Chapter 3-4
*🔥💦BAN AIKATA BA🔥💦*
Story & Written By
Fatima Abdulhadi
Fateyzahraah
Destiny
Betrayal
Love
* Dedicated to Na'ima Sulaiman Sarauta (Nimcy Luv) Allah ya ƙara girma da ɗaukaka❤️🥰 My Mentor🤍🌹*
Mikiya Writers Ass...
Page......3⃣__4⃣
Fita suka yi daga cikin makarantar suna ɗaukar hanyar nashi Office ɗin, bai ce komai ba har suka iso. Building ne Babba mai hawa shabiyar ko sama da haka yayi kyau sosai, ga flowers a ko ina birjik securities ne ta ko ina a ciki parking suka yi tare da fito wa aka bude masa ƙofa yayi kusan ten to fifteen minutes sannan ya ziro kafar sa waje, gaba ɗaya ya fito lokaci guda Masha Allah kyakkyawa ne ajin farko duk wanda ya kalle shi sai ya ƙara kana ganin shi kamar halfcast yake, ciki suka nufa yana tafiya cikin ƙasaita duk inda suka bi jama'a sai gaishe shi suke har ya isa Office ɗin sa tsayawa bayanin tsarin haɗuwar Office ɗin ma ɓata lokaci ne a kujera ya zauna yana janyo system ya fara aiki. Wayar sa ya ɗauka yayi kira minti kadan wanda ya kira ya shigo "Yau da wuri haka Mahboob?, Madam tayi ƙoƙari gaskiya chabbb" ya faɗa yana zama ƙaramin tsaki Mahboob yaja yana cewa "Duk ba wannan ba Lukman, Salma ce ta kira ni ina da guest kuma nazo ba ta nan guest ɗin ma Are not around, mene matsalar?" Dan jimmm yayi bai ce komai ba yana nazari "Baƙi?, Daga ina?" Ya faɗa yana kallon shi ɗaga masa kafaɗa yayi alamun i don't know "Gaskiya ban san da zuwan su ba, sai dai ka tambayi Salma" dan nisawa yayi sai kuma ya cigaba da cewa "Kai imfact ma yau babu schedule ɗin baƙi" shiru yayi na wasu ƴan mintina sai kuma yace "Okay yayi you can go" bai ce komai ba ya tashi ya fita dama ya bar aiki da yawa a gaban sa har ya kai baƙin kofa ya waiwayo ya kalleshi yana cewa "ka tuntuɓe ta yanzu kaji dalilin da yasa ta faɗa ma haka" gyaɗa masa kai kawai yayi ya faɗa duniyar tunani...
Thirty minutes later ☞👌☞
Ɗago kai yayi daga kan aikin da yake a system ya ƙara kallon agogo a lokaci na barkatai tsaki yaja ya cigaba da aikin can ba jimawa ya janyo wani ɗan abu ya danna sai ga ƙara ta karaɗe Office ɗin, gurin minti ɗaya babu wanda ya shigo ya ƙara danna alarm ɗin knocking yaji "Come in" yace turo ƙofar tayi Matashiyar budurwa ce sanye da riga da wando shara-shara kamar tsirara ta hau magana tana wani fari da ido "Sir I'm sorry, traffic jam ne ya riƙe ne yanzu na iso, kuma..." Bata kai karshe ba saboda ɗagor da yayi yana kallonta daka mata tsawa yana cewa "How dare you?, Is this our dress code?👗, Sannan kin kira ni tun farar safiya ina da guest tunda na zo ban gan su ba ina suke?" Da sauri ta girgiza masa kai ta buɗe baki zata yi magana ya daka mata tsawa "You Are very stupid, out of my office" yace rai a ɓace karyar da kai gefe tayi "sir" tace da sauri, ɗaga mata hannu yayi yana cewa "Out now" tare da nuna mata ƙofa, sum sum kamar an fasa kwai a cikinta ta fice fuskarta dauke da wani yanayi mai wuyar fassara jakarta ta ɗauka tana ficewa fuuu daga cikin office ɗin, dafe kansa yayi sakamakon sara masa da yayi abubuwa sai cakude masa suke lumshe idanunsa yayi sunyi ja bayan wani dan lokaci ya buɗe su wayar sa ya ɗauko number yayi dailing tare da kira.....
🤍𝙉𝙪'𝙖𝙮𝙢𝙖𝙝🤍
Tana shiga cikin Palour direct hanyar da zata sada ta da ɗakinta tayi bata kallo Mamma dake zaune ba tsawa ta daka mata tana hararar ta tare da cewa "zo nan" jiki a sabule ta ƙara so kusa da ita tana me zama a ƙasa tare da cewa "gani Mamma" "Nu'aymah!" Mamma ta ambata tana kallonta fuskar ta a haɗe amsa wa tayi ba tare da ta ɗago idanunta ba "wane irin Iskancn banza ne kika fito da shi yanzu?, Ke kaɗai Allah ya halatta masa ya aura da zaki ringa yin haka?, Tun wuri ki chanja shawara wannan ba hali kwarai bane" shiru Nu'aymah tayi bata ce mata komai ba, balbale ta da faɗa tayi ta inda take shiga ba ta nan take fita ba ta nan take fita ba daga karshe tace ta ɓace mata da gani, jiki ba ƙwari Nu'aymah ta miƙe ta shiga ɗaki ta kwanta. Wayarta ce tayi ringing sai da ta kusa katsewa kamar ba zata ɗauka ba ta ɗaga sallama tayi muryar ta a hankali take fita alamun har yanzu ranta a ɓace yake
"Ya naji muryar ki wani iri?" Ya faɗa daga can muryar shi da alamun damuwa
Ƙaƙalo murmushi tayi da ƙyar ta furta "Kaina ne yake ɗan ciwo yanzu zan kwanta, Ya aiki Yallabai" ta faɗa tana lumshe idanunta, ajiyar zuciya ya sauke wanda har sai da taji sannan ya ce "Alhamdulillah gashi muna ta fama"
"Me yake damun ka Habiby?" Ta tambaye shi "Ba komai, tunda naji kuna lafiya bari in cigaba da aikina"
"Humm tun ba ka daɗe da tafiya ba har ka fara missing ɗina" sassanyar murmushi ya saki ba tare da yace mata komai ba ya kashe kiran, itama daga ɓangaren ta murmushin tayi "Habiby kenan, Allah ya bar mu tare" tace tana gyara kwanciyar ta...
Around 10:00Am
Da ƙarfi aka turo ƙofar palour Mamma tana zaune tana kallon Africa TV 3 tana kallon wani program tare da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ɗaga kanta tayi daga kallon TV tana jiran mai shigowa da gudu ta shigo Fuskar ta ɗauke da murmushi Kyakkyawar yarinya ce a ƙalla zata kai shekaru biyu zuwa uku sanye take da gown anyi mata parking gashin ta baƙi mai kyau riƙe take da teddy a hannunta, wata matashiyar budurwa ce ta shigo tana cewa "Anoosh ki ringa yi a hankali kar ki ji...." maganar ce ta maƙale sakamakon arba da tayi da Mamma zaune zubewa tayi a ƙasa tana cewa "Barka da safiya Mamma" wani kallo tayi mata da kyar ta amsa da "Barka dai Haulat, Har kun dawo?" Jinjina mata kai tayi, Babyn da suka shigo tare ce take wasa da teddy hannunta tare da zama kusa da Mamma "Mimi" ta ambata a hankali tana kallon Mamma wadda itama ita take kallo, murmushi tayi mata sai kuma ta ɗago ta kalli Haulat tana ce mata "Wuce da ita, tana cikin ɗaki" Mamma tace da Haulat, Thom tace mata tana miƙewa tare da riƙe hannun Anoosh suka shige ciki.
"Mimi Mimi" yarinyar take ta faɗa tana tafiya da gudu cikin ɗakin da sauri Nu'aymah wadda take kwance ta tashi tana saukowa daga gadon faɗawa jikinta tayi tana cewa "Mimi" murmushi tayi mata tana cewa "I missed you my Baby, Haulat shigo mana" tace tana kallon Haulat wacce ta tsaya a ƙofar ɗakin shigowa tayi tana mika wa Nu'aymah jakar hannun ta tare da gaisheta amsa wa tayi tana tambayar "da fatan bata yi kuka ba?"
"Aunty bata yi ba ai kan nata ma bai yi datti da yawa ba, kuma ta haɗu da ƴarinyar ta suka yi ta wasa, bari in tafi"tace tana miƙe wa
"Anoosh tashi ku tafi" Nu'aymah ta faɗa tana ɗan ɗago ta daga jikinta
Leka fuskarta tayi ganin tayi bacci yasa ta cewa "Laaah Aunty har tayi bacci ma, bari in tafi in ɗora girki"
"Anoosh Sarkin Bacci, Sannu da ƙoƙari Haulat sai na fito" ta fada tana gyara wa Anoosh kwanciya a jikin ta......
*A ko da yaushe comments ɗin ku shine ƙarfin gwiwa ta Fans😊🙏*
# like
# comments
# share
~EXPERT PENS ✍️ 2024🔥~
1.𝐁𝐀𝐍 𝐀𝐈𝐊𝐀𝐓𝐀 𝐁𝐀
NAH
Fateyzahraah
2.BURIN ABDUL-JALAL
NAH
Harira Salihu Isa
Uwar batool
3.DR HIBBAN
NAH
Habibty Muhammad (MUHAB)
4.GAYYA CE
NAH
Fatima Alaramma Alaramma
Arewa Books: fatimaintisar1
Wattpad: fatimaintisar1
***
07077791941