Kuyi following,like da kuma comment
by @umaimah2024
KUKAN KURCIYA
BY OUM AHMAD
UMAIMAH ADO GAYA
( MRS.NAZEE)
zinariyar taskira 🔷
page 14
... ***...
KARKASHIN JAGORANCIN
💪📚📚
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*****
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda Allah ya bawa ita. da hikimar mu muke Alfahari_
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
Bismillahirrahmanirrahim
NAFEESAT : Kallon ta kawai yake yana yiwa Allah tasbihi a zuciyarsa tabbas Nafeesat ƴar baiwa ce, duk kasancewar ta babbar mace don aƙalla za su yi kusan sa'anni sannan ta ɗauki ciki ta raine shi a jikin ta har ta haife shi bama yaro ɗaya ba yara har biyu amma ba dan sanar da shi da tai ba kuma mahaifinta shima ya sanar da shiba wallahi da cewa zai ƙarya take duk da zahirin ganin yaran da yai masu tsananin kama da ita sak, haka nan fatar jikin ta da cikin ta babu wani alamun yanƙwanewa ko wani abu, ya ƙara shafar gefen fuskarta da tai dama dama da hawaye tai jajir saboda kukan da ta sha kaana yabi hawayen ya goge sannan ya ƙara jan ta jikin sa yana mai karanta duk addu'o'in da suka zo bakin sa akan ta da auren su.
Asubar fari Nafeesat ta farka kasancewar ta riga shi barci sai dai ganin yadda ya ƙanƙame ta kamar wani zai ƙwace masa ita abin ba ƙaramar dariya ya so bata ba, lallaɓawa tai a hankali bayan ta gama ƙarewa fuskarsa kallo ta fita daga riƙon da yai mata ta sanya masa pillow kana ta shafi gemun sa da yake matuƙar burge ta tana murmushi ta shiga toilet, kasancewar jiya sai da sukai wanka sannan sukai bacci ya sanya Alwala kawai ta ɗauro ta fito ta sanya hijabi da doguwar rigar ta ta tada sallah tana mai yiwa Allah godiya bisa ni'imar samun miji one in town da yai mata da kuma neman yafiyar bisa tarun zunuban ta kasancewar ta mutum kuma ƴar Adam.
Tun sanda ta tsaya kallon sa ya farka sai dai bai nuna mata ba saboda yana son ta samu nutsuwar kallon nasa da kyau, yadda ta dage tana yiwa Allah godiya da neman gafarar sa da kuma yi masa addu'a ba ƙaramin tausayin ta da ƙaunarta ya ƙara ji a zuciyarsa ba, haka kawai yake fatan Allah ya bashi ikon kula da rayuwar ta da kuma kyautata mata da bata farin ciki yadda zata ji tamkar babu kamar ta a cikin mata, sai da aka kusa kiran assalatu sannan ya tashi zaune ya sauko daga gadon lokacin ita kuma tana raka'a tanil fajr ya shiga toilet ɗin yai alwala ya fito sai da shima yai nafilar sannan ya fita masallacin yana tsokanar ta,
Kasancewar yana daɗewa kafin ya dawo daga masallaci don idan ya shiga masallaci da asuba idan har ba yana da wani abu mai muhimmanci ba sai rana ta fito sosai yayi walaha sannan yake komawa gida, hakan yasa tana idar da sallah ta fara gyara gadon ta share ɗakin duk da ba wata shara sannan ta wanke toilet din dakin ta fito tai mopping kana ta fesa swiss air freshner kana ta jona bonner ta sanya turaren wutar ta mai matuƙar ƙamshi, kana ta fito ƙaramin falon shima ta gyara ta sanya turare sai da ta buɗe ɗakin sa shima ta ƙara gyarawa duk daa gyare yake sannan ta fito babban falon ta ga har masu aikin gidan sun fito suna gyarawa hakan ya sanya kawai ta juya ta koma ƙaramin falon ta shiga ƙaramin kitchen ɗin ta haɗa musu sassauƙan breakfast sannan ta jera a dinnig kana ta koma ɗaki ta sheƙa wanka ta sanya rantsatsiyar shadda maroon wadda tai matuƙar haska ta ta zuba ɗauri mai kyau kana ta ɗauki flat shoe ta sanya ta fito falo da wayarta a hannu tana laluben number Ammi sai zabga uban ƙamshi take,
LATEEFAH:
Sai around 11 :am ta farka daga bacci shima Haseeb ne ya tashe ta ganin rana na ƙoƙarin yi amma bata tashi taci abinci ba, shafa kyakkyawar fuskarta yake cikin wani irin salo kafin ya dora hannunshi akan lips ɗinta yana zagayewa, slowly ta buɗe kyawawan idanunta da sukai sirkin ja saboda uban baccin da ta sha , kai tsaye kuma suka faɗa cikin na Haseeb dake gefen ta yana bin ta da wani sihirtaccen kallo lumshe idanun tai ta buɗe wanda hakan ya sanya Haseeb ƙara narkewa, kwantowa yai jikin ta cikin raɗa yake faɗin "me yasa kike son zauta ni ne? Juya idanu tai tana faɗin "how? Sai da ya ja yaji sannan yace "da wannan salon naki mana? "Hmm Ya Haseeb kenan ni wane salo na yi kuma? Kallon cikin idanun ta yai sannan yace "shagwaɓar ki, kallon ki da suffar ki duk suna matuƙar zauta ni, bazan ɓoye miki ba Lateefa kibiyar son ki ta fito ne kai tsaye daga idanun ki sannan ta caki zuciya ta,domin na faɗa soyayya da ke ne a ranar farko da na fara ganin ki ta hanyar kyawawan idanun ki, gani na biyu kuma shagwaɓar ki ce ta ja hankali na gare ki wanda har kishi na ji da ya kasance ba ni kaɗai naji wannan shagwaɓar ba, Lateefa ina matuƙar son mace mai tsafta, ƙamshi,shagwaɓa,tarairaya uwa uba ta kasance perfect at bed kin gane ai! Ya ƙarasa maganar yana kashe mata ido ɗaya,zabura tai da sauri ta nufi toilet da gudu tana mai mamakin rashin kunyar Haseeb, shi kam cikin ɗaga murya yake furta I HATE THIS SHY OF YOU WALLAHI!
*****
NURADDEEN : Tun daga farfajiyar gidan daɗaɗan turarukan Nafeesat suke masa sallama haka nan yake jin wani irin shauƙi da farin ciki yana mamaye dukkan ilahirin jikin sa wanda kallo ɗaya idan kai masa zaka tabbatar da hakan, a babban falo wanda ya haɗa part ɗin su da wanda suke tare da da Feenah suka haɗu da feenah hannun ta riƙe da kwandon da ta shirya musu breakfast, tun daga nesa suke jefawa juna murmushi har suka haɗe cikin zolaya Feeah ke faɗin " Allah ya ja zamanin Angon Nafeesatu yayan Nafeesatu , Ango kasha maiƙo ka sha ƙamshi, wannan irin murmushi haka kamar an maka bushara da samun gida a Aljanna? Yana ƙara faɗaɗa murmushin nasa yake faɗin "ai samun mar'atussaliha wata alama ce dake nuni da dace daga duniya zuwa ƙiyama", kaɗa kai tai tana faɗin gaskiya ne bestie gashi naga Amaryar tamu sarauniyar ƙamshi ce gaba ɗaya yau gidan namu ya koma na Amare,
Tare suka shiga falon wanda ƙamshin swiss airfeshner da ƙamshin haɗin turarukan ta banda na tsinke da ta sanya haɗi da sanyin air condition suka haɗu suka bada wani irin ƙamshi mai ban Al'ajabi ga daɗi ga sanya nutsuwa , guɗa Feenah ta sanya tana faɗin Ahayye! Rai fessss! Allah ja zamanin hajiya consultant Nafeesat wannan ƙamshi haka ai sai ki zauta yaya na!
Murmushi kawai Nafeesat ke yi tana riƙo hannun Feenah take faɗin welcome sis sai yanzu nake ganin idon ki? Riƙe baki tai tana kallon Nuraddeen da ke bin Nafeesat da kallo tace ni na isa na shigo gidan sabbin Amare da wuri? Sunkuyar da kanta Nafeesat tai tana murmushi yayin da Nuradden ya riƙo hannun ta yana faɗin wato iya bestie kawai kika gani baki ga noor ɗin na ki ba ko hayatee?
Kama kunnuwan ta tai tana faɗin "am sorry noor barka da shigowa da fatan ka tashi lpy", ɗage gira yai yana faɗin kai! Ba dai hayateen tawa bata iya gaida miji ba? Yamutse fuska tai alamun rashin fahimta sai dai kafin tace komai taji ta tsamo tsamo a jikin sa kana yana kissing fuskarta, ƙoƙarin janye jikin ta tai amma sam ya hana ta sai da ya gaji dan kansa sannan ya sake ta suna mai da numfashi, da sauri ta wuce bedroom tana mai tsananin jin kunyar sa dama Feenah da tuni ta fece bayan ta dire musu basket ɗin don taga bestien nata ya zurma da yawa a iya kwana guda tak!
Sai da Nafeesat ta haɗa masa ruwan wanka wanda yaji haɗin turaren wanka masu matuƙar ƙamshi sannan ta fito ta sanar masa, janta yai har bathroom ɗin yana faɗin madam ni fa wallahi yanzu na bar gauranci kuma bazan ringa abin gauraye ba ato! Idan ma zaki shirya ki shirya yau dai wanka kam sai dai ai min....
*****
HASEEB :
Tun da ya tashi da asuba yai sallah ya nufi part ɗin Haseeya daga masallaci inda ya tarar da ita akan sallaya itama tana azkar, zama yai a gefen gadon yana jiran ta kammala kana yana kallon yanayin ta wanda ya nuna daran jiya sam bata samu wani ishasshen barci ba, sai da ta shafa addu'a sannan ta naɗe sallayar da hijabin ta adana a inda suke kana ta nufe shi cikin takun ta da yake zautar da Haseeb, zama tai gefen sa tana shigewa jikin sa tare da sauke wata rikitacciyar ajiyar zuciya wadda ta ratsa sassan jikin Haseeb, cikin muryar raɗa ta furta i really missed you my Haseeb! Ta ja Haseeb ɗin da wani irin toungue wanda ita kaɗai tasan ma'anar sa, ƙara shigar da ita jikin sa yai yana mai shaƙar ƙamshin sabulun da tai wanka da shi, shower gel turaran wanka dama daɗaɗan humras da tai amfani da su ajikin ta ɗazu, sauke nannauyar ajiyar zuciya yai shima cikin nashi salon ya furta " i missed you more than words my seeyah ! Wallahi ina matuƙar ƙaunar ki da duk wani abu naki, samun macen da ta amsa sunan mace kamar ki yana da matuƙar wahala a duniya ni shaida ne irin ku baku da yawa a doron duniya haseeya!" Girgiza kai tai tana faɗin banga alamun haka ba Haseeb tunda har ka iya nemo wata macen ka aura saboda wani laifi da na aikata maka wanda ni kai na nayi nadamar hakan kuma laifin yafi min illa fiye da kai kanka, ta ja shassheƙar kuka tana faɗin Haseeb zuciyata tana min ciwo a duk sanda na tuna cewa yanzu kai ba nawa bane ni ɗaya kamar yadda nake hasashe da kuri a baya, ina jin kamar zan mutu Haseeb saboda raba min soyayya ta da kai da wata, Haseeb ina tsoron wata rana a wayi gari babu so na ko kaɗan a cikin zuciyar ka , ina mai tabbatar maka da cewar wannan rana ba zan ƙara shaƙar iskar duniya ba, saurin rufe bakin sa yai da nata yana kissing ɗin ta a zafafe zuciyar sa na tuhumar sa da laifin me tai masa da ta cancanci kishiya a ƙananun shekarun ta dana auren su, tun suna kissing juna a hankali har suka koma romantic way, ganin abin ya ƙi ƙarewa ya sanya Haseeya janye jikin ta a hankali duk da cewar tana tsananin buƙatar sa sai dai kishin da take masa ba zai sanya ta bashi kanta ba bayan ya gama da wata kucakar matarsa, kuma bazata so ta shiga haƙƙin amaryar tasa ba kamar yadda itama baza ta so su yi mata haka ba wata rana, ƙara janyo ta jikin sa yai yana lasar gefen wuyan ta, kana hannun sa yana yawo a sassan jikin ta, cikin wata murya da Haseeya kaɗai ta san shi da ita ya furta "please Haseeya kar ki katse mana jin daɗi mana? Nasan bazaki iya jurewa ba and me too," girgiza kai tai cikin ƙaramar murya take faɗin "bana so na cutar da matar ka ka jira zuwa rana ta i will make sure na maka abinda ban taɓa maka ba, " Oh no please Haseeya Lateefa tana kan period ɗinta and kin san bazan iya jira ba kuma ke ma baki da wanda zai miki bayan ni so please! Badan Haseeya ta so ba ta amince masa sai don ta san tabbas da gaske yake ita da shi ba zasu iya jurewa ba,
Sai wajen 9:am suka fito daga ɗakin bayan sunyi wanka sun canza kaya, Haseeb da kansa ya shiga kitchen ya taya ta haɗa breakfast wanda ya kaisu har kusan 10:35 sannan ya nufi ɓangaren haseeya,
Bayan ya tashi haseeya tayi wanka ta shirya cikin riga da skirt na material wanda ɗinkin yai matuƙar dacewa da surar ta domin ba ƙarya Allah ya horewa Lateefa sura mai ban shawa, fara ce ita sol amma farin ba mai muni ba, sannan tana da tsawo dai dai misali, Allah ya bata both shape da kowace mace ke fatan samu a jikin ta, sannan tana da kyawun fuska dai dai gwargwado ba mai yawa ba kuma ba kaɗan ba, sannan kuma uwa uba ta iya ado more especially ma na english wears da suka fi yawa cikin kayan ta, shima Haseeb sai da ya sake wanka saboda gaba ɗaya ƙamshin girki yake yi sannan suka nufi side ɗin Haseeya don a can zasu ci, tun daga bakin ƙofar side ɗin Haseeya ƙamshi ke musu maraba wanda ya sanya jikin Lateefa yin sanyi tunawa da nata side ɗin ko arziƙin gyara bai samu ba, Da sallama suka shiga falon wanda ƙamshin abinci, airfreshner dama haɗaɗɗen turaren wuta ke tashi suka haɗu suka bada wani ƙamshi na musamman, more especially ma da a.c a kunne take, shigar su yai dai dai da lokacin da Haseeya ke fitowa cikin wata irin kwalliya mai ban sha'awa kamar wadda zata je zaɓen sarauniyar kyau ta duniya, sosai tai ado cikin wani sky blue din less wanda yai matukar dacewa da jikinta, ɗinkin half bubu da straight skirt, ta yi ɗauri mai sauƙi amma mai tsananin kyau wanda ya ƙara fito da choco face ɗin ta, kunnuwan ta sun sha wani fashion mai tsananin kyau sai walƙiya yake, haka nan hannuwan ta dauke da abin hannu wanda duk sanda ta motsa sai sun yi ƙara, ƙafar ta kuma sanye da flat shoe shima sky blue, yayin da fuskar ta ke ɗauke da simple makeup wanda ya ƙara fito da zallar kyawun ta, sai walainiya take , gabaɗayan su suka buɗe idanu, hanci dama baki suna kallon tsantsan kyawun da tai, yayin da ita kuma take takowa cikin nutsuwa da yauƙi kana da salo mai jan hankali, sai da ta zo gaf da su sannan Lateefa ta sunkuyar da kai tana faɗin "barka da safiya Aunty," sai da tai jim kamar baza ta amsa ba sai dai ganin yadda Haseeb ya kafe ta da idanu ya sanya ta faɗin barkanki ya baƙonta? Alhamdulillah kawai tace yayin da Haseeya ta rungume Haseeb tare da sakar masa wani shu'umin kiss a gefen wuyan sa, sosai abin ya daki zuciyar Lateefa sai dai ganin yadda Haseeb yai saurin janye ta tana nuna mata ita ya sanya taji sauƙi a ranta, cikin kwarkwasa Haseeya ta furta muje ga breakfast can gashi har rana ta kusa yi....
*****
NAFEESAT & NURADDEEN
Bangaren Nafeeesat da Angon ta kuwa sai da suka shafe tsawon sati biyu suna kwasar Amarcin su, wani irin soyayya da kulawa gami da tarairaya sukewa junan su, burin kowannen su a yanzu shine ya farantawa ɗan uwan sa, kullum cikin rigegeniyar ɗawainiya da juna suke, Feenah kam ba ƙaramin farinciki take ba ganin yadda cikin ƙanƙanin lokaci Nafeesat da Nuradden suka canza suke kuma cikin farin ciki, tun tana jin kunya tana barin su idan suna wani abun a duk sanda suke tare har ta saba itama, wani lokacin har tsokanar su take, ba tare da sanin su ba ta shirya musu honeymoon a ƙasashe uku swizland,turkey da kuma hongkong sai ana waje gari jirgin su zai ɗaga sannan ta basu ticket ɗin, sannan ta taya su shiri suka wulla sararin samaniya inda basu da masaniyar canzawar ƙaddarar su a wannan tafiya , ƙaddarar da zata sanya su zubda hawaye ƙunar rai da saɓani mai tsanani,
Tsawon watannin su biyu kenan da baro Nigeria kuma a gobe ne suke sanya ran baro ƙasar hongkong wanda ita ce ƙasa ta ƙarshe da suka je, kwance Nafeesat take akan cinyar Nuradden da yake tura saƙo ta ipad ɗin sa game da kamfani wanda tanan yake aikin tun da suka baro nigeria, ita kuma tana chart da su Ammi, kamar da wasa wata number ta turo mata message kamar baza ta buɗe ba sai dai ganin kamar hoto ne sai tace bari dai ta buɗe ko wani saƙo ne mai muhimmanci sai dai me? Abinda ta gani yai matuƙar daga mata hankali wanda bata san sanda ta zabura da ƙarfi ba tana faɗin innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, tuni wayar ta faɗi ƙasa yayin da ita kuma ta ɗora hannu a kai tana girgizawa, Nuraddeen da hankalin sa yai matuƙar tashi ganin lokaci guda ta fita hayyacin ta ya sanya shi riƙo tana yana kiran sunan ta sai dai sam bata san inda kanta yake ba, janyo ta yai jikin sa ya matse sosai idanunsa na kawo ruwa don shi sam hankalin sa bai basa a waya aka turo mata abinda ya ɗaga mata hankali ba , addu'o'i yake ta faman tofa mata har ta samu nutsuwa ta fara sauke ajiyar zuciya, zaunar da ita yai kan kujerar sannan ya nufi bottle wata dake kan freezer wanda ɗazu ya sha ya ɗauko tare da glass cup ya kawo mata sai dai kamin ya ƙaraso inda take ya saki cup ɗin da ruwan ganin yadda jini ke bin ƙafafun ta wanda ita sam bata ma san da shi ba saboda gaba ɗaya bata cikin nutsuwar ta, da sauri ya kinkime ta ba shiri ya fita ba tare da yayi la'akari da irin shigar dake jikin su ba saboda tsabar gigita.
END OF PART ONE
SHIN MENE NE SABUWAR ƘADDARAR NAFEESAT DA NURADDEEN DAKE KUSANTO SU?
SHIN MENE NE ABINDA AKA TUROWA NAFEESAT A WAYA DA HAR YA TAYAR MATA DA HANKALI HAR HAKA?
YA RAYUWAR AUREN LATEEFA,HASEEB DA KUMA HASEEYA ZATA KASANCE? HASEEYA DAI TAFI LATEEFA WAYEWA DA KUMA SANIN MAKAMAN HASEEB SHIN LATEEFA ZATA IYA KARAWA DA ITA?
YA RAYUWAR LATEEF TAKE KASANCEWA ? SHIN YANA BARIN HOMO KO KUWA?
SHIN MOMY DA DADDY IYAYEN SU LATEEFA SUNA YIN NADAMA DA DANASI AKAN RASHIN KULAWA DA TARBIYYAR YARAN SU KUWA?
INA AKRAM BABAN TWINS ƊIN NAFEESAT YAKE? SHIN YANA ZUWA AMSAR YARAN SA KO KUWA? WAI MA YASAN DA SU KUWA?
INA SUHAIL MIJIN FEENAH YAKE ? SHIN YA RAYUWAR SA TAKE KASANCEWA BAYAN RABUWAR SA DA ITA?
DUKA WAƊANNAN AMSOSHI SUNA CIKIN LITTAFIN KUKAN KURCIYA PART TWO DAMA WASU DA BAN LISSAFO SU BA,
KU DAI KU HANZARTA GURIN GANIN KUN SHIGA GROUP DIN MU DAMA CHANNEL DIN MU DOMIN SAMUN CIGABAN LABARIN,
SHIN WAI KO KIN BIYA KUƊIN KI NA LITTAFIN ABIN SARRI NE KUWA? NACE KIN BIYA? TO KI SAURARA KADA KI BARI A BAKI LABARIN WANNAN LITTAFI DOMIN LITTAFI NE DA YA KAWO ABUBUWA MABANBANTA DA ZASU AMFANE KI AMATSAYIN KI NA MACE KUMA AKAN FARASHI MAI SAUƘI,
WANNAN LITTAFI YA ƘUNSHI MAGUNGUNA? ADDU'O'I DAMA WASU SIRRIKA DA YA KAMATA BUDURWA, MATAR AURE DAMA BAZAWARA YA DACE TA SANI, AKWAI AMSOSHIN WASU TAMBAYOYI DA YAWAN MATA SUKE YI AKAN ZAMANTAKEWAR AURE KE DAI KI HANZARTA KI BIYA NAIRANKI ƊARI BIYU KACAL DOMIN A SANYA KI CIKIN GROUP NA ABIN SIRRI NE( MATA KU NE GIDA ! )
TALLAH! TALLAH ! TALLAH!
INA MASU FAMA DA ƘURAJE NA PIMPLES, TABO DAMA DARK SPOT?
INA MAI SON FATAR SA TAI KYAU,KYALLI WALWALI DAMA SHEƘI?
INA MAI SON FATAR JIKIN TA TAI LUMUI MAI GIDA YANA TAƁAWA YANA SANTI 😄?
TO KU MATSO GA DAMA TA SAME KU UMAIMAH ADO GAYA MARUBUCIYAR KUKAN KURCIYA TA SHARE MUKU KUKAN KU TA HANYAR FAƊAƊA KASUWANCIN TA NA
ƳAR GAYA SCENT AND SKIN CARE PRODUCT INDA TA GWANGWAJE KU DA SABULU MAI KYAU MAI INGANCI WANDA ZAI SANYA FATAR KI TAI FRESH TAI KYAU, TAI SANTSI, KYALLI DA WALWALI, SABULUN YANA MAGANIN ƘURAJEN FUSKA DANA JIKI, YANA GOGE TABO, YANA SANYA FUSKA TA WASHE TAI KYAU BA TARE DA KIN YI BILICIN BA KUMA BA TARE DA YA CUTAR DA LAFIYAR JIKIN KI BA, KE DAI HANZARTA KI SAI NAKI SABULUN DOMIN GYARA FATAR KI DON ƘARA ƘAYATUWAR ADON KI, MATA ADON GARI IN BAKU BA GARI IDAN KUNYI YAWA GARI YAI DAƊI ☺,
HAKA NAN MUNA MARABA DA MASU SARI KO SIYAN ƊAI ƊAI