Who I'm 7
by @maidambu41
'YAR MACE....🌺
*Mai_Dambu*
Paid book
07
Shirun Mama babu alkhairi a cikinsa, domin kuwa girman Hajiya Amina take gani yasa tayi shiru wanda nasan Hajiya Amina tana barin gidan Mama ba zata daura maganarta. Don haka na ce mata "Mama Amina zan koma." Ba iya ita ba hatta Mama naga mamakina a fuskarta. "Zaki koma fa?" Suka tambaye ni bakinsu a haÉ—e, cikin wani irin shashekar kuka na ce musu. "Eh zan koma!" "Ummu babu inda zaki kome, ranki baya son gidan Tafida yanzu idan kika koma kamar cutarwa ne ga rayuwarki!" "Babu abin da zai same ni!" Na fada ina kuka, sai kallona Mama take ita dai bata ce min dole ba, amma kuma a ranta tasan bata kyauta min ba. "Kiyi tunani Hajiya Hadiza tunda kika haifi Ummu ta tab'a miki musu? Duk abin da kike ce shi take miki, akwai hisabi a tsakaninmu da Yaranmu." "Hajiya Amina ni fa bance mata dole ba, kin ga na mata magana ne?" Ta fada kamar ranta ya b'aci, murmushi Hajiya Amina tayi tana faÉ—in. "Shi kenan, Ummu ki yi duk abin da ya dace. Wanda zai gyara miki yau É—inki da domin kuwa shi rayuwarki na gaba. Ita mahaifiyarki!" Sai kuma tayi shiru tana kallona kafin ta mike tana faÉ—in. "Allah yasa haka shine mafi alkhairi! Ni zan tafi." "Amina kamar ranki ya b'aci?" "A'a raina ba zai b'aci ba, Ummu Hadiyya yarki ce ni kuma makociyarki ce kina da yadda zaki yi da ita. Ni kuma babu yadda zaki yi da ni, sannan ina ga mu bar zancen nan kawai Ummu Hadiyya mun gode sosai fa, kamar kin san ina niman kudi ido a rufe, sai an jimanku!" Ta saka kai ta fita nasan Mama Amina ranta ya b'aci sosai, tana fita ko minti goma ba ayi ba, Mama ta sabi mayafinta tana faÉ—in. "Amina ita ce bangon da nake jingina na ji dadi, ita É—aya take tayani kuka lokacin kuka, gara na shirya kafin a fara mana dariya." "Sai kin dawo!" Na fada ina jijiga Mufid. "Kawo shi na goya shi!" Goya shi tayi suka fita, hawayen da suke ta zuba min na goge, ban san ta kuma dawowa ba sai ce min tayi. "Kuka ba zai miki magani ba Ummu Yaran nan zaki duba, ya rayuwarsu zata kasance idan baki tare da mahaifinsu. Dama Allah ya baki kada kiyi wasa da shi wurin lalata aurenki, Allah ya buda miki kika gidan aurenki ma bai saka kin rasa kome ba shawara nake baki fa ban ce dole ba." Share hawaye nayi ina kallon Mama da ina ga kamar dole take min na koma gidan Tafida, fita tayi tana faÉ—in "kowa rai ya amfana baya ga mai shi ne." Kamar Tafida yana jiran ta fita sai ga kiranshi. Kallon wayar nayi kafin na dauka. Dariyarshi na ji tare da yan iskan abokan shi. "Ummu!" "Hmm!" "Uwar gida Sarautar Mata, dama na kira na gaya miki ko zaki samu lokaci zuwa wata sati zamu je Umra da ke!" "Tafida!" "Na'am Matar so!" "Bana son aurenka! Kayi hakuri ka rabu da ni." "Amma Ummu baki ga kamar yayi sauri ace mun rabu da juna duka-duka shekarar mu nawa da auren da zamu rabu da juna?"
"Ai ko kwana É—aya ne nace ba zan zauna ba!" "Ba zaki zauna da ni ba, tow me nake miki da kike jin haushina." "Ba kayi kome ba, ba zaka tab'a min kome ba saboda bana bukatarka yasa nake son rabuwa da kai." "Ummu Hadiyya kin ga ina ganin girman Iyayenmu yasa nake bin ki cikin lumana idan kika bari wani abu ya taso ba zan miki da dadi ba!" "Ni dama bana son ka min dad'i" daga haka na kashe wayar ina ganin yana ta turo sako amma fir naki budewa. Tunda na fahimci ni ce matsalarshi na saka a raina zan rabu da shi, amma shi ya kasa fahimtar haka.
**
SA'ADIYYA.
Amarya Tafida wacce suka sha alwashin dole ta zama first lady, ana ta gyara ciki da waje domin tun barin Ummu Hadiyya gidan har yau bata gane kan kusar yakinta ba, duk wani abin da suke karbowa na barbadawa da turarawa, bai yi tasiri akan Kusar yaki ba domin kuwa yana da matukar taurin kai, sannan Tafida duk rashin jin shi ya tsare salloli biyar nan baya wasa da su, Allah yayi alƙawarin kuma yana cikata akan wadanda ya daukawa, shi yasa duk haukarsu baya tab'a sh, sai da suyi ta asara wanda kowa yasan bata da dad'i. Tunda aka rantsar da shi bakiɗaya yan uwanshi da yan daki daya da waɗanda suke yan uba, suka kara shigewa Sa'adiyya wacce ita basu ne a gabanta ba, ga gidan nan dai Ummu ta bari sai me? Tafida ne kuma babu hadin kai yaƙi kulata ma, tana zaune a parlournta tana shan fruit Wanda ya sha kayan Mata, aka kirata a waya. Dauka tai tana yatsina fuska. "Tanko shi dade, Hajiya Larai ce shugaban Mata, na kira na tayaki murna sannan na tuna miki da alƙawarin da kika mana!" Wani haɗe rai tayi tana faɗin. "Tow ai bamu shiga gidan gwamnati ba ko?" Ta tambaye ta, sannan ta kara da cewa. "Idan muka shiga xan kira ki!" "Yawwa haka ne kan, Hajiya ko kin ga abin da yake faruwa Mai girma gwamna da wata mata da Yaranta hala kishiyarki ce ko?" Wani irin dauke wuta Sa'adiyya tayi kafin ta ce mata. "Ban gane ba?" Ta fada da sauri, "Eh tow ki duba zaki ga ana ta daura hoton a media! Sai an jima" matar ta kashe wayar, sororo tayi tana bin wayar da yake hannunta da idanun. Jikinta yana rawa ta buɗe data, abin da ta fara gani shine sakon da arewa fashion trending suka turo na *Mrs Tafida Mama's Kitchen! Long live Mr and Mrs Tafida!* Jikinta yana kerma ta shiga duba notifications hoton Tafida da Ummu ne, a yadda aka yi ta daura hoton zaka ɗauka soyayya ake zubawa a asibiti amma a zahirin gaskiya, rigimarsu da suka.fara ce take yawo a tsakaninsu yayinda media suka kafa hujja da cewa soyayya ce kawai.. a wani page da ta ga wata tana faɗin. *OMG maza kyawawa sun iya karewa a jikin Mata munana ba mamaki yayi breaking heart din kyawawan Mata Allah ya jarabce shi da auren wannan yar karamar yarinyar!* a kasar comments din aka rubuta. _Ke dalla ba yarinya ba ce, dakyar idan ya bata shekaru me yawa domin nasanta a dan gaba damu take Aunty Baby! Akwai mutunci da kirki* still yarinyar farko ta kara cewa *Amma ance su biyu ne ko?* *Eh su biyu ne akwai Amaryanta idan kika ganta wallahi sai ki dauka aunty Baby Yar aikinta ce saboda kyau da haduwa amma ki ga yadda ya kare* sai a lokacin Sa'adiyya ta sake murmushi, karamar wayarta ta dauka ta kira wani number. "Zan ajiye maka sako ta Whatsp! Kasan yadda zaka yi ka ruguza abin da ake daurawa a social media! Zan turo maka 20k!" "Ki nime wani yayi miki aikin ba zan yi ba" aka fada mata, tasan matsalarshi da maganar kuɗi. "Ok 50k!" "A'a bana bukata!" "Zan baka 150k yayi!" Ta fada a hankali, "tow ba damuwa bari mu tashi kura!" "Yawwa nasan zaka iya!" Ta kashe wayar tana me ɗaukar screen shot ta tura mishi ta Whatsp. _Kin san bana aikin banza ko? Don haka turo na miki aikin da zai zama trending!_
_Na sani! Sannan idan da hali ka karyata abin da ake fada na soyayya suke ! Ka gaya musu gaskiya Ummu ba zata dawo rayuwar Tafida ba aurensu mutuwa zai yi suna haka ne don hankalin mutane ya kau akansu! Zan kara maka idan har ka girgiza media!_ take ta tura mishi dubu dari da hamsin din. Tana jiran aiki domin tasan smarty matuƙar yace zai yi aiki tow babu me hana shi a duniya.
Bayan awa guda aka yi ta kiranta, ana tambayarta. "Sa'adiyya kin ga meke faruwa kuwa?" Dake tasan me ta kulla ko a jikinta. "Me ya faru?" "Hmm ke dai duba!" Bude data tai kamar da gaske ta ga abin da ya daura da cewa! *Labarin da ake ta damun kowa soyayya soyayya! Hmm soyayya for ma foot! To karya ce!* anan yayi ta rubutu akan wasu hotunan Ummu Hadiyya, da tafida. Yayi magana marasa dadi da kyau akan Ummu Hadiyya da Tafida. tare da kafa hujjar idan ana ganin karya ne a bincika Ummu bata tare da Tafida yanzu haka tana jiran takardan sakinta ne. Wannan abin ya saka mutane suka fara kokwanto akan maganrshi. Yayinda wasu suka yi ta zaginshi suna mishi mugun fata da Allah ya sakawa Ummu da Tafida.
Dariya tayi sannan ta karawa Smarty wasu kudadden, ta kashe wayar tana kad'a kafarta musamman inda Yaron ya rubuta. *Allah Sarki Uwar marayu gatan mai iyaye! Turmin tsakar gida shaluguden mahassada! Kin yi naki kin yi na me karamin karfi! Hajiya Sa'adiyya Aliyu Tafida! Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana! Madara mai kama da nono* wannan kalaman sun tsaya mata a rai! Sai kallon kanta take a wayarta. Tana murmushi ita yanzu idan da smarty ba zata kashe wa wani dan iska kudi ba, shi kadai zai yi draging kome out! Bayan la'asar aka yi sallama tana kwance bata tashi a wurin da take ba. Aunty Rukayya ce tare da yarta Naziha. Ita fa sun fara damunta daga ranar da aka tabbatar da Tafida ne ya ci zabe suka hanata sakat, amma dake makira ce mikewa tayi tana murmushi ta ce musu. "Aunty Ruky ke ce!" "Eh wallahi mun zo ganin Alhaji ne na ce bari na zo na gaishe ki!" "Ina wuni!" Naziha ta gaida ta sama sama, domin Allah bai had'a jininsu ba. "Mammy bari na shiga cikin gida!" "Au baku shiga ba ne?" Inji Sa'adiyya, "eh yanzu shigowarmu!" Aunty Rukayya take fada, "Ayya!" Ta fada fita yarinyar tayi, Aunty Rukayya kuwa tayi ta zuba tun da suka shigo bata kira an kawo mata ko ruwa ba, suna zaune aka kirata. Cikin dauki da murna ta ce mata. "Tow sai kun iso!" "Laraba!" Da sauri matar ta fito tana faɗin. "na'am hajiya!" "Yawwa maza a gyara parlour ki ce Rose ta hada kayan ciye-ciye ga matar mai taimakin gwamna nan zuwa da Yaranta!" "An gama Hajiya!" "Masha Allah yau gidan da baki kenan! Ai da sun fada da wuri ko abinci da anyi musu!" "Eh ba kome haka ma yayi" ta nufi dakinta tana hararan Aunty Rukayya, dake bata san meke faruwa ba. Ta tsaya aka gyara parlour sannan aka jera musu abin tabawa. Kafin karfe shida bakin sun iso, nata so Aunty Rukayya ta zauna ba, amma haka ta share suka yi ta ina zaka saka ina zaka ajiye da iyalin mataimakin Gwamna. Sai bayan Isha suka tafi shima lokacin Tafida ya shigo suka kara gaisawa, sannan suka rako su. Juyawa suka yi cikin gidan Aunty Rukayya ta shiga tattara abubuwan da aka sakawa baki tana zubawa a wani leda abin ya bawa Sa'adiyya haushi. A cikin gidan kuwa tunda Alhaji Muhammad Jadda ya ga Naziha ya tambaye ta. "Ina Mamanki?" "Tana can bangaren Uncle Tafida!" Jinjina kai yayi yana faɗin. "Ai haka yayi!" Yana sane da abin da suke ya zuba musu idanun ne kafin Allah ya hukunta su daidai da laifinsu. Ko da yayi magana za su ce yana bayan Ummu ne Gara ya zuba musu idanun tukun indai shuwa ce Allah zai kawo karshen abin da suke yi. Har aka yi sallah Magariba bata shigo ba sai bayan sallah ta shigo sama sama suka gaisa. "Naziha muje gida dare yayi!" "Tow!" Ta fada tana kallon Alhaji Muhammad Jadda, "Abba Allah ya baka lafiya, zamu tafi!" "Ku gaida yaran da mai gidan!" Suka fito da sauri tana faɗin. "Zai ji in sha Allah!" A kofar dakin Inna suka tsaya"tsohuwa zamu tafi ban samu shigowa ba!" "Ai kai kud'a me kwadayi ne ban yi mamaki dan baka shigo ba, a gaida Yaran!" Dariya ta yiwa mutanen gidan sallama suka bar gidan domin Tafida ya bada motar da za a kaita gida. Shiga dakinta tayi tare da kiran Uwarta. "Mommy na gaji! Wallahi na gaji haba don Allah akan shi aka fara zama gwamna ne? Ace kai da gidanka ya zama kamar gidan gandu, kowa zuwa yake bakin arziki ma sai anyi ta shige musu!"
"Kiyi hakuri lokaci ne zai tabbatar da haka, ina sane da kome. Sannan kiyi amfani da ruwan nan fa da hayakin da turaren" "Shi kenan!" Ta kashe wayar, ban daki ta shiga tayi wanka da ruwan rubutun tayi turaren da kome sannan ta wuce kitchen ta dafa mishi indomie aka barbad'a kayan aiki kafin ta wuce dakinshi, yana ta aiki a laptop. Karatun Sheikh abdurrahman sudais yake tashi a wayarshi. Ta kawo ta ajiye mishi, "sannu da hutawa!" "Yawwa!" Ya fada yana aikinshi. "Ga abinci!" "Me kika dafa?" "Indomie ne!" Ta fada tana kallonshi. "Barshi kawai xan sha tea!" Ya fada yana me cigaba da aikin. "Na hado maka?" "A'a ina aiki idan na gama zan sha!" Ya fada yana ta aikinsa kamar ta fashe da kuka tana zaune a wurin har barci ya fara daukarta, ya mike ya haÉ—a tea sannan ya bude drower dinsa, soyayyen nama ne da dambun nama, ya zuba a wani flat ya dauki bread guntu ne ma jiya Deen ya saya musu. A hankali yake ci yana jin dandanon kayan haÉ—in abincin Ummu, daukar tea din yayi da kayanshi ya kai parlour sannan ya dawo ya dauki wayarshi ya koma parlourn. Yana shan tea yana me kiran Ummu. Sai da ta kusan yankewa ta dauka da "hello! Waye?" "Kiyi tunani Ummu Hadiyya me kyau ga dambuna ya kare waye zai min irin naki?" Kashe wayar aka yi, ya kira yaji wayar a kashe bakiÉ—aya. A can dakin kuwa yana jin motsin fitarshi ta farka tare da bin shi ta makale tana me saka kunnenta. Jin sunan Ummu abin ya bata mamaki, wannan wacce irin masifa ce haka? Tana Barka an rabu da bukar ashe an haifi habu. Kwafa tayi tana me barin jikin kofar ta kwanta karshe barcin da bata yi ba kenan har sai.da ya shigo a saninta shi din yana da bukatar mace a koda yaushe, amma sai ta ga tun barin Ummu Hadiyya gidan ya rage sosai asalima tana zuwa dakin zai dauki pillow ya shimfida bargo ya kwanta a kasa. Wannan abin ya mata ciwo ko yana mata ciwo kamar wacce tayi mishi wani abu bakiÉ—aya ya janye daga kulawar da yake bata. Dakyar barci yayi gaba da ita cikin takaici.
***
"Waye ya kiraki a wannan daren!" Kallon Mama nayi kafin nace mata. "Tafida!" Sannan na gyara kwanciyana. "Yaron nan yana ta kokarin ya ga kun daidaita amma kin ki ban san wani irin taurin kai yake damunki ba, amma ba xan daina gaya miki gaskiya ba domin kuwa shi ne gatan da zan miki." Kasa magana nayi ina kallon gefen da take kwance, a hankali naji alamar barci ya É—auke ta.
Gyara kwanciya nayi ina son na tuna me yasa na rasa wanda zai tsaya min akan abinda Tafida yayi min? Me yasa Mama take niman juya min baya? Me nayi da zafi haka da kowa yake ganin kada na rabu da Tafida.
-
Sunana Ummu Hadiyya a sanina ni agola ce Mama ta auri Baba Alhaji Bulama bayan ta yaye ni. Alhaji Bulama yana da mata biyu da Mama uku Hajiya Balkisu ita ce uwar gida kuma me manyan Yara dakinta tana da yara biyar, Ahmad Bakura yana aiki a abuja yana da mata daya da Yara biyu, sai Muhammad sani Kawu Gwani sai Salman Bamai, sai Safina wacce ake kira Taima.....
***