HASKEN MAKAFI

8

by @mommuhseen

🅿️........8


Ishaq an bashi sabon office da komi da komi da zai buk'ata aharkar binciken mutumin daya addabi al'umma, ogan su tsaye yake wajen kara mashi gwarin guiwa saboda da yawan sauran ma'aikatan dake wajen sun nuna kishi da jin haushin sakar ma ishaq aikin, saboda suna ganin zai k'aru kuma in har aka cimma manufa za'a k'ara mashi girma, ganin haka yasa ogan nasu yake karfafa ma ishaq d'in don ya samu kwarin guiwa.


Tunda aka sallama masa aikin baya zaune ko gida rabon da su ganshi an kwana biyu, tun safe inya fita sai sun kwana yake dawowa don cikin k'ananun staff an bashi wanda zai ringa taimakon sa watau abokin sa amininsa *Sa'id bello sa'id* tasu tazo d'aya tun da ya shiga aikin Dss dashi ya fara kyakkyawar mu'amala, yana da kirki yana kuma son shi kamar yadda shima sa'id d'in yake son sa.


Tunda ya yafara gudanar da aikin ya tabbatar ba karamin aiki ne gaban shi ba,amman bazai ba zuciyar sa daman sarewa ba zai iyakar kokarinsa ganin ya cimma manufa zai kuma had'a da rok'on Allah don shine zai taimakesa ya zame masa *HASKEN MAKAFI* ya nuna masa hanyar da shi baya gani.


Duk da yau weekend ne bai hana ya shirya fita ba ga gajiya da ciwon jiki da yake fama dasu kwana biyu saboda rashin hutu, ga rikicin waccen yarinyar tana neman sa mishi hawan jini, ga Bilkisu na fushi dashi bai san dame zaiji ba.............."ASSALAMU ALAIKUM"


Sassanyar muryar ta mai shiga rai ta tsinke masa tunanin da yake ciki, can k'asan mak'oshi ya ansa sallamar yana dire kyawawan idanun sa akanta, ganin tayi wai fayau alamun kamar ta rame.


"Yaya ina kwana"


D'an lumshe idonsa yayi sannan ya amsa da cewa,"lafiya"


Taji haushi daman bata zauna ba sai ta juya tana turo baki cike da haushi yadda ya ansa mata gaisuwa,tace "Daman baffa ke neman ka yana falo"


Tai tafiyarta har ta bud'e kofa zata fita taji yace cikin kakkausar murya,

"SOFIYYAH"


ras ras taji gabanta ya fad'i duk iskancin ta tana bala'in tsoronsa ainun, juyowa tayi ahankali kafin ma ta dawo hayyacinta ya iskota runtse ido tayi tana damk'e hannunta, har hawaye sun cika idonta yana isowa sai yaji wani abu yana sukan shi, kasa yin abunda yai niyya yayi ya lumshe idonsa yana jin zuciyarsa kamar zata narke.


Cikin sanyin murya yace, "kukan na miye? Na dake ki ne?"


Girgiza kai tayi tana sadda kanta k'asa tana goge hawayen, yace "meyasa bakijin magana, ban hanaki turo mun baki ba"


Cikin rawar murya cike da kuka tace, "kayakuri"


Wani sanyi yaji ya ratsashi har cikin k'ok'on zuciyarsa ya koma cikin falon ya zauna sannan yace, "zo nan"


Kamar wadda kwai ya fashewa aciki haka ta taka zuwa inda yake, tun kafin ma yace ta zauna ta zauna a kasan kafen gefensa, hank chef dinsa ya mika mata ta ansa tana goge fuskar ta goge tas sannan ta mik'a masa ya ansa.


Duk sukai shiru ganin lokaci na jaa tatashi tace "zan tafi"


Kallon ta yake tayi yayin da ita kuma take ta wasa da wani zobe dake hannun ta, yace "saina fito"


Ta juya tatafi saida ta fice sannan yaja wata nannauyar ajiyar zuciya, kanshi zuwa fuskar shi yake shafawa,akwai k'alubale gaban sa amman ya shirya ansar koma miye hannu bibbiyu.




"Bilkisu bana son wannan kukan don bashi na tambayeki ba, ban san yaushe kika lalace da kuka ba kamar sofiyyah ki mun shiru ki bani ansar tambayar da nayi maki"


Shashsheka take tana ajiyar zuciya sai tsikar gashin bargon dake shimfide a gadon nata take, daker ta iya cewa "ummi ni nake son shi, amman shi Sofiyya ce gaban sa"


Ummin tace,"ya tab'a gaya miki cewa sofiyya yake so?"


Girgiza kai tayi tace, "Aa nina ke zargin haka daga yadda yake nunawa"


"Meyake nunawa?"

Ummin ta sake jefarta da wata tambayar,kwalla suka sake silalo mata tace,


"Ni kawai na fahimta ne"


Ummin tace, "uhmm to abunda zan gaya miki shine ki kauda kanki akan ishaq, idan Allah yasa shine mijinki falillahilhamdu, idan kuma ba rabonki bane shi rabon yar uwarki ne sofiyyah ki taushi zuciyarki kikuma nuna ma yar uwarki farin cikin ki akan haka, bana son wata b'araka ta shiga tsakanin ki da sofiyyah so nake ku zama y'an uwa tamkar uwa daya uba daya, Baffa ba abunda bai mana ba cikin yi yake don haka bai kamata ki nuna kishin ki akan jinin sa ba, koda wasa bana karki sake ki nuna masa kin son sa ki kama ajin ki ki kima dage da addua Allah ya zab'a miki abunda yafi alkairi,ni inso samu ne ki ba faisal dama tunda ya nuna yana sonki kuma d'an uwane na gida kowa yabon sa yake, amman bana son muyi garaje ki cigaba da addua"


Cikin sanyin murya tace, "to ummi insha Allahu, kiyi hakuri idan na b'ata miki rai"


Ta shafa kanta tace, "na yafe maki duk abunda kikai mun na n'acin rai Bilkisu, abunda kawai nake so kija yar uwarki ajiki hakan zai faranta mani"


"Zamu shirya ba zamu sake fad'a ba insha Allah ummi"


Jin alamun fitowar ummin yasa tai sauri har tana tuntub'e tabar wajen, zuciyarta tana bugawa wani spare d'aki ta shige ta kulle kanta ta silale jikin k'ofar tana sakin kuka marar sauti, tun daga k'asan zuciyarta take fiddo kukan ko zata samu sassaucin halin da zuciyarta take ciki, me kunnenta yajiyo mata Bilkisu tana son yayan su itama, wayyo Allah meyasa haka takasance? Shikenan na rabu da abunda zuciyata ta girma dashi don bazan tab'a auren wanda yar uwata take so haka ba, na hakura dakai yah ishaq na yafe ka na barma yar uwata kai............taci kukan ta takoshi saida ta tabbatar Bilkisun tatafi school sai ta fito ta koma dakin nasu ta kwanta.



Ishaq durk'ushe falon Baffa bayan sun gaisa yake masa maganar ya aikin nashi yake kasancewa,cikin natsuwa yake gaya mashi halin da ake ciki da kuma bibiyar Abu zayyad da yake yi ba dare ba rana, abu guda yake son sani yanzu shine schedule's d'insa na kowacce rana, Baffan yace "zan taimaka maka insha Allah, yanzu abunda yasa na kiraka guda ne zuwa biyu"


Kirjinsa saida ya doka yace, "ina jinka Baffa"


"Idan kana da wadda kake so ka gabatar mun da ita cikin sati biyu, idan kuma har wayau babu ka barmun zab'in to karkayi kuka dani nan gaba idan nace maka ga zab'ina"


Yayi iyakar yinsa wajen b'oye rud'anin sa sai shafa kai yake ya rasa ta inazai fara, tabbas yasan Bilkisu na sonshi da dad'ewa kuma kaf halayenta sunyi kama da nashi, itace zatayi dai-dai da matarsa saidai kuma zuciyarsa wadda take so daban.

Bakin sa bazai iya cewa ga wacce yake so ba,don baya son ya k'untata rayuwar Bilkisu, ya rasa madafa inda zai dafa Baffan ya katseshi da cewa "kana da sauran lokaci nan da kwana 14, idan kuma suka wuce hakan na nufin ka bani zab'i kenan"


Cikin yar damuwa yace, "to Baffa ba zanje nayi tunani"


"To Allah ya tabbatar da alkairi"


Jiki a salub'e ya tashi ya fita d'an murmushi Baffa yayi yasa waya ya kira Ummi ba jimawa sai gata tace "ya kukai dashi"


Yace, "na tada mashi hankali ne yadda zai fiddo bunda yake boyewa, nan da sati biyu na bashi yazo mun da wacce yake so"


"To Allah ya zab'a bunda yafi alkairi"


Tayi d'an shiru na dan lokaci Baffan yace, "mariya kina ko tunawa sa d'anki?"


Bata d'ago daga sunkuyen da tayi da kanta ba muryar ta da rauni sosai tace, "idan ba kayi mani maganarsa ba ni tuni na yafe Abbakar, abu guda nake masa fata shine shirya kafin ta Allah ta kasance kashi"


Tausayi ta bashi sosai yad'an rik'o hannunta cikin kulawa da tausasawa yace, "insha Allah zai shiryu kuma zaizo watarana ya durk'usa ya nemi yafiyarki, na daya dag abunda yasa zai yi nawa aikin kodan komi yazo ya faru ya wuce, ki cigaba da yi masa addua Allah zai karba"


Kwalla ta silalo mata yai saurin tare ta da hannun sa yace, "Aa ummin sofyya, ban sonki da haka ba ki kara hakuri kiyi fatan cinye wanan jarabawar"


Da lallashi da kalamai masu taushi da sausasawa Baffa ya samu ummin ta dawo natsuwarta.


      *********


Har zaman da ake yanzu Anty taki yarda ta shirya da yaya, ni kaina abun ya shafan don Anty ta kulle mu muduka sai yanzu muke gane muhimmancin ta, bama dai kamar shi yayan don dai yanzu baya zaune yan tafiye-tafiye ne yake zuwa k'asashe harkar kwayoyi, tunda nake da yaya ba wata hark'allar sa da ta tab'a bani haushi na tsaneta irin wannan sabuwar harkar, don bilhakki da gaskiya ya zama dillalin safarar k'wayoyi, har cikin raina abun bai mun ba kwata-kwata na natsani harkar a tafiyar da yayi ne muka fara zana weac, har sannan kuma wannan yarinyar bata daina addabata da son kulla *Abota* ba, ni kuma raina bai kwanta da ita ba shiyasa nak'i bata dama.


Ana gobe yaya xai dawo ne ta nuna man wacce muke kama da ita sosai, har saida naji mummunan fad'uwar gaba dana ga matar, amman duk da haka ban ba yarinyar dama ba tunda na kalli hoton a waya na kauda kaina muna gama exam akazo dauka ta, har bakin mota ta rakoni da zata rufe mun kofar tace "Banzo miki da cutarwa ba face alkairi ina fatan zaki fahimceni kafin mu gama jarabawa kowa ya watse, a sauka lfy FATIMA ABU ZAYYAD"