki nayi da ruwan zafi sosai sannan nayo alwallah nayi isha'i, sannan bacci ya figeni.