HASKEN MAKAFI

6

by @mommuhseen

🅿️........6



"Mariya nayi dogon nazari nayi iyakar hangena na akan wacce ta dace da Ishaq acikin y'ay'an dangina banga wacce tayi dai-dai da halin Ishaq ba sai *BILKISU*, shin kina ganin zab'in da nayi masa yayi kuma zasu dai-daita? Ko kuwa ya kika gani d'an kine ke kika raine sa tun yana d'an sheraka goma har kawo yanzu, kinsan abunda yake so da wanda baya so"


Shiru ummi tayi tana sauraren Baffan har yakai aya, jimm tayi na tsawon lokaci kafin ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Baffan, cikin girmamawa da natsuwa tace masa "Baffa da Ishaq da Bilkisu duk yaranka ne kuma kana da iko dasu fiye da kowa, har Raina wannan had'in yayi mani saidai akwai abunda yake damuna, nake zargi akanshi"


Cikin mamaki yace, "meke nan mariya? Hanzarta ki sanar dani"


Taja iska tace, "game da *ISHAQ DA SOFIYYAH* ne, na dad'e ina nazarin su sudukan su bazan ce ga dogon lokacin dana dauka ina nazartar suba amman andad'e, na fahimci kowannen su yana son d'an uwansa miskilancin Ishaq bazai bari agane ba, haka shiriritar Sofiyya da tsilla-tsillar ta bazata bari agane ba amman ni uwar su na gama fahimtar komi"


Tsitttt Baffa yayi kamar ruwa ya cishi don lamarin yad'an tab'a shi sosai, ta cigaba da cewa "Amman har yanzu ban tabbatar ba domin dukan su basu bani wannan damar ba, amman abunda za'a shine ka tirke sa tunda shine maiyin Auren nan, kuma shi zai zauna da matar nan ka matseshi saiya gaya maka in akwai wadda yake so"


Baffan yace, "ba dashi zan fara ba kira mun sofiyya in bata tafi ba"


Tatashi ta wuce cikin gidan don Bilkisu ta dad'e da tafiya itace take shekarar karshe, sofiyya kuma duka aji biyu take school of nursing sadda ta fito ta barta tana shiri zata je wuse gidan k'anen Baffan.


Dai-dai fitowarta daga dakin cikin shirinta tayi kyau sosai don sofiyya kyakkyawace kai tsaye zakace tafi Bilkisu kyau, haske kawai Bilkisun zata nuna mata.


"Ummi daman nemanki nake, zan tafi kilan na kwana acan"


"Watau baki d'auki wayar ba har yanzu kenan? Meyasa bakijin magana shi wanda ya siya miki zaiji dad'i kenan, to karki dauka zamu saka k'afar wando d'aya dake"


Diddira k'afafu take tana kukan shagwab'a tace, "don Allah ummi kiyakuri zan dauka fa"


Tace, "oya maza kije ki dauko ta ki saman falon Baffan ku yana nemanki"


Ta d'aga kai sannan ta aje bag d'inta ta wuce d'akin ummin don har lokacin bata koma d'akin su ba, koma wa ummin tayi ta same shi zamanta babu dad'ewa sai gata ta shigo da Sallama, gefen k'afafun ummin tai burki ta zauna tace "Baffa gani"


Kallonta yake yana nazarinta kafin cikin kulawa ya kira sunan ta yace, "Sofiyyah!"


Dan danan jikinta yai bala'in sanyi ta ansa a kasalance tace, "Na'am"


Cigaba yai da cewa, "bana son kiyi mun k'arya ban sanki da ita ba, kuma nasan bazaki koya ba zan shedeki ta nan b'angaren, don haka ki gaya mun gaskiya"


Gabanta na fad'uwa tace, "insha Allah Baffa"


Yace, "masha Allah, abunda nake so dake ki gaya mun idan akwai wanda kike so saboda inason na had'e bikin ku dana Bilkisu da isma'il Abbanku Bilyamin"


Ras ras gabanta ya fad'i ta shiga ukunta wace irin ranace wannan, bata shirya mata ba koda wasa to me zatace ma Baffa? Gashi yace baya son k'arya shiru-shiru bata ce komi ba ummi tace, "ko kin zama kurma ne"


Girgiza kai take idonta na son cika da kwallah, Baffan yace "Kinga Bilkisu ta tsayar da wanda take so bana son ke nai maki dole, don bazan Aurar da ita ba ke in barki"


Sai ta saka kai aguiwa tana kuka d'an murmushi Baffan yayi shikad'ai zai iya gane halin yarsa, don shine ya reni abunsa cikin lallashi yace "kibar kukan tunda ba dukanki akai ba, gaya mun waye? Zan je na samesa inji"


Bata san sadda bakinta yake magana ba tana cewa cikin kukan, "Kar same sa Baffa saboda baya sona, ni gara ka zab'a mun wanda kake so"


Ummi kanta saida tayi murmushi tace, "kinga an sofyn Baffan daina kuka kinji ko,koma waye shima zai soki daure ki gaya mana ko waye"


Sai kawai tatashi tabar falon tana cigaba da kukanta, ba zata tab'a iya cewa tana son yah Ishaq ba, yadda baya sonta gara ta mutu da sonshi inma Bilkisun yake so yaje yaita sonta.


Baffa ya kalli ummin yace, "maganarki gaskiya ce zan magana da ishaq d'in insha Allah"

Akan haka suka tashi shi ya fita aiki ita kuma ta wuce cikin gidan b'angaren kanen sa Abba shafi'u wajen matarsa hajiya ubaida.


**********


"Yaya don Allah ka bar Anty Nawwara ta cigaba da koya mun karatun nan, ina fajin dad'in sa"


B'ata fuska yayi yana cewa,"bana son gardama Jelly kin sani ke biki ga duk yadda kika rame ba saboda bata barinki ki huta every weekend?ni gaskiya bana so"


Na turo bakina ban sake mashi mitar ba don bazan canza magana ba, ciwon sa ya warke sai abunda ba'a rasa ba, duk wani aiki dazai fita to agida yake yin kayan sa zuwa yanzu duk wata dukiyar sa da gwaska ya mallake ta dawo hannunsa, saboda naga yadda komi na gidan yake canza wa bushasha kawai ake ko jiua da dare k'attin raguna aka gashe anan compound, akai walima maza da mata birjik saidai kaje ka yanko da wuk'arka kazo ka dauki duk irin lemon da kake so ka sha, nida Anty Nawwara muna ciki ba damar mu fito.


Yaya kau bai shigo na sai cikin dare ban san lokacin ba, saidai naji sadda yake sumbatar goshina ya gyara mun kwanciyata ya fita, bushashar kud'i kawai yake daga ya siyo mun wanan sai ya siyo mun wannan, ganin haka yasa nace masa.


"Yaya ka siya mun waya"


Hankalin sa na kan wayar sa yajawoni jikinsa na dora kaina saman kirjinsa yana shafawa,cikin lallashi yace "bazan siya miki waya yanzu ba Jelly,bana ma tunanin ko kin gama school zan siya miki"


Na b'ata rai zan masa rigima yai saurin dura hannunsa kan bakina cikin muryar k'asa-k'asa kamar baya so wani yajiya kawo bakinsa wajen kunnena yace, "shiiiiiit, bana son wannan rikicin oky?"


Ina shashshab'e fuska na d'aga kai yai kiss kaina yace, "oya tashi ma muje yawo ai zaki rakani ko?"


Na d'aga kai yana murmushi yace, "maza jeki canza kaya ina mota"


Aguje nai cikin gida don canza kayan nasan muda dawowa sai dare yau, indai zamu je yawo dashi to fa bama dawowa da wuri sai dare ya tsala.


Ina shiga mukai karo da Anty Nawwara nai tsaye ina kallon ta saboda ganin katon trolley da take jaye dashi idonta yai jajir tasha kuka har ta gode ma Allah, gabana ya dage ya fad'i nace "Anty ina zaki? Kuka kikai innalillahi don Allah karki tafi kiyi hakuri"


A ranar naga dariya had'e da kuka ta girgiza mun kai tace, "ke zama da wannan azzalumin ya zamar ma dole Fatimah, amman ni kau yau ko zai kashe ni bazan sake kwana anan gidan ba, duk da bani da sauran wajen zuwa zan tafi ahaka"


Rud'ewa nai jikina har yana rawa ina hawaye na rik'e hannun ta nace, "bazaki tafi ba Anty Nawwara, babu inda zaki kibarmu tare muka taso anan kuma tare zamu cigaba da rayuwa, komi yaya yayi maki kiyi hakuri zan masa fad'a amman karki tafi kibarmu muna buk'atarki"


Zagaye ni tayi kurin ta nufi waje, aguje kamar na zare haka na bita ina kwala mata kira ina kuka sauri-sauri kawai take ta isa get don yadda takejin zuciyar ta tana tafarfasa idan ta tsaya fashewa zatai, tsanar Abu Zayyad zata iya sawa ta kashe shi har lahira.

Ita kuma bata shirya ma makomarta ba tana burin gyara rayuwarta tayi kyau ta cigaba da yima iyayenta addua,..................wata irin fincikowa taji anyi mata ta juyo a sukwane kadan ya hana bata kifa ba, ido cikin ido suke kallon juna ita dashi ya zare glass d'insa ya wurgar, cike da bala'i da masifa wanda na jima ban ganshi a ciki ba hannun sa manuniya yake nuna ta dashi cikin wata dakakkar murya yace, "Ban sha gaya miki cewa keda fita anan gidan ba saidai gawarki? Yanzu ma zan kuma nanata miki *NAWWARAH* keda fita koda bakin get ne sai idan nine na mutu ko kuma ke, karya kike wallahi duk duniya nine kad'ai zaki zauna dani ba wani d'an iskan da ya isa ya rab'eki bayan ni, don haka ki koma cikin gida cikin lumana ba tare da tashin hankali ba"


Hawaye ne ki zarya fuskarta ba k'ak'k'autawa ta girgiza kai bayan ta saki murmushi tace, "to yau ko gawar tawa sai ta fita anan gidan *ABBAKAR ZAYYAD I ZAYYAD* nagaji nagaji nagajiiiii!!!, ni ba baiwar ka bace ni ba hadimarka bace *NIMA MUTUMCE KAMAR KOWA* bazan cigaba da rayuwa dakai ta k'ask'anci ba, kana treating d'ina kamar wata dabba baka san muhimmanci na ba sai idan zakai jima'i, anan ne kawai kake sanin darajata amman dani da karnukan gidan ka banida bambanci, tunda na had'u dakai rayuwata ta gama lalac......wa"


Kuka sosai take har jikinta yana rawa kamar an jona mata shock, tana kallon sa ta cigaba da cewa "ka rabani da kowa nawa, ka rabani da iyayena dangina da abokan arxik'i ka danfarar dani agidan ka babu abunda nake kwankwad'a sai zallar bak'in ciki, to na gaji wallahi tafiya zan saidai kai gunduwa gunduwa da namana"


Yadda Anty Nawwara ke kuka haka nakeyi don tunda nazo gidan ban tab'a ganin sunyi wannan tashin hankalin ba, ina tsananin kaunar Anty Nawwarah jinta nake har cikin jinin jikina, ganin da gaske fita zatai ya daka ma mai gadin wani uban ihu daya kewaye gidan baki d'aya aiko ya ruga don rufe get d'in, amman ba alamar zai rigata isa ganin haka yasa kamar wani mahaukaci yaje ya bud'e kejin karnukan sa ya tura mata su, ko ajikin Anty da gaske fitar take niyyar yi, har ta bud'e karamar k'ofa ga kuma wani kumurcin kare da suka dumfarota bilhakki da gaskiya kuma kanta sukayo,ni kaina ban san sadda na ganni tsaye bayanta na ina huci ina zubar da kwallah,nace ma yayan cikin d'aga murya "inhar zasu cinye Anty Nawwara gara su fata cinyeni sai su isa gareta, bazan bari su cutar da ita ba"


Kamar mahaukaci haka yaya ya koma ganin karnukan sunyo wata sufa kaina kuma muddin suka hauni mai cetona saidai Allah, sosai nake gunjin kuka kan kace kwabo yai wani tsalle ya tare su,yana huci yasa aka kora su kejin su wata fincika yayi mani saidai naji wani zazzafan mari da tunda nazo duniya ba tab'ajin azaba irin wannan ba, jinai jina da ganina sun dauke na wucin gadi,bai bi ta kaina ba ya cakumo wuyan Anty ya wurgar da ita gefe yana huci yace ma masu gadin shi kaf tun daga masu kula da gida da shuke shuke,da guard d'insa da masu gadi da sauran ma'aikatan dasuka zagaye mu. "Wallahi tallahi muddin kukai saken da ta fita koda kofar get ne sai na lahira yafiku jin dad'i,"


Ya sun kuce ni yai cikin gida dani ba abunda nake sai kuka,wace irin ranace wannan yau nice yaya ya daga hannun sa ya mareni,?lallai na jinjina irin kaunar da yake mani amman hakan bazai saka na huce ba, don marin ya shigeni ba kadan ba.


Duk yadda nake wulle-wullen k'afafu da son kwace kaina bai kula ni ba saida muka dangane da d'akin sa ya direni, na sake fashewa da kuka ina dira k'afafuna durk'usawa yayi gabana idonsa kamar an zuba attarugu aciki, ya dago kaina da zafi-zafi cikin wata irin murya yace "FATIMAH da idona ya cigaba da ganin abunda kikai yau gara ki saka bindiga ki harbi zuciyata, ina kishinki ba kuma normal kishi irin wanda kika sani ba, inajin kishin ki fiye da duk yadda zaki hasashe sa aranki, ba namiji kad'ai ba har ita waccen da kike nuna tafini muhimmanci akanta zan iya kashe ta da inga irin abunda kikai, in kasheta kuma nima in kashe kaina,ke.....k.....ke wai kin san irin yad.......yaddda zuciyata take tafarfasa akanki kuwa?"

Ya daki gefen kaishi da karfi jikinsa yana rawa yana karkarwa ya tashi kamar wani mayunwacin zafi ya b'aro da wata locker yana laluben abu aciki,saiga wata arniyar binduga ya dauko yazo gabana cikin zafin nama ya saka cikin hannuna kasa rik'eta hannun yayi saboda yadda jikina da bakina ke b'ari ainun, saboda tashin hankali ya ce "gas.......gashi nan ki kasheni da kanki Jelly, tunda har kina iya sadaukar da rayuwarki akan waccen kucakar bama akaina ba, shin ta dalilin wa kika santa ehy???! Ya fad'a da wata dakikiyar tsawa saida na saki wani wahalallen fitsari mai zafin gaske, numfashina yana wani irin fizga, bindigar ta fad'i k'asa saboda razana baya baya yayi ya buga bayansa da bangon d'akin, yana zubewa kan guiyawun sa kanshi k'asa dakin yai tsit sai shashshekata ke tashi, ban tab'aganin b'akar rana ba irin wannan a rayuwata.


Zuwa can ya dauki bindigar ya saita ga kanshi yana kallona yace cikin wahaltuwa "tunda bazaki harbeni ba, ni bari na kashe kaina saiki cigaba da rayuwa da Nawwara uwarki ko??"