ALLON ƘADDARA

34

by @oumfatima33

✨✨✨✨✨✨✨✨  

 _*ALLON ƘADDARA*_

        _*By*_

   *_OUM FATIMA_* 

_*(Hakimar D. A. W. A)*_

✨✨✨✨✨✨✨✨ 


     _*DASHEN🌲ALLAH*_ 

_*WRITER'S📚ASSOCIATION*_


            _*TEAM*_

_*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*_





 *PAGE 34* 


_*بسم الله الر حمن الر حيم*_





***** Cike da farin ciki Aliya da Mahaifiyarta suka koma Gida domin kuwa sun san Hajiya ta hau fiye da yanda suka zata. Isar su kenan mai aikinta ke shaida mata cewar tana da baƙuwa dake jiranta, cikin mamaki suka ƙara sa parlourn da tunanin wacece. Sakina ƙanwar Momy suka samu ta ɗau wanka na alfarma tana danna wayarta, da fara'a suka ƙara sa domin kuwa Aliya ta shaidata don harkar Kasuwanci na haɗa su wasu lokutan ita Hajiya Sakinar ke sayen kaya wurin Aliya.


Sun samu tuni an aje mata drinks da snacks don haka zama suka yi suka shiga gaisawa, bayan sun gama gaisawa ita Ummi ciki ta shige ta basu wuri don ita bata wani san Sakinar ba. Hira suka ɗan taɓa da tambayar yaushe gamo kafin Sakina ta maida fuskarta serious ta fuskanci Aliya tace. "Wata magana ce ta kawo ni wurinki Aliya, ban san ko kin san da ita ba". Aliya ta gyara zamanta tace. "Ina jinki wace magana ce wannan?".


"Kin san da cewa Mijinki zai ƙara aure? Kin kuma san wa zai auro maki?". Sakina ta ƙare cike da salon bugun cikin mutum da kuma tunzura shi. "Lokaci ɗaya Aliya ta haɗe face dinta tace. "Na san da magar auren, wacce zai aura ɗin ce ban sani ba kuma bana buƙatar sani don ba amfanin da hakan zai min tun da ba yiwuwa auren zai yi ba matuƙar ina raye kuma ina amsa sunan Aliya".


'Anzo wurin'. Sakina ta faɗa cikin zuciyarta kafin ta gyara zamanta tace "Ke kuwa kike da buƙatar sani domin ki ƙara zage dantse wurin tarwatsa al'amarin don kuwa ba ƙaramar makira Mijinki ke ƙoƙarin jajibowa kansa ba". Ta faɗa da sigar firgita Aliya.


"Duk sheɗancin ta ni na na fita domin kuwa nima ba kanwar lasa bace, sai dai maganarki ta sa ina son sanin wacece wannan? Da har kika taso don sanar dani a game da ita". Aliya ta faɗa ranta na ɓaci. "A Gidan su Yaya Habiba take ƴar ƙanen Mijinta ce Hanan mai aiki a gidan rediyon nan ƴar wajen Harira, itace wacce ta mallakewa Yaya Habiba ɗanta Nabeel ya lalace a kanta ƙarshe sai da suka kashe shi suka huta, kuma sannan ta maƙalewa Matar Hammansu itama bata ganin laifinta a karshe dai itama sai da ta mutu yanzu ta koma kan Mijinta da ƴarta da ta bata ita tun kafin ta mutu, yanzu haka rikicin da ake akan ƴar ita da iyayen Marigayiyar, tun wuri gara ki san hannu wa Mijinki zai faɗa don wallahi ina tabbatar maki matuƙar kika bari Mijinki ya shiga hannunsu ita da munafukar Uwarta da ta gaji komai a wurinta ke da shi har abada!". Sakina ta ƙare cikin sigar razanar da Aliya.


Ai kuwa ta hau fiye da yanda ta zata don lokaci ɗaya ta firgice tana ta fadar magan-ganu. Sakina bata bar Gidan ba sai da ta tabbatar da ta gama famfa Aliya fiye da zato.


Ai kuwa da ƙyar Mahaifiyar Aliya ta lallaɓata akan ta bari suga abinda Hajiya Asma'u zatayi kafin su ɗau wani matakin. Da ƙyar ta lallaɓata ta koma Gidanta a ranar ɗin ko wurin aikinta bata jeba.




***** Da zazzaɓi sosai na kwana wanda dole sai da Baba Malam ya kira Hamma Jabeer akan yazo ya dubani ko akawo ni Asibitin yace masa gashinan zuwa Gidan.


Ba'afi mintuna sha biyar ba sai gashi ya iso, tare suka shigo da Ammy ta rakosa har ɗakina. Sai da ta fara shigowa ta ga yanda nake, ai kuwa daga ni sai guntuwar rigar barcina da bata wuce cinyoyina ba. Tashi na tayi ta taimaka min na saka doguwar riga mara nauyi ko kaɗan kafin ta koma ta shigo da Hamma Jabeer.


Ina jin sallamar da yayi a saman laɓɓansa na juya masa baya don wani irin haushinsa nake ji. "Tashi Habebty ga Hammannaku zai duba ki". Ammy ta faɗa tana kamani ta zaunar da ni bayan ta saka min pillow a bayana. Fuska na yamutsa nace "Ammy nifa naji sauƙi ba sai ya duba niba". 


"Maza tashi bana son shiririta". Ammy ta faɗa tana hana ni kwanciyar da nake ƙoƙarin komawa. Gyaran murya kaɗan yayi kafin yace "Taci wani abu ne?".


"Ina fa taurin kanta zai barta tayi wannan abin arziƙin, tun ɗazu nake fama da ita akan tasha ko tea ne amma taƙi". Ammy ta faɗa cikin sanyin da jikinta yayi.


"A kawo tea ɗin mai ɗan zafi". Ya faɗa a nutsensa ba tare da ya kalli inda nake ba. Mikewa Ammy tayi tana faɗin "Yauwa bari in kawo kila kai ta yarda ta amsa". Ammy na fita na koma na yi kwanciyata.


 Nutsatstsiyar muryarsa mai fita da ɗan ƙarfi ce ta ratsa kunnuwana. "Tashi ki zauna". Ya faɗa ba wasa. Kamar kar in tashi sai kuma dai na tashi ina tutturo baki gaba ina mitar takuranin da yayi. Yana ankare da duk abinda take, ƙasa-ƙasa yake kallon mitsitsin bakinta yana motsawa ya san halin take yi. "Fitinanniya kawai". Ya furta a ƙasan maƙoshinsa. Sarai naji abinda yace don haka na ɗago da niyar zuba masa harara cikin rashin Sa'a idanuna suka nutse cikin tsakiyar nasa idanun ya kuma sarƙafesu ya hanani ciresu. "Ni? Mai na maki to?". Ya faɗa yana kaɗa idanunsa alamar wai shi nake harara. Da kyar na samu na fizge idona da ƙyar har ina sauke ajiyar zuciya kamar wacce ta tsira daga wani harin da aka kawo mata.


Miskilin murmushi ya saki iya laɓɓansa ya furta "Mara kunyar ƙarya". Kansa ya maida saman wayarsa yana daƙikarta Ammy tayi sallama ta shigo ɗauke da milk tea da ta haɗo min sai faten dankalin turawa da yaji haɗi sai tashin ƙamshi yake. Tana ajewa ta kuma fita ta barni da shi. Zamansa ya gyara ya matso kujerar kusa sosai da gadon kafin ya maida fuskarsa serious ya ɗauko tea ɗin ya nufi bakina da shi.


Fuska na yamutsa zan ɗauke kai ya zuba min azababbun idanunsa yana min kallon 'ansa mana' haka kamar zan yi kuka na buɗe baki na fara sha kaɗan-kaɗan. Ban aje ba sai da na shanye tas sabo da ɗandanonsa yayi min daɗi, bai yi magana ba ya buɗe plate ɗin ya saka spoon ya ɗiba ya nufo bakina. Hannu nasa na karba na fara sha ina yamutsa fuska masifa fal cikina sai dai ba fuska don haka nake na zabga masa harara a fakaice ina mita a raina.


Yana kallon duk abinda take amma yayi kamar bai gani ba yaci gaba da daƙilar wayarsa. Ko rabi ban sha ba na aje ina faɗin "Gaskiya na koshi ni dai". Bai ce komai ba sai wayarsa da ya aje ya matso ya shiga dubani. Goshina ya taɓa har yanzu da zafi, jakar da yazo da ita ya buɗe ya shiga haɗa allura. Ina ganin haka na zabura zan miƙe ya ace "Koma ki zauna". Ba alamar wasa a muryarsa don haka na zauna ina kwaɓe fuska dan da nan hawaye ya cika idona don nasan shike nan nazo hannu ba tsira zan ba, bayan kuma gudun allurar ne ya sa naƙi yarda da zuwa Asibitin tun farko.


Dariya ce ke ciyo shi ganin yanda ta kasa zama wuri ɗaya tun ba'ayi allurar ba fuskarta ta jiƙe da hawaye. Sai da ya gama haɗawa kafin ya matso da kyau ya zauna kusa da ni, bai ce komai ba sai hannuna da ya kamo ya dai-daita gurin da zai tsira allurar.


Gam na rintse idona bayan na ƙanƙame ɗayan hannunsa da na riƙo sa na ɓoye fuskata a bayansa. A hankali cikin tsananin kulawa ya tsira allurar yana hura mata iskar bakinsa har ya gama juye ruwanta gaba ɗaya kafin ya zare yana sakin ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ni kuma nayi tawa a bayyane ina sakin hannunsa. Magani ya shiga ɓallawa yana bani ina haɗiyewa da ƙyar fuska duk hawaye da majina, tissue ya zaro ya bani na karɓa ina tura baki na share fuskata tsaf kafin na koma na kwanta na juya masa baya.


A nutsensa ya buɗe baki ya fara magana cikin wani irin sanyi sai dai miryartasa tana fita da amo irin wanda aka san Muryar na miji da shi, sai dai maganar gaskiya muryarsa tana min daɗin sauraro "Mene matsalar kuma uhm?". Shiru na masa naƙi cewa komai. "Kin fiye rigima Sofiyyah kina son ki yi ta rashin lafiya kina tadawa Ammy da Baba hankali?". Cikin sanyin murya ya ƙare maganar yana ɗan dafe goshinsa kaɗan.


Baki na buɗe zan yi magana sai kawai na fashe da kuka na kasa cewa komai. "Ya Arrahaman! Mene kuma?. Ya tambaya yana kallon fuskarta da ta juyo tana fuskantarsa. "Kai ne kace zaka kawo min ƴata amma kaƙi kawota kuma kullum idan kazo baka bari na ganka kake gudawa don kar nace ka ɗauko min ita!". Na ƙare maganar da iya gaskiyar dake cikin zuciyata don damuwa ta kenan a halin yanzu.


"To ya zakiyi da ita idan na kawo maki ita anzu? Keda zakiyi aure ki tafi ki barta gaba ɗaya ma!". Ya ƙare maganar cikin wani irin sanyin da yasa na ɗago na zuba masa ido. Ganin ya tsare ni da ido alamar amsa yake jira daga gareni yasa ni cewar "Ai da ita zan tafi ko?".


Idonsa ya waro yace "Ki tafi da ita ina ɗin? Kin san dai ina raye ƴata baza taje agolanci ba ko?". Ya ƙare da sigar tambaya da kuma son jin ta bakinta.


Ni kuma lokaci ɗaya hawaye suka fara sauka saman fuskata na shiga faɗin "To ai ƴata ce tun da Aunty Kalisat ta bar min ita kuma kai ma da bakinka kace ka bani, kuma ai ina da shaida tunda a gaban Hajjo aka yi komai don haka ƙararku zan kai Kotun Baba Malam ya amsar min ƴata". Na ƙare maganar cikin kuka da iya gaskiyata. 


Ido kawai ya zuba mata yana mata wani irin kallo da shi kaɗai ya barwa kansa sanin ma'anarsa, a hankali yace "Ai Auntynnaki cewa tayi ki auri Babanta ki kula da mu ba ki auri wani ba ki tafi da ita agolanci ba ko?. Ya ƙare still idanunsa a saman fuskarta da har tayi ja sabo da kukan da tayi.


Jin taki cewa komai ya sashi faɗin "Ko ba haka aka yi ba?". 


"To kai wa ya faɗa maka?" Nima na tambaye shi. "da kunnena naji mana. Shiru nayi na rasa ta cewa, fahimtar hakan da yayi ne ya sashi faɗin "Kinga in kin kai ƙaran namu sai ki faɗi gaskiyar magana ko?. Shiru nayi masa ina harararsa ta ƙasan ido bakin nan kamar zai taɓo bango. "Shike nan kwanta ki huta banda rigima ok". Ya faɗa yana miƙewa ya fice bayan ya ɗauki remote control ɗin AC ya dai-daita min ya fice a ɗakin.


A hanya suka ci karo da Ammy da ta dawo daga wurin Baba Malam tayi masa godiya ya wuce ita kuma ta shigo ta same ni a kwance ina ta tunane-tunane. "Ya jikin naki?". Ammy ta faɗa tana taɓa wuya na. ", Alhamdulillah". Na bata amsa a taƙaice. Abin rufa ta jamin ta rufe ni tace inyi barci in huta ita kuma ta tattare kayan abincin da ta kawo min ta fice ta barni ni kadai kasancewar Anisa tun da safe ta tafi Gida sabo da kiran da Dad ɗin ta yayi mata akan zata yi baƙi.





**** Kamar yanda Hajiya Asma'u ta buƙata Alhaji Mahmud da Bilal sun amsa kiranta, inda ta tuɓure tace maganar auren da Bilal zai ƙara ta soketa tunda bai sanar da Matarsa ba kuma tace matuƙar aka yi sai ta kashe su. Duk yanda Alhaji Mahmud yaso shawo kanta akan tayi haƙuri an riga an gama magana gashi a Gidan manyan mutane aka nemi auren ba zasu iya zuwa suce sun fasa ba ƙi tayi. Don cewa tayi ita zata iya zuwa tace an fasa ɗin in su baza su jeba. Da ƙyar ya lallaɓata akan ta bari zai nemi ƴan uwansa su yi shawara yanda za'a yi da suka fito.


Sai da suka fito Alhaji Mahmud ya rarrashi Alhaji Bilal akan yayi haƙuri abi abin a hankali har su shawo kan Hajiya, sannan shima ya lallaɓa Aliya ta amince da maganar don innhar ta sami Hajiya da kanta tace ta amince to shikenan. To kawai yace ma Mahaifinsa ya tafi ransa a ɓace da abinda Aliya da Mahaifiyarta suka yi. Yayi alƙawarin a wannan karon zai bata mamaki domin kuwa ko me zata yi sai ya ƙara aure don ya gaji da halinta.


Gida ya nufa kai tsaye ba tare da ya koma wurin aikinsa ba, bai yi mamakin tarar da ita a Gidan ba don ya san maganar aurennan ba za ta barta samun natsuwa ba har sai taga an fasa abinda ba zai yiwu ba kenan. Bai wani tsaya rarrashinta ba kamar yanda Mahaifinsa ya ce ba sabo da ya san ba zasu taɓa dai-daitawa ba sai dai ma abun ya ƙarasa lalacewa. Don haka sama kawai ya haura ba tare da ya ko kalli inda take ba, hakan da yayi kuwa ba kaɗan yaɓata mata raiba don haka ta bishi ta sauke masa duk abinda ta ƙunsa na bakin ciki daga wurin Sakina wanda har tayi ta gama bai ko kalli inda take ba haka ta fice da kuka wiwi da shan alwashi iri-iri.


"Nonsense!' ya furta furiously ya shige toilet yana rufo ƙofa da ƙarfi ya sakar ma kansa ruwa ko zuciyarsa tayi sanyi...




Barkanmu da wannan lokacin



 *Oum Fatima* 


***