Page 5
by @reefat24
馃挒 *KAREN BANA*馃挒
( Cigaban laifin mijina )
*5*
Marubuciyar
*SIHIRTACCIYa*
*Laifin mijina ne*
*Nida shugaban kasa*
*Shine zabina*
*Mai sona*
*Nasarar Rayuwata*
*Hijra*
*Rayuwar yau*
*Mace zinariya*
*Hukuncin uwa*
*Jauro bajam*
Momy (khady ) na falo tare da y'ay'an nata Wanda mata suka Fi yawa cikinsu kullum tana tare dasu tana kokarin ganin ta jasu a jiki don gudun fadawa rayuwa ta y'ay'an zamani irin Wanda take gani, shiyasa bata fiye barinsu suna fita anyhow ba daga gidan Ayshu sai gidan meenah sai Kuma Wani lokaci sukan tafi Hutu gun Yasmeen wacce take aure a Kano sai Kuma idan sukaje yola Hutun December tare da Abby , Meenat ta shigo tare da sallama suka amsa mata Nan suka fara ihun murna dama sun shaku da ita saboda duk zuwansu yola suna zuwa su kwana gidanta.
" Anty Meenat yaushe a gari ?
babbar y'arsu ce tayi wannan magana , khady na murmushi tace
" y'ar gidan hajja Dada an diro tarayya kenan matar likita "
" Ina yini momy "
" Lafiya ya gida ya jikin Dada "
" Alhamdulillah da sauki " nan suka gaisa da yaran inda ta shaida musu yau tazo , ruwa aka kawo mata da lemu tace tana sauri zata tafi nan kuwa aka hado mata sakon Siyam ta karba sukayi sallama akan cewa zasu sameta gidan Oummu.
ta Bude motar ta shiga tana murmushi ta jefa ledojin a bayan mota tana cewa
" sorry na dade koh "
" Never mind ai kece , da wata ce da tuni na tafi "
" Kai yaya nah kana Kara narkar da zuciya ta wallahi "
" Allah yasa ta narke har ki gudu ki dawo wajena "
" Kana da masauki ne idan ma dawo ?
" Niko nake dashi , ke kinsan nan da 2 months zan Baki mamaki koh "
" Mamaki Kuma na me ?
" Auren zanyi my girl".
Wani mugun kallo ta jefa masa tare da cewa
" Amma dai wasa kake koh?
" Allah am serious "
" Akan wane dalili?
" Backup kafin ki dawo gareni ".
" Gaskiya A'a ni bana so "
" Kaji ki da wata magana, idan dare yayi kina makale da mijin ki ni Kuma Ina ta harbin gini shine Wani ce min A'a "
" Ni Babu abinda mukeyi , wannan soloniyon uban me zai min da ya dawo aiki yace ya gaji shikenan ya bingire sai bacci ".
Wani dariyan shakiyanci Haidar yayi Wanda ya dada tunzura Meenat ta b'ata rai tana kallon window, ya sagaita dariyan Yana murmushi
" Um... sorry "
" Ba laifinka bane Yaya "
" C'mon sorry mana ".
hawaye ne ya fara fitowa tasa hannunta Wanda yasha Jan lalle ta fara sharewa abinka da farar fata lallen ya kara mata kyau ba kadan ba, parking yayi gefen titi ba tare da Wani tunani ba ya jawota jikinsa Yana shafa gefen fuskarta Wani irin yarrr...taji a jikinta
" Sorry kinji my angel kiyi hakuri bazan Kara ba ok "
" Ni ka sake ni don Allah "
" A'a sai kin daina kukan "
" Amma dai kasan Babu kyau taba matar aure koh "
" Umm na sani mana , amma ai ke tawa ce koh " turo baki tayi tana kokarin raba jikin nasu ya Kara kankameta lumshe Ido tayi tana Jin Wani irin yanayi na shigar jijiyoyin jikinta da sauri ta fusge ta koma jikin seat ta kwanta tana Maida numfashi, lumshe Ido Haidar yayi tare da cusa hannu cikin gashin Kansa " ohh...shit girl I need wallahi "
hararinsa tayi tace
" Sai ka Jira na kashe auren koh "
" Ni I wonder me kike Jira har yanzu , me zai Baki Wanda ni bazan iya Baki ba tell me please"
" Babu abinda yake bani sai abinci da takaici don baya biya min bukata , highest 5 minutes ya gama komai ya sauka ni kaina nagaji da auren wallahi tsoron Abba ne ya hanani Neman saki Allah "
" Gaskiya nagaji da jiran ki kije ki nemi Mafita idan bahaka ba aure zanyi seriously".
hararinsa tayi tace
" Kai dai ka shiga uku da jaraba "
" Gaskiya da sauki a wannan sabgar kullum sau biyar zan Baki ". Ya karasa zancen Yana murmushi,
" Allah ya shiryeka sau biyar kamar ibada "
" Toh ba ibada bane ko kin manta "
" Ni ka tada mota mu koma kasan tsohuwar can da fitina yanzu ta hadani da Oummu"
Marairaice fuska yayi Yana mata Wani shu'umin kallo yace
" Baki cika alkawarin ba my angel "
Juya idanu tayi tare da cewa " ohh really..da ka dauka da gaske ne ?
" Uhmm..why not toh "
" Gaskiya A'a "
" Haba angel me a ciki bafa Wani abu zanyi ba kawai dai...
hannu tasa tana toshe masa Baki , murmushi yayi yace " toh muje a min Ina son tabbatar da abinda Ake gayamin a chat "
" Ba yau ba gaskiya saboda Babu privacy"
" Muje office dina"
" Yamma tayi Yaya nah "
" A'a don Allah muje ".
Bai Jira amsarta ba ya kunna mota Kai tsaye hanyar kamfanin Ayshu motors ya nufa tafiya ce me dan tazara kafin suka iso yayi parking securities na tsara mishi cike da girmamawa, ta fito sanye da face mask don boye fuska batasan cewa idan da sabo sun Saba in dai Haidar ne ya kawo mata sunfi hamsin kuma Babu Wanda ya taba damuwa saboda kowa na harkar da ta damesa Babu me kula Wani.
Lift suka shiga zuwa last floor inda office din nasa yake, akwai ma'aikata kowa na aikinsa suna faman d'aga masa gaisuwa dake yamma tayi wasu sun tashi daga aiki shiyasa dai daiku ne suka rage.
Suna shiga yasa makulli ya kulle katafaren ofishi ne me matukar girman gaske ga kayan more rayuwa Babu abinda aka rasa a ciki ,
" Wow... gaskiya office naka ya hadu Yaya "
" Thanks "
Ya furta Yana murmushi daga nan ya zagaya ya rungumeta ta baya lumshe Ido tayi a yayinda taji Wani abu ya taso mata tun daga tsakiyar Kai har zuwa tafin kafa,
" Yaya don Allah...
hancinsa yakai gefen wuyarta Yana goga mata a jiki Yana shakar qamshin turarenta, tuni jikinta ya dauka dama haka halittar ta yake abu kadai ke d'aga mata hankali tana kokarin kwace kanta amma inaa hannayensa ke yawo bisa ilahiriin jikinta nan kuwa jikinta ya fara kyarma , juyo da ita yayi ya had'a bakinsu ya fara aika mata Wani irin passionate kiss Wanda bata taba samun irinsa ba a rayuwa gaba d'aya tsayuwar ya gagareta tana Neman zubewa a kasa ya tarota suka koma bisa 3 seater nan ya shimfideta ya haye ruwan cikinta.
Meenat tayi Nisa ta manta wace duniyar suke ciki hannu yasa ya bude zip din abayar tata nan kuwa ya Saukesu bisa tudun kirjinta, Wani ajiyan zuciya ya Sauke bai Jira komai ba ya dawo wajen Yana mata Wani irin salo mai rikitarwa gurnani ta fara masa nan kuwa ya tura hannunsa kasan mararta .. firgigit ta Farka daga dogon mafarkin da take tuni hankalinta ya dawo jikinta yayinda ta tattara dukkan karfinta ta turesa ya Fada kasa ta tashi tana gyara kayan jikinta, innalillahi wainna ilaihirraji'un....
Shi kadai take nanatawa cikin zuciya Wani kuka yazo mata ta fashe da kuka ta koma ta jingina da bango tana innalillahi...yau me ta aikata haka saura kiris komai ya faru astagafirullah... hanyar Kofa tayi Haidar yayi saurin riketa Yana kokarin rungumeta ta turesa tana kuka ,
" Yaya you almost had sex with me ....
" Am sorry my angel wallahi na kasa controlling din kaina ne sorry please "
" Kasan me muka aikata kuwa ?
" Sorry sorry is ok...Hakan bazai sake faruwa ba". runtse Ido tayi tana hawaye ya jawota jikinsa ya fara aikin rarrashi abin takaici ta kasa hanashi rungumarta shin wane irin so takewa Haidar Wanda duk abinda yace mata Bata iya sallakewa ,
" Ki daina kuka is just a romance ai ba Wani Abu ok ".
lumshe Ido yayi Yana cizon lebe gaskiya yau yaga samu yaga rashi da ya rage zafi, Meenat kuwa tsoro ne ya kama ta da yau yayi sex da ita da ta shiga uku idan tayi ciki Kuma me zata fadawa duniya tun da Dr yasan ya dade baiyi muamalar aure da ita ba, tunani iri iri cikin zukatansu daga karshe ya share mata hawaye tare da sake bata hakuri suka fice zuwa mota. Tun da yadau hanyar gida babu Wanda ya sake magana cikinsu har suka shigo layin gidan nasu nan ya bude gaban mota ya cire bandir din kudi ya ajiye mata bisa cinya , batayi magana ba har suka shigo harabar gidan kafin ta cusa kudaden cikin bag nata a hankali ta furta " thanks ".
daga nan ta Suri ledojin sakon tayi cikin gida tabar shi zaune cikin mota bashi da niyyar shiga gidan.
Jikinsa ya tashi donhaka bai shiga gidan ba ya kira wata yarinya yace su hadu a office dama kullum suna tare sunanta Blessing ita take biya masa bukata akoda yaushe duk da cewa Basu taba yin sex ba amma tana gamsar dashi ta hanyar wasanni, Yana shiga ko minti goma baiyi ba ta shigo Igbo ce fara sol y'ar gayu ce sosai sai zuba qamshi take tana tauna chewing gum tayi fari da Ido tana kallonsa tace
" handsome wannan Kiran yamma haka hope am safe "
" My baby I'm missing you ne kawai Babu Wani abu ".
Murmushi tayi a kullum babban burinta shine Haidar ya mallaka mata Kansa amma yaki amincewa sai yace mata Babu kyau a addinin musulunci wato zai nuna Yana da wayo kenan bayan tasan cewa ko a Christianity Babu kyau abinda suke aikatawa na romance din amma bai taba furta hakan ba, ajiye jaka tayi ta fada jikinsa ba tare da Wani b'ata lokaci ba suka kama sana'ar tasu tamkar su hadiye juna sai gab magariba kafin ya sallameta bayan ya cikata da kudade masu yawa sannan ya kama hanyar gida dole sai ya koma yayi wanka kafin zai fita sallah don kayansa Babu tsarki.
___________________
Bayan sallar magariba tana kallon News tare da mahaifinta wayarta ya fara ringing new number ne batayi saurin d'agawa ba sai a karo na biyu ta dauka tana " Hello "
Muryarsa me tattare da nutsuwa da sanyi ya ce
" Assalamu alayki "
" Wa'alakassalam "
" Barka da dare mom nah "
Yana fadin haka ta gane Mai magana, satar kallon bangaren da mahaifinta yake tayi hankalinsa na gun TV nan ta tashi ta sulale zuwa d'aki lokacin Hari na sallah ta kwanta bisa gado ,
" Mom...
" Um Ina yini "
" Lafiya mom ya gida "
" Alhamdulillah ya gajiya"
" Lafiya kalau "
" Masha Allah sunana Adeel, ba tare da b'ata lokaci ba Ina son ki ne Kuma Ina da burin auren ki idan Allah yasa da rabo Ina fatan babu Wanda ya rigani koh ?
Murmushi tayi tace
" Allah sarki my son kazo a kurerren lokaci saboda tuni na Maka Uba "
" Allahu Akbar Allah bai kaddara d'a zai dauki mahaifiyarsa ba sai akayi rashin dace uba ya fara zuwa "
Murmushi tayi tana tuna kyakkyawan fuskarsa,
" Uhmm hakane "
" Shikenan tun da Ina matsayin d'a bazanyi fushi da uban nawa ba , zan tayaku da adua Allah ya tabbatar da alheri idan Uba ya tsaya wasa Kuma sai na masa kwace "
' "Allah koh "
" Allah da gaske nake , duk da cewa addini ya haramta nema akan nema amma ni zan Jira sai ranar daurin auren ki kafin na cire rai ,donhaka kiyi hakuri duk lokacin da na samu dama zan kira mom dina mu gaisa ta samin albarka idan Babu matsala "
" Babu matsala nagode d'a nah Allah ya Maka albarka "
" Amin mom amma fa yaron ki ya fara kukan zuci tun yanzu "
" Kayi hakuri ka zama jarumi kaji yaro nah "
" Uhmm zan rarrashi kaina saboda bani da Mai rarrashi na a halin yanzu " " wayyo Allah don Allah kayi hakuri kaji "
" Babu komai na Saba da irin wannan rayuwar, kawai zan fadawa Abby ya tayani da adua ita Kuma me sunan ki idan na gaya mata zata shiga damuwa shiyasa bazan fada mata ba ".
gaba d'aya jikinta yayi sanyi ta rasa me zata ce masa " mom!
Ya kira sunan
" Na'am..
" Mom kar ki bari tausayi ya rinjaye ki don zan iya kwace gwamnatin wancan uban nawa " murmushi tayi tana Jin zuciyarta na mata Wani iri ,
" C'mon ni ban fada Miki don ki tausaya min ba please, bana son ki shiga damuwa saboda ni I'll be fine ok "
" Ka tabbata?
" Uhmm..am very sure don ni bana daukar abubuwa da tsanani "
" Toh shikenan Allah ya Maka albarka "
" Amin mom sai da safe ?
" Allah ya tashemu lafiya zan kiraka da safe kaji "
" Nagode mom " " ok bye".
Tabe baki Hari tayi dama Allah Allah take ta gama wayar don ta amsa mata tambayoyi, aikuwa tana kashe call din ta juya tana fuskantar ta tace
" Ke uwar Yan iya Ina kika samu Wani son da uban son ?
" Umma...
" Ke banson hauka wato kin tsaya son son kina korar samari koh , Humaira zan b'ata Miki rai cikin gidan nan kina ji koh "
" Umma me amfanin yaudara ba gwara na fada masa gaskiya a samu a rabu lafiya ba "
" Gaskiyn me don ubanki, kina da tsayayye ne ko kina da mijin aure , ai Kya bari yazo muga kamun ludayinsa y'ar banza zaki tsaya kina Wani kwainanen son son...
dariya kasa kasa take nan ko Hari ta shaka ta tashi ta Maka mata dundu a gadon baya
" Shegiya y'ar bakin ciki wato dariya na Baki koh, zaki ci ubanki kwanan nan wallahi zan aurar dake na huta na bakin cikn da kike kuntsa min "
" Bakin cikn da kike kunsawa kan ki dai saboda son abin duniya"
Abba ne ya shigo d'akin Basu sani ba Yana tsaye bakin kofa Yana kallonta ya cigaba da cewa
" Ina hanaki wannan munanan dabia amma baki ji Harira "
" Kai Sule ka dakata min kaji , Kai bakasan zafin yarinyar nan ba ni nan nafika sanin zafinta kai dai kayiwa uwarta ciki ta haifeta shine kawai matsayin Ka amma wallahi baka fini sonta da sanin zafinta ba ehen...
Girgiza kai yayi cike da takaici ya fice don yasan idan ya biye mata zata bashi kunya gaban y'ar tasu shiyasa baya biye mata idan ta fara haukar nata gashi ya kasa rabuwa da ita ta zame masa karfen kafa,
" Ke Humaira karki biyewa sule ya kaiki ya baroki kinsan ance ciwon y'a mace na y'a mace ne ni macece nasan komai shiyasa nake guje Miki auren matsiyaci , dani da uwarki Nana Munci bakar azabar talauci kafin Allah ya kawo rufin asiri, ke bana son Baki tarihi ne da sai kin zubar da hawaye.. Allah sarki nana baiwar Allah, ashe Babu rabon tazo nan taci arziki..Allah ya jikan ki nana da nayi ta kishi Ina mata hauka iri iri, har labe nake mata ranar girkinta baiwar Allah Wayyo Allah Nana...
ta fyace majina tana share hawaye,
Aysha ta buga tagumi tana kallonta Kai Hari daban take wajen iya kissa tana kuka kamar gaske nan kuwa Aysha ta fara bata hakuri dakyar ta samu ta daina kukan.
*Allah ka shirya bayinka ka kawo sauki cikin wannan rayuwar da ake ciki inda Zina ya zama tamkar ado idan baka iya ba baka waye ba , Allah ka shiryar da Mazaje masu bin matan banza a waje ka shiryar da matan aure masu aikata zina da aurensu ya Allah ka yafe mana hmmm...muje zuwa akwai aiki a gaba *** nagode masoyana*