FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
A.k.a Candy 🦋 Student Midwife 🌺 Writer ✍️ Graphic designer🪄 Muslimah 🤲 Proudly Nigerian 🇳🇬 Kuma Bahaɗejia🐎.
Sample · Trailer
*💔-ƘAWA ZUCI-💔**©Salma Ahmad Isah*THRILLER*KAUYEN KINKIN, YANKIN KABILAR HADZABE, KUSA DA TAFKIN EYASI, AREWACIN TANZANIYA, AFRIKA.*"Ya ku jaruman wannan ƙabila ta HADZA! Ku sani cewa wannan daji da za ku shiga farauta cikinsa daji ne da ya gagari iyaye da kakaninku! Domin akwai muggan namin daji masu cutarwa da dama a ciki, idan har ku ka yi nasarar farauto dabbar da sarki ya umarceku, rayuwarku za ta sauya, sauyi irin na har abada, idan har kuma mutum ya yi saken bari mutuwa ta riske shi a can!..."Cikin dandazon jama'ar ƙauyen, ɗaya daga cikin amintattun sarkin ƙauyen KINKIN yake shelar da babbar murya, yayin da gaba ɗaya jama'ar ƙauyen da ba su fi a ƙirga ba suka taru a fadar sarki, kusan duk shiga iri ɗaya ce a jikinsu, domin kowa ka kalla a cikinsu fatar jikinsa ta rine da jan taɓon da suka saba shafawa a jikkunansu da kuma gashin kansu. Hakan yasa hatta da tufafin da suke sakawa ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.