ƊANDAUDU

03

by @109051246447263646587

ƊAN DAUDU 👳🏾‍♀️


*©️AuntiMamee*


_Page 03

  

Ɗ/B GIDAN KAJI 


Sosai Mamma ke taya ƴarta farin ciki

na sakamakon jarabawar su da ya fito, inda duk wani alama na matakin tafiya bautar ƙasa ya nuna da Mumtaz inta za ayi sai dai ta fitittike Indai ba a Kano za tayi ba, sai dai duk wahalar da aka sha a baya ta tashi a banza dan wannan karon ba wani daɗin baki da za a zo mata da shi kam, dukda bata san ya bautar ƙasar ta ke ba amna tana Jin ana cewa ana sauyawa mutum gari zuwa inda yake.

Ita dai Mumtaz bata tanka ta ba, dan farin cikin da take ji ba mai misaltawa bane ba shiyasa ta bar Mamma da sunbatu ta je wajan da Baaa ke kwance tana masa hirar nasarar da ta samu. Da ido kawai yake binta zuciyar sa fal cike da farin cikin nasarar da tilon ƴarsa ta samu da kuma jin daɗin farin cikin da ya gani shimfiɗe a fuskar ta.

  


IMAM

Sosai yake nuna godiyar sa ga Ubangijin da yake jiɓantar lamuran sa a koda yaushe da irin nasarar da ya samu.

Kamar wani ƙaramin yaro kamar kuma yadda ya saba a kowanne lokaci idan abin nasara ko farin ciki ya sameshi, wajan Amminsa yake zuwa yayi ta zayyano mata farin cikin sa dan yana da yaƙinin zata iya ji mayarwa ne kawai zai gagare ta.

Sai da ya gama raba farin cikinsa shida Ammi sannan ya miƙe ya nufi ɗakinsa zuciyar sa cike da tararrabin abinda zai yin.  

Kamar koda yaushe, nombar a kashe take, hakan ya saka jiki a sanyaye ya zare wayar daga kunnen sa tare da ajiye ta gefe yana tunanin lafiya Imtiaz yake kuwa? Ko dai wani abinne ya sameshi a hanyar sa ta dawowa gida? Da sauri ya kori wannan tunanin daga zuciyar sa tare da fatan koma mene Yana masa fatan Alkairi a duk inda yake.***


Sanye take cikin wata Abaya ƙirar Dubai, wanda yayi matukar dacewa da kalar fatar jikin ta.

A nutse take tafiya kamar kullum. Tafiyar ta cike ta ke da jan hankali wanda sai mutum ya ɗauka da gayya take yi wanda kuma ba haka bane a haka Allah ya halicce ta.

Kamar kullum, ta ƙaramar ƙofa ta shiga cikin gidan.

Kallo ɗaya ta yiwa mai gadin da ke zaune ta kauda kanta ta cigaba da tafiya zuwa ciki.


  Tana isa palon ta zaro wayar ta haɗi da dannawa uwar ɗakin ta ta kira dan shaida mata isowar ta.

Bata wani ɓata lokaci sosai ba ta fito a yanayin da ta saba mai rikita ƙananan ƙwari .

Kallon ta budurwar ta ke fuska cike da murmushi har ta ƙaraso ta zauna a hashimƙe

 "Ina miƙo gaisuwa" budurwar ta tare ta da shi

Guntun murmushi Madam Dija ta saki tare da girgiza kanta. A iya sanin ta da yarinyar, bata taɓa mata cikakkiyar gaisuwa ba, saidai ta miƙota a lanƙwashe .

"Komai ya fa kankama ta ɓangare na, ina miƙa godiya ina fatan kuma ɗan kwikuyon ki ya shiga jeji neman na baka" matashiyar ta faɗa idanun ta kan Madam Dija 

Wani Nishaɗi ne na lokaci guda ke shigar Madam na ganin gobe zata munana wa wasu 

"Gobe Sarki zai iso masarauta, kinga kuwa akwai sabon naɗi" ta faɗa cikin nishadi 

Murmushin jin daɗi kawai matashiyar ke yi da faɗin

"Lallai za ayi abu ba ido" 

"Wa ya gaya miki?" Madam ta katse ta da tambaya, bata jira cewar ta ba kuma ta ɗora

" Lallai ina son nan da sati ɗaya na ganki a daidai wannan lokacin" tana faɗa ta zame jikinta ta baje sosai akan kujerar tare da lumshe idanun ta fuskar ta cike fal da annuri

Wani sautin fito matashiyar ta saki tare da miƙewa tana gyara mayafin abayar ta, ita ma fuska cike fal da nishaɗi.

Bata yi wa Madam Dija sallama ba ta nufi hanyar fita.

Gabanta ne ya yi wani irin bugawa sanda ta fito daga palon Madam Dija, ƙwayar idanun ta bata sauka a ko ina ba sai cikin nashi.

Yatsine fuska kawai ta yi tare da fara takun ta mai ɗaukar hankali ta nufi hanyar fita .

Kasa janye idanun sa yayi a kanta har ta ɓace wa ganin sa.

Wani wawan numfashi ya saki tare da ƙara tasbihi ga Ubangiji dan sanda ya haɗa idanu da ita, dan wani irin bugawa ƙirjinsa yayi wanda bai san Dalili ba..

So ya ke ya tuna inda ya san me kama da fuskar amma ya kasa.

Hannu ya ware irin na alamun bai damu ba tare da tamke fuskar sa.**


( Hmmmmm! 

Kufa shirya yanzu za a fara buga wasan an gama sharar fage dukda rubutun Aunty mamee bai cika tsawo ba, amma za ku nishaɗantu.

Ina cigiyar ƊANDAUDU dan Allah, na ga tun a UNIMAID ban sake jin labarin sa ba)


Ɗ/B ESTATE 

  "Ai na sani wallahi Dija, Allah bai sa nayi dacen haihuwa ba wallahi, ace wai mutum da ƙwaƙwalwar jaki? Na fa kashe kuɗina a banza fa kenan. Shekara da shekaru ina zubin dashin da ba ɗauka? To wallahi kaji na rantse da Allah na gama maka dukkan wani abu da zan maka a rayuwa, inba mutuwar zuciya ba ma ace ƙato mai shekara talatin yana zaune ba cas ba ass? to wallahi na gama kashe maka kuɗi idan kaga dama ka zama ɗan iska idan kuma kaga dama ka tattara ka barmin gida kaga idan zan damu Ni Wal......."

 "Calm down Alhaji" Madam Dija ta katse shi.

Dattijo ne da kallo ɗaya za kayi masa ka fahimci jini da tsokar IMAM tasa ce, amma saboda makirci da zalunci irin na Matar uba, ta shiga ta fita, ta raba wannan alaƙar mai ƙarfi wanda ko a Lahira ana sa ran wani zaici arziƙin wani.

Katse shin da Madam Dija tayi ne yasa ya koma ya zauna kan kujerar kansa na kallon silin yana ta huci saɓanin da da yake tsaye akan Imam yana ta zazzaga masa masifa bayan sanar da shi da Imam ya yi na yana da matsala a makaranta sakamakon sa bai yi kyau ba.

Shi dai Imam bai ce komai ba yana zaune a ƙasan kapet kansa a ƙasa, in banda tafasa ba abinda zuciyar sa keyi na irin munana kalaman da mahaifinsa ke jifansa da shi.

"Kayi haƙuri mana Pappi, nasan abin da ciwo ace kaita ƙoƙari akan yaro kana hidimta masa amma shi sam baya gani ba kuma ya tausaya maka dole ka ji ba daɗi to amma ya zakayi? Sai haƙuri tunda kome za kace kuma ko me za kayi shi zuciyar sa ta riga da ta ƙeƙashe ba komai a zuciyar sa sai ƙyama da tsanar ka, gani yake yi a kaf duniya baida wani maƙiyi sama da kai, ni kuma bana jin daɗin hakan shiyasa na zo da wata shawara" Ta faɗa tare da wurgawa Imam harara daidai shima sanda ya ɗago da kansa dan ya kalleta da son Jin yau kuma wanne sabon makircin ta zo masa da shi.

Shima hararar ya wurga mata tare da maida kansa ƙasa zuciyar sa fall cike da tsanar ta.

Ba ƙarya, taji ciwon harara da ya yi matan a ranta amma sai ta dake tare da ƙawata fuskarta da murmushi tana kallon Pappi da ke kallon silin yana ta huci dan kalaman da Madam Dija ta faɗa na ɗansa baida maƙiyi sama da shi ya taɓa zuciyar sa, hakan ya saka ya sake harzuƙa da yaron a ransa yana ayyana shi dai kam baiyi dacen samun ɗa ba.

 "Kaga baida wasu takaddu da inyaje neman aiki za a ɗauke shi, sannan kuma kaga ya yi girman da zaka haɗa shi da wani yaje ya koyi sana'ar hannu, dole naka sai naka Pappi hannunka baya ruɓewa ka yanke ka yar shine na ce me zai hana ka ɗauke shi aiki a Companyn k....."

  "What?" Pappi ya faɗa a zabure tare da miƙewa zaune sosai yana zare wa Madam Dija idanu 

"Amma Dija ba kida tunani mai kyau wallahi, wannan abin kike so na kai masana'anta na kuma kinsan tsarin Kamfanin nawa?" ya faɗa tare da nuna Imam da yatsa

Murmushin mugunta Madam Dija ta yi tare da kwantar da murya

"Shi nake so amma bazan ɓata maka tsarin aiki ba, ai ba administrative nace ka kai shiba tunda bai da wannan matsayin a matakin karatu ba kuma zaiyu dan yana ɗanka a kaishi inda bai cancanci nan ba, dan nasan nan ɓangaren na masu basira da ƙwazo ne waƴanda sukayi karatu tuƙuru domin su farantawa iyayen da suka ɗauki hidimar ɗawainiyar karatun su" ta ƙarashe tare da kashewa Pappi ido da shima itan yake kallo dan yana son jin me take nufi da Imam yayi aiki a company ba tare da takaddu ba.

Wani yawu mai ɗaci Imam ya haɗiye yayin da zuciyar sa take harbawa da sauri saboda ɓacin rai. Dan yasan wannan kalaman dama ta shirya sune domin ta cimasa fuska ta kuma ƙara fusata ƙiyayyar mahaifinsa a kansa.

Wani hucin zafi ya fesar ta bakinsa haɗida taune ƙasan lips insa da ƙarfi har saida ya fara jin zafi zafi sannan ya saki.

  "So nake kawai yaje koda wajan masu gadi ne ko a matsayin masinja idan wata ya ƙare a yi masa albashi kaga ai baka ƙwaresa ba, ka kuma sauke haqqinka na mahaifi kuma ka ga ka ƙara bashi wata dama" ya tsinkayi Muryar ta tana watso wani wulaƙantaccen bayani wanda ya kejin a wannan gaɓar gaskiya zai nuna yana da zuciya a ƙirjinsa, zai nuna shi mutum ne mai daraja, amma ba zai ce komai ba, zai tsaya yaji cewar mahaifin nashi.

Shiru Pappi yayi Yana nazarin maganganun Dija a ranshi, a can ƙasan zuciyar sa yana jin kamar hakan bai dace ba amma kuma ba shida wani zaɓi bayan wannan koya jininsa jininsa ne zai dai amince ya dinga shiga company ana masa albashi dan ya fi ƙarfin hakan amma gaskiya bazai so yaje matsayin Maigadi ko masinja ba, hakan ya sa ya hura bakinsa tare da fitar da iska ta bakin yana fuskantar Dija da ta tsare shi da idanu

 "Duk yadda kikayi daidai ne kuma na san kina sona ne kuma kina ƙaunata shiyasa kike son ganin kin haɗa alaƙata da ɗana dan ni wannan tunanin kwatakwata bai zomin ba na kuma gode amma gaskiya banda masinja da aikin gadi dan tsarin masana'antar kenan ba a bawa matasa wannan aikin kamar an dakushe musu gobensu ne munfi bawa wanda ya manyan ta dan ko kai matashi idan kazo neman ɓangaren da kanka mukan bada shawara ne akan suje suyi karatu zamu basu matsayi mai kyau inkuma baka da halin yi, haƙuri muke basu. Ya dai dinga zuwa Company kullum da safe yana sign in da 7:30 da yamma kuma 6:00pm yayi sign out ƙarshen wata nayi a biyashi kamar kowa" ya ƙarashe idanunsa akan Dija

Wani iri ta ji a ranta dukda irin hakan na kasancewa tsakaninta da Pappin, ba kowacce maganar ta yake na'am da ita ba amma ba tayi tsammanin a wannan gaɓar zai musanta ba, amma duk da hakan ba damuwa koba komai tasan an takure shi ba kaɗan ba dukda ba haka ta soba, amma ba zata takura ba saidai ya zama wajibi ta sake sabon shiri. Hakan ya saka ta ƙawata fuskarta da murmushi cikin kwantar da murya ta fara faɗin

"Kai Masha Allah hakan yayi Pappi Yana godiya" sannnan ta waigo ɓangaren da Imam yake da faɗin 

"Sai kayi masa Godiya dan idan ba Uba mahaifi ba, ba wanda ya isa ya maka wannan gata da alfarmar"

Shiru ya yi kansa a ƙasa yayin da ɓacin ransa ke sauka yana komawa zuwa takaici wani iska ya furzar haɗi da miƙewa ba tare da yayi godiyar da ta umarta ba

"Nima bana son godiyar taka mai baƙin zuciya da baƙin hali kawai, idan kuma kaga dama ka gaida uwar taka da jiki" ya tsinci muryar Pappi na fada sanda yeke barin palon pappin

Wani abu mai kama da mashi ne yaji ya caki ƙasan zuciyar sa, hakan ya saka ya fara tasbihi da ambaton sunan Allah dan shi kaɗai ne maganin damuwar shi.

 Madam Dija kuwa matsawa tayi kusa da Alhaji tana masa kissa da kisisina kamar wata uwar bariki dan ta wuce a shekarun ta ace ƴar bariki sai dai Uwar barikin hakan yasa ta fara kallame shi dan buƙatu ne sosai da ita na kuɗi*****

   ƊANDAUDU 

Kamar kowanne lokaci da ya saba yunkurin kiran shi, yauma haka ta kasance hannunsa riƙe da waya, so yake ya kira Imam ya shaida masa irin nasarar da ya samu, amma wata zuciyar na kwaɓarsa, dan shi gaskiya bai shirya karɓar mita da ƙorafin Yaya Imam ba, amma kuma sai yaushe ne zai kira? Ajiyar zuciya ya saki tare da nemo nambar Imam ya fiddo ta daga cikin kwandan sharar da ya saka tun ranar da suka bar UNIMAID.

Kara wayar ya yi a kunnen sa yayinda wayar ta fara ƙara yaji ƙarar na fusata bugun Numfashin sa.

  Dawowar su kenan daga asibiti shida Sabira ya rakata tana zazzaɓi, tun safe suka fita sai azabar suka dawo, hakan ya sa kai tsaye ɗakinsa ya wuce ba tare da ya leƙa ɗakin Ammi ba, dan ruwa kawai yake so yaji ya sauka a fatar jikin sa.

Fitowar sa kenan yana tsane jikinsa da towel yaji wayar sa ta na ƙara, da kamar ba zai ɗauka ba dan kaya yake son sawa ya nufi masallaci amma sai ya nufi wayar da ke kan Gadon 

Daram! Yaji ƙirjinsa ya buga ganin sunan IMTIAZ ya fito ɓaroɓaro a fuskar wayar tasa.

Kamar wanda aka tsikara kuma yayi saurin ɗaukar wayar tare da karata a kunnen sa

 "Yaya Imam ɗan daudu ne" yaji sautin Muryar a kunnen sa daidai sanda ya ɗaga kiran

"IMTIAZZzz" Imam ya ambaci cikakken sunan shi tare da jan sunan ba tare da yasan ya ja ba.


*Comment*

*Vote*

*Share*

*Follow me on *Wattpad@*AuntiMamee*Arewa witers


And