SHU'UMAR MASARAUTA 2

2

by @ameeraadam

*SHU'UMAR MASARAUTA*


      ©AMEERA ADAM


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*


Tsokaci: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a wata kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.

 

  *BOOK 2*

  

 SHAFI NA BIYU


GIDAN SARIN KAYA🥳🔥

Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada.


   Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi.


 Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa.


 Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰


  Akwai cotton material da lesuka da atamfofi siyan ɗaya ko sari.

    Tuntuɓe ni a wannn lambar ***




  Papa na gab da shiga ɗakin Rawiya ta bi bayansa a guje cikin tashin hankali, da sauri ya juyo haɗe da dafa kafaɗarta. Har lokacin hannunta bai daina raɗaɗi ba.


 "Papa zafi yake yi mini kamar ana ɗiga mini ruwan dalma."  

 Rawiya ta furzo kalamanta cikin zubar ƙwalla, a wannan karon mamakinsa ya bayyana a fili ƙarara, a gefen wata kujera ya zaunar da ita ya saka hannunsa ɗaya ya sharce gumin da ya tsattsafo masa.

 "Zauna bari na ɗauko wayata na kira Dr Fatuhu, idan babu dama kuma mu wuce asibiti." 

 Papa furta yana saka mukullin ɗakin ba tare da ya ji amsar Rawiya ba. Yana shiga ɗakin ya sake saka mukulli ya datse ta sosai, daga hannun hagunsa wata 'yar ƙaramar ƙofa ce da ba ta wuce tsayi da faɗinsa ba. A ɓangaren dama kuma tsafatacciyar gawar wani matashi mai ƙusunbi ne a tsaye, daga jikin kafaɗarsa wata ja da baƙar doguwar riga ce a saƙale. Hannunsa ɗauke da farin ƙoƙo, bakinsa yana ɗigar da jini kaɗan-kaɗan, daga ƙasan ƙoƙon an fafe shi, jinin yana ɗiga a kan wata tafkekiyar sarƙa mai ɗauke da tambarin zanen kan ƙwarangwal da ƙafafuwa.

 Sai da Papa ya tuɓe kayan jikinsa gabaɗaya, sannan ya zura jar rigar mai hula. Ya ɗauki tafkekiyar sarƙar da jini yake ɗiga a kanta, ya dangwali jinin jikinta sannan ya ƙarasa bakin ƙaramar ƙofar da aka yi ta domin shigar mutum ɗaya.


 "Madogara! Madogara!! Madogara!!!"


 Ya furta sau uku, nan take wani jan haske mai kama da harshen wuta ya mamaye shi, yana shiga cikin ƙofar ya tsinci kansa a gaban shuɗaɗɗan kabarin da ke cikin hatsabibin daji.

  

 "Ya Shugabana haƙiƙa wani muhimman al'amari ne yake tafe da ni mai rikitar da ƙwayar ido, mai kuma hargitsa kwanya da ban mamaki." 

 Papa ya furta a sanyaye tamkar kazar da aka jefa da wuƙa.

 "Na san dole za ka zo!" 

 Shugaba ya furta fuska babu walwala.


 "Duk tsananin bincike tsafina ya gagara bankaɗo mini labulen sirrin yaron nan, har ta kai ga ya damƙa mata saƙon da na gagara tantance inda ya dosa. Shugaba ka taimaka mini..."

 Ajiyar zuciyar da Shugaba ya saki ce ta katse kalaman Papa, ya miƙe daga kan kujerar da yake kai rai a ɓace. Sai da ya ƙarasa gaban Papa ya ƙura wa ƙwayar idonsa kallo har sai da ƙirjin Papa ya buga, wani irin tsoro ya mamaye shi.

 "A karo na farko ƙungiya na taya ka murna da samun magajiya, domin yanzu haka 'yarka Rawiya ta kasance ɗaya daga cikin halartattun 'yan cikin ƙungiyar nan. Yaron da kake magana a kai ba kowa ba ne face wancan." 

Shugaba ya ƙarasa furucinsa yana nuna tsafatacciyar katangar da ke cikin da'irar ƙungiya.


 Tun da Ramadan ya shiga mota yake furzar da iska mai zafi haɗe da sauke ajiyar zuciya, lokaci-lokaci Mubarak yake kallonsa yana girgiza kai. A haka har suka ƙarasa gida kowanne da abin da yake saƙawa a zuciyarsa. Mubarak na yin parking tun bai kashe motar ba, Ramadan ya fice daga cikin motar kai tsaye ya wuce ɗakin da kayansa suke ciki.

 A gaggauce ya fara saka kayansa a cikin jaka, a wannan lokacin Mubarak ya shiga ɗakin. Ya jingina da jikin ƙofa yana bin sa da kallo, jin motsin Mubarak ya sa Yarima zuba wa ƙofar idanu yana nazari sannan ya ci gaba da haɗa kayansa. Murmushi Mubarak ya yi don ya sa halin Yarima Ramadan sarai da zuciya, amma me zai sa ya fara haɗa kaya bayan ba wani abu aka yi masa ba?


 "Wannan kayan da kake haɗa na mene ne Yarima?" 

 Mubarak ya furta yana ƙarasawa cikin ɗakin. Tamkar ba zai amsa masa ba, sai da ya laluba wurin da takalmansa suke ya ɗebo su ya saka a jaka sannan ya furta.


 "Gida zan wuce."


Ajiyar zuciya Mubarak ya sauke, ya ƙarasa haɗe da riƙe hulunan da Ramadan yake kokawar sakawa a akwati ya ce.

 "Da aka yi maka me za ka tafi gida? Wai abin da ya haɗa ka da yarinyar nan ne za ka huce a kaina. Ko ka manta ba ni na kar zomon ba? Kuma ko rataya ma ba a damƙa mini ba." 

 Ramadan bai tanka masa ba, ya cigaba da haɗa kayansa sannan ya faɗa toilet. Bai ɗauki lokaci ba ya fito yana tsane ruwan jikinsa, jikinsa ne ya ba shi har yanzu Mubarak yana zaune. Don haka kamar yana ganinsa ya turɓune fuskaya furta.


 "Fita ka ba ni wuri, ina son shiryawa. Kuma a sanar da Jakadiya ina son ganawa da Mai martaba yanzu."

 Yadda ya yi maganar ba ƙaramin dariya ya ba wa Mubarak ba, a fili ya saki murmushi ya furta.

 "Amma ka san ni ba bawanka ba ne da za ka dinga ba ni umarni." 


 Shiru Ramadan ya yi bai tanka masa ba, ganin ba shi da niyyar ya tanka masa ɗin ya sa Mubarak ya fice. Don ya san kafiya da taurin kansa ko sama da ƙasa za ta haɗe tun da ya ce sai ya tafi, babu wanda ya isa hana shi tafiya. Mubarak yana fita harabar gidan ya sa aka kira masa Jakadiya, ya sanar mata da saƙon Yarina Ramadan. Sai da ya tabbatar da Yarima ya kammala shirinsa sannan ya koma ɗakin, a tsaye ya same shi yana kaiwa da kawowa. Kamar ya yi masa magana sai kuma ya rabu da shi, ba su ɗauki lokaci mai tsayi ba Jakadiya ta ƙaraso ta sanar da shi Mai martaba yana maraba da zuwansa.


 Sai da Mubarak ya sallame ta sannan riƙo hannun Ramadan da niyyar yi masa jagora, da sauri ya fisge hannunsa ai kuwa lokaci ɗaya Mubarak ya saki dariyar da ke ransa.

 "Wallahi na lura so kake ka ja mini masifa a wurin Takawa, don ya ce ba na kula da kai yadda ya kamata ne kake fisge hannu Yarima?"

 Mubarak ya furta cikin dariya, ran Ramadan ya sake ɓaci don haka ya yi gaba ya saka baƙar sandarsa yana laluben hanya. Yana tafe Mubarak yana biye da shi duk hanyar da ya ga zai bi wacce ba ita ba ce, sai ya ja hannunsa ya sauya masa ita. Duk wurin da suka bi sai dai bayi su zube ƙasa suna kwasar gaisuwa, a haka har suka ƙarasa sashen mai martaba. 

 Da sallama ɗauke a bakinsu suka shiga, bayan Takawa ya amsa sannan suka shiga cikin girmamawa, sai da Ramadan ya zauna sannan Mubarak ya fita ya ba su wuri.


 "Barka da hutawa ranka shi daɗe." 

 Ramadan Ya furta cikin girmamawa haɗe da russunar da kai.

"Barka dai Sarkin gobe da yardar Allah." 


"Godiya nake ranka shi daɗe, Allah Ya taimake dama wani uzuri ne ya taso mini cikin gaggawa ba tare da na kammala abin da yake tafe da ni ba, amma idan na gama da wancan zan dawo na kammala wannan cikin ikon Allah." 

 Ramadan ya furta yana ɗan shafa kansa, kallon tsaf Takawa ya yi masa. Sai da ya yi murmushi sannan ya furta.

 "Allah Ya kai Yarima gida lafiya, za mu sanar da Dogari Sallau su haɗa duk abin da ya dace na tafiyarka Masarautar Huddam." 

 Yarima Ramadan ya sake russunawa cike da ladabi sannan ya furta. "Godiya nake ranka shi daɗe, Allah Ya ja kwana Ubangiji Ya ƙarawa mai babban ɗaki lafiya." Kasancewar Mubarak yana bakin ƙofa yana jin duk abin da suke tattaunawa, jin sun kammala ya sa ya nemi izinin shiga bayan Takawa ya amimce masa ya riƙo hannun Yarima Ramadan suka wuce sashensu.

 Ba tare da an ɓata lokaci ba Sarki Yunus ya bayar da umarnin haɗa dakarun da za su yi wa Yarima rakiya zuwa gida, duk yadda Mubarak ya kai ga tambayar Ramadan dalilin tafiyarsa ya ƙi tanka masa. A haka suka yi sallama da shi, su Yarima suka ɗauki hanyar Masarautar Huddam. Suna shiga cikin ƙasar Huddam ƙirjinsa ya buga da matsanancin ƙarfi, zuciyarsa ta dinga harbawa tamkar za ta yi tsalle ta faɗo daga ƙirjinsa. Sannu a hankali ya fara jin wani irin zafi yana ratsa shi, wata hayaniya sama-sama ta fara tashi a saman kansa. Daga can gefe ta wajen motar da yake ciki ya ji sautin dariyar macen da kusan koyaushe ta zame masa jiki, tun yana jin dariyar daga nesa har ya ji ta a tsakar kansa tamkar za za ta tarwatsa kwanyarsa.

 

 Runtse idonsa ya yi da ƙarfin gaske, ya saka hannu biyu ya toshe kunnuwansa. A hankali yake motsa bakinsa yana karanta duk wata addu'a da ta zo bakinsa, wata zufar wahala ta shiga karyo masa a ilahirin jikinsa. Kamar an yi ruwa an ɗauke, haka ya ji komai ya lafa masa. Babu zato ya ji motar da yake ciki ta daki wani abu mai kama da gungunmen ice. Salim direba da ya yi saurin taka birkin motar, cikin hanzari ya fito bayan ya kashe ta. Sai dai ga mamakinsa babu wani abu da ya yi tozali da shi, a tsammaninsa Yarima Ramadan zai tambaye shi abin da ya faru. Amma sai ya ji shiru, don haka ya sake tayar da motar ya ci gaba da tafiya har suka ƙarasa cikin masarautar Huddam.


 Tun da su Yarima Ramadan suka shiga masarautar bayi da Dogarai suka shiga zubewa suna yi masa barka da zuwa. Kamar yana ganinsu haka yake faɗaɗa fara'arsa yana amsa musu, da yake ya san cikin gidan nasu ciki ba bai kamar yunwar cikinsa. Sai ya ciro sandarsa kai tsaye ya wuce sashen mahaifiyarsa.


 "Barka da hutawa Ammi."

 Yarima ya furta bayan ya zube a gaban mahaifiyarsa. Murmushi ɗauke a fuskarsa ta furta. 

 "Barka dai Yarimana! Kai ne da doshin magriba babu ko waya?" 


 Yana shirin yin magana ta katse shi, ta hanyar kiran baiwa Hanne domin da kawo masa kayan ciye-ciye.

 "Ammi ina son zuwa na gaida Mai martaba, idan ta kawo a ajiye mini ina dawowa."

 Ramadan ya furta yana laluben sandarsa. Miƙe masa ta yi, ya miƙe ya fita tana bin bayansa da wani irin kallon ban tausayi.


 Tun daga sashen gidan mahaifiyarsa har zuwa sashen Takawa, duk hanyar da ya keta sai dai Bayi da Dogarai su zube ƙasa cikin girmamawa suna gaishe shi. Koda ya ƙarasa sashen mahaifinsa sai da ya tsaya a bakin ƙofa ya yi sallama, Takawa ya amsa masa sannan ya shiga cikin ɗakin. Cike da girmamawa ya doshi saitin mazaunin mahaifinsa, yana yunƙurin russunawa domin ya gaishe shi Takawa ya kama hannunsa ya zaunar da shi cikin tsananin soyayyar irin da ɗa da mahaifi.


 "Barka da hutawa ranka shi daɗe." 

 Yarima ya furta da murmushi kwance a fuskarsa.


 "Barkanku dai Yarima! Muna fatan kun baro Mai martaba lafiya." Mahaifinsa ya furta.


 "Allah Ya taimake ka, Mai martaba ya jadadda gaisuwarsa ga duk ahalin wannan gidan, musamman ma kai ranka shi daɗe." 

 "Muna amsawa! Amma Lafiya kuka dawo kwatsam babu waya? Ko har kun gama aiwatar da komai yadda ya dace?" Shiru Yarima ya yi yana nazarin abin da zai sanarwa da mahaifinsa, a hankali ya fara motsa baki zai yi magana Takawa ya katse shi.


 "Faɗuwa ai ta yi daidai da zama, domin jiya aka kawo mana wani magani daga ƙasar Duna. A yadda muka samu labari, magungunan mai maganin suna da matuƙar kyawun gaske. Don haka za ku yi alwala, ku yi sallah raka'a biyu bayan kun idar ku zuba garin a ruwa ku wanke fuskarku da shi sau uku." Mai martaba ya ƙarasa maganar yana damƙa wa Yarima maganin a hannunsa.


 Baiwa Salame da ke ɗauke da babban tire cike da kayan marmari, ta sake raɓewa da bango tana jinjina kai da jin furucin Mai martaba. Murmushin gefen baki ta saki a cikin ranta ta furta.

 'Ai kuwa an yi shuka a idon makwarwa don haka dole na kwarawa kwaɓarku ruwa ta yi tsululu, tun lokaci bai ƙure mini ba.' 

 Jakadiya da shigarta sashen kenan ta buga mata tsawa.


"Salame uwar me kike lasa a bango da kike fitar da harshe waje?" 

Jiki yana karkarwa Baiwa Salame ta yi saurin barin jikin bangon ɗakin Takawa ta ce. 

  

 "Me zan lasa a bango kuma Jakadiya? Ke fa kika bayar da umarnin kawowa Takawa kayan..." Murmushin da Jakadiya ta saki ne ya katse kalamanta. Baiwa Salame ta sake kallonta a ranta tana tsinewa Jakadiya da irin bin diddigin da take yi musu.


 "Na san halinki sarai Salame, tamkar kwarkwasa haka kike wurin lasar maiƙo. Ki bi a sannu kuma ki dawo hayyacinki, ki tuna gidan sarauta ba kamar ragowar sauran gidaje ba ne." 

 Baiwa Salame ta haɗiyi tawu mai ɗaci, tana shirin sake yin magana Jakadiya ta ɗaga mata hannu sannan ta karɓi kwandon da ke hannunta.


 Idanun Yarima ne suka ciko da ƙwalla, ya riko hannun mahaifinsa murya a sanyaya ya furta.


 "Ina matuƙar godiya ranka shi daɗe." Murmushi Takawa ya yi masa yana sake jin soyayyar Ramadan a ransa.


 'Haƙiƙa Ubangiji yana jarraba kowanne bawa ta fuskoki da dama, tabbas na tabbata wannan lalurar da ka saukar wa Ramadan tana daga cikin layin da ƙaddarata da gindaya mini. Allah ka san ina tsananin ƙaunar wannan bawa, Ubangiji ka ba shi lafiya.' Takawa ya furta a ransa idanunsa suna yunƙurin zubar da ƙwalla.


 "Ranka shi daɗe, ba don kada na bayyanawa duniya raunina ba, da sai na ce kawo yanzu ya kamata mu haƙura da nemawa idona maga..."  

 Nan take idon mahaifinsa ya yi jajir kamar sabon barkono, ya dube shi rai a bace ya ce.

 

 "Koda wasa, kada mu kuskura mu sake jin kalmar rauni a bakinku. Domin rauni ba zubin gida da tsarin gadonmu ba ne, ku kula sosai domin ba kowanne furuci za ku dinga furtawa ba, kada ka manta masarauta tana ɗauke da idanu marasa adadi. Kuma kowanne ƙwayar ido da kuka sani a masaraurar nan tana kanka." Cikin gamsuwa da ƙwarin gwiwa Ramadan ya jinjina kai yana sake zubawa mahaifinsa godiya.


 Bamaguje yana gama magana bai jira jin ta bakin Umaima ba, ya shiga cikin kogon tsafinsa. A kan wata ƙasaitacciyar kujarar tsafinsa ya zaunar da ita, tana yunƙurin tashi ya damƙi wata jar ƙasa ya watsa a daidai wurun da take. Lokaci ɗaya wata baƙar yana ta mamaye ta, duk yadda ta kai ga son motsawa ta kasa. Bamaguje ya saki murmushi mai tarin ma'anoni, sannan ya saka kai ya fice daga ɗakin. Wani surƙuƙin daji ya shiga, bai yi tafiya mai nisa ba ya murza wani guru da ke ɗaure a damtsen hannunsa. Lokaci ɗaya wata baƙa guguwa ta mamaye daidai wurin da yake tsaye, kamar ƙiftawar ido sai ganinsa ya yi a bakin murgujejiyar bishiyar kukar.


 "Ko a tarihin da kake ba ni ban taɓa riskar bishiyar kuka mai girman wannan ba mahaifina!" 

 "Wannan bishiyar ana yi mata laƙabi da tudun tsira, kakana boka Isshu ya ce mini a ƙalla bishiyar nan tana da shekara sama da dubu ɗari biyar. Duk wani abu da yake neman gagare maka, kana iya kawo kokenka a wurin bokayen aljanu da mutanen ciki." Bamaguje ya sauke ajiyar zuciya bayan ya tuna tattaunawarsa da mahaifinsa. A hankali ya fara takawa har ya ƙarasa bakin kogon bishiyar mai kama da kogon ƙaton dutse. Tafiya ya yi kaɗan, ya hango shi zaune a katafariyar kujerarsa.


 "Ban yi mamaki da ganinka ba, domin na san duk taƙamar kumfa ta sabulu ce Bamaguje." Gajere kuma kakkauran wani mutum, mai ɗauke da suffa mai ban tsoro ya furta cikin isa da ƙasaita.


 "Na yi rantsuwa da gundarin tsafin da na gada a wurin iyaye da kakannina, da a ce buƙatar ta takaina ce ko zan mutu ba zan nema a wurinka ba Boka Jassu."

 Bamaguje ya furta yana jin wata izza ta isa da taƙamar tsafi na yawo a kansa.

 Kujerar da Boka Jassu yake zaune ce ta kama da wuta, sai da ya saka hannu ya damƙi harshen wutar sannan ya miƙe ya fara takawa har zuwa gaban Bamaguje.


 "Wanne mai sa'a da dace ne ya turo ka wurina?"

 Boka Jassu ya furta cike da tsantsar mamaki.


"Masarautar Huddam! 'Yarka wato 'yar cikina Umaima, sai kuma jikana Basiru."

 Bamaguje ya furta cikin ɗacin zuciya da ɓacin rai.



***

Ummou Aslam Bint Adam🌚