KAWA ZUCI

Trailer

by @salmaahmadisah

*💔-ƘAWA ZUCI-💔*



*©Salma Ahmad Isah*



THRILLER




*KAUYEN KINKIN, YANKIN KABILAR HADZABE, KUSA DA TAFKIN EYASI, AREWACIN TANZANIYA, AFRIKA.*


"Ya ku jaruman wannan ƙabila ta HADZA! Ku sani cewa wannan daji da za ku shiga farauta cikinsa daji ne da ya gagari iyaye da kakaninku! Domin akwai muggan namin daji masu cutarwa da dama a ciki, idan har ku ka yi nasarar farauto dabbar da sarki ya umarceku, rayuwarku za ta sauya, sauyi irin na har abada, idan har kuma mutum ya yi saken bari mutuwa ta riske shi a can!..."


Cikin dandazon jama'ar ƙauyen, ɗaya daga cikin amintattun sarkin ƙauyen KINKIN yake shelar da babbar murya, yayin da gaba ɗaya jama'ar ƙauyen da ba su fi a ƙirga ba suka taru a fadar sarki, kusan duk shiga iri ɗaya ce a jikinsu, domin kowa ka kalla a cikinsu fatar jikinsa ta rine da jan taɓon da suka saba shafawa a jikkunansu da kuma gashin kansu. Hakan yasa hatta da tufafin da suke sakawa wanda UNICEF da sauran ƙungiyoyin tallafi ke raba musu sun dauɗaɗe a cikin jan taɓon.


Kuma duk da zamani ya sa sun sauya tufafin da suka saba sakawa tun a zamaninsu na baya bai sa sun daina amfani da sauran kayansu na al'ada ba, domin al'adu su ne jigon kafuwar ƙauyen na Kinkin.


Tun da ta fello da gudu daga saman tsaunin da ta hau ba ta dakata ba sai da ta fara dosowa fadar sarki, kuma tun daga nesa take jiyowa shelar da ake kan farautar da za a tura samarin garin. Tun kafin ta ƙarasa ta hango Nikamba cikin samarin da aka zaɓa, hakan yasa ta ƙara gudun da take.


Lokacin da ta ƙaraso har sarki ya bawa matasan damar tafiya, shewa da iface-ifacen jama'ar ƙauyen ta karu, domin a bisa al'ada wannan ihun nasu alama ce ta nuna murna ko kuka ƙwararawa matasan gwiwa. Tana isa wurin ta nufi Nikamba dake kan gaba, ta riƙo hannunsa ta juyo da shi, hawaye ko tuni suka ɓallo mata.


“Nikamba akwa oonta?” (Nikamba ina za ka je?)


Ta tambaye shi cikin harshen Hadzane.


Nikamba ya yi murmushi yana kallonta, a lokaci guda kuma yana mamakin yanda akai ta san cewa har da shi za a tafi farautar, duk da ya yi ƙoƙarin ɓoye mata hakan, domin ya san ba za ta so tafiyarsa ba.


"Ti sho kaka Akira!" (Farauta zan je Akira!)"


Ya bata amsa a taƙaice, Akira ta girgiza kanta tana ƙara riƙe hannunsa, hawayen dake zubo mata suka ƙara gudun da suke.


"Zalikma Nikamba! Bania shir'ala" (Ban yarda ba Nikamba! Ba zan barka ka tafi ba).


"Akira! Ninahitaji kiwenda!" (Akira! Dole na tafi)


Ya yi maganar yana cire hannunta a kan nasa da ta riƙe, kuka ta saki mai sauti tana zubewa a ƙasa, lokacin da ya juya mata baya ya bi sauran abokan tafiyarsa da suka fara yin nisa, duk da shi ma ransa bai so ya tafi ya bar ƙanwar tasa ba. Sai dai abij da alƙalamin ƙaddara ya zana ya fi ƙarfin ruwan hawaye ya wanke shi.


_____________________



*Dutse, Jigawa state, Nigeria.*


"Wai Mama har yanzu Saama bai dawo ba?"


Adali da shigowarsa gidan ke nan ya tambayi Mama da ya iske zaune a tsakar gida tana wa Ruwaida firfita, wadda ta yi bacci tun wajejan ƙarfe takwas. Mama ta ɗaga kai ta kalle shi tana amsawa da.


"Bai dawo ba Adali, ni kaina rashin dawowar tasa da wuri ta so ta dameni, amma da yake yau yace wai suna da wasa, shi yasa ma ban damu sosai ba, wata ƙila ya tafi kallon wasan ne!"


Adali dake tsaye ya girgiza kansa.


"A'a, tun ƙarfe goma aka gama wasan, sai dai in akwai inda ya tsaya..."


"Ko yana wurin su Audu ba?"


Cewar Zahra da ta fito daga ɗaki, sanye da hijabi, alamun fita za tai.


"To, Allah masani, amma tun da fita za ki yi sai ki tsaya wurin zaman su Audun ki ga ko yana nan, in ba ya nan kuma sai ki tambayi su Audun"


"To Mama"


Zahra ta amsa sanda ta nufi soro.


"Ina za ta je?"


Adali ya tambaya, Zahra da ta kusa ficewa ta dakata tana amsashi da.


"Siyan siga zan je shagon Ɗan Ƙani"


Kuma ba ta jira ya amsa ba ta sa kai ta fita, sai da ta je ta siyo sigan, kafin ta biya ta ƙofar wani shagon drinks, inda ta san yayan nata na zama tare da abokansa a kan bencina idan yamma ta yi ko da daddare. Amma da ta je sai ta iske iyaka abokansa biyu ne kawai a wurin babu shi, kuma cikin abokan nasa har da Audu, su ma suna ganinta suka miƙe a tare, kamar masu jiran zuwanta. Duk da yake yanzu haka shawara suke na yanda za a yi su tunkari gidansu Saamari da batun cewa 'yan sanda sun kama shi, cikin girmamawa Zahra ta gaishesu, suka amsa ba yabo ba fallasa.


"Ya Audu ka san inda Ya Saama yake?"


Ta jefa musu tambayar bayan sun gaisa, juna suka kalla, kafin Audu ya sake kallonta.


"Umm da ma yanzu muke shirin zuwa gidan naku..."


Idonta ta ƙifta a kansu su biyu tana gyara tsayuwarta, alamun tana sauraronsu.


"Ɗazu da rana 'yan sanda suka kama Saama, a bisa zargin satar mashin lokacin zanga-zanga!"


Zuciyar Zahra ta harba dai-dai da faɗuwar ledar sigan dake hannunta.


_________________


*Ƙauyen Yarimaru, Gembu, Mambilla, Taraba.*


"... Ai dole ma a ɗauki mataki a kan yaron nan mara mutunci, yaro ya bi ya gagari kowa a gari, shi ne saka yara sata shi ne saka yara shaye-shaye, babu kalar mugun laifin da yaron nan ba ya aikatawa!"


Cewar wani bafulatanin mutum cikin faɗa, yayin da suke tafe a gefen gonar Lipton shi da wani abokinsa.


"Yanzu dai haƙuri za ka yi Tijjani, tun da ya shiga hannu, kuma da yardar Allah za a ɗauki mataki a kansa!"


"Ai Halliru ko kuɗin da na tara a duniya zai ƙare wurin ganin an hukunta Guru bani da asara Wallahi! Me ake da rayuwa irin ta wannan yaron!..."


"Tijjani!"


Halliru ya ambaci sunansa yana tsaka da tsinewa rayuwar Guru, ganin Halliru nasa ya tsaya yasa shi ma ya dakata yana kallonsa.


"Ya aka yi?"


Tijjani ya tambaya cikin harshen fulatanci. Halliru ya haɗiyi yawun tsoro, jikinsa na ɓari, kuma idonsa tsaye ƙyam a kan ƙofar gidan Tijjani.


"Wai me nene?"


Ya tambaya yana kai dubansa zuwa ga inda Halliru ke kallo, wato ƙofar gidansa, kaɗuwar da ya yi ta fi wadda Halliru ya yi, sakamakon ganin Guru zaune kan wani dakali a ƙofar gidansa. Da ka masa kallo ɗaya za ka shaida suffa ta kamilin mutum, domin ko kusa ko alama ba za ka taɓa danganta shi da harkar daba ko wani abu makamancinta ba. Shigar manyan kaya ce a jikinsa, har da hula, hannunsa riƙe da carbi yana ja. Yana kallonsu ya saki murmushi, kafin ya miƙe tsaye.


"Kun samu ƙarasowa ke nan? Ai na daɗe a nan ina ta jiranku!"


Tijjani da Halliru suka dubi juna, kowwanne a cikin ransa rayawa yake tasa ta ƙare, ya ya za ai mutumin da suka bari kulle a ofishin 'yan sanda na cikin gari zai kasance a nan? Ba ma wannan ne abin tambayar ba, yanzu su mecece makomarsu? Domin ta waje ne Guru yake da suffar masu imani da kamala, ta ciki baƙin mugu ne mara imani, sannan ba shi da tausayi ko na mis ƙala zarratin.


________________


*Shekara ta 2010*


*Lençóis town, Brazil.*


Cikin tsohon daren da ya kamata ace yana bacci a dai-dai wannan lokacin, duk da ƙarancin shekarun da yake da su. Zaune yake a kan steps ɗin ƙofar shiga gidansu, ya haɗe jikinsa wuri guda yana kallon sama. Damuwa da kewar mahaifinsa ne ke ɗawainiya da shi, sai kuma yunwa da ta gama galaɓaitar da shi, domin rabonsa da ya ci wani abu tun safe, da safen ma gidan Lala ya je ta ba shi guntun abincin da ta yi karin safe da shi.


"Pedro!"


Sophia ta ƙira sunan nasa a hankali kamar mai raɗa, bai ko juya ya kalleta ba lantana ya amsata. Cikin sanɗa ta fito daga falo, hannunta riƙe da bowl kamar wadda ta yi sata, sai waige-waige take, gudun kada Ma ta fito ta ganta. A gefen ƙanin nata ta zauna tana kallonsa.


"Pedro"


Ta kuma ƙiran sunan nasa, sai a lokacin ya kalleta.


"Ga abinci ka ci"


Ta ƙarashe tana miƙa masa bowl ɗin hannunta dake ɗauke da miyar Faijoada, wadda ake yinta da baƙin wake da naman akuya, sai kuma biredi da ta saka masa a gefe. Ya kalli bowl ɗin, sannan ya kalleta.


"Ka ci"


Ta faɗa tana ƙara miƙa masa, sai ya gyara zamansa zuwa zaman cin tuwo, sannan ya karɓi bowl ɗin.


"Na san yau kwata-kwata Ma ba ta baka abinci ba, dole za ka ji yunwa"


Sophia ta sake faɗi tana kallon ƙaninta cike da tausayawa. Yayin da shi kuma ya ƙurawa abincin ido, kamar mai ƙirga adadin waken dake cikin miyar, ganin ya tafi tunani sai ta sa kafaɗarta ta bigi tasa, ya ɗago ya kalleta, da ido ta masa alama da ya ci, ya jinjina mata kai, kana ya ɗaga hannunsa na hagu zai saka cikin abincin Sophia ta yi saurin riƙe hannun nasa.


"Ka manta da abin da Papsi yake faɗa maka kan cin abinci da hannun hagu?"


A take idanuwansa suka soma tara ƙwalla, domin ta sosa masa inda yake masa ƙaiƙayi, gane hakan yasa ta yi saurin sakin hannunsa, ya sauƙe na hagun ya ɗaga na dama ya gutsiri biredin, sannan ya haɗa da miyar, ya kai saitin bakinsa.


"Bismillah"


Ya yi bismillah kamar yanda Papsi ya koyar da shi a duk sanda zai ci abinci. Bai haɗiye lomar farko ba ya ƙara ta biyu, ita dai Sophia kallonsa kawai take tana murmushi, hannunta ta sa ta shafa sumar kansa da take a nannaɗe.


"Badar!"


Ta ƙira ɗayan sunan nasa, ya kalleta, bakinsa cike da abinci.


"Shopia in tambayeki?"


Cikin mamakin tambayar da yace zai mata ta gyara zama tana gyaɗa masa kai alamun ta ba shi dama ya mata tambayar, abincin dake bakinsa ya haɗe, sannan ya kalli ƙarama ƙofar gidan nasu yana furta.


"A ganinki Ma ce ta haifeni? Saboda na san duka iyayen abokanaina suna son 'ya'yansu, amma ni ban da tawa mahaifiyar, shi yasa na fara kokwanton ko ba ita ta haifeni ba?"


Ya ƙarashe yana kallon Sophia da idanuwanta suka tara ƙwalla, saurin girgiza masa kai ta yi tana faɗin.


"Silly Boy, wa ya gaya maka wannan zancen? Ma ita ce ta haifeka, ka manta da hotonka da na nuna maka sanda kana jariri? A baya Ma ta soka kamar yanda take sona am?..."


"To me yasa yanzu ba ta sona?"


Ya yi saurin katseta hawayen idonsa na zubowa, Sophia ta yi shiru.


"Badar!"


Ta ambaci sunansa tana ɗora hannunta ɗaya a kan kafaɗarsa.


"A ganina da za ka koma addinin Christianity da Ma za ta soka kamar yanda take sona a yanzu...! Kuma za ka hutar da kanka daga wannan baƙar wahalar da kake sha a wurinta"


Ya yi shiru yana kallonta, kafin kuma ya ɗaga plate ɗin hannunsa ta buga shi da ƙasa, Sophia ta yi saurin tashi tsaye tana kallonsa.


"Badar mi ye haka?"


Ba tare da ya kalleta ba yace.


"Wannan dalilin yasa kika bani abincinta?"


Saurin girgiza kai ta yi kamar mai tsoronsa.


"Na zaɓi addinin da Papsi yake so na tashi a kai sama da wanda Ma ke son na bi, kuma har kawo yanzu ban yi nadamar yarda da hakan ba, na yarda na ci gaba da shan azaba a hannun Ma matsawar kasancewata Musulmi shi ne zai jawo min mutuwa a hannunta... Idan abin da ya fito dake ke nan cikin wannan daren to ki koma!"


Magana yake mata cikin kaushin murya kamar shi ne yayanta, ya juya mata baya alamun ya yi fushi, kuma hakan yasa ta tsorata da shi, dan da ba haka yake ba, bayan mutuwar Papsi ya sauya ya koma haka...


"Sophia! Sophia!"


Suka jiyo Ma na ƙwalawa Sophia ƙira tun daga cikin gida.


_"Pedro!"_


A firgice ya kalli Ibrahim da ya tasheshi daga ɗan gajeran baccin da ya kwashe shi, dan bai ma san baccin ya yi gaba da shi ba.


"Lafiya kuwa?"


Saurin jinjina kansa ya yi yana ɗauke idonsa daga kansa, domin tunawa da Sophia da ya yi, da kuma yanda mutuwa ta raba shi da ita.


__________________


Rayuwa na da wahala a kauyen da al'adi ta fi muhimmanci sama da rayuwar mutanen cikin kauyen. Ko da ace kana da masu sonka a kauyen rayuwa za ta maka wahala ballantana ita da ta taso kowa na mata fatan mutuwa! Mutuwa? To me yasa? Me yasa suke fata mata mutuwa kafin lokacinta ya yi?.


Akwai ciwo a auren da rai ba ya so, ta tsallake matakai masu tsanani da wahala a rayuwarta, daga ƙarshe sai ga shi ta ƙare a auren wanda ba ya sonta, kuma ita ma ba ta sonsa... Auren kiyayya? Wa ya daura shi? Yaya zaman zai kasance?


Akwai ciwo a burin da aka gaza cika shi. Buri? Fata? Mafarki? Su ne abubuwan da a ko da yaushe sai ya yi mafarkin samunsu, amma har kawo yanzu burin nasa ya gaza cika, wani irin buri ne wannan da cikarsa ta zamewa mai shi alaƙaƙai?.


Fansa ita ce abin da yake kwanta yake tashi da ita a ransa. Fansa? Wace fansa ce wannan? Me akai masa da yake son sai ya rama?


Kowa a garinsu kallon ganga ba rufi yake mata, don me? Saboda kawai ana ganin cewa ba a san asalinta ba, ba wannan kaɗai ba, ba aje ko ina ba wata jarrabawar da ta fi wannan ta faɗo mata, jarrabawa? Wace irin jarrabawa ce wannan?

Yaushe zaren ƙaddarar zai yanke? Yaushe ido zai daina zubar da ƙwalla? Yaushe burin zai cika? Yaushe mafarkin zai zama gaskiya? Sai zuwa yaushe ne ƙiyayyar da sukewa juna za ta koma soyayya?


Find out in ƘAWA ZUCI (The beautiful game of love and revenge).


Wanda zai fito nan ba da sabuwar shekara idan Allah ya kaimu. 1/12/2024 da izinin Allah.



#SalmaAhmadIsah

#Candy

#Bahadejia

#KawaZuci

#Sa'ad

#Hammad

#Akira

#Zahra

#BadarPedro

#Aminatu