Chapter 1
by @oumamjad01
*💦ANYI WALƘIYA💦*
MALLAKAR
*Faiza Almustapha Murai*
( Fa'eehbg )
&
*Maryam Muhammad Bello*
(Oum Amjad)
Daga Alƙalamin✍️
Oum Amjad
Fa'eehbg
*Haɗakar marubutan ƙungiya biyu*
*HAZIƘAN MARUBUTA*
AND
*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*
*Wannan labari sadaukar ne ga ɗaukacin Masoyan mu na nesa da na kusa,muna Alfahari da ku,muna ƙaunar ku,kuma muna godiya sosai.🥰Allah ya bar zumunci.Amin.*
_____________________________________
*Muna roƙon Ubangiji kamar yadda muka fara rubuta wannan labari lafiya Allah yasa mu kammala shi lafiya,Ya Ubangiji ka bamu ikon isar da saƙon da muke son isarwa.Amin.*
*Wannnan labari ƙagaggen labari ne bamuyi dan tozarta kowa ba,idan ki/ka ga yayi shige da rayuwar ki Ayi muna afuwa haka labarin yazo muna.*
*Bamu yarda A juya muna labari ta kowa ce siga ba sai da izinin mu idan ki/ka yi da gangan Mun barki da Rabbi.Domin kayan mune a barmuna abun mu.🤗*
*Bismillahir Rahmanir Rahim*
*( RUBUTUN MARUBUTA )*
*( Dan Allah idan anyi sallah k ajiye karatun wannan littafi d.s kije ki sauke farali, banda barin mai gida gantale,sannan banda barin yara na gararan ba,banda barin girki na ƙonewa, kuma kina nan kin nace wa book ayi haƙuri ayi aikin gida,akula da gida in an gama sannan a cigaba da karatun*.
*Idan har aka kira sallah da sauran su baki ajiye ba gaskiya bamu da laifi wannan laifin ki ne.✍️)*
<<<<<>>>>>>
Book one.
Page 1.
Yammaci ne mai cike da ni'ima kasancewar yanayin bazara da yafara ganyayyaki suna kaɗawa A hankali musamman kasancewar gurin kamar bayan gari haka da ita tuwa sukayi wa shinge.Nishi take saukewa a hankali bayan wani ƙaton iccen da take zaune a bayan sa da tulelen ciki a jikin ta wanda a ƙalla zai kai wata shidda haka.Ɗago kan ta da tayi ne cikin razana jin takon tafiya yana doso ta ne ya bamu damar ƙarewa kyakkyawar fuskar ta kallo.Babbar mace ce kyakkyawa da ita tana sanye cikin wata riga mara nauyi kamar ta bacci kanta babu ɗan kwalli ƙananan kitson da ke kanta gashi nan kwance abayan ta tayi Busu Busu da ita daganin ta galabaice take.
Wasu hawaye ne masu zafi suka silalo mata tana tunanin Tata ta ƙare ƙara tabbatar da su ɗin ne dai mutanen da ke neman illata rayuwar ta da ta jaririn cikin ta wanda baizo duniyar ba ma.
Share hawayen tayi tare ta shafa cikin nata tana ƙara shan jinin jikin ta cikin tausayin kanta da na jaririn nata.
Muryoyin su ne taji suna magana wadda ke nuna ita ɗin suke cigaba da nema kamar tun ɗazu da asuba da suka biyo ta a zaton ta ta rabu da su ashe basu ɓace ba.Suna bibiye da ita.
" Wai ita wannan a saranyar ina ta shiga ne tun ɗazu sai fama muke yi da ita bata gashi za,a rage muna kuɗin mu idan bamu cika aiki ba "
Rainbow kenan wanda ya kasance shugaban yan ƙwayar ko muce thugs.
Shine yake magana baki akarkace kai da ganin sa kaga cikakken ɗan hau na gidi bakin sa har ya karkace saboda shaye shaye da ƙwayancin sa.
" Ogaahh "
Wani daga cikin yaran sa ya furta baki akarkace.Sannan ya ƙara furtawa bayan ganin ogan nasu ya maido da hankalin sa kansa.
" Kawai mu ƙara bincikawa nan guraren nasan bazata wuce nan ba,wannan tulun na jikin ta bazai bata damar yin tafiya mai nisa ba,Amma fa tayi ƙoƙari ace tun asuba mun kasa kamata sai wahala take bamu ".
Yakai ƙarshen zancen yana cije baki irin na yan hau.
Kai Rainbow ya girgiza kafin ya furta wani abu kawai suka ji motsi....a chan gaba dasu sai kuma suka ji ƙara kamar ta sautin mutun.
Itakuwa wannan mata dake sauraren su cikin tashin hankali jin furucin da yaron rainbow yakeyi bata an kara ba sai ga wani ƙaton kadangare ya faɗo mata ajiki cikin tsoro da neman agaji ta saki yar ƙaramar ƙara wadda bata wani fita sosai saboda yadda take agalabaice.Miƙewa tayi a hankali cikin tashin hankali tuna yanayin da take ciki bayan saukar ƙadangaren ajikin ta.
Kama hanya tayi tana cigaba da tafiya cikin fitar hayyaci hawaye na mata zuba a idanu.
A ɓangaren su Rainbow da yaran sa kuwa da sauri suka bazama fahimtar itaɗin ce dai maganar yaron sa ta tabbata.
Haka suka cigaba da Binta har yakai sun fara hango ta kasancewar sun fita kuzari kuma energy na mace dana na miji ba daya ba ga kuma tsohon cikin jikin ta.
" Gata chan ku kama muna ita ".
Rainbow ya faɗa a hasale bayan hango ta.
Da sauri kuwa yaran sa sukayi kanta.
Sai dai cikin ikon ALLAH kafin su an kara ta ɓace musu domin kuwa wata hanya ce ta faɗa wadda ta rabu gida biyu wanda sai ka shiga daga cikin zaka gane hakan.
Bayan shigar su gurin kuwa sai suka rasa ta wane gefe tabi sai dai cikin dubara suka raba kan su gida biyu inda suka cigaba da kutsa kai cikin dajin kamar masu farautar namun daji.
À ɓangaren wannan mata kuwa taci gudu har ta gaji bayan shigar ta hannun dama inda anan ma ta samu wata yar ƙaramar hanya wadda ba kowa ke iya gane hanya bace a cikin gurin.Dai dai ta kawo cikin wasu manyan gonakki ta faɗi ƙasa cikin galabaita da neman ceto rai ga wata mahaukaciyar ƙishirwa da ke taso mata Babyn cikin ta kuwa sai motsi yake yi yana shure shure kamar shima agalabaice yake.Dishi dishi ta fara gani bayan kaiwar ta ƙasa cikin ƙatuwar gonar da ake ta faman cire abun da Allah ya wadata ta da ita.Tun tana fahimtar yadda duniyar ke juya mata har Takai Numfashin ta yaɗauke ƙaf ta faɗi summammiya a gurin.
***
A ɓangaren Su Rainbow cikin jin haushin rashin samun ta akaro na biyu suka yanke shawarar kiran wanda yasaka su aikin.
Dan shaida masa yadda ake ciki kamar ɗazu.
FUSKA BIYU.shine sunan da yayi dialing a call log ɗin sa wanda da lama ma da ita kawai ake waya da wayar yau dan duka sunayen ne kai.
Kira ɗaya aka ɗaga kiran.
" Hello Rainbow ya ake ciki hope dai aiki yayi kyau "?.
Wannan itace tambayar da mamallakiyar wannan lamba wadda aka yi saving da fuska biyu ta furta kuma da alama mace ce saboda Muryar da ke kamar handsfree ana ɗan jin fitar zancen ta.Inda Tayi tambayar cikin jiran jin amsar sa wanda ke nuna a ƙage take dama abun da take jira kenan.
" Hajiya wallahi taƙara kufcemuna ".
Shine abun Rainbow ya furta mata kai tsaye cikin hau ɗin sa.
" Innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un Rainbow again Baku ganta ba kaman ta da sharaɗi na narage muku kudaɗe,me yasa kuka yi saƙaƙe haka har kuka bari kuka rasa ta akaro na biyu,yanzu dai Rainbow deal zai ƙara hawa tabbas idan kuka nemo ta kuka aiwatar da abinda nasaka ku zan ƙara muku da abun da baku yi zato ba,ina jiran ku da Albishir mai Daɗi ".
Ƙitt ta kashe waya.
Rainbow dake sauraren ta shida sauran yaran nasa cikin jin Haushin Hajiyar suka haɗa baki suna jan tsaki kafin Rainbow ya kalli wayar kamar itace gaban sa ya bata ƙatuwar harara yana Furta " Matar nan shegiyar gari ce,tasan dole mu kara himma shiya sa ta furta muna haka ,Ni Na gaji ma tun safe muke abu ɗaya sai faman ɗurawa cikina sigari nake yi,na gaji,Amma tunda tace haka mu ɗan ƙara zagayawa ".
Yakai ƙarshen zancen yana ƙara furta " Fuska biyu,Guba,Fuska biyu aganki a dara ,fuska biyu mai zuciyar shaiɗan,Fuska biyu badai imani ba " ".Sannan ya kece da wata mahaukaciyar dariya inda suma ya ran nasa suka taya sa.
Har sun kama hanya sai ɗai daga cikin su wanda yake shine na gaban goshin Rainbow ya furta " Oga Kawai mu samu guri mu ɗan yada zango bayan yan mintuna ko awaya haka sai mu kira ta mu shaida mata mun kashe ta da yaron cikin nata mun jefa ta rafi ma acikin dajin da muke agabanmu ruwa ya wuce da ita,tunda dai mun san Asirin mu bazai tonu ba kaga riba biyu mu karɓe kuɗin mu sannan in taji daɗin aiki zata iya neman muna wasu customers irin su hajiyoyi ".
Wata irin dariya Rainbow ya kece da ita kafin ya daki kafaɗar yaron nasa yana furta " kai mugun ƙwaro ashe haka kanka ke ja shiya sa nake ji da kai,ka kawo shawara mai kyau haka za,ayi ".
Wuri kuwa suka samu suka zauna suna ɗan taɓa fira kaɗan cikin hau ɗin su dan kamar ma wasun su a buge suke.
🌼🌼🌼🌼🌼
*DUKKU*
A wannan yanki akwai makiyaya sosai kama daga Fulani Daji, Fulani Gida, yanki ne mai albarka da yawan mutane, yana ɗaya daga cikin yanku nan da ake alfahari dashi a cikin "Garin Gombe".Gabas wanda yake fuskantar ƙauyen "DUKKU" Ƙauyen Dukku, Faffaɗa kuma yalwataccen gari ne iya ganinka da hangenka, wanda ya wadatu da korayen shuke-shuke tsarara da kuma shokoki masu kyau nau'oka daban-daban masu kyau, wanda ubangiji ya hukunce su da fitowa cikin wannan garin mai tarin ni'imomi.
Wani ɗan madaidaicin gida ne irin na Alhazawan nan na cikin ƙauye waɗan nan matasan ƴan'mata suka shiga, gida ne dai'dai na masu rufin asiri, daga kan kofar gidan har izuwa fentin gidan dukka sun nuna alamun mai gidan mutun ne mai zuciyar yi, kun san ba neman kuɗin ba, zuciyar yi ita ce, akwai masu kuɗin da kuɗinsu basu ciwuwa kamar kuɗin cizo suke, akwai kuma wanda zaku gani talaka ne, amma mai zuciyar yi, baya samu sosai kamar sauran mutane, amma da yake akwai zuciyar yi ɗin, sai ku ga ƴaƴansa da gidansa duk kusan dai'dai da na wani mai kuɗin, to haka wannan gidan yake komai mai kyau zaku ga ya sayawa ƴaƴansa da matarsa ɗaya gwanin burgewa.
Ko'ina na cikin wannan gida siminti ne, babu ƙasa kamar ba gidan ƙauye ba, an wanke ko'ina fes babu alamar datti ko kaɗan, kana sako kafarka a cikin gidan ma wani daddaɗar kamshin turaren wuta ne zai daki kofofin hancinka, gwanin burgewa gidan yasamu mai kula da shi yadda yakamata.
Babbar parlour ce a tsakiya mai ɗauke da ɗakuna huɗu a cikinsa, kowane ɗaki da toilet a cikinsa, ɗaya na matar sai na waɗan nan yaran da suka shigo yanzu sai na mai gidan sai kuma can gefe akwai wani ɗaki Babba mai ɗauke da toilet na saukar baƙi, filin tsakar gidan yana da girma sosai babu laifi, akwai kitchen a tsakar harabar gidan sai toilet ɗaya da ake yi karshen ginin tsakar gidan.
Wannan mai gida yana da ƙoƙari sosai, har da bohol suke da shi a cikin gidan nasu mai makon rijiya kamar sauran gidajen ƙauye da suke da rijiya idan babu sai dai suje waje su ɗebo, suna da ruwa available, ruwa abokin aiki kenan abokan rayuwa idan babusu ai rayuwa bazatayi ba.
Parlourn nasu tamkar sauran kowani parlourn na masu rufin asiri ne irin gidajen birni , kujeru ne set ɗaya manya manya masu laushi, launin brwon , sai ƴar madaidaiciyar TV plasmarsu, akwai ƴar karamar freezer a ciki ta kusa da TV, sai wasu kyawawan jeren flowers da aka kawata parlourn da su, fanka ce garesu , sai dai kasan parlourn nasu fa tiles ne mai kyau da zanen flowers a jikinsa, launin milk, ya sha mopping sosai, sam babu alamar datti, ga karamar welcome carpet a bakin kofa, abin dai gwanin birgewa da ban sha'awa, sai tashin kamshi wannan parlourn yake yi, ko'ina tsab kamar ba'a amfani da abubuwan cikinsa.
Tsafta akwai daɗi, kai da kanka idan ka tsaftace waje sai kaga ya yi wani irin masifar kyau, komai talaucin mutun idan yana da tsafta yana da sha'awar kallo wlh a ko ina zai iya shiga.
Bakinsu ɗauke da cikakkiyar sallama irin ta addinin Musulunci waɗan nan yara suka shigo cikin gidan nasu.
Daga cikin ɗaki aka amsa masu cikakkiyar sallamar tasu tare da cewa. "Ƴan mata na an dawo?".
Babban cikinsu ce ta amsa da. "E mama mun dawo".
Tana magana tana cire hijabin jikinta, kafin ta wuce izuwa cikin parlourn.
Ita kam karamar dama tun shigowarsu ta sanya kai izuwa cikin parlourn da sauri abinta tana faɗin. "Mama baba ya aiko mun da kwakwarmu?"
"Aa babbanku bai aiko ba" cewar mamar tasu.
Babansu ɗan kasuwa ne cikin kasuwar ƙauyensu yake da shagon sai da kayan masa rufi da yake sayowa a cikin birnin gombe, yana kuma noma dan Babbar gonarsa tana bakin hanyar shigowa cikin garin Dukku, yana noman kayan abinci yakai birni yasai da.
"Familyn Alhaji Yusuf kenan da matarsa Sa'adatu ƴaƴansa ukku mata biyu namiji ɗaya Hafsa ce Babba sai Ruƙayya sai kuma auta Aliyu wanda shekararsa biyar yarasu sakamakon jinyar wuni guda Allah yakarbi abunsa..........."
A wannan yanki akwai makiyaya sosai kama daga Fulani Daji, Fulani Gida, yanki ne mai albarka da yawan mutane, yana ɗaya daga cikin yanku nan da ake alfahari dashi a cikin "Garin Gombe".Gabas wanda yake fuskantar ƙauyen "DUKKU" Ƙauyen Dukku, Faffaɗa kuma yalwataccen gari ne iya ganinka da hangenka, wanda ya wadatu da korayen shuke-shuke tsarara da kuma shokoki masu kyau nau'oka daban-daban masu kyau, wanda ubangiji ya hukunce su da fitowa cikin wannan garin mai tarin ni'imomi.
Wani ɗan madaidaicin gida ne irin na Alhazawan nan na cikin ƙauye waɗan nan matasan ƴan'mata suka shiga, gida ne dai'dai na masu rufin asiri, daga kan kofar gidan har izuwa fentin gidan dukka sun nuna alamun mai gidan mutun ne mai zuciyar yi, kun san ba neman kuɗin ba, zuciyar yi ita ce, akwai masu kuɗin da kuɗinsu basu ciwuwa kamar kuɗin cizo suke, akwai kuma wanda zaku gani talaka ne, amma mai zuciyar yi, baya samu sosai kamar sauran mutane, amma da yake akwai zuciyar yi ɗin, sai ku ga ƴaƴansa da gidansa duk kusan dai'dai da na wani mai kuɗin, to haka wannan gidan yake komai mai kyau zaku ga ya sayawa ƴaƴansa da matarsa ɗaya gwanin burgewa.
Ko'ina na cikin wannan gida siminti ne, babu ƙasa kamar ba gidan ƙauye ba, an wanke ko'ina fes babu alamar datti ko kaɗan, kana sako kafarka a cikin gidan ma wani daddaɗar kamshin turaren wuta ne zai daki kofofin hancinka, gwanin burgewa gidan yasamu mai kula da shi yadda yakamata.
Babbar parlour ce a tsakiya mai ɗauke da ɗakuna huɗu a cikinsa, kowane ɗaki da toilet a cikinsa, ɗaya na matar sai na waɗan nan yaran da suka shigo yanzu sai na mai gidan sai kuma can gefe akwai wani ɗaki Babba mai ɗauke da toilet na saukar baƙi, filin tsakar gidan yana da girma sosai babu laifi, akwai kitchen a tsakar harabar gidan sai toilet ɗaya da ake yi karshen ginin tsakar gidan.
Wannan mai gida yana da ƙoƙari sosai, har da bohol suke da shi a cikin gidan nasu mai makon rijiya kamar sauran gidajen ƙauye da suke da rijiya idan babu sai dai suje waje su ɗebo, suna da ruwa available, ruwa abokin aiki kenan abokan rayuwa idan babusu ai rayuwa bazatayi ba.
Parlourn nasu tamkar sauran kowani parlourn na masu rufin asiri ne irin gidajen birni , kujeru ne set ɗaya manya manya masu laushi, launin brwon , sai ƴar madaidaiciyar TV plasmarsu, akwai ƴar karamar freezer a ciki ta kusa da TV, sai wasu kyawawan jeren flowers da aka kawata parlourn da su, fanka ce garesu , sai dai kasan parlourn nasu fa tiles ne mai kyau da zanen flowers a jikinsa, launin milk, ya sha mopping sosai, sam babu alamar datti, ga karamar welcome carpet a bakin kofa, abin dai gwanin birgewa da ban sha'awa, sai tashin kamshi wannan parlourn yake yi, ko'ina tsab kamar ba'a amfani da abubuwan cikinsa.
Tsafta akwai daɗi, kai da kanka idan ka tsaftace waje sai kaga ya yi wani irin masifar kyau, komai talaucin mutun idan yana da tsafta yana da sha'awar kallo wlh a ko ina zai iya shiga.
Bakinsu ɗauke da cikakkiyar sallama irin ta addinin Musulunci waɗan nan yara suka shigo cikin gidan nasu.
Daga cikin ɗaki aka amsa masu cikakkiyar sallamar tasu tare da cewa. "Ƴan mata na an dawo?".
Babban cikinsu ce ta amsa da. "E mama mun dawo".
Tana magana tana cire hijabin jikinta, kafin ta wuce izuwa cikin parlourn.
Ita kam karamar dama tun shigowarsu ta sanya kai izuwa cikin parlourn da sauri abinta tana faɗin. "Mama baba ya aiko mun da kwakwarmu?"
"Aa babbanku bai aiko ba" cewar mamar tasu.
Babansu ɗan kasuwa ne cikin kasuwar ƙauyensu yake da shagon sai da kayan masa rufi da yake sayowa a cikin birnin gombe, yana kuma noma dan Babbar gonarsa tana bakin hanyar shigowa cikin garin Dukku, yana noman kayan abinci yakai birni yasai da.
"Familyn Alhaji Yusuf kenan da matarsa Sa'adatu ƴaƴansa ukku mata biyu namiji ɗaya Hafsa ce Babba sai Ruƙayya sai kuma auta Aliyu wanda shekararsa biyar yarasu sakamakon jinyar wuni guda Allah yakarbi abunsa..........."
wasu dogayen riguna ne ash, iri ɗaya kayan komai nasu iri ɗaya ne, tundaga kayan sawa zuwa takalmi ban bancin kawai shine na Hafsa sunfi na Ruƙayya girma saboda tafita shekaru, ita Hafsa tana da 13 yeah Ruƙayya na da 10.
Fitowa suka yi sukayi zuwa tsakar gida wajen mama dake aikin abinci, su tayata dan haka sukeyi indai ba tahafiz sukeje ba ko boko shine kawai zatayi aiki ita kaɗay, kafin zuwa magarib har sun ƙarasa komai dama kaɗan ne bata ƙarasa ba suka dawo jin kiran sallah mama ta musu magana suka tashi,
Famfo tsakar gidan suka je suka kunna, Hafsa ce ta fara gabatar da alwala kafin ta bawa Ruƙayya waje ita ma ta ɗauro alwalar, da alamu mamansu ce ta sabar masu da yin komai cikin tsari,
Ciki suka koma, dai'dai lokacin aka kawo wutar nepa, sallah suka je cikin bedroom nasu da yake tsab tsab suka gabatar, ita ma mamar alwalar ta ɗaura ta wuce nata bedroom ta gabatar da tata sallah.
Abun mamaki cikin nutsuwa suke gabatar da sallar nan tasu tamkar wasu manya Allah ko manyan ɗay ɗayko ne suke sallah cikin natsuwa amma waɗan nan ƙananan yaran sunyita yadda yadace.
Bayan sun idar ne suka fito parlourn, suka zauna basu daɗe da shigowa ba mamansu ta fito parlourn bayan ta zauna suka gaida ita ta amsa musu cikin sakin fuska, sakamakon wasu iyayen da basa amsawa balle wani sakin fuska.
Da gudu Ruƙayya ta nufi kofar fita daga parlourn jin an taɓa kofar gida, faɗi take yi oyoyo Baba oyoyo Baba. Da sauri Hafsa ma ta rufa mata baya, a take suka fara zuba murmushi na ganin mahaifinsu, sai dariya sukeyi.
shi sai dariya yake musu hannunsa yana rike da wata leda irin mai zanen baƙi da yellow, kayan tsarabarsu ne a cike a cikin ledar.
Hafsa tana zuwa ta fara kiciniyar karɓawa baban nasu ledar hannun nasa, ita kam Ruƙayya tuni ta yi tsalle ta haye jikinsa tana dariya har da kyakyatawa.
"Rukyyn Baba Anyi yi sallah?".
Shi ne tambaya ta farko da wannan uban na garin ya fara yi masu, ya yi maganar kuma yana sakewa Hafsa ledar fruit dake a hannunsa, yaran kirki, yana da kyau duk wata uwa ta koyawa ƴaƴanta karɓar duk abun da mahaifinsu ya shigo da shi, hakan shi ne tarbiya mai kyau, daga mata har maza matan zatayi musu amfani gidan aurensu kema za'a samiki albarka a duk inda suka shiga.
Hafsa ce ta bashi amsa da. "Mun yi baba, mama ma tayi tana parlour".
Ita kuwa Zainab Baba ya ɗagata sama suka nufi cikin parlourn.
Bakinsa ɗauke da cikakkiyar sallama ya shigo cikin parlourn.
Mama ta amsa mashi sallamar.
Ƙarisowa ciki ya yi tare da nufar ɗaya daga cikin kujerun dake a cikin parlourn ya zauna, har cikin ransa yake jin daɗin shakar wannan daddaɗar kamshin turaren wutar da yake tashi a cikin parlourn Shiyasa yake alfahari da kasan cewar Sa'adatu matarsa, yazauna yana ɗauke da Ruƙayya a saman kafaɗarsa.
Ajiye ladar da ta karɓo daga hannun baban nata Hafsa ta yi a tsakiyar parlourn, sannan ta yi sauri ta bi bayansa kan kujera.
Maman takawowa babansu ruwa mai sanyi data ɗauko a firezer da cup ta tsiyaya masa , ta bashi yakarba yana murmushi bayan yasha taƙara masa barka da dawowa, kafin ta miƙe zuwa ɗakinsa dan ta haɗa masa ruwan wanka kamar yadda tasabayib masa.
Bedroom ɗinsa ta wuce ruwan wanka ta haɗa masa, kafin tafito har yashigo ɗakin ta taimaka masa ya rage kayan jikinsa ya wuce toilt ɗin, ta ɗauke kayansa ta aje inda yadace tafito masa da marasa nauyi , ta zauna jiransa yafito
Bai daɗe ba yafito taimaka masa tayi ya shirya ya ɗauko turarensa mai daɗi zai fesama jikinsa,tasa hannu ta karba turaren tafara fesa masa tana ƙara zuzutashi wai yayi kyau sosai.
Babu ƙarya fa Babansu Hafsa yana da kyau sosai fari ne tass yafi mamarsu kyau nesa ba kusa ba, Haka ma maman tasu tana da kyau sai dai ita chacolate colour ce, Su Ruƙayya duk babansu suka ɗauko sai Hafsa da taɗan ɗebo mamansu amma ba duka ba.
Bayan ta gama fesa mashi turarensa ɗin ne ta ɗauko mashi wayarsa babba da karamar da suke a saman shinfiɗaɗiyar bed ɗinsa, gadon ya sha gyara kam, babu karya maman Hafsa akwai ƙoƙari wajen sake jiki ta yi aikin gidanta da kyau da kyau, yanzu haka wannan kayansa na shan iska ita take wanke masa su ta goge suyita walƙiya kamar wankin inji, chacul na wuta ita fa maman Hafsa wayayi yace ko cikin karkaran , da alama gugan kaya baya yi mata wahala, dan harta bedsheet dake a shunfuɗe a saman bed ɗin nan ya sha guga sosai, da yake ma sun saba shan guga sai ka gansu da karin gugan ya fito baro baro, ya riga ya kama kayan, to abu ne da ake yi ba jiya ba ba shekaran jiya ba, an jima ana yinsa, dole kunga su kama karin guga, duk wani abu da yashafi har kar wayayi to da Maman Hafsa zakiji ana kwatance a garin, Ai da cikin birni take wllh sai tafi haka waye wa Allah kuwa.
Parlourn suka fito, a nan ya isko sanyin idaniyarsa wato ƴaƴan nasa sune komai nasa a duniya, Hafsa tana kallon Tv, ita kuma Ruƙayya tana rike da wayar mamanta tana buga game.
"Rukkyn Baba zan je masallaci amin addu'a".
Ya faɗa yana nufar kofar fita daga cikin parlourn. Har suna rige rige ita da Hafsa wajen zuba mashi addu'ar a dawo lafiya Allah ya tsare ya kiyaye hanya.
Da amin ya amsa masu kafin ya fice. Har tsakar gidan maman nasu ta rako shi kafin ta dawo parloun suma suyi sallahr issah'i kafin yadawo.
A parlourn ta isko su Hafsa a saman Sallaya, sallah suke yi, wucewa nata bedroom ɗin ta yi, dan ta yi sallar issha.
Bayan sun idar da sallar, zama suka yi a saman sallaya suna bitar karatunsu, a haka babansu ya dawo daga masallaci ya samesu, a lokacin kuma mamansu ta idar da nata sallar har ta zo ta ɗauko kayan abinci kafin ya shigo tana ajewa tsakiyar parloun.
A parlourn ta isko baban nasu tare da su Ruƙayya, suna jiranta tazo ta zuba musu abinci.
Plate ta jawo ta zuzuba ma kowa jallof ɗin shinkafa da salat ta turama kowa gabansa ta zubama kowa ruwa a cup.
Abincin suka fara ci cikin nutsuwa, maman Hafsa ba dai iya girki ba, ta ƙware sosai, idan kana cin girkinta idan ka yi wasa sai ka fara zuba santi ba tare da ka sani ba, saboda daɗi da iya tsara girkin sai kace wata chef🤗......
***
*GOMBE*
" Hajiya aiki yayi kyau mun aiwatar da umurnin ki har da ƙari ma domin kuwa gawar ta namun daji muka bawa da suka kusa chanye wa sai muka jefa ta a cikin rafi tabi ruwa nasan daga chan kada zata chanye ta".
Rainbow ne yake zuba wannan bayanin bayan yada zangon da suka yi anan cikin dajin wanda sai da suka ɗauki kusan awa ɗaya sannan suka kira ta suka shaida mata hakan kamar yadda suka tsara da wannan ƙarin da suka ƙara haɗawa ayanzu.
Wata iriyar dariya aka kece da ita a wanchan ɓangaren kafin ta furta cikin bushewar zuciya da alamar rashin imani " Lallai dole wannan aiki naku ya ci ƙari aikin ku na kyau shiyasa Ako da yaushe ni kune karnuka na,dan haka yanzu zaka ji alert sai kuma wani karon idan ta ƙara tasowa duk da nasan na rufe ƙofa har abada ".
Mai fuska biyu kenan tana gama zancen ta kuwa ta yanke kiran ta ƙitt kake ji ta yanke wayar.
Rainbow kuwa wani munafukin murmushi yayi yana lumshe idanun sa da suke cike da maye wanda yayi tatil shida sauran yaran sa.Sannan ya furta " Shegiya ƙarya,shegiya Naira cin halak ɗin ki wahala cin haram ɗin ki wahala, kutt Kai Amma fa asaranyar nan ta raina muna da wayau mune karnukan ta hmm zaki sha mamaki kuwa karnuka sai kin ga komai ya buɗe miki"...Dariya dukkanin su suka kece da ita kafin suka bar yankin baki ɗaya wata lanƙwasashshiyar mota da suka ajiye a gefen titi suka hau suna barin gurin suna dosar cikin gari cikin tuƙin ganganci.
*ABUJA*
" Areef,Aseef Ku zo nan ".Wata mata ce da bazata wuce shekara Arba'in zuwa hamsin ba ke wannan zancen bayan kutsa kan da mukayi a wani haɗaɗɗen gida mai rai da lafiya tunda ga tsarin sa daga waje zaka gane hakan an zuba Naira kuma Naira na aiki a cikin sa.Babbar macen kuwa da ke magana tana zaune ne a kan two sitter Dake cikin ƙaton falon na alfarma wanda yaji kayan more rayuwa,Falo ne mai kama da gari guda kasancewar sa ƙato ta faɗin sa da tsawon sa.
Sai da ta sake maimaita maganar Sannan sai ga wasu samari guda biyu sun ɓullo bayan buɗe ɗai daga cikin ƙofofin dake cikin ƙaton parloun,Tun daga yanayin shigar su zaka fahimci twins ne twins ɗin ma identical domin kuwa kamar su da juna babu banbanci a ƙalla a shekaru zasu yi shekara ishirin da huɗu haka.
Kai tsaye suka doso inda take zaune ta kafe su da idanun ta ji take kamar ta tashi ta zazzane su sai dai a yanzu kota ce ta dake su a banza kasancewar sun tasa sai dai hankalin ne wala rashin jin magana kala kala.
" Amma gamu ".
Suka haɗa baki gurin furtawa cikin natsuwa kamar wasu salihhai.
Kai kawai Matar nan da suka kira Amma ta girgiza da alama mahaifiyar su ce domin kamar su da ita a bayyane take.
Tun daga yanayin hasken fatar tasu.
Ɗan ƙara kallon su tayi.Sannan ta furta. A hankali " Wai twins bakwa gajiya ne fisabilillah Areef,Aseef girma kuke ƙarawa Amma babu hankali yanzu abinda kuka yiwa Yar wajen Yagwal gwal kun kyauta haka kawai kun sako mata ya gaba,Har da duka Areef haka na baku tarbiyya kullum cikin saka ni surutu dama ace shi wanda kuke tsoro yana ƙasar da na rage zafi Amma ko yanzu ba komai ai yana hanya karku kimtsa kan ku,ku cigaba da abinda kuke yi ".
Tsurru sukayi da ido suna kallon ta jin furucin ta na ƙarshe wai yana hanya.Dukkanin su sai da ƙirjin su ya buga take cikin tashin hankali suka kai ƙasa suna riƙe gwaiwarta suna furta " pls Amma dan Allah yaushe zai dawo ".?
Sagage tayi tana kallon su Bama faɗan ta suke yiwa ba kenan furucin ta na ƙarshe.A hankali ta sauke murmushi guntu tana girgiza kanta tana furtawa a zuciyar ta mai hali baya chanza halin sa.
Bayan wucewar ta kuwa ɗaramm Areef wanda yafi Aseef ƙwaranci duk da kasancewar shine ƙarami ya furta .
" Bros kaji Abunda Amma ke faɗa wai zai dawo ranar fa munyi waya dashi bai ce muna zai dawo ba ".
" Yo to ya za,ayi ya faɗa muna dama ".
Areef yayi furucin a natse dan shi bai cika tsoro Sosai ba kamar Aseef.
Ɗan Jimm sukayi kafin Aseef ya katse shirun nasu yana furta " Sai munyi maganin wacchan ya gwal gwal ɗin Bros nasan ita ta gayawa Amma wannan magana da alama bataji Tausayin jikin yar ta ba ".Dariya suka sanya gaba ɗayan su.
Yar ƙaramar Muryar tace da tayi sallama a cikin falon ta ratsa kunnuwan su ta sanya su kowanne ɗagowa yana zuba mata idanu.
Daburcewa tayi sai ta toge Agurin sanin halin yayyen nata.Ga kuma mugun tsoron su da take ji.
Ƙaramar yarinya ce wadda bazata wuce shekara goma sha biyar ba ko sha shidda.
Sanye cikin uniform masu kyau wayen da suka karɓi fatar ta tayi kyau sosai cikin riga da siket ɗin sai yar ƙaramar hula da bata rufe kan ta gaba ɗaya ba.Kasancewar makarantar tasu haka suke shigar su.
Ƙaramin lunch box ne a hannun ta da jakarta maƙale a bayan ta.
Wani mugun tsaki da Aseef yaja ne ya sanya yan hanjin cikin ta kaɗawa kafin ya miƙe yana barin falon cikin yin ƙwafa bayan tunawa da zancen Amma ɗin.
Shima Areef ba tare da ya ƙara furta komai ba ya kama hanyar da ɗan uwansa ya bi bayan zabga mata uwar harara da yayi.
Hawaye ne dake shirin zubowa akan kyakkyawar fuskar ta ta goge da sauri kasancewar ta yiwa Wani daga cikin yayyen nata alƙawarin ba zasu ƙara zuba ba.
Ɗago da kyakkyawar fuskar ta tayi tana ƙarewa falon kallo kamar yau ta fara ganin sa.Wani shuɗaɗɗen lamari take tunowa acikin gidan inda take taji komai ya fice mata arai musamman yadda su Areef suke wulaƙanta ta kamar ba ƙanwar su ba.
" Aah yan makaranta Andawo ".
Wata mata ce ta fito daga cikin kitchen tana wannan zance.
" Eh Ya gwalgwal na dawo ".
Ta bata Amsa cikin sakin fuska da ƙawata fuskar ta da murnushi.
" Sannu Farha kinji ayi ta haƙuri komai mai wucewa wayen nan yayyen naki fitinnu duk zasu bar abinda suke yi kar ki kinji ki dage da karatun ki kawai ".
Kai Farha ta gyaɗa tare da yin Murmushi tana ayyana maganar Ya gwal gwal a zuciyar ta inda ace su Areef zasu ji take kira su fitinannu da yau sai kwana gidan ya gagare ta ya lafiya kura bare ma an taɓa ta.
" Bari naje na watsa ruwa ya gwal gwal ''.
Farha ta furta cikin natsuwa.
Sannan ta kama hanyar da zata sadata da ɗakin ta dake sama chan kusa da na Amma kasancewar itace kaɗai mace A gidan.
***
*GOMBE*
" Jahida ! Jalila ! Wallahi idan kuka bari na sa me ku a ɗakin nan sai na ɓaɓɓala naman ku guri ɗaya fitinannun yara kawai ".
Aiko da sauri suka faɗo ƙaton falon suna haki tare da zarar idanu kamar Wa ƴanda suka yiwa sarki ƙarya.
Yan mata ne guda biyu masu kama da juna shigar su iri ɗaya har kamar su ma sai dai kamar ɗaya tafi tsayi kaɗan kuma bakowa ke iya banbancesa ba sai Wanda yayi musu farin sani.
" Kneel down,hands up and close your eyes ".
Ya furta cikin tsare gida yana gyara zaman sa akan kujerar da yake zaune ta alfarma.
" Hamma Umar har da ɗaga hannuwa sama kamar wasu ɓarayi Abban mu yace fa Kadaina saka mu irin wannan Wahalar mu mata ne bamu da irin ƙashin maza ".Duk ɗan mintsinin ta da Jahida ke yi bata tsai da maganar ta ba sai da takai aya.
" Zanci ubanki Jalila ki kiyaye ne ke mai tsaurin ido da kafiya ko karki yi abinda na san ya ku, tsaya zuba mini surutu ".
Ya furta azafafe.Domin idan ba haka ba yasan halin Jalila bakin ta yana da wuya ya mutun tun kafin su kai haka ga kafuwar bala'i da rashin ji duk da Kowannen su nada rashin ji Amma nata yafi yawa shine kawai take shakka a gidan ko shi ɗin wata rana da kyar yake yi da ita sai taga dagaske yake yi take shiga taitaiyin ta.
Turo bakin ta gaba tayi kafin ta cika umurnin sa.
Chan bayan kamar minti biyar ta fara buɗe ido ɗaya tagani idan yana kusa.
Ganin shi kuwa tayi zaune ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya sai faman latsar wayar sa yake yi ƙirar iphone Wadda ake yayi a yanzu.
Cije leɓen ta tayi na ƙasa kafin ta ɓare baki ta fasa kuka na yarinta.Sannnan ta furta " Hamma Umar wai me mukayi ne don Allah ka yafe muna mun tuba mun bi Allah da Manzon sa mun bika ka tausayawa ƴan ƙannen nan na ka ".
Takai karshen zancen tana matso hawaye.
Duk da cike yake da Haushin su sai da ya murmusa A cikin zuciyar sa A hankali ya furta cikin zuciyar sa ƴan biyun Umma badai rashin ji ba ga Shegen tsoro.
A fili kuwa ya furta mata cikin tsuke fuska " Jalila idan kika sake magana sai kin kwana nan gurin ƙarfe nawa yanzu biyar saura,na rantse zan iya barinki haka kin sa halina kuma kin san abinda zan iya,ke kaɗai ce mai baki ita Jahida mai yasa bata yi magana ba ".
Shiru tayi kamar ruwa yaci ta kafin ta cigaba da matse hawayen ta.Ita kan ta Jahida matsewa kawai take yi ga kuma tsoron da ya cika mata ciki.
Sai da suka kusan minti goma sannan Allah ya kawo musu ɗauki.
Babbar mace ce ta ke saukowa a kan step step ɗin cikin shigar ta ta manyan mata masu ado da Naira ta sha ado har ta gaji.
A ƙalla zata kai shekara arba'in.
Cikin murmushi ta furta " Umar me kuma suka Aikata yau sarakunan rigimar ".?
Takai ƙarshen zancen tana kallon su cikin tausayi babu kamar Jahida wasu lokuttan tana biyewa yar uwar ta ne kawai Amma bata da hayaniya sosai kamar ta Jalila.
Murmushi ya mayar mata shima kafin ya furta " Umma Sashen Hajiya suka je suka suka faffasa mata flask har biyu kamar wasu ƙananan yara fisabilillah yanzu shekarar su sha biyar bai ci ace sun yi hankali ba,Kullum da ɓannnar da suke yiwa Hajiya duk soyayyar da take nuna musu baiwar Allah nan badan Umma ta nuna tana so abarta mata ku so tayi A bata ku ta raine ku tun kuna ƙanana take son ku Amma da kuka tashi abinda zaku saka mata dashi kenan".
Numfashi wannan matar da aka kira Ummu tayi wadda da alama mahaifiyar su ce kafin ta furta " A ina kasamu wannan labari Umar "??
" Mai aikin ta ce ta sanar Dani Ummu taje in k'ara ja musu kunne basa jin magana. ".
" Hmmm kawai Ummu ta furta tare da ƙara furta Allah ya kyauta,gaskiya Jahida baku kyau ta ba kece Babba ma amma kiyi ta biye mata kuna barna kamar wasu ƙananan yara yanzu ko Arwan da little ai basa yin abinda kukeyi An Jalila na adaina bana son ya cigaba da hora mun ku haka kuna mata "..
" Umar a yafe musu kaji alfarma muke neman " .
Murmushi yayi kafin ya furta " Umma banso kika saka baki ba wallahi naso kibar Ni nayi maganin bakin wacchan sakaryar " Yakai ƙarshen zancen ya na nuna Jalila wadda ta Turo baki gaba tana furta Allah ya tsare ta Hajiya ta raine ta har abada jin abinda Ya'yan nasu ya furta yanzu.
" Ku tashi tsaye ya furta A kausasshe ".
Miƙewa kuwa sukayi da ƙyar Kafin ya buga musu warning kar ya ƙara ganin su sashen Hajiya idan ba ita ta neme su ba.Tun da ɓarna ke kai su.Sannnan ya ƙara yi musu faɗa wanda ya shiga ta ɗayan kunne ya fita ta ɗaya musamman Jalila yana gama wa yayi wa mahaifiyar sa Sallama ya bar sashen nasu baki ɗaya yana komawa sashen sa dake ke ɓanci guri ɗaya acikin ƙaton gidan mai sassa daban daban.
Yawan comment taƙaita ranakun update
Share fisabilillah❤