{70..}
Wajen ƙarfe goma Hajar ta sauko downstairs ta ɗauki sweeper da packer ta wuce room dinta, sai da ta share room dinta snn ta fito corridor shima ta share daga nan kuma tayi ƙasa, tass ta gyara ko ina yayi fess snn ta zuba turaren wuta a burners tabi kan hayaƙin da freshener mai sanyin ƙamshi, saida ta gama gyara gidan snn ta shiga kitchen ta dafawa kanta breakfast taci, shima kitchen din ta gyara sa bayan ta gama amfani dashi, room dinta ta koma ta kwanta gefen gado, sosai bayanta ya riƙe don aiki tayi tuƙuru mara algus, a hankali ta tashi ta ɗauki wayar aron daya bata ta koma ta kwanta, har wani fargaba ta ringa ji tana tsoron kiran Umma, da kyar dai tayi shahada ta kirata, har suka gama waya da Umma ba taji wani canji ba, Hajar ta sauke ajiyar zuciya tana jin daɗi har cikin ranta knn Anty bata gayawa Umma ba, bayan Hajar ta idar da sallahr Azahar ne ta sake sauka downstairs, direct kitchen ta wuce, tsaye tayi ta jingina da cabinet tana tunanin me zata dafa, at last dai ta ciro froze chicken daga freezer ta fara girkin, before 3 na rana ta gama girkin, wata irin aroma ce ta bulale girman kitchen din, wasu sabbin warmers ta ciro daga kwalinsu ta wanke ta zuba abincin, bisa kitchen island ta jere warmers din, ta juye ragowar abincin a plate da haka kuma ta kimtsa kitchen din ta fita. Sai ƙarfe biyar Nurain ya dawo, kana ganinsa kasan he is exhausted, ɓangarensa ya wuce ya ajiye briefcase din hannunsa, refreshing kansa yayi ya fito daga bathroom yana goge sumarsa da towel, yana gama shirya kansa cikin ƙananan kaya ya fito corridor yana jan rigarsa, kallon few seconds ya yiwa ƙofar ɗakinta kafin ya sauka downstairs, kitchen ya shiga zai dauki ko da fruits ne yaci kafin anjima ya wuce gida yaci solid food, idonsa akan warmers dake jere kan island ya fara sauka, ya ringa kallon warmers din kafin ya ƙarasa ya buɗe, aroman data daki hancinsa kaɗai ma ta isa ta ƙara masa yunwar dake cinsa, tini ya manta da wani batun fruits ya dauki plate ya zuba abincin daga haka ya bar kitchen din. ƙarfe takwas na dare Hajar ta fito daga wanka, tayi shafe shafenta ta fesa perfume mai sanyi kamshi, kaya ƴan sawai sawai ta saka don ba kwanciya za tayi ba akwai abinda za tayi a kitchen kafin ta kwanta, ta saka hula ta rufe baƙin gashinta ta fita a ɗakin, walking gently ta sauka downstairs ta shiga kitchen, tana riƙe da door handle ta ƙarewa kitchen din kallo, surely bai daɗe da fita ba don sosai taji pure scent dinsa, taɓe baki tayi bayan ta lura da coffee maker a jone, murmushi Hajar ta saki bayan ta buɗe warmers din abincin taga kaɗan ya rage, daman abincin ba wani yawa ne dashi ba, tayi kwafa har lokacin murmushin beyi fading a beautiful face dinta ba. Nurain na zaune a balcony yana waya da Mr Lee from China, suna gama wayar Nurain ya tashi ya shiga ciki, ba tare da ya cire airpod din dake right ear dinsa da ya gama wayar ba ya buɗe ƙofar kitchen, coffee dinsa ya tsiyaye a mug ya ɗauka zai fice a kitchen din sai kuma ya juyo jin motsi, Hajar ce ta fito daga store da roba a hannunta, da sauri ta saukar da kanta ta ajiye robar kan cabinet, a hankali tace "ina yini", Nurain ya dawo da baya ya jingina da cabinet ya ringa kallonta without blinking, lokaci guda ya cire airpod dake kunnensa still staring at her, tana ɗago kanta sukay ido huɗu, turo baki tayi ta saukar da kanta, knife ta ɗauka ta fara feraye dankalin da ta debo, da gefen ido ta fakaici kallonsa kawai taji wata azaba a hannunta, ba shiri ta saki wuƙar gami da yin ƴar ƙara, da sauri Nurain ya ajiye mug din hannunsa ya isa inda take, riƙe hannun da take yarfewa yayi yana so yaga inda ta yanke, ƙoƙarin amshe hannun ta ringa yi, lokaci guda ya saki hannun nata ya rutsa flat tummy dinta ya ɗorata kan cabinet, ya riƙe hannunta with care, tamkar robot da aka dannawa remote haka ta ƙame, ta ringa kallonsa without blinking, wnn shine karo na farko da tayi masa wnn kallon, yana ɗago kansa sukay ido hudu, suka ringa kallon juna after few seconds Hajar ta janye idonta, zamowa tayi zata sauka yayi saurin haɗe goshinsu waje ɗaya, tayi saurin runtse idonta, ya sauke ajiyar zuciya yace "Please be more careful..." da haka ya janye goshinsa a nata ya dauki mug din coffee da airpod dinsa ya fita, saida Hajar taji ƙarar rufe ƙofa snn ta samu kwarin guiwar buɗe idonta da ta lumshe, numfashi ta sauke tana turo baki ta diro ƙasa, ta duba finger dinta inda ta yanke taga kaɗan ne ma yankan, ko jini babu sosai sai wnda ya tsattsafo yanxu, ta isa gaban sink ta buɗe tap ta wanke ciwon, kasa yin aikin tayi kawai ta buɗe ƙofa ta fita, tana zuwa room dinta ta saka kayan bacci tabi lafiyar gado, uhmm saidai tinda ta kwanta ta kasa baccin juyi kawai take tana naɗewa waje ɗaya tamkar ƙadondoniya, lokaci zuwa lokaci take turo baki ta juya lulu eyes dinta. Ranar Thursday da yamma Nurain ya isa gidansu, yana shiga main palour ya tarar da baƙi, both his paternal and maternal Aunties na zaune palourn da kuma close friends din Maminsa, da ladabi Nurain ya gaishe da mutanen palourn, Mama Mardiyya ƙanwar Abba tace "Uthman ya iyali...?", yace "Alhmdllh" yana shafa kansa, da haka ya tashi ya wuce part din Mami, Sakeena ya tarar a palour tana sealing envelope da aka cika da sabbin kuɗi, Nurain ya ƙarasa palourn yace "wani abun ake ne naga ƴan uwa..?", Sakeena tace "kai komai baka sani ba, yau fa za a kawo lefen Noory", ya waro ido yace "Oh right... Mami ta gayamin", Mami ta fito daga bedroom dinta da 2 notes na kudi a hannunta ta miƙawa Sakeena tace "suma kisa a envelope", Sakeena ta amshi kuɗin tace "Ohk", bayan Nurain sun gaisa da Mami yace "Abba na nan...?", Mami tace "Nope yaje Abuja sai 7 nake jin zai dawo", Nurain yace "Alright". wajen ƙarfe biyar masu kawo lefen Noor suka iso, aka tarbesu da girmamawa snn aka musu shimfiɗa ta fuska da kuma ta tabarma, da suka tashi tafiya ma aka bisu da abin arziƙi. Da daddare wajen ƙarfe takwas Mami na zaune main palour tare da Sakeena, ga uban kayan lefen da aka kawo zube kan Carpet, Sakeena tace "Our Mami baki ga kayan ba kona ɗaɗɗaga miki...?", Mami tace "No dear zan duba later", Sakeena tace "Tom" ta cigaba da duba box din kayan shafa, Nurain ya fito daga great room din Abba, paper din hannunsa ya miƙawa Mami snn ya zauna kan Sofa, Mami ta kalli papern sai kuma tace "i don't understand, wane calculation ne wnn..?", Nurain yace "kayan da nace miki zasu zo to nasu ne...", Mami tace "Masha Allah, Allah yasa rabo ne yasa albarka", yace "Ameen", Mami ta miƙawa Sakeena papern ta tashi ta shiga great room din Abba don daman so take suyi mgana dashi akan bikin, buɗe baki Sakeena tayi tace "Brother wane irin houses zaka siyamin a Villa..?", ya waro ido yace "irin wnda kike so", Sakeena tayi murmushi tace "Toh wai me kake a hospital?", straight forward yace "Help", Sakeena ta ajiye papern kan kujera tace "saidai hakan", ta cigaba da duba kayan da take, can after few minutes tace "Yauwa bani kuɗin kayan Hajar ma", Nurain ya dubeta ya ɗage gira yace "kayan me?", tace "Outfits da zata saka a biki mna", yace "Outfits kuma is she the bride?", tace "yeah she's your bride wcca kake ma favor" ta ƙarashe tana galla masa harara tace "kaga babu enough time saura 2weeks", yace "2week sukay fixing..?", tace "yeah", yace "ohh account digit", ta gaya masa account digit dinta, bayan ya tura mata ya ajiye wayar yace "done", wayarta ta duba bayan alert din ya shigo, ganin kuɗin daya turo tace "bafa 20set za a dinka ba", yace "sunyi kaɗan ne..?", tace "No sunyi yawa sosai zan maka refunding half", yace "no need", a lokacin Mami ta fito tana kallon Nurain tace "Abba yace zaka wuce China..?", Nurain yace "yeah..", Mami tace "when..?", yace "insha Allah on Monday", Mami tace "hope ba zaka daɗe ba", yace "Sure 10days zanyi", Mami tace "Alright... sai ka kawo Hajar nan..", yace "Tom". Before 10 Nurain ya koma gida, sharp sharp yayi wanka ya saka white pajamas don so yake ya sauka downstairs ya zuba abinci, a gidansu yana ganin ana ci yaƙi ci don ynxu sosai taste din abincinta ya kama masa baki, yana buttoning rigar jikinsa ya sauko downstairs ya shiga kitchen, tini ya ɗauki plate ya fara zuba abincin da yau kwana uku knn sai ya tarar a ajiye, yana gama zuba snow rice ya buɗe warmer din stew, yana fara zuba stew din aka buɗe ƙofa, daskarewa yayi a yacca yake da serving spoon a hannu, Hajar tafi seconds biyar tana kallonsa sai kuma ta taɓe baki ta wuce ta ɗauki ruwa, har ta nufi door zata fita sai kuma ta juyo, wata shegiyar dariya ce ta taho mata ganin ya kasa cigaba da zuba abincin sai jujjuya serving spoon din hannunsa yake, tayi gyaran murya tace "kai ma kana tayasu ci knn...?", haɗe gira yayi yace "what are you talking about...?", Hajar ta fashe da dariya tace "Aljanun kitchen fa na ajiyewa shine ka cinye musu..", Nurain bai san lokacin da ya ajiye serving spoon din ba yace "yah... i was only helping them sai an zuba a plate suke ci ai idan a warmer ne baza....", shiru yayi jin ta tuntsire da dariya, ita za a yiwa wayo bayan ita take wanke plate din da yaci, kallonta yake without blinking har tana riƙe ciki, Nurain yayi blushing ya shafa kansa, ya harɗe hannu yana kallonta, saida ta more dariyarta snn ta ɗago tace "wayyoh Allahna", ganin yana tahowa kusa da ita tayi sauri ta buɗe ƙofar kitchen din ta fita, saidai dariyar da take tayi weakening dinta tasa kafin ta hau stairs yayi nasarar fixgota, ta tsala ihu tace "i know you were just helping them, daman su suke cin jagwalgwalo kai baka ci", sakinta yayi ta haura sama da sauri, yabi bayanta da kallo sai kuma ya juya ya koma kitchen yana blushing, stew din ya ƙarasa zubawa ya ɗauki ruwa da lemo ya fita, a palour ma yayi zamansa yaci abincin, sha biyu da rabi na dare Nurain ya rufe laptop din da yake operating, ya tashi daga kan gadon bayan ya zura room slippers ya fita palour, yayi sliding door ya fita daga ɓangaren nasa, a hankali ya murɗa ƙofar ɗakinta ya shiga walking gently without making any sound, kwance ya ganta kan gado ta rufe da duvet, hasken ɗakin ya rage yabar dim, ya matsa gaban gadon yana kallonta da ɗan hasken ɗakin, a hankali ya kwanta daga bayanta ya ɗora kansa a pillow dinta, yana ɗaga duvet Hajar ta farka don daman baccin nata beyi nisa ba, ganin zata miƙe yayi saurin rumgumota ta baya, scent dinsa da ta shaƙa ne yasa taji relief amma kuma saita fara ƙoƙarin fixge kanta, da taga dai bazata iya kwacewa ba ta marairaice tace "please let go off me this is not proper fa..", ya sake haɗata da ƙirjinsa har tana jin bugun zuciyarsa, lumshe idonta tayi jin saukar numfashinsa a gefen wuyanta tace "dan Allah let me go..", murya can ƙasa yace "No.. sai kin faɗi wa kike yima dariya ɗaxu", turo baki tayi tace "nifa ba da kai nake ba, Aljanun ne suke bani dariya..", tummy dinta ya riƙe ya mirginasu suka koma suna fuskantar juna yace "really.. Aljanun kike yima dariya..?", da sauri ta runtse idonta ta gyaɗa kai don idan tace zata buɗe baki tayi mgana toh tabbas dariya ce zata biyo baya, a bazata taji ya haɗe goshinsu waje guda sai kuma yayi brushing lips dinsu, yace "lokacin da kike dariya ai buɗe baki kikay so now answer me bana son nodding talk Silly girl", tini zuciyarta ya fara racing, ta daddage tana matsawa baya don ta raba goshinta da nasa, da sauri ya tallafo kanta ya hanata raba goshin nasu, tana buɗe baki da shirin tsala masa ihu ya rufe bakin da nasa, this time around ba iya brushing lips dinsu yayi ba he sucked her small lips deeply, tini Hajar ta fashe da kuka jikinta har na rawa tace "Ummana wayyo Ummana...", Nurain yayi murmushi mai sauti yana kallon lips din nata da bai gaji da sucking ba, yace "Shhh in ana dariya ba a kuka fa", ba tasan lokacin da ta shiga banka masa harara ba tace "Ni ka sakeni dan Allah, ni fa ba kai nake yiwa dariya ba", yace "Ohh really su Aljanun da kike jin tsoro kike ma dariya knn..?", da sauri ta gyaɗa masa kai, ehen ai kam da kiss din da ya matuƙar firgitata ya gigitata ya mata tinin ba nodding saidai tayi mgana, yana sakar mata lips ta fashe masa da kuka harda shessheƙa, garin riƙeta sbd fincikewar da take ne ya kasa controlling kansa, abu daga tsokana sai kuma ya fita daga sahun tsokana har ya wuce gejin kiss, firgitar da tayi yafi na ranar nan, don wnn karon anje inda ba'a aje ba ranar nan, da kyar ta samu chance din da ta kwala uban ihu sai kuma ta ja numfashi tamkar zata shiɗe tana kiran Ummanta, sai a lokacin Nurain ya sarara mata, gefenta ya kwanta yana sauke nannauyan ajiyar zuciya, Hajar ta ja rigar baccinta data koma wuya tana shessheƙa, daman ba a maganar bra don ita cilli akay da ita may be ma ta kai gaban mirror, gaba ɗaya jikinta rawa yake tamkar an jona mata shoking, yau ita taga jalala da ƙarshen tashin hankali, hantsilowa tayi daga gadon ta kwanta kan carpet ta ringa rusa kuka kamar ranta zai fita, Nurain ya lumshe idonsa yana jinta, idan yace zai rarrasheta to tabbas ba rarrashi zai yi ba wani kukan zai sakata ko kuma ma ya sumar da ita tinda ya lura matsoraciya ce, after 30mins yaji ta dena kukan saidai shessheƙa time to time, da kyar ya tashi zaune snn yayi buttoning rigarsa, a hankali ya sauka daga gadon ya duƙa gabanta, ya rage murya yace "Hajar... Hajar... Hajar", jin shiru bata amsa ba ya ɗauketa ya mayar da ita gado ya rufa mata duvet, daga haka ya fice walking slowly don ya kunnowa kansa ruwa. Washe gari Hajar tayi gurgumi a ɗaki taƙi fita ko ina, daga taji motsi saita kyalla bathroom, tsoron encounter dashi take har cikin zuciyarta, gashi tana so ta sauka kitchen don yunwa take ji amma kuma bazata taɓa iya fita ba, tin safe ruwa kawai ta ringa ɗurawa kanta, wajen ƙarfe biyu na rana ta miƙe a hankali ta matsa gaban window, curtain din ta yaye ta leƙa waje tana kallon compound, parking space ta kalla taga babu motarsa guda ɗaya, hakan ne ya bata hope din baya gidan knn, ai da sauri ta nufi door ta buɗe ta fita, sharp sharp tayi frying egg ta tafasa black tea, jikinta har wani ɓari yake don tayi sauri ta gama ta fita, haka ta shanye shayin da zafinsa yana ƙona mata baki, tana gamawa ta buɗe ƙofa ta fita, a lokacin shima ya shigo palourn da leda a hannunsa, sanye yake da manyan kaya farare tass sbd yau Friday kuma daga mosque ya dawo, Hajar ji tayi kamar zuciyarta ta koma ciki ganinsa, da sauri ta koma kitchen don hawa saman ma ya mata nisa, ta yarfe hannu kamar zata fashe da kuka tace "na shiga uku", jin an murɗa handle ta koma da baya tana zaro ido, sai taji dama ta iya irin magic din nan na cikin films din da Noor take kallo, da babu abinda zai hana ynxu tayi applying dinsa a wnn taƙin ta ɓace ɓat ta huta, sulalewa tayi ƙasa after realizing tabbas shine ta haɗe kanta da guiwa, Nurain ya ajiye ledan fruit da ya shigo dashi, ya ringa kallonta kafin ya fara tafiya gently towards her, ya duƙa gabanta yace "yau ba gaisuwa?"......✍️