HASKEN MAKAFI

9

by @mommuhseen

🅿️........9


Zan iya cewa tunda nake da Anty Nawwara ban tab'a ganin ta cikin tsananin farin ciki irin na yau ba, tunda na shigo karamin falo na ga canji don an gyara shi banda k'amshi babu abunda yake, anyi masa decoration sosai sakara na koma wajen kallon falon ban kara shiga mamaki ba saida na shigo babban falon anan naga ado da k'amshi, na hango dining anjera shi yai kyau womers kala da kala a saman dining d'in alamun anyi dishes daban daban kenan, duk sai na zama geluwa ina bin ko ina da ko ina na gidan da kallo saboda ni dai a wajena sabon abune, hangota nayi ta fito daga corridor d'in dazai kaika d'akin Yaya, kwalliya naga tayi wadda ban tab'a ganin ta tayi irinta ba anty bata damu da shafa ko jambaki ba amman yau cikin y'an awannin da nayi bana gida harda k'unshi da kitsonta kalaba ta zubo ga gadon bayanta, kasancewar Tana da gashi kamar ni.


Riga da siket ne ta sanya na wani dank'areren less da yaya ya tab'a siya mana da wata karamar sallah, ita bata tab'a sanya nata ba don bata damu da kwalliyar ba amman yau shi ta sanya, tana hangoni ta k'awata fuskarta da murmushi waya ce hannun ta take daddanawa ta k'araso wajena jan hannuna tayi tana cewa, "ya ya dai Yar k'anwata kin tsaya daga nan kamar biki tab'a ganin antyn taki ba"


Na rufe bakina daya kasa rufuwa nace, "Anty bake ce ban saba gani ba abubuwan da kike yine ban saba ganinsu ba, sannan murmushinki kanshi bazan ce ga ranar da kika yi mun shi ba"


Janyoni jikinta tayi tana cewa, "karki damu Jellyn yayanta daga yau wannan antyn taki zata kasance cikin kulawa da Fatimah zaki sameni kullin cikin raha da walwala insha Allahu"


Nace, "Anty wani abune yafaru har kika canza lokaci guda haka?"


Tace, "kawai dai naga hakan bashida amfani ne shiyasa naga ya dace na gyara alak'armu nidake da yayanki, yadda zamu kasance cikin farin ciki akodayaushe yanzu muje na shiryaki zamuje taryar Yayanki airport"


Makalkaleta nayi ina dariya cike da farin ciki nace, "Anty dagaske kin yafe ma yaya? Zaku shirya kenan wayyo dad'i don Allah karki ce mun ba azahiri bane"


Dariyar tayi itama tana bud'e dakinta muka shiga tana cire mun yar hijab d'ina da bata wuce guiwar hannu ba, tace "sha kuruminki yar lelen Antyn ta, duk komi da kikaji kika gani zahirine ba mafarki kike ba"


Sake makalkaleta nayi ina jin dad'i har cikin raina, domin dai ina son ganin farin ciki acikin gidan mu bama dai akan fuskarta.


Ta taya ni na cire kayan ta bani towel na d'aura muka shiga ta had'a mun ruwan wanka saida na shiga cikin shi sannan ta barni tatafi, sadda na fito ta aje mun wasu kananun kaya riga da siket rigar zanzaro ake da ita cikin siket d'in, sannan bai kai har k'asa ba kamar dai tree quarter kayan sunyi bala'in kyau harda belt baki a siket d'in, shikuma siket d'in red ne sai top d'in mai dogon hannu fara sol, na saka pant da bra sannan na saka top din ta kamani sosai yadda har Boob's d'ina suka fito sosai tubarkallah, Anty ta tayani nai stocking da yake kaina kutaccene ta gyara mun shi ta tubke mun jelar har gadon bayana, sannan tayi mun rolling da babban veil daya sauko ya rufe mun kirjina ta gyara mun fuskata nai kyau sosai, nace "Anty daman kin iya kwalliya har haka meyasa bakyayi"


Murmushi tayi tace, "to bagashi yau nayi ba kuma zan cigaba dayi don yayanki yana son kwalliya"


Na rausauyar dakai kurin sannan muka fito naje na sanya takalma hills da suka dace da kayan dake jikina, tace "zaki ci abinci ko sai mun je mun taroshi"


Nace "inajin yunwa Anty, ki d'an lasa mun kayan dad'in can kafin mu dawo"


Dariya tayi mun tajani mukaje bud'e duk womers din tayi da bowl bowl d'in dake wajen, wani kafirin miyau na had'iye saboda yadda abubuwan suka saka miyauna tsinkewa, zama nai ina cewa zuba mun wannan.


Atakaice dai saida na kusa k'oshi sannan muka fito, muftahu ne zai jamu zuwa airport d'in tare da ayarin mota uku kacal, muka doshi tashar jirgin saman kafin mu k'arasa saida Anty ta sai flower da zata tarbesa da ita, raina fes Yaya zai samu tarba ta musamman daga Anty, sanda muka iso saura minty biyar jirgin ya sauka muka tsaya inda kowa ke tsayawa kafin saukar tasu, duk na zak'u inga yaya don kusan watan sa daya da sati baya gida duk banjin dad'in rashin ganin sa na yan kwana kin ba, ina can ina tunani na na hangosa tun daga nesan na ga yadda yai wani irin kyau da haske, idonsa bakin Glass ne yai masifar yi masa kyau ya ratayo wata jikka yana sanye da suit mai three pieces ya rik'o yar ta saman ga hannun sa,k'agare nake ya k'araso inda muke naje na rungumesa ba k'adan nayi kewarsa ba, aiko yana isowa guard d'insa suka je suka anshi abubuwan dake hannunsa banyi wata-wata ba na ruga nai masauki cikin k'irjinsa, had'emu yayi da Anty Ya rungume tsam ajikinsa, fuskarsa kad'ai zata nuna zallar farin cikin dayake ciki janyo ni yayi gefe yana kallona sai kuma ya juya ya kalli anty, kowa murmushi ne a kan fuskarsa kasa cewa komi yayi har muka k'araso wajen mota, gaba na shiga na barsu baya da Anty don naga yadda ya kama hannunta ya k'wak'ume, har raina naji kishi amman na danne don nasan yana cikin sauk'in ganinta a yanayin da bai zata ba.


Can k'asa naji yace mata, "kinyi surprising d'ina Nawwara"


Banji ansarta ba amman nasan murmushi take masa ya sake cewa

"Please kici gaba da kasancewa a haka har abada, yau kin mun kyau sosai pls ki cigaba da yin irin wannan kwalliyar,sannan fad'a miki ne banba zamanki cikin k'unci yana k'untata mun don Allah ki cigaba da farin cikin ki"


Ba tace masa komi ba ta dai lafe jikinsa shi kuma bai wata-wata ba yasaka hannayensa ya rungumeta, wani abu nakejin ya tokare mun mak'oshina yaki wucewa zafi nakeji a raina da tsananin Kishi, watau ni duk kwalliyar da nayi baigani ba ta matarsa kawai idonsa ya gani, bakin sa ita kurin yake iyama magana kenan? Duk yadda raina yaso karya b'aci na kasa control d'insa, amman nayi bakin iyawa ta na danne ban sake jin maganarsa ba har muka iso cikin gidan, hankalin sa ma baya kaina nai sad'ab-sad'ab na shige cikin gidan dakina kawai na wuce don in basu space, yau ba tani yake ba sahibar sa ta sauko ta huce ta ita yake yi.


Ji nai duniyar ta mani zafi duk yadda nake son shirin su ashe azahiri abun bazai mun kyau ba, ashe yar dad'in da muke dashi don bata bashi kulawa ne, kenan yanzu idan hakan ta d'ore ni banida sauran amfani kenan? Sai kawai na kama kuka saboda aduniya ina tsananin kishin sa, ba abunda yake saurin raunana zuciyata kamar inga ya juya mun baya, shi baya son nayi masa amman ni donme ya kemun bacin yasabar mun da kulawar sa tattalinsa shagwabawar sa, shine yau d'aya don yaga canji zai gujeni ban san iyakar lokacin dana d'auka ba bacci ya kwasheni.............


********


Kwana ki sunyi ta tafiya gabaki d'aya yaya ya canza mun, ba wai baya mun magana bane ko baya sakar mun fuska ba Aa yadda dai yake ji dani ada yanzu ba haka bane, Anty Nawwara ta kanai naye sa zan iya cewa sai abunda tace sanna zaiyi mun, rabon dana zauna ma ko kusa dashi na mance ko makaranta zanje yanzu driver aka ware mun na daban shi kadai yake kaini ya dauko ni, idan abu nace masa ina so zai kira muftahu ya had'ani dashi muje in siyo gaba d'aya canjin ya daman, ban saba dashi ba shiyasa duk na zama wata silent sosai duk da daman banda wannan hayaniyar amman na sake zama shiru-shiru, ita kanta Antyn inba lokacin cin abinci ba bata nemana tana can tare dashi, idan abun ya daman sai inyi kuka kozan samu sauki.


A wannan halin da nake ciki wannan yarinyar ta school d'inmu wadda har yau ban san sunan ta ba tayi galaba akaina, ta shawo kaina da kulawar ta da jana ajiki da kalamanta masu taushi, har mamaki nake karamar yarinya ta iya janye hankalina kanta, yanzu muna fira da ita sosai yadda na dauke ta mai dagin kai da isa da sauki, duk da ta bayyana mun cewa ita yar gidan wazeeri ce wazeerin sarkin Abuja banyi mamaki ba don yana yinta ya bayyana hakan.


Mun samu hutun interval na tsakanin weac da neco, yanzu mun gama weac nan da sati uku zamu fara neco ranar ba dad'i muka rabu da *Sadiya* sunan ta kenan, har ta bani contact d'inta in nasamu waya na kirata.

Tunda muka fara shiri da ita ban tab'a kuskuren bata labari na ba, duk yadda take bani labarin *MASARAUTA* da labarin gidansu yayyunta mata da maza ni ban tab'a kuskuren furta mata wani abu daya shafeni ba, itama kuma data fahimci ban shirya gaya mata komi akaina ba sai bata tab'a tambayata ba.


Muna cikin tafiya nida driver na munyi shiru daman kuma bamu saba yin fira dashi ba, sai ta kama idan abun maganar yazo ko yaya ya bashi sak'o wajena ina can ina ta tunani da sabuwar rayuwar da na ke fuskanta agidan namu saidai naji k'iiiiiiiiiiiii.............habibu driver yaci uban burki da mugun karfi har saida goshina ya bugu da kujera, ban ma dawo hayyacina ba naji an bud'e inda nake anyi mun wata irin fizga an jefa cikin wata jeep an bar habibu anan ni kuma kan kace me sunyi ciki dani, kwalwata nan take ta dawo aiki dana gane dai kidnapping d'ina akai, ai saina daddage na wage dan bakina na fasa wata gigitacciyar k'ara don neman d'auki,wata irin mangara aka kai mun kaina ya bugu da kofar motar, sannan mutumin ya yago salatif ya dad'e mun bakina sannan ya murgud'eni ya tattaro hannuwa na ya daure da wata igiya, fuskar sa rufe da Mark's yace "to kiyi ihun sosai tare da haure hauren"


Duk da abunda yai mani ban daina shure-shure da ihuba amman bamai gane inayi, su biyu ne guda yana jan motar guda kuma shi ya fincikoni ya jefo cikin motar, tun ina ihun da neman mafita har na hak'ura saboda dai bama maijin abunda nake yi, kuka kau idona har ya k'afe, na koma na takure kaina waje guda.


Mutumin yai dariya yace, "kinji uwar bari ko"


Basan iyakar nisan tafiyar da mukai ba bacci ne ma yasace ni mai nauyi baccin wuya don nasha kuka ga yunwa.


********


"Yallab'ai nifa tsoro nakeji kar agane mu, idan oga yaji mun sato yarinyar nan ransa zai b'aci sosai"


Ishaq dake tsaye bakin window da cup d'in coffee hannun sa yana siffing gudan hannun kuma cikin aljihun wandon sa, ya jima baice komi ba kamar ma baiji abunda sa'id yace masa ba zuwa can yace,


"Duk abunda nake ina sane karka dagula mun lissafi,inhar ba kai zaka gaya masa meye na sanyo sunan sa idan ba zaka iya aikin nan dani ba kofa abud'e take"


Cikin girmamawa yace, "kayi hakuri yallab'ai ba wai ina neman kware maka baya bane, na tuna maka ne ko ka mance da gargad'in da yayi mana"


Juyowa yayi yana aje cup d'in saman table d'in dake wajen yace, "ina sane duk abunda zan na riga na tsara shi, kana gani dai lokaci jaa yake cikin lokutan da aka bamu, idan banbi wannan hanyar ba ta ina kake son mu fara"


Sa'id din yace, "Haka ne yallab'ai Allah ya bamu sa'a,bari na kai mata breakfast sai na d'an fara tab'ata inji, idan na kasa zan yo maka waya"


Jinjina masa kai yayi sannan yace, "zan je gida na d'anyi bacci kwana kin nan banda natsuwa ko kad'an"


Sa'id din yace, "yallab'ai aganina karka yi zurfin ciki ka cuci zuciyarka akan abunda kake so saboda wata"


Murmushi yayi yana cewa, "bari naje saina jika karfa kayi mata da wasa"


Girgiza kai kawai sa'id d'i yayi yana binsa da kallo Ishaq jarumin gaske ne, yana da juriya akan komi ba kowa ke iya gane halin da yake ciki ba sai shi, shima d'in a kaikaice yake ganewa baya son bayyana wacce yake so saboda *KARAMCIN* ummi, ya gwamma ce ya saka zuciyarsa acikin k'unci akan ya zabi abunda ransa ke so.


Idon sa har yana kullewa a haka ya samu ya iso gidan, wanda ya kwana wajen uku bai zo shi ba yana can yana fad'i tashi da wannan case d'in, ga shi baison had'uwa da Sofiyya saboda shi kanshi hukuncin daya yanke masu idan ya kalleta yana jin wani irin rauni da mugun tausayinta yana dirar masa a zuciya.


Yana kunno kan motar cikin get d'in gidan ya hango Bilkisu ta fito cikin shirin tafiya makaranta, d'an lumshe idonsa yayi yaja iska sannan ya gama parking ya fito ya ga suna magana da driver dake kaisu makaranta, yana yin tafiyar tashi kad'ai inka gani zaka san agajiye yake kuma yana cikin son bacci, isowa yai wajen su cikin girmamawa driver ya gaidashi ya ansa mashi Bilkisun tana jujjuya wayarta tace "Yaya ina kwana"


Idonsa a lumshe yace, "lafiya, menene naga kunyi cirko cirko"


Kanta k'asa tace, "daman makaranta zanje shine yace motar tayi faci jiya daya dawo da sofiyyah"


Mik'a mata key d'in yayi yace, "zaki iya kai kanki?"


Tana d'an murmushi tace, "Yaya ban wani kware ba"


Jefa mata yayi ta cafe yana cewa, "idan baki hawa yaushe zaki kware inkikai wasa kanwarki zata rigaki iyawa"


Murmushi take tayi tace, "nagode yaya saina dawo"


Yai gaba yana cewa, "Allah ya bada sa'a"


Yai cikin gidan har baya gani sosai so kawai yake ya ganshi kwance kan gadon sa ya saki Ac, yana sallama main falon sukai kicib'is da Ummi ta fito dakin Baffa,

Tace "Na dauka munyi maka wani gagarumin laifi ishaq"


Murmushi yake ya zauna cikin kujerun falon yana gaidata yace "ba wani laifi ummi wlh aiki ne kawai, yanzu ma bacci na gudo inyi idona har yaji yake"


Tace, "to Allah ya kyauta, ka isa ka kwanta zan saka Sofiyyah ta had'a maka breakfast kafin ka tashi,ni ma fita zanyi faisal aka kwantar asibiti jiya ulcer shi tatashi zanje ganin sa"


Yace, "munyi waya da Abban ai sai dare na lek'a inba asallame shi ba, in kuma an sallamai naje gidan"


A haka suka rabu ya wuce dakin shi huncewa yayi dagashi sai gajeren wando da singlet ya saki Ac ya hau bacci, kwalwarsa na sake tuna masa ummi bata nan sofiyya ce kawai agidan, hakan dama ce ya samu zai kuma yi amfani da ita sai ya cigaba da baccin sa............