ƊANDAUDU

07

by @109051246447263646587

ƊAN DAUDU 👳🏾‍♀️


*©️AuntiMamee*


_Page08


Ji yayi Numfashin sa na neman barin jikinsa wanda hakan ya sa ya yi saurin sauke ɗanyatsan sa da ke nune a saitin Hanyar da ta bi tare da dafe ƙirjin sa da shi.

Runtse idanun sa ya yi da ƙarfi  har sai da ya ji jijiyoyin idanun sun amsa sannan ya buɗe su tare da sakin wani irin wahaltaccen numfashi da ya tawo masa da ƙarfi mai ɗauke da ajiyar zuciya.


Yana tsaye a wajan har ta dawo hannunta ɗauke da ɗan ƙaramin tray


Tun da ya ji alamun ta ya ɗora idanun sa a kanta yana kallon yanayin tafiyar ta.

Binta kawai yake da ido tun daga tsakiyar kanta har zuwa tafin ƙafar ta da ke ɓoye cikin Safa kamar yadda ya santa a ɗandaudu


Ba abin da ya sauya na daga sifar fuskarta  a sanda suke UNIMAID, sai hasken fata kaɗan da ta ƙara, tafiyar ta ce ya ga banbanci dan a UNIMAID a shegance da gayya ake tafiyar, saɓanin yanzu da yake kallonta ya fahimci tafiyar da take a yanzu ne  asalin tafiyar ta


Ɗan ja da baya tayi tare da dakatawa da tafiyar ganin har lokacin yana tsaye a wajan, ga wani kallo da yake binta da shi da kaifaffaun idanun sa da bata taɓa sanin tasirun su ba sai yau

Ɗan motsa baki ta yi tare da yatsine fuska ta cigaba da tafiyar zuwa ƙofar ta.


Wani wawan numfashi ya sake tare da barin wajan ya nufi ɗakinsa, yana shiga ɗakin ya faɗa kan gadon sa haɗi da dunƙule hannun sa na dama ya naushi gadon da ƙarfi

"Why?" Ya furta cikin karaji  kamar da wani yake a cikin ɗakin.


Wanne irin illa matar ubansa take son yi masa da har zata tura wata tayi spying insa?  Duk abin da ta yi wa Ammin sa bai wadatar ba? Har sai ta haɗa da shi shima?  ta raba shi da mahaifinsa  hakan  bai wadatar ba?  Har sai ta takure masa rayuwa tare da  saka masa matakan tsaro sai kace wanda ya yiwa Gwabnati sata?


To wai ya akayi ma shi sam ƙwaƙwalwar sa ta toshe?  Ya akayi yana rayuwa da mace amma ya kasa ganewa? Ya akayi sanda ya fara ganin ta a cikin gidansu ya kasa gano ainihin kamar ta

"Saboda yarda da amana, kayi wa Imtiaz wata iriyar yarda da amanar da ko da wasa baka taɓa sako sa a sahun maƙiya ba, ka ɗaukeshi jininka, aminin ka sannan masoyin ka"  zuciyar sa ta bashi amsa


Amma ko yaya, ya ci ace ya ga alama.

  Yes akwai alamomi da yawa dan dai shi ba mai lura bane zuciyar sa ta ayyana masa.

Idan ba zai manta ba, lokacin suna UNIMAID akwai ranar da su Imtiaz zasu yi exam da safe.

Shi lokacin ba su da pepa hakan ya sa shi ƙara gyara kwanciyar sa akan gado.

A lokacin kallon Imtiaz da ke kakkaɓe shimfiɗa ya keyi da takaicin Imtiaz in na ganin yanayin zafi ne amma ya kasa cire rigar shi ta gado

Taɓe baki ya yi da niyar juyawa ya hango kamar exam card a ƙasa


"Wannan ba exam card inka bane a ƙasa?" Ya tambayi Imtiaz tare da nuna masa saitin da exam card in ke yashe a ƙasa da bakin sa


A wani sukwane ɗandaudu ya juyo a lokacin tare da wurga idanu dan ganin inda exam card in nasa yake, yana gani ya ɗaukeshi tare da cusa shi cikin aljihun rigar sanyin jikinsa haɗi da sakin Ajiyar zuciya,     sai kuma ya waigo gun Imam da sauri da tambayar

"Ya akayi kasan exam card Ina ne?"

Galala Imam yake kallonsa tun lokacin reacting insa na farko, tambayar da ya sake yi masa kuma a ganin sa ta rainin wayo a lokacin ita ta goge batun razanar da yaga ya yi da faɗin    "kasan faculty sun ware na ƴan daudu siyasa da an gani ake ganewa"  ya basa amsa cikin takaici tare da gyara kwanciyar sa ya juya masa baya. 

A lokacin ba zai ce ga yanayin sa ba, dan bai tunani ya cigaba da gyaran gadon, dan ko minti biyu ba ayi ba ya ji alamar fitarsa daga ɗakin

Wani tsaki ya ja a lokacin tare da Allah wadarai da iskancin Imtiaz

sai dai tun daga lokacin zai iya tunawa,  Imtiaz bai sake koda ajiye hand out insa a fili ba, bai kawo komai ba a ransa, dan ba ɗabi'arsa bace tsawaita abu


Wani irin hucin numfashi ya fitar tunawa da ranar da ya kamata ace ya gane Imtiaz wane shi, a lokacin ya yi imani da ya tsawaita bincike zai iya sanin gaskiyar wani abin


A ranar Imtiaz ya tashi da ciwon ciki, ba yadda baiyi da shi kan ya kaishi school clinic ba amma ya ƙi,

Sai ce masa ya yi a lokacin, ya duba cikin kit insa akwai declopain ya ɗakko masa ya bashi zai sha

Lokacin mamaki ya yi na meye haɗin ciwon ciki da maganin sai Imtiaz ya ce masa ai painkiller ne Yana kashe kowanne nau'in ciwo.

Bai Musa ba ya buɗe kit in dan ɗakko magani ,  sai kawai cin karo ya yi da sanitary pad.

Cike da mamaki yake kallon abin, haɗi da   tambayar Imtiaz me ya keyi da shi.

Ba zai iya cewa ga yanayin da Imtiaz ya nuna a lokacin ba, dan yana ƙudundune ne waje guda sai dai a ƙalla ya ɗauki kusan minti biyu kafin ya bashi amsar cewa  Aminiyar shi ne ta bashi sautu ya siyo mata jiya da ya fita

A lokacin kuma ya alaƙanta jinkirin da yayi na bashi amsa da yana cikin ciwo.


A ranar shi ya dafa mishi ruwan wanka ya kai mishi amma firr Imtiaz ya ƙi yin wankan wai jiri yake ji, idan ya miƙe zai iya faɗuwa sannan kuma  yanajin sanyi. 

Ba dan ya soba ya kyale shi a lokacin, haka ya yafi lecture ya barshi a ɗakin  sai dai yana dawowa daga lecture ya samu mutumin a shirye fes  cikin wasu kayan harda kofin shayi a hannun shi yana kurba

Kamar yadda ya saba, bai tsawai ta binciken ya akayi ya miƙe ya yi wanka ko ya shirya ba, ya dai tambayi lafiyar shi ne

Da yamma kowa na kan gadon shi  hannun kowa ruƙe da waya suna sarrafa wa

Imam ya ji kansa ya damesa da ciwo, tuna wa ya yi da yaga paracetamol a akwatin Imtiaz ya saka shi miƙewa ba tare da ya tambayi Imam baya nufi akwatin ya buɗe


Da mamaki ya maida dubansa ga Imtiaz cikin ɗan ɓacin rai da tambayar    "suwaye suka shigo ɗakinnan?"


Cikin rashin fahimta Imtiaz ke kallon sa a lokacin sai kuma ya maida dubansa inda Imam ya ke  na ɗan wani lokaci , sai kuma ya saki wata Shashashar dariya da faɗin

"Ɗazu Aminiya ta kirani a waya wai na ɗakko mata saƙonta guda ɗaya za tayi amfani da ita wai na bar sauran a wajena intakai ɗakinsu sacewa akeyi,


kuma bata shigo ba ma iyakacin ta bakin hostel shine na lallaɓa na kai mata, bayan na dawo ne naga tunda nayi wannan tafiyar bari kawai nayi wanka na huta gaba ɗaya,  Amma gobe da safe idan zani lecture zan tafar mata da gayyar ta"


Sosai ya gamsu da dogon sharhin da yayi masa a lokacin

Dan dama takaicin sa ace mace ya bari ta shigo musu ɗaki,  Ashe abin haushin da mace yake rayuwa

Muhalli ɗaya makwanci ɗaya.


Wani irin  tashi zaune ya yi a fusace sakamakon wani tunani da ya yi a zuciyar sa.

Zumbur ya miƙe, ya tunkari hanyar ƙofarta gadan gadan, sai dai ina?  Tuni yau ba jira,  tuni har ta shirya tayi tafiyar ta office dan yau kam ta san akwai ƙura.

Banda tana da abinda take so tayi mai muhimmanci a office in , Aida wajan uwar ɗakin ta zata fara nufa sai dai koba aiki tasan Pappi sirikin ta na nan.


Jin ƙofar a kulle ne ya sa shi dukan ƙofar da ƙafarshi tare da juyawa ya koma ɗakinshi da niyar shirin zuwa kampani shima


Tana tsaka da aiki a office ta ji an banko ƙofan ba tare da knocking ba, wanda hakan ya mutuƙar tsorata ta tare da ɗagowa dan kallon me ke faruwa.

Tsoranta ne ya ninku sanda idanun ta suka sauka cikin ƙwayar nashi idon, amma tuna inda suke ne ya sa ɓoye tsoron ta  tare da janye idanun ta ta cigaba da aikin gabanta, duk da a zahiri ba aikin ta keba dan kwatakwata bata da wani kuzarin aikin amma ta zaɓi buɗe takaddun da ita kanta bata san na mene ba


Kallon ta ya keyi cike da mamakin ƙarfin halin ta.

Girgiza kansa kawai ya yi tare da sakin wani murmushi takaici sanan

ya zaro wayar sa daga cikin aljihun kayansa haɗi da kiran wani layi


Ƙaramar wayar ta ce ta fara ringin wanda har wani Ajiyar zuciyar daɗi ta yi a sace ganin ta samu hanyar da zata ɗauke hankalin ta ta gujewa illar da ƙwayar idanun sa kewa jikin ta.


Hakan ya sa da sauri ta janyo wayar da ke ajiye can ƙarshen  table inta


Sai dai me?  "YAYA IMAM" ta gani rubuce a kan fuskar wayar wanda hakan ya saka ta kallon fuskar wayar ba tare da ta sake motsin komai ba


A ƙalla sai da wayar ta yi ƙara sau bakwai.   da ta yanke zai sake danna mata wani kiran


"Ka ɗaga mana  ɗandaudu,  neman shawara nake"  ya faɗa cikin kwantar da murya kamar ba shine ya gama kumbura ba yanzu


Shiru ta yi bata ce komai ba wanda hakan ba ƙaramin fusata shi ya yi ba, a fusace ya ƙaraso gaban table in nata tare da saka duka tafukan hannayen shi ya buga teburin da su haɗi da sunkuyo da kanshi daf da kujerar ta da faɗin       "ka ɗauki wayar nan ɗandaudu magana na ke son yi da kai" a fusace


"Please" ta faɗa a hankali tare da haɗe tafikan hannun ta kamar roƙo 

"Bana son cin zarafin ka, dan haka dan Allah ka fita a office innan" ta faɗa har lokacin tafukan hannayen ta na a haɗe


"Cin zarafi?" Ya tambaya tare da ƙanƙance idanun sa yayin da ya sake kusanta fuskar shi da nata, sai kuma ya saki wata bazawarar dariya da ita kanta tasan dariyar bata kai zuci ba


"Kasan kuwa zan amshi cin zarafin nan da muhimmanci dan abin da zai goge min tabon abin da kayi min kawai nake nema.  Cin zarafi ka ce ko? Shi na ke jira ɗandaudu"

ya faɗa cikin karajin da sai da ta toshe kunnen ta saboda sunkuyowar da ya yi ba ƙaramin kusanci ya haifar tsakanin fuskar ta da nasa ba


"Ka cika butulu,  azzalumi, mara tsoron Allah, mara ɗigon Imani a zuciyar sa, nayi dana sanin sanin ka a rayuwa ta,  na tsane ka, mai ƙaunar ka ma bana ƙaunar sa ɗan daudu.

Kai baƙin maciji ne, kai kura ne lulluɓe da fatar akuya, kai ba komai bane face karen farauta wanda ina mai tabbatar maka muddin ka gama aikin ka a daji za a ɓatar da kai ko wataran ayi amfani da naman ka wajan ƙosar da sabbin karnuka,  kuma har kullum kana nan a matsayin namiji kuma ƊANDAUDU dan da shi na sanka ba zan kuma sauya daga  yanda na sanka ba"


Yana gama faɗar hakan ya fice a zafafe tare da Banka mata ƙofar da ƙarfi wanda hakan har Saida ya sa ta runtse idanun ta.


Wani ƙaƙƙarfan numfashi ta fitar da karfi wanda take da tabbacin da ace ta cigaba da riƙe shi to da ba shakka sai ta sume a wajan


Tunda ya fara magana take kallon ƙasan table inta yayin da kowacce mummunar kalma da zai faɗa a kanta ta ke jinta kamar ɗigon narkakkiyar dalma a fatar jikin ta.

Wani huci mai zafi ta fitar tare da miƙewa ta tattare ƴan komatsan ta da niyar tafiya gida dan sam bata jin zata iya yin komai na cikin office inta a yau.


Tana ƙoƙarin buɗe ƙofan motar da tazo ne  taji ance   "ƊANDAUDU"

Ko bata juya  ba tasan wane, amma sai ta zaɓi juyawar tare da ƙawata fuskarta da murmushi


"Idan dai ba an ginu da cin haramun ba,, ya ci ace ka san yanzu ba lokacin tashi bane ba ko?"

Ya faɗa tare da tsare ta idanu, dan har ga Allah so yake ya tuzura ta, ya ƙuntata mata iya ƙarshen ƙumtatawa ko ya samu abin da ya keji na daga zafin zuciyar sa ya ragu


Wani murmushin tura takaici ta yi da faɗin     "Indai akan Madam Dija ne, to ba abin da baza iya yi ba,  idan kana da saƙo ka faɗa sauri nake"  ta ƙarashe maganar tare da duba agogon da ke saƙale a bayan hannun ta

Jin shirun bai ce komai ba ne ya saka ta shigewar ta haɗi da bawa motar ta wuta ba tare da ta sake bin ta kanshi ba


Ajiyar numfashi ya sauke tare da cigaba da addu'ar da yake yi a zuciyar sa tun sanda ta fara magana


Shi kanshi ya san ƙarfin addu'a ne ya yi tasairin hana shi zuwa ya kwashe ta da mari sanda take masa Maganar Madam Dija, dan ji ya yi wani irin ɓacin rai ya taso tun daga cikin hanjin sa har zuwa maƙogaron sa, hakan ya saka shi ambaton sunan Allah da tasbihi ga Ubangiji tare da addu'ar kada Allah ya sa ya biye wa zuciyar sa abin da take raya masa na yaje ya kwashe ta da mari, dan ya san sam ba ɗabi'a ce mai kyau ba,  dan ko Pappi, bai taɓa jin ya zagi mace ba , bare duka

Juyawa ya yi izuwa inda

yake zama tare da ci gaba da tasbihin sa a zuciya.


*Comment*

*Vote*

*Share*

*Follow me on *Wattpad@*AuntiMamee*Arewa witers