HASKEN MAKAFI

10

by @mommuhseen

🅿️........10


Tun daga lokacin da Habibu ya iso a fujajan ya sanar dasu halin da suka shiga komi ya tsaya agidan, tashin hankalin da basu saka mashi rana ba tun rana har wayewar gari ana abu guda.


Saboda yadda taga ya gigice ya d'imauce akan b'atan Fatima dole ta sa takeji aranta kamar bata kyauta ba, amman sai ta maze tana k'ok'arin control d'insa duk yabi ya tada hankalin jami'an gidan, shikau habibu bawan Allah yasa an daure shi kamar goro yace idan bai fad'o sunan no din motar ba saiya cire masa gabar hannu, waya yake bugawa daga ya kira wannan sai ya kira wannan, kallo daya zaka yi masa kasan ya haukace ma gaba d'aya domin kwata-kwata shi ba wanda yake zargi, saboda duk abokan gabarsa suna kurkuku daure ba zasu samu damar yi masa wannan aikin ba, rashin sanin wanda zai iya masa wannan aikin shiya gigita shi ya fitar dashi hayyacinsa, kowa na gidan a tsorace yake daya motsa zai taso kamar zai mari Nawwara yace, "duk keki jaa komi, kece umulaba'isin haddasa wannan aikin, kin kanai nayini kin hanani kulawa da yarinyar da nakeji da ita fiye da zinari, duk don na samu abunda nake so tattare dake na biya bukatata, to gashi nan"


Jikinta yai bala'in yin sanyi kalau tace, "kayi hakuri banyi da wata manuf...........Nawwara ki rufen baki kafin na hau kanki, karki nemi cewa komi kin rabani da Jelly hankalin ki ya kwanta...............karka mun muguwar fahimta bafa ni na sace Fatima ba, sadda aka saceta ban sani ba na sandai taje makaranta"


Huci kawai yake fiddawa yana safa da marwa acikin compound d'in gidan, ya joyo a fusace yace "muddin ban samu Jelly ba bake ba duk wanda ke gidan nan yashiga uku ya lalace."


Ya juya a fusace yana kwalama muftahu kira,aguje ya taho yana bud'e masa mota ya shiga, kai tsaye yace "police station zamu"


Ba tare da b'ata lokaci ba ya tashi motar su kad'ai suka fice kamar walk'iya, kafafunta har rawa suke sadda take saurin shiga cikin gidan, wayar ta kawai take son isa inda take kwata-kwata ba haka taso ba inhar asirina ya tonu bata san irin gallazawar da ABU ZAYYAD zai mata ba,karshe saiya nakastata.


********


Kasancewar duk wayoyin sa yabi ya kashe ba wanda ya dame sa da kira har yai baccin sa na a wanni ya tashi yana jin pressure dake bisa kansa ta ragu sosai, mik'a yayi yana salati ya kalli agogo yaga karfe shad'aya ta gota wayarsa k'arama ya kunna sannan ya barta ya shiga toilet ya fara sakar ma kanshi ruwa, wanka yayi ya fito ya fara shiri cikin natsuwa kananun kaya ya fiddo masu kyan gaske rigar dark purple mai dogon hannu mai links, wandon kuma black ya gyara kanshi ya sanya kayan yai feshin turare masu dad'i k'amshi,yana cikin fesawar yaji motsi acan falo kafin ya dawo hankalin sa wayar sa ta soma vibrating.


Kallon no d'in kawai yayi ya gane ko waye, dauka yayi yasa ga kunnensa bai magana ba ya makaleta da wuyansa yana daura agogo ga hannunsa, kamar ba magana ake masa ba amman baice uffan ba karshe ya sauke wayar ya soka aljihu sannan ya kwaso sauran suma yasanya ko wacce aljihu sannan ya nufi fitowa.


Baiga kowa ba ya duba ko ta kawo masa breakfast d'in amman bai gani ba, ga yunwa ya tashi da ita sai ya fita xuwa can cikin gidan kitchen yaji motsi sai kawai yaji ransa ya biya daya je can, duk da suna da y'an aiki kila wata ce a kitchen d'in amman jikinsa na bashi Sofiyya ce.


Oat ce ta dama tana motsawa ta saka suger da madara, ga soyayyar indomie da kwai ta juye ga plate sai ferfesu dake saman wuta yana idasa dahuwa, bai shiga ba daga bakin k'ofa ya jingina kafadarsa side guda ya rungume hannuwan sa yana kallonta, Allah kad'ai yasan meke cikin ransa amman kana kallon idonsa zaka fahimci wani abu.


Yadda take aikin a kasalance ya dauki hankalin sa bayanta yake kallo daga kanta zuwa kafafunta, d'an lumshe idonsa yayi ya bud'e kafin yaja iska kadan ya cigaba da tsayuwarsa.


Haka nan taji jikinta yana bata ana kallon ta, dakata wa tayi da aikin amman bata juya ba kafin taji zuciyarta tana bugawa wani k'amshi ya shigar mata hanci, da sauri ta zaro idanun ta sannan ba shiri ya juya idonta akan sa saurin juya wa tayi ta kashe gas d'in sannan ta juye masa ferfesun a d'an bowl, d'an tire ta dauko ta jira kayan a sama ta bud'e frig ta dauko masa ruwa ta saka empty cups guda biyu sannan tajiyo tana kallon sa gabanta yana fad'uwa.


Kasa tayi da kanta cikin siririyar muryar ta tace, "gashi nan tun d'azu nake kokarin na gama, naje na lek'a baka tashi a bacci ba"


Duk a duburce take yin maganar ba abunda yake kallo sai fuskarta, ta rame sosai bama kadan ba idonta yayi ca ciki fuskarta tayi wani fayau kamar tayi ciwo abunka da fari, yar ajiyar zuciya yaja yace "dauko mun ki fito"


Ya juya ya tafi saurin dauko tiren tayi tana bin bayansa ganin ya nufi falon sa, sai tabisa har can d'in da sallama ta shiga yana tsaye duka hannunwan sa acikin aljihun sa, yana kallon k'asa jiran karasowar ta kurin yake.

Saman babban center table d'in falon ta aje tiren tana kallon sa yana jin ta aje ya dago ya sauke idonsa akanta, ita kuma tai saurin sunkuyar da kai tana murza zoben ta takasa tafita, don tasan magana zai da ita amman shegen miskilancin sa bazai barshi yayi abunda zaiyyi tatafi ba.


Sai ta yanke shawarar tafiya cikin hanzari ta nufi k'ofa ko taku uku batai ba taji muryar sa ta dirar mata yace, "Bakiji ba"


Har zuciyarta saida ta tsaya na y'an seconds kafin ta juyo kamar wata yar yarinya tace, "Ni"


Lumshe idonsa yayi tare da jinjina mata kai alamun ehy ita d'in yake magana, kamar wadda k'wai ya fashewa aciki take takawa zuwa garesa ganin nawarta yayi kafin ta iso shi sai ya taka suka had'e, cak ta tsaya tana sadda kanta k'asa aranta tana cewa meke shirin faruwa da ita yau, bacin ta riga ta gama jinyar zuciyarta ta kuma yanke hukunci............a bazace taji ya dago hab'arta idonta ta ware akansa tana had'iyar wani busashen miyau, tuni muryarsa ta canza lokaci guda idonsa cikin nata da tattausan lafazi yace,


"SOFIYYAH!!!"


don dole ta kawar da kanta daga kallon sa tace, "Na'am"


Ya fesar da huci ganin tsayuwar ba tayi yajata kurin suka zauna kan kujera two seater, jikinta ya fara kerma saboda hakan bakon abune wajenta.


"Meke damunki? Karki mun karya na gani acikin idonki, sannan fuskarki yana yinki ya bayyana mun halin da kike ciki"


Mai neman kuka ne aka jefesa da kashin awaki, dan danan sai kwallah sharrrrr suka fara zuba, tasaka fuskarta cikin tafin hannunta tana yar shashsheka, me za tace masa ya dameta? Bata da bakin magana hankalin sa ya tashi, ya rasa yadda zai mata baya son kukan ko kad'an, sake kiran sunan ta yayi cikin Raunanniyar murya.


Ya ce, "Sofiyyah ba kuka na tambayeki bafa"


Kasa daina kukan tayi saboda duk sadda yai mata magana zuciyarta sake yin Rauni take, ahankali ta fara rage kukan tana jan ajiyar zuciya hank chef dinsa ya zaro ya bata k'in ansa tayi, yace "baki so kenan"


Sai lokacin ta ansa tana ida tsane fuskar ta bashi yace, "kin shirin rasa wani abu naki mai muhimmanci ne?"


Bata dago ba kanta yana k'asa muryar ta takoma yar karama saboda kukan da tasha tace, "nama rasa ai"


Lumshe idonsa yayi kadan yace, "meyasa biki gaya mun ba"?


Sai lokacin ta kalle sa suka had'a ido taga yadd nashi suka canza kala, ya sake cewa "kinfi sha'awar kibar damuwa aranki bakizo mun rabata tare ba?"


Wani abu taji har cikin ranta, ashe yasan halin da take ciki meyasa shi bai tab'a nuna mata yasan me take nufi ba, saida bakin alk'alami ya bushe, muryar ta na rawa tace "Daga gareka ne, domin baka bani damar hakan ba"


Saidai taji saukar maganar cikin kanta batare data shirya ba taji yace,


"Inajin tsoron in rasaki Sofiyyah"


Bashiri tadago tana kallonsa, lumshe ido yayi yana jinjina mata kai sai taji gaba daya jikinta ya mutu murus, wasu zafafan hawayen suka silalo mata bata damu data share ba tace, "Abunda yasa ni cikin damuwa kenan nima, shiyasa har kaga hakan cikin idanuna da fuskata domin nima inajin tsoron abunda kakejin tsoron"


Tana kallo ya sark'e hannuwan su waje guda su duka bin hannayen sukai da kallo, kafin suka kalli fuskokin juna har sannan kwalla na fita daga idonta, muryarsa tayi sanyi sosai da sosai yace "BAFFA ya riga yayi mun zab'i Sofiyyah, amman saboda karya tauye mun hakki shine ya bani sati biyu akan na kawo mashi zab'ina, ni kuma inajin tsoro da shakku"


Tana jan majina wasu hawayen suna zuba bata kallai ba tace, "ka mance baya ka tari gaba domin gaban itama Alkairi ce agareka"


Bata tab'a zaton ganin abunda ta gani ba, hannunta dake cikin nashi taji wani abu mai zafi ya d'iga a sama, a zabure take kallon fuskar sa zuciyarta kamar zata dako tsalle ta fito, muryar ta da alamun son fashewa da kuka tace "Yaya karka idasa karya mun zuciyata, bacin d'an karfin dana aro na sa mata acikin kwana kin nan, shin idan ka zubda hawayen ka ni me zan zubar kenan"


Hannunta dake cikin nashi ya matse sosai sannan yakai bakin sa ya sumbata, har ranta taji abun ta dago tana kallon sa saida ya bari suna kallon juna sanan cikin wata irin murya mai kashe jikin duk macen da ta saurareta yace,


"ina sonki sofiyyah"


Murmushi take sannan kuma ga hawaye suna zubar mata, ta lumshe masa idanun ta tace "nima Ina sonka yah ishaq, amman yar uwata ta fini sonka bazan iya aurenka ba na barmata"


Wani rikitaccen kuka yazo mata ta durkushe tana rera abunta mai ratsa zuciya, janyota kawai yayi yasa cikin kirjinsa don baisan abunyi ba, ji yake da zai iya bud'e kirjinsa ya sata ba wanda zai sake ganinta, hakika suna cikin rad'ad'in kaunar juna amman su duka dole zasuyi *SADAUKARWA*, sosai take kukan ajikin sa cikin kirjinsa yayin da numfashin ta yake dukan fatar kirjinsa, yana huda masa zuwa zuciyarsa hakika yana son sofiyyah kamar yadda ya yarda da son da take masa.


Sunkuya wa yayi da kanshi wajen kunnenta cikin salon kauna yace, "kibar kukan haka nan, idan ya wuce haka zan iya komi don inga kiyi shiru"


Difff kakeji kamar ruwa ya dauke tayi shiru a jikinsa kafin ahankali ta tashi tana ta soke kai k'asa, ajiyar zuciya yayi ya sauko da tiren kasa yana hada oat d'in ya fara sha, ganin zata lallab'a ta fece yasa shi saurin cewa "karki tafi kibarni"


Kunya ce duk ta kamata ta kasa cewa komi ta zauna inda take, har saida ya gama cin abunda zaici sannan yaje ya wanke bakin sa ya dawo, inda take ya koma ya zauna yana kallon ta yace "jinai yunwa zata kayar dani shiyasa"


Rausayar dakai kurin tayi, ya sake matsowa yana lek'ota yace, "jinake bazan iya hakuri dake ba zan gaya ma Baffa cewar yarsa sofiyya ta hanani sukuni azuciyata"


Boye fuskarta tayi cikin tafukan hannayenta shi kuma yasa hannu ala dole saita cire hannun, yace "don Allah kibarni yau in kalleki in more, karki hanani"


Kalaman sa ba kadan ba suke sata jin tana shawagi a samaniya, ji take ma kaunar da take masa tafi ta kullin, tana wasa da hannun ta tace "ummi tana gab da dawowa, Antyna kuma nasan tana hanya"


Kunnenta ya kama yace, "wacece antyn taki?"


Yar kara ta saki cikin salon soyayya tana rik'e hannun nashi tana rokon ya saki karya cire mata kunne, yace "watau har ta zama antyn ki ko"


Kwallah ta fara masa dole ya saki kunnen yana tallabo fuskar tata cikin so yace, "I'm sorry da zafi ko?"


Cikin shagwab'a take d'aga mashi kai, share mata kwallar yake da hannun sa yace "it's ok bazan sake ba, yanzu yaushe zamuje yawo"


Zaro ido tayi tace, "yaya Ishaq saidai da Bilkisu"


Shan mur yayi yace, "tunda dai ba yaune aurena da ita pls kidaina inaso ko yaya na ringa tuna moment d'inmu"


Kanta k'asa tanajin wani d'aci saboda tunawa da tayi cewar ba zasu tab'a samun juna ba,ta goge kwallarta tace "duk sanda ka samu lokaci"


Riko hannuwanta yayi cikin kauna ya sassauta muryarsa yace, "muddin zaki cigaba da kasancewa cikin kunci da damuwa akan haka, to bazan saurari zuciyata ba sadda zan sanar da Baffa da ummi cewar muna son junan mu, inhar kin iya kauda kai kin saka dangana bazan sanar da kowa ba amman inkika cigaba da kuka,............kema kin sani"


Har saurin goge fuskar take tace "na daina to"


Ya lumshe mata idonsa sannan yace" good my love, dauke kayan zan fita yanzu komin dare zan nemeki"


Tace, "komin dare kuma?"


Murmushi yake yace, "yes komin dare ko bazaki fito ba"


Idonta duk awaje tace, "Bilk............saurin rufe bakinta tayi ganin zai dille mata shi, ta rausayar dakai tace"to to zan fito"


Saida yaga fitatar ta sannan ya yashi yashiga ya gyara jikinsa ya fito da wani mukullin tunda baiji dawowar Bilkisun ba.


*******


Tunda na bud'e ido na ganni a wannan d'akin duk inda hankalina yake ya tashi, kwalwata ta sake tariyo mun abunda ya faru dani har zuwa yanzu wata kara na fasa ina fashewa da kuka da neman d'auki amman banga alamar ma anajina ba don daga tagar d'akin har k'ofar jingim suke, ga fitsari inaji ga yunwa inaji ga jikina yayi tsami har wari wari naji inayi saboda rashin wanka, ban sa waye zai aikata mun wannan aikin ba nasan sai bazai rasa nasaba sa yaya ba ta dalilin sa ne akai mun wannan aikin, haka nai ta kuka ina adduar Allah ya kawo mun d'auki, adaidai lokacin ne naji an bud'e k'ofar anshigo a firgice na tashi ina raba idanu, ganin mutum nayi rabin fuskarsa a rufe ya aje mun kayan breakfast da iyakar karfina na ingijesu ina kuka nace, "bazan ci ba sai ka maidani inda ka dauko ni, menai maku mekuke so dani?"


Tsawa ya daka mun yana cewa inyi masa shiru,kin shirun nayi na ringa ihu ina harbe harbe duk na watsar da kayan dake cikin tiren, wajen halbe-halben na halbo plax din ruwan zafi ya zube mun ga k'afa wata azaba ta xiyarci kafar tawa har cikin raina wannan zafin, ihu nake ina kuka ina rik'e da k'afar duk iya kokarin sa na ganin ya saitani abun yaci tura, ya dauko tsumma ya daure mun bakina ya daure hannu na, ina gani jikinsa har rawa yake ya fice ya sake kulleni, hawaye kawai nake ga azabar da k'afata take yi don sosai ruwan zafin ya k'onani na gaji da kukan bacci ya sake sace ni ban sake farkawa ba.


Sa'id hankalin sa tashi yayi saboda ganin wannan haukan duk zaton shi yarinyar aljannu ne da ita, kiran Ishaq yayi wanda yana hanya dawowa nan gidan bai dauki wayar ba saboda ya riga ya shigo get din, jiran sa yayi har ya shigo yana isowa yace jikinsa yana rawa, "yallabai yarinyar can kilan aljannu gareta, kaga wai yadda ta ringayi mun, ni tsoro naji na daure bakinta na fito duk kayan breakfast din nan yallabai ta wargazasu yadda kasan yar dambe ce, anya bai koya mata wrestling ba kuwa"


wani kallo da yake auna mashi shiya sashi yayi gum da bakin sa yana sosa kai, yace "Allah ya baka hakuri yallab'ai ka shiga ka ganta har k'onewa ma tayi ga k'afa sosai wallahi"


Ko Mark's d'in bai sanya ba ya nufi d'akin kai tsaye saidai wata irin dokawa da zuciyarsa tayi bai tab'ajin hakan ba, dakata wa yayi yana ambaton sunan Allah sannan ya murza key din ya shiga, inajin an bud'e kofar nai firgigi daga baccin da nake tumin dana gani gabana tsaye saida kirjina ya doka sau ba adadi, kallon kallo mukeye dashi ko 'kefta idona na kasa shima kamar zai cinyeni da kallo, zuwa can ya iso har gabana sosai ina ta kallon sa yazaga da hannunsa ya kunce mun bakina, wani nishi na fitar ina ajiyar zuciya muryata ta sik'e saboda kuka nace, "don Allah ku kaini wajen Yaya ni ban muku komi ba, ku sakeni na tafi wajen ya..............shiiiiiiiiiit yayi yana dora yatsa ga bakinsa alamun nai masa shiru, kwarjini yayi mani na kasa cigaba da maganar ya kalli yadda nai waja waja da kayan breakfast d'in, ya maido idon sa kaina ya daure fuska tamau har saida naji gabana ya fad'i yace,


"Watau tarbiyar daya baki kenan tayin watse da abinci ko? Wani nacan yana kwana da yunwa ke kin samu har watsi kike dashi ko!"


Ya dakan wata tsawa da saida naji tsari yana tsilalo mani don daman ya mugun kamani, kuka na sake rushewa dashi yace, "keep quite!"


Ya sake dank'ara mani wata tsawar jikina ko ina rawa yake, tunda uwar data haifani ban tab'ajin tsawar data gigitani irin haka ba bayan ta yaya, hakora na har gamewa suke ya kalli k'afata dana k'one tayi jajir kamar an shafa fenti, ya dalla mun harara yace "idan kina son kanki da arxik'i duk tambayar danayi miki direct answer me kinaji na"


Majina da hawaye suka game waje guda na gyada kai tashi yayi yafita kuka na cigaba dayi saboda dai nasan yau kwana kila sun k'are, wannan yafi wancen azaba da mugunta, duk naji na tsani jikina ga fitsari ga daud'a ga zufa ga rauni ga ga ga ga din tayi yawa, burumm naji ya banko k'ofar ya dawo shida wannan na farkon sake durk'usawa yayi gabana ya aje maganin shafawa ciwona ya zaro bindiga itama ya aje, wani kulululu naji cikina ya bada sautin sa na had'iye wani kafirin miyau kallona suke kawai, yace "zab'i ya rage naki ko ki amsa mun tambaya ko bullet d'in dake cikin bindigar nan gida d'aya ya ratsa kanki, in kika amsa mun kuma ga maganin zafi nan na shafa miki ga ciwon ki"


Hawaye da majina kawai nake ja zuciyata kamar zata fito waje, sau biyu naga bindiga a rayuwata yau da kuma ranan nan na sake hadiyar busashen miyau, muryata tama dishe sosai nace masa cikin rauni da marairaita.


"Bawan Allah ka ceci rayuwata banda kowa sai YAYA tunda na taso rayuwata bansan komi ba sai dabbobi da namun daji, dasu nake rayuwa kwatsam Allah ya jefo mun YAYA acikin rayuwata tun ban kai haka ba ya dauko ni yake d'awainiya dani, dukkan wani jin dad'in rayuwa yana bani cikin bani yake,ya fifitani fiye da komin sa yana sona fiye da kanshi duk abunda na nuna zai bani har wanda ban nuna ba, ni bansan wacece ni ba ABU ZAYYAD shi kadai zan iya nuna wa ince nawa, kuma aduniyar nan bayan shi bana jin akwai wanda nake so a rayuwata, Bawan Allah ABU ZAYYAD yafi mun uwata yafi mun ubana yafi mun duk wani mahaluki dazai nuna kanshi yace shi nawa ne, zan iya bayar da rayuwata dominsa duk da yadda nake son rayuwar tawa, nasan me kake sonji daga bakina bai wuce na fallasa maka sirrinsa ba saboda ka sami hujjojin dazaka kama shi, tabbas ya cancanci a hukuntashi amman kayi hakuri bawan Allah bakina bazai iya fad'ar kalma guda dazata tona masa sirrin sa ba, Abu guda zan iya cewa game da YAYA shine ABU ZAYYAD babban mai laifi ne daya kamata hukuma ta kamashi ta hukuntashi, amman bazan iya gaya maka abunda ya wuce wannan ba, kuma ko kad'an bana jin haushin abunda yakeyi domin yadda yake kulawa da rayuwata dani kaina.................yake dai koya miki salo-salo na iskanci"

Cewar sa'id dake tsaye yana daukar abunda take cewa, wani kallo ishaq ya jefesa dashi dole yai shiru kallon sa nayi nace cike da rashin kunya "Kwartanci yake koya mun kaji k............dagewa yayi cicin karfin sa ya dalle mun bakina wata kara na fasa ina dafe bakina na saki kuka saboda zafin daya ratsani, yace mun "Gaban hukuma kike idan kika sake fad'ar wata kalma marar dad'i zan zubar da yan iskan hakwaranki"


Kuka nai tayi sosai ina cikin kukan ya fizgi k'afata yana shafa man zafin, wulle-wullen da nake ya sashi dauko bindigar yana dora min ga kai, ba arxiki nai tsit har ya gama shafawa sannan ya kunce ni daurin hannun da akai mun, ya tashi yace "kafin na dawo tas nake son ganin wannan wajen"


Ya jefa mata wata leda ga fuska yace "kiyi wanka ga toilet nan ki canza kaya kiyi salolinki daga na jiya zuwa na yanzu"


Sa'id ya bi bayansa suka fita suka sake sa mata mukulli.