35
by @oumfatima33
✨✨✨✨✨✨✨✨
_*ALLON ƘADDARA*_
_*By*_
*_OUM FATIMA_*
_*(Hakimar D. A. W. A)*_
✨✨✨✨✨✨✨✨
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S📚ASSOCIATION*_
_*TEAM*_
_*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*_
*PAGE 35*
_*بسم الله الر حمن الر حيم*_
Wasa-wasa sai da nayi kwana biyu da zazzaɓin kafin ya sakeni na koma bakin aikina. Alhaji Bilal yazo dubiya kamar yanda ya faɗa inda ya jibgo min uwar sayyayyar da ta ƙara baƙanta ran Momy ta motsa hassadarta. Domin kuwa kaya ba kaɗan ba ya kawo da kuma rabon kuɗi da yayi wa yara harma da manyan, wannan abin yasa ta ƙara ɗaukar alwashin lalata auren nan don bata ƙaunar ganin ci gaban Harira da ƴarta don haka ta kira ƙanwarta a waya ta tambayeta inda zance ya kwana.
Kwantar mata da hankali Sakina tayi akan ta gama komai kawai ta saurari abinda zai biyo baya ba da daɗewa ba. Ba don ta samu natsuwar ba ta ƙyale ɗin don sosai take jin baƙin cikin yanda Harira ta fita a komai na rayuwa bayan kuma tare suka taso, asalima Mahaifinta shi ya jawo Mahaifinta a harkar Kasuwanci har ya samu nasa rabon. Amma tazo ta shige mata gaba a komai.
***** Koda wasa Alhaji Bilal bai sanar da ni game da abinda ke faruwa ba sai dai ni da kaina ta fara fahimtar akwai matsala don sosai na fahimci cewar yana cikin damuwa a kwanakin nan, dana tambaye shi kuma sai ya bani izurin ayyuka ne suka masa yawa shi yasa baya samun lokaci sosai. Ban ja zance ba na bar maganar sabo da har yanzu ba wani sosai na damu da al'amarinsa ba.
Tsakanina da Hamma Jabeer kuwa tun da ya ƙara dawowa sau ɗaya ya dubani shike nan na ware bamu ƙara haduwa ba ko nema na a waya, sai dai yana turo min text message da bai wuce tambayar yaya jikina ba. Sau ɗaya na mayar masa da reply ɗin cewar na warke shike nan ya shiga sabgogin gabansa akan shirin bikin buɗe sabon Companynsa da za'ayi sati mai zuwa in sha Allah.
★★★
Duk yanda Alhaji Mahmud da sauran ƴan uwansa suka lallaɓa Hajiya akan ta yi hakuri ta janye maganar soke auren Alhaji Bilal da Hanan ta tuɓure ta nuna sam bata yarda ba, don can Aliya ta tare ta riƙa mata kuka har da rashin lafiya sai da Mahaifin Aliyar yazo har nan yaci ƙaniyarta kafin ta koma Gidanta.
Rikicin tsohuwar yasa dole suka yanke hukuncin zuwa su bawa Iyayen Hanan haƙuri sai dai kunya ta hana su zuwa domin kuwa ba ƙanananun Mutane bane da za'a tare su da irin wannan raininin hankalin kai tsaye. Ko da suka zaunar da Alhaji Bilal suka bashi haƙuri kasa cewa komai yayi, sai tashi da yayi ya fice ransa a ɓace da tunanin irin hukuncin da zai yanke wa Aliya a wannan karon.
Da ƙyar dai Alhaji Bukar da ɗan uwansa Alhaji Mahmud suka daure suka nemi ganawa da su Alhaji Babba. Cikin jin nauyi suka yi musu bayanin halin da ake ciki tare da bada haƙuri akan ba laifinsu bane halin rikicin Mahaifiyarsu ne ba yanda zasu yi. Sosai ran Alhaji Babba ya ɓaci ya fara faɗa sai da Baba Malam ya bashi haƙuri da faɗin "Ba komai Allah yasa haka shi yafi alkairi". Godiya suka yi suka fita da sanyin jiki da rashin jin daɗin yanda al'amarin ya kasance.
Shiru parlourn yayi bayan fitarsu na ɗan lokaci kafin Alhaji Mukhtar yace " Yanzu miye abin yi Yaya wannan ai rashin mutunci ne". Ya ƙare maganar furiously. Ajiyar zuciya Alhaji Babba ya sauke kafin yace "Ba komai ai baza a fasa auren nan daga yanda aka sashi ba, don haka kar kowa yaji wannan maganar a bar shi a yanda aka saka shi za'a ɗaura in sha Allah".
Da haka suka gama magana kowa ya nufi uzurinsa. Koda Ammy ta fuskanci damuwa a saman fuskar Baba Malam lokacin da take taimaka masa yake shirin fita wurin karatunsa ta tambaye shi bai faɗa mata komai ba, itama bata matsa masa jin abinda ke damun nasa ba tunda tasan idan yana son ta sani ɗin da kansa zai sanar mata. Don haka ta gama abinda zatayi ta tafi nata uzurin.
Aliya ta samu yanda take so don Hajiya Asma'u ta shaida mata an janye maganar aure don haka take cikin tsananin farin ciki. Yau da wuri ta koma Gida tayi girki da kanta taci kwalliya ta zauna zaman jiransa don so take su shirya ko ta samu natsuwar komawa kan harkokinta da kwana biyu bata maida hankali akai, yana dawowa aka taresa da iyayi ana masa shagwaɓa. Bai yi mamaki ba sabo da yasan ta samu labarin fasa auren shine tazo take masa abinda ko sati bazata iya ɗorewa da yi masa ba.
Sai da yayi matuƙar ƙoƙari kafin ya danne kansa ya amsheta a yanda tazo masa don ya shirya bata mamakin da zai girgizata kwana kusan nan, ita kuwa sakaran ta ɗauka komai ya wuce da gaske don haka tana ganin ya sake ta koma rayuwwrta yanda ta saba hankali kwance.
**** Anyi bikin buɗe Companyn Hamma Jabeer lafiya inda aka shirya walima mai ƙayatarwa akaci aka sha akayi hotuna aka watse inda Company ya fara aiki cikin jajircewa da kuma kyautatawa. Tun waccen ranar bamu haɗu da shi ba sai yau a wurin bikin buɗe Company. Sosai kwalliyarsa tayi matuƙar yin kyau cikin Black Mandarin Collar Suit 2 pieces da suka zauna a ginannen jikinsa suka masa kyau, Black Grandioso Gancini Leather Loafers ne masu azabar kyau sanye a ƙafafunsa sai wal-wali suke. Tsintsiyar hannunsa ɗaure take da agogon Rolex mai kyau da tsada. "Masha Allah". Na furta a ƙasan maƙoshina domin kuwa Hamma Jabeer maƙura ne wurin iya tsara ado, ga kyau ga kwarjini sai abin ya haɗe masa ya zama na musamman.
Sai da aka zo ɗaukar hotuna ne sannan nazo kusa da shi ganin Little a hannunsa, da matuƙar farin ciki na miƙa masa hannu ya bani ita.
Miƙa mata ita yayi yana zuba mata ido ganin yanda take farin ciki harda sauke ajiyar zuciya. Cikin wani irin yanayin da shi kaɗai ya barwa kansa sani yake kallon su ita da ƴar tata sai wasa take mata suna ɓangalar dariya, hakan yake jin wata irin natsuwa na saukar masa cikin jikinsa. A haka aka yi ta ɗaukarsu hotuna masu matuƙar kyau a tare da juna.
Zuwa sallar la'asar taro ya tashi cike da farin ciki bayan an raba kyautuka kowa ya koma Gida. Da ƙyar na iya bada Little da zasu koma ɗin harda ƙwallata.
★★★
Kwanci-tashi ba wuya a wurin Allah biki nata matsowa ba tare da na ƙara ji daga ango ba, tun ban damu ba har dai naga shirun yayi yawa na neme shi da kaina nake tambayarsa konlafiya. Kamar dai wancan lokacin uzurin ayyuka suka masa yawa ya bani muka bar zancen a haka.
A ɓangaren Ammy da Aunty Ade kuwa shiri sosai suke na bikin don har na fara amsar gyara a wurin Aunty Ade. Ganin da Momy tayi ana ta shirin aure ba fashi ne yasa ta zuwa Gidan Sakina da kanta suka yi maganar, anan take sanar mata ai ba maganar auren don Aliya ta sanar mata Kakarsu ta hana auren kuma har an maido musu kayansu. Mamaki ya kama su da tunanin to me yasa ba'a faɗa ba. "Ƙila sadaka zasu bawa wani gudun jin kunya!". Sakina ta faɗa cike da shaƙiyanci.
"Kai zan dai bincika nasan in dai har an maida kuɗi Alhaji bazai rasa sani ba tunda sune masu bada auren". Momynta faɗa.
Da haka ta koma Gida sai da tayi yanda tayi ta tabbatar da an fasa maganar a bakin Mijinta sai dai bai sanar da ita cewar za'a ɗaura da wani ba. Daɗi kamar ya kasheta sabo da tasan Harira zata ɗanɗani bakin cikin fasa auren ƴarta a karo na biyu bayan sakin da aka mata ko kwana bata yi a gidan Mijinta na farko ba. Don haka ta saki ranta ta zuba idon ganin ta inda magana zata ɓullo ta kuma shiga tunanin yanda zata bawa Alhaji Bilal Aminatu ya aura sabo ta ƙara baƙanta musu, duk da tasan abin ba mai sauƙi bane.
Ana saura sati biyu ɗaurin aure Alhaji Babba ya nemi zama da Jabeer da Mahaifiyarsa suka tattauna magana mai muhimmanci. Sai dai bayan maganar Jikin Hajiya Mama yayi sanyi sosai amma dai bata ce komai ba. Shi kuwa Jabeer dama ba'a gane masa sai in yaso don haka ba wanda ya fuskanci komai.
Zuwa wannan lokacin raina ya fara ɓaci da abinda Alhaji Bilal yake na rashin nemana amma dai na daure ban kuma kiransa ba sai Anisa da na samu da maganar, kwantar min da hankali tayi akan ba komai in masa uzurin kamr yanda yace. Duk wani abin da ya kamata ayi min ana yi min shi har kayan da zan yi fitar bikin dasu duk Ammy ce tafitar min cikin order kayanta da aka kawo, wasu ma takanas don ni kaɗai ta sa aka kawo su don ba ƙaramin shiri tayiwa bikin ba saɓanin na farko da ba wani jinsa take a ranta ba sabo da gudun abinda zaije yazo dama.
Da yake ba wani event na shirya ba shi yasa ban wani damu da neman Alhaji Bilal ba akan shirye-shiryen bikin ba kamar yanda bai neme ni ba. Sai dai hakan ba yana nufin banji haushin abinda yayi min ba tunda ko ba komai ai kulawa tana da daɗi ko, har zuciyata ta fara raya min ko dai tsoron Matarsa yake ita ta hana shi?. "Koma dai miye su suka jiyo bai damu Hanan ba". Na faɗa cikin ko inkula ɗin nan.
Bani da wasu ƙawaye a rayuwata sai Samha sai kuma Anisa da take ƴar'uwata Kuma ƙawata, sai fa ƴan Matan Gidanmu don haka ba wanda na gayyata su Samha ne akan komai na shirin Bikin, wannan karon Momy bata hana Aminatu shiga cikinmu ba sabo da ta san wahalar banza muke ba maganar aure.
Ana saura sati ɗaya ɗaurin aure Alhaji Bilal ya aiko da saƙo aka kawo min, ban bi ta kan saƙon ba sai da dare dana ƙare duk wasu uzurorina nayi shirin barci kafin na jawo Embulop ɗin na buɗe. Kuɗi ne sababbin da zasu kai kimanin 1m sai guntuwar takarda mai ɗauke da gajeren saƙo na ban hakuri da fatan alkairi. Ban fahimci komai ba game da abinda saƙon ya ƙunsa ba na linke na mayar da tunanin yana bani haƙurin rashi zuwansa ne kwana biyu, kuɗin kuma na ɗauka na kaima Ammy don ba abinda zanyi dasu.
Itama Ammy tayi mamakin yawan kuɗin amma sai bata ce komai ba ta barshi a matsayin kyautatawa ce ya mata tunda yana da halin hakan, sai kawai ta aje su ta shiga sabgogin gabanta....
*Oum Fatima*