ƊANDAUDU

07

by @109051246447263646587

ƊAN DAUDU 👳🏾‍♀️


*©️AuntiMamee*


_Page 07


A ɗaya ɓangaren ma shirun ne ya biyo baya kamar ba za ayi magana ba, sai kuma can aka magantu

"Tsakani da Allah kira nawa nayi maka yaya Imam?" Aka faɗa da ƙorafi


"An hana mai zuwa yiwa Ammi na addu'a shigowa gidan mu" Imam ya furta a hankali kamar mai yin raɗa ba tare da ya kare kansa na ƙorafin da akai masa ba


"Kan bala, baban kuturu da makaho? ban gane ba?" Ya tambaya a zabure


"Kamar yadda ka ji "  ya sake bashi amsa a hankali, dukda ya san ba sanin issue na gidansu Imtiaz ya yi ba, but hakan kawai ya ji ko ba zai fahimta ba ya gaya masan ko zai samu sauƙin abin da ya ke ji.


"To sai me dan an hana wani zuwa ya mata magani? ba sai ka ɗauke ta ka kaita inda ka ga dama ba? Gari da yawa ai maye baya ci kansa ba, yo daman Ina zaka maƙalewa wani kamar rai ace sai abin da yazo ya yi muku ai zama waje ɗaya yasin tsautsayi ne yaya Imam a fita neman magani bakin rai bakin fama" 


Shiru Imam ya yi Yana nazarin maganar ɗandaudu tare da ganin yuwar hakan ko akasin hakan


"Idan ba zaka iya fita da ita daga gidan ba, sai ka ɗakko wayar ka ka rubuta sunan lalurar Tata, wallahi yaya Imam ina gaya ma duk wani wanda ya yi bayani akan ciwon sai an watso maka shi, sai ka zaɓi guda ɗaya wanda ya yi maka ka nemi inda yake ko a sace ne kaje ka masa bayani, ko a ɓoye ne kana amso mata magani in kayi ka gwada ba nasara sai ka canza sheƙa,  ha a'a, yo har mu za awa wulaƙanci" cabbbb!"


Wani irin numfashi mai haɗe da dariya ne ya zuwa Imam wanda har sautin sai da ya fito amma ya yi saurin gimtsewa tare da gyara zama


Ƙitttttt ya ji wayar ta katse, hakan ya sa cikin takaici zare wayar da ga kunnen sa da faɗin "Imtiaz" a fili da sautin gargaɗi


Ajiyar zuciya ya sauke tare da kwanciyar rugingine yana fuskantar cilin.

Shiru ya yi Yana nazarin maganganu da Imtiaz ya sanar masa a waya yana hasaso nasarar da za a samu tare da ƙalubalen hakan

Haka kwai ya ji ɓacin ransa na sauka yayin da yake jin bugun zuciyar sa na daidaita.

Wani ƙayataccen murmushi ya saki tare da lumshe idanun sa .


Sabira kam kasa motsawa ta yi bayan Imam ya shige ɗaki a fusace, 

Waje ta samu a kujerar palon ta zauna zaman jira 

a ƙalla ta ɗauki kusan awa guda amma bata ji alamun sa ba, hakan ya sa kai tsaye ta tunnkari ƙofar Amaryar gidan


Tana zaune a palon ta hannun ta ɗauke da waya tana sarrafa ta taji an turo ƙofar amma hakan baisa ta ɗago kanta ba dan wani muhimmin saƙo take son turawa office 


"Magana na zo muyi dan ALLAH" ta tsinkayi Muryar Sabira a kusa da kujerar da take zaune


"Maganar ta shafeni ne?" Ta tambaya ba tare da ta dakata da abinda take yin ba


"Ba ta shafeki ba amma ta shafi wanda kike kira a matsayin mijinki" Sabira ta bata amsa a nutse 


"Ɗan hanzarta to" ta sake faɗa still kanta na abin da take yi

"Hmmmm!". Sabira ta faɗa tare da girgiza kanta cikin takaici tare da faɗin


"Shin biki taɓa hasashen zaki iya zama kamar Ammi ba nan gaba? Ba kya tunanin koda ba Akhi ba nan gaba za kiyi Auren soyayya?  Ya zakiji idan mijinki ya yi miji kishiya amma kika daure dan a zauna lafiya saidai burin wannan kishiyar taki a koda yaushe ta ga ƙarshen ki a matsayin ki na uwar gida? Ya zakiji idan kishiyar nan taki ta miki asirin da aka farraƙa wannan soyayyar da ke tsakanin ki da mijinki zuwa ƙiyayya? Kuma bayan wannan hakan bai isheta ba sai da ta nakasa miki halitta?"


Cakkkk ta tsaya da abin da ta keyi ba tare da ta ɗago kanta ba amma kallo ɗaya zaka mata ka fahimci hankalin ta gaba ɗaya ba a kan wayar ya keba


Numfashi Sabira ta ja da faɗin  "ko da ba zaki saurare bi ba, a yau zan gaya miki takaitaccen tarihin gidannan" 

Ba kuma ta jira cewar ta ba ta fara


   "Pappi da Ammi auren soyayya suka yi hakan ya yi sanadin haifar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin su kamar yadda na ji ana faɗa.


Pappi ɗan Asalin garin Kano ne, yayin da Ammi ƴar haifaffiyar garin Gombe ce, sun haɗu da Pappi ne a wata sallah da ta zo gari Kano ziyara gidan ƴar mamanta a wajan hawan sarki.

Haɗuwar farko Allah ya haɗa su wanda Ammi bata bar garin Kano ba, sai da Alƙawarin aure ya shiga a tsakanin su da pappi


Zaman da su ka yi zama ne na amana, wanda har hakan ya saka dangin Pappi suka dinga ƙananun maganganun Ammi ta ma Pappi asirin gwambawa Wai duk ya bi ya tare a gindin ta.

Ana haka kuma sai wata magana ta ɓullo na rashin haihuwar Ammi da ta shafe shekara guda gidan Pappi ba haihuwa


A lokacin Pappi na zaune ne a unguwar ƙofar waika a madaidaicin gidansu, kuma a lokacin a kasuwar singa yake sana'ar sa.

Suna a wannan yanayin ne wani abokin sa ya zo masa da shawarar suyi haɗin gwiwa su buɗe kampanin madara koda mutum huɗu ne, inyaso kayan nasu ba sai ya dinga fita ba ko ina ba a cikin kasuwar ma zasu iya raba kayan su.


Pappi mutum ne mai ɗaukar iyali da muhimmanci wanda ko me zai yi sai ya yi shawara da Ammi

A lokacin da da ya je mata da wannan batun sai ta nuna ta amince da shawarar buɗe Company amma gaskiya shi ya buɗe iya nashi dan haɗaka har mutum huɗu bata da daɗi


A lokacin Pappi kallon rashin hankali yake wa Ammi na ya za ayi ya iya buɗe kampani shi shi kaɗai? inda yana da wanan halin tun farko ai da ba sai wani ya zo masa da shawarar hakan ba.

Fahimtar yanayin sa ne ya sa Ammi murmushi a lokacin tare da gaya masa ya Saida komai na shi daya gada 

Ita ma zata saida komai nata da ta gada na ɓangaren mahaifi da mahaifiya kasancewar ta marainiya kuma tilo wajan iyayenta masu tarin dukiya da arziƙi irin na fulanin gwambawa


A lokacin Pappi nunawa ya yi bai yadda ba sam ta saida kadarorin ta Saida ta nuna masa ɓacin ranta har tana nuna bare sun fita tunda su ya amince da su suyi kasuwanci tare , ita ce bai yadda da ita ba.

Ganin abin har zaman lafiyar su ya shafa ne ya amince amma ba dan ya so ba


Sanda labari ya je wajan dangin Ammi sanda ta je sanar da su, ba ƙaramin taƙaddama a kayi ba, da ƙyar suka amince sakamakon gorin da Ammi ta yi musu na dukiyar ta ne ba na wani ba da faɗin idan kuma so suke su cinye mata sai ta sani


Sunji haushin maganganun ta matuƙa dan har cewa su kayi zasu barta da mijin nata amma kuma dukiya

Sam basu biye mata sunyi fushi da ita ta wannan fannin ba sai dai zasu bata kayan ta sl dan sunsan da yarinta shiya sa suka nemi mijin nata ya zo ayi komai a rubuce.


Bayan komai ya kankama ne Ammi ta nemi alfarmar Pappi ya sirrinta wannan al'amarin ga dangin sa kar ya sanar da su ta ce tunda dangin ta suna da shi a rubuce hakan ya wadatar.

  

Sanda ya jewa abokin sa da maganar abokin bai nuna wata damuwa ba dan ce masa ya yi ma shi kansa ya so ya sameshi da maganar akan su haƙura dan bai samu haɗin gwiwa daga sauran ba ya kuma taya pappi farin ciki sosai 


A wannan yanayin ne kuma mariƙiyar Pappi ƙanwar mahaifinsa ta bijiro masa da auren ƴarta da ta jima ba miji tana zaune


Fituk ya fitittuke a lokacin da faɗin ba wanda ya isa ya yi masa auren dole da matar da bai da ra'ayin ta

Ai hakan sai ya sake rura wutar ƙiyayyar Ammi ana ganin ta shiga ta fita ta yiwa Pappi asiri ta raba shi da danginsa zata sa ya butulcewa iyayen sa

Sai suka ɗauki salon zuwa har gida suna zaginta da cin mutumci a ciki kuwa harda Mahaifiyar zaunanniyar budurwar da ake so ya aura


Ganin abin ya ƙi ci yaƙi cinyewa ne yasa Ammi zama da Pappi, bata ɓoye masa komai ba na cin mutuncin da danginsa suke mata daga ƙarshe ta haɗa da rokon inhar yana san zaman lafiyar su yana kuma son tarayyar su ta jima ya taima keta ya amince da maganar auren ayi kowa ya huta ta kuma nusar da shi illar ƙin amincewar"


Shiru Sabira ta yi ganin har lokacin ba wani sauyi na daga yanayin Matar Akhin nata.

Hakan ya saka ta yin wani murmushin takaici ta cigaba


"A taƙaice, a lokacin da Madam Dija ta shigo a matsayin matar Pappi a daidai lokacin kamfanin su ya fara fitar da kaya na ban mamaki, wanda hakan ya sa dangin Pappi murna da faɗin ƴarsu mai ƙashin arziƙi ce


Zaman Ammi da Madam Dija, zaman kishi ne da zagon kasa a lokacin, kwatsam ciki ya bayyana a jikin Ammi wanda hakan ya yi matuƙar ɗaga hankalin Madam Dija wanda tun daga nan Kuma Ammi ta gama zama lafiya domin zaman kishin rikiɗewa yayi ta hanyar da Madam Dija ta bi na gabatar da malamai da bokaye a sha'anin gidan Auren ta


Allah ne kawai yayi rantsuwar zuwan Akhi duniya, badan hakan ba da babu shi a raye.

a lokacin sunan sa dangin Ammi suka zo suka ga halin da take ciki, hakan baƙaramin ɗaga musu hankali ya yi ba, amma mazan da matan suka kai musu rahoto suka ce a barta ta horu dan dama sunsan dole wannan ranar za tazo a barta har sai ta nemi dangi 


Tunda Ammi ta haifi Akhi, har yau Allah bai ƙara bata haihuwa ba" 


Dakata wa ta yi da maganar ganin murmushi shimfiɗe a kan fuskar Amaryar gidan tasu,  wanda hakan ya sake bawa Sabira takaici da tabbacin wannan makirar idan ba ayi wasa ba sai ta fi Madam Dija illa


Girgiza kanta kawai ta yi sannan ta ci gaba 


"Madam Dija ta shigo da makircin nunawa Akhi soyayya a gaban Pappi a bayan idanun sa kuma zagi da hantara wanda hakan ya sa ko kaɗan Akhi bai taɓa kallonta a mutum ba.

A haka rayuwar gidannan ta cigaba cikin tsana da ƙiyayyar Ammi da Akhi da aka sakawa Pappi saidai Yana kokarin sauke haƙin sa daidai gwargwado dukda wani sa ilin da gori yake musu kamar an sashi dole 


Bayan da Akhi ya gama secondary school, a lokacin Allah ya ƙara ɗaukaka kasuwancin pappi har suka dawo zuwa wannan ESTATE in Kuma lokacin ne Pappi ya nemi tsohon abokin sa suka ƙulla hannun jarin buɗe kampanin magi


A wannan lokacin ne kuma Allah ya jarabci Ammi da lalurar daina tafiya da magana ba ƙoƙarin da Akhi baiyi akai ba, na maganin asibiti amma hakan ya gagara, hakan yasa ya haƙura

A kuma lokacin ne ni da Manana muka kawo wa Ammi ziyara a matsayin wakiliya da aka naɗa mamana na ta zo taga sabon gidan da Ammi ta ce sun koma,   ganin halin da Ammi ke ciki ne yasa mamana bari na a gidan ta koma Gombe a ranar cikin tashin hankali dan sanar da dangi

Saidai abin takaici yanda dangin mu suka zo haka suka koma dan a lokacin da motar su ta sauka a lokacin Madam Dija na shirin fita, cikin ƙasƙanci ta kore su tare da shaidawa mai Gadi muddin ya bari suka shiga to a bakin aikin shi wanda tun daga ranar har zuwa yau ba wanda ya sake marmarin takowa.

Wani ƙarin Abin takaicin kuma, tun mutuwar maman Madam Dija, ba wani dangin Pappi da ya sake takowa zuwa cikin gidannan dan ko bikin ku, ƙawayenta ta tara ba dangi ba.


Mamana tayi kiran duniya da naci akan na dawo gida ita da baba na amma na ce bazan taɓa barin Ammi a wannan yanayin ba dan Ammi matsayin Mahaifiya take a wajena dan da Ammi da baba na cousin ne"


"Kin ga kuwa kin zalunci Madam Dija da kike kiranta da azzaluma tunda har yau banji kince ta miki wani abun ba"   ta faɗa sanda take maida hankalinta wajan cigaba da sarrafa wayar ta ba tare da ta ɗago kanta ba


Galala Sabira ke kallon ta cike da mamakin baƙar zuciya irin nata


"Allah ne yayi zamana shiyasa bata damu ko da da ta ganni a gidan ba, sannan kuma nafi ƙarfin makircin ta dan Allah na tare da Ni" Sabira ta faɗa mata cikin tabbatar wa


"Ohoo" ta faɗa tare da mirza gashin girar ta sannan ta ce  "me kike jira har yanzu biki basu dafa'in naki ba da zasu gagari Madam Dijan?"


"Anya kuwa kina da imani a zuciyar ki?" Sabira ta tambaya a maruƙar raunane idanun ta taf da hawaye


Cakkkk ta tsaya da abin da take yi tare da ɗago kanta tana wa sabira kallon sama da ƙasa.

Wani shimfiɗaɗɗan murmushi ta saki tare da miƙewa 

"Na barki lafiyar Amryar Imam, Ohhh sorry Amaryar Akhii" tana gama faɗa ta bar wajan cikin takunta na nutsuwa ta shige bedroom inta


Wani irin abu ne ya tokare wa Sabira a maƙoshi wanda bata san mene shi ba.

Jiki a saɓule ta miƙe ta bar palon tare da shigewa ƙofar Ammi tana jin zuciyar ta kamar ta rabe biyu.*******


Yanayin garin yau an tashi cikin sanyi sanyi, wanda hakan ya sa tun sallar asuba bata tashi daga kan gado ba tana duƙunƙune dan Allah ya yi ta da mugun jin sanyi koya ya ke ba kamar zafi ba

Jin cikinta na ƙugi ne ya sa dolen ta miƙewa zaune tare da yaye bargon jikinta.

Sakkowa tayi a gadon ta nufi drowan kayan ta.

Safar hannu da ta ƙafa ta ɗakko ta sa sannan ta janyo wata rigar sanyi mai hula ta ɗora akan doguwar rigar baccin da ke jikin ta.

Jin cikinta na ƙugi ne ya sa ta barin wajan tare da tunkarar ƙofa.


Fitowar sa kenan daga ƙofar Ammi daidai lokacin ita ma ta fito idanuwan su suka sauka cikin na juna


Wani irin bugawa da ƙarfi ƙirjin Imam ya yi tare da zaro idanunsa waje ya nuna ta da ɗanyatsa da faɗin

"ƊANDAUDUuuu IMTIAZZzz" ya faɗa a rarrabe 

Zaro idanun ta tayi waje tana kallon sa sai kuma ta maida duban ta zuwa jikin ta.

Kallon shigar jikin ta take yi daga sama zuwa ƙasa, babu maraba da shigar ta ta UNIMAID hakan ya sa ta faɗin

"Opssss" tare da sakin guntun tsaki, can kuma ta maida duban ta a kansa da har yanzu bai sauya daga reaction insa ba hakan ya sa ta sakin wani malalacin murmushi tare da fari da ido da faɗin  "MUMTAZ dai Yaya Imam, MUMTAZ ASSADIK MATAR EL-BASHIR MUHAMMAD" tana gama faɗa ta nufi hanyar kitchen cikin salon tafiyar da ya sannta da shi sanda su na UNIMAID matsayin ƊANDAUDU


*Comment*

*Vote*

*Share*

*Follow me on *Wattpad@*AuntiMamee*Arewa witers