ƊANDAUDU

10

by @109051246447263646587

ƊAN DAUDU 👳🏾‍♀️


*©️AuntiMamee*


_Page 10

    

   


Saida ta gama shirin ta na office gaba ɗaya sannan ta fito da niyar ta yi break a main palon daga nan ta yi wucewar ta cos tunda ya san wace ita, ta raba haɗa hanya da shi dan muddin suka haɗu sai ya caccaɓa mata magana hakan yasa ko driving Insa ta dena bi 

Wani lokacin har mamakin shi take yi na yadda zai iya shafe sama da minti uku yana mata masifa, dole ta yi mamaki mana dan har suka gama UNIMAID tare ba zata iya nuna mutum guda ta ce ga abokin hirar sa ba ballan tana abokin faɗa amma gaba ɗaya yanzu ya sauya duk da ta san abu ne ke masa yawo a zuciyar sa, kuma abu ne da bai taɓa zaton faruwar kwatankwacin sa ba ko da a mafarki ne sai ga shi ya farun a lokacin da bai yi zaton faruwar hakan ba amma kuma rashin juriyar da ya ke nunawa da yadda yake nuna jin zafin abin a fili dole ne ta ce ya sauya daga sanin da da tayi mishi


Ko da ta fito daga ƙofar ta gaba ɗaya hankalin ta na kan hanyar kitchen sakamakon yunwar da ta je ji, hakan ya sa ba ta lura da zamansa a ɗaya da ga cikin kujerun palon ba.


Cakk ta tsaya ganin kitchen in ƙwalam, ba alamun anyi amfani da shi duk da cewar tana da tabbacin anyin

Kai ta jijjiga tare da kunna gas ta ɗora ruwan zafi kawai, tana a tsaye har ya tafasa sannan ta juye shi a kofi

A tsaitsaye ta haɗa tea ta sha sannan ta fito da ga kitchen in daidai sanda Sabira ta fito daga ƙofar su cikin shirin da kallo ɗaya ta a yi mata ta fahimci fita za tayi itama


Kamar da bazata kulata ba dan har ta yi hanyar fita yayin da Sabira ke binta a baya itama

  

Cakkkk ta tsaya har Sabira ta zo ta zata gifta ta hakan ya sa ta saka hannun ta ta tsayar da Sabirar ta hanyar ja mata mayafin jikin ta 


Cakk itama ta tsaya ba tare da ta juyo ba, hakan yasa ta cika mata mayafin ta tare da takawa har gaban ta tana fuskantar ta


"Ba shawara nake baki ba, Umarni ne kuma na ƙarshe" ta faɗa cikin rage girman idanun ta dan ta fuskanci Sabira bata gama fahimtar wace ita ba da abin da zata iya aikatawa da abin da ba zata aikatawa ba


"Ko wanda kike zaman sa bai kai ya min horon yunwa ba akan me ke zaki kemin? Ni mai na tauye ki da shi?" ta faɗa cikin ɗaga sauti dan yau Sabirar ta kaita bango dan sam bata wasa da cikinta ko kaɗan


"Jiranki fa nake" ya faɗa cikin ɗaga murya

Imam da tun shigowar su cikin palon yake bin motsin kowa da ido, ganin an fara hasala ga Sabira na faman girgiza kamar mai shirin dambe ne ya sa katse abin


Maida idanun ta da ya fara sauya launi zuwa ja tayi ga inda ta ji sautin Maganar sa ta fito 


Dawo da duban ta tayi ga Sabira da itama ƙiris ta ke jira da faɗin 


"Idan kin cika ke yar Halak ce, ki sake gwada min horon yunwa a cikin gidan Aurena ni kuma na rantse miki da Allah sai na tabbatar miki ke ba koman komai bace face baiwa wadda ke zaman jiran gaibu, inkuma biki farga daga baccin da kike ba, ina mai tabbatar miki wataran sai kin goya ɗana a bayanki a matsayin ɗan raino" 


Tana gama faɗa ta wuce a gadaran ce ta fice daga palon ba tare da ta bi ta kan mukullin motan da ke ajiye a Centre table ba kamar yadda ya saba ajiye matan idan ba tare za su fita ba, amma bata ɗauka sai ta ga daman ɗaukan


Kallon Sabira da ke faman cika tana batsewa ya yi, hakan ya sashi gyara zaman shi da kyau a kan kujeran tare da nuna wa Sabira da ke kallonsa kamar shi ya yi mata lefin waje itama ta zauna 


Ƙwafa ta yi tare da neman waje ta zauna tana ta faman kumbura da wani ɗauke kai 


Shiru ya yi tsawon sakanni kamar ba shine ya nuna mata wajan zama ba, hakan ya sa ta kallon inda yake


Ɓata fuska ta yi kamar za tayi kuka ganin ita ya ke kallo 


"Me ya sa kike son Jan magana ne wai?" Ya tambaye ta ganin tana shirin maganar da yana da tabbacin ba ta da wani amfani


"Me kuma na yi?" Ta faɗa cike da mamaki mai haɗe da takaici


"Me yasa biki ajiye mata abinci ba?" Ya tambaya cikin tsare ta da idanu


"Saboda ba zaman ta nake ba"ta amsa a hasale, a kuma yanayin da bai taɓa sanin ta da shi ba


"Amma ai ni zamana ta ke ko? Kuma a tunani na ko kare ne yake ƙarƙashin kulawa ta ya cancanci ya ci arziƙi na a wajanki ko?" Ya tambaya still idanun sa a kanta


"Wannan sheɗaniyar ce ke zaman ka Akhi? Zaman Madam Dija dai" ta faɗa tana wani ciccin magani


"Haka na ce miji? Ko mun taɓa hirar da kene?" Ya tambaye ta tare da ƙanƙance idanunsa yana mata kallon mamaki


Idanunta ta rufe tare da buɗesu lokaci guda haɗi da juya masa ƙeya


Ƙansa ya girgiza tare da ziro harshen sa ya lashi ƙasan leɓensa.

Kamar ba zai magana ba, zuwa can kuma ya fara


"Sanda nazo sanar da Ammi Pappi ya kirani ya faɗamin ya yi min mata a lokacin kuma kina ɗakin Idan zan iya tunawa ban ambaci sunan wata mata ba a ciki right? Dan pappi kawai na ambata and shi na ce ya yi min matar aure, inaji daga nan kuma ban ƙara cewa komai ba akan maganan sai ke da kika buƙaci idan zanje Gombe sanar da bikin za kimin rakiya and for all a take na ce miki ba wanda zaizo daga dangin Ammi inaji kuma ban sanar da ke ra'ayina akan hakan ba ko?" Ya tambaye ta idanun sa a kanta


Motsa bakin ta tayi kamar mai shirin magana and kuma ba maganar za tayi ba maganganu ne kawai ta keta yinsu a cikin zuciyar ta.


Wani murmushi ya saki da faɗin


"Ban san ki canza daga inda na sanki Sabira, ko lokacin da kukayi abinnan ranar da naji ta ce ki dinga girki da ita I think na sameki a ɗakin Ammi da maganar na faɗa miki ta ci albarkacin aure na da ke kanta ki dinga yi da ita a zauna lafiya amma ban faɗa miki alaƙar zamantakewa na da ita ba da har za ki budi bakin ki da na sani a koda yaushe alkairi ya ke faɗa amma ki kirata da sunan sheɗaniya?"


"Kenan duk abin da tayi min ba ka gani ba?" Ta faɗa idanun ta taf ƙwalla yayin da zuciyar ta ke wani irin tafasa


"Na gani mana, a gabana fa komai ya faru " ya bata amsa cike da mamakin ta na yanda ta sauya da bijiro da wasu hali da bai santa da shi ba


"Me yasa ita ba kayi mata maganan abin da tayi min ba sai ni da ba abin da na tofa amma tawa tayi zafi" ta faɗa tana ƙara cika baki


"A yanzu ni da kene kawai kuma hakan ya kamata na nusar da ke kuskuren ki ba tare da wani ya ji ba likewise ita ma idan zan mata magana ba sai nayi gaban ki ko wani ba two is for two right? Kawai ki kiyaye. Tashi mu tafi" ya faɗa tare da miƙewa ya fice ba tare da ya kalli inda mukullin motan ke ajiye ba duk da yana da tabbacin bata ɗauka ba.


Baki shanye da mamaki Sabira ke kallon shi yayin da zuciyar ta ke son fassara maganar da ya gaya mata ta fuska mabanbanta, ganin za ta ɓata lokaci ba tare da tsaida tunanin ta waje ɗaya ba ne ya saka ta miƙewa jiki a sanyaye ta bi bayan shi.


Aiki kawai ta ke tuƙuru, duk da yunwar da ke ƙoƙarin kassara ta amma hakan ta daure take aikin gabanta.

  

Duban agogon cikin system inta tayi taga 3:54pm ɗan zaro idanu tayi waje haɗi da saurin adana bayanan da ta rubuta da niyyar idan ta dawo gobe ta idasa.


Rufe system in ta yi tare da kifa kanta akan table inda ke gaban ta tana ajiyar numfashin wahala.


Duba ɗaya za ayi mata a fahimci yadda idanunta suka yi ciki ciki sabo da yunwa da gajiya.


Wata hamma ta saki daidai sanda taji alamun an taɓa ƙofa ta ana da niyar shigowa. 


Hakan ya sata tashi zaune tana fuskantar ƙofar 


Janye ƙwayar idanun ta tayi akan hanyar ƙofar tare da fara kwashe tarkacen ta dan sam bata shirya sartse da yawu yanzu ba 


Waje ya samu a kan kujerar da ke fuskantar ta ba tare da ya janye kaifaffun idanun sa a kanta ba dukda ba shi take kallo ba amma ya san za ta ji tasirin kallon da ya ke mata a jikin ta


"Magana ce ta kawoni" Ya faɗa ganin tana niyar miƙewa


Jimmm tayi kamar ba zata koma ta zauna ba sai kuma ta zaunan tare da kallon agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannun ta haɗi da ɓata fuskar ta 


Nunawa ya yi bai fahimci abin da take nufi ba, hakan ya sashi shima ɓata fuskar tare da gyara zama sannan ya fara magana


"A zahiri bansan da sunan da zan Kiraki da shiba, ƊANDAUDU, IMTIAZ ko MUMTAZ? amma ba wanannan ne muhimm ba, the most shine akan abin da kika min"


"You betrayal me, na amince da kai ohh am sorry na amince da ke a lokacin da nake miki kallon ɗan uwana na jini, and kinyi wasa da tunani na wajan ɗora ni akan keken ɓerar da zai haddasa kyara da hantara tsakani na da mahaifi na, and the wotst tafiyan Malam Nasiru, biki yiwa Ammi adalci ba dan bata tsare miki komai ba, ƙarin abin takaicin a fuskar da na sanki a matsayin ƊANDAUDU wai kece ke bani shawara na kar na damu, Hmmm!"


Ya dakata sakamakon wani abu da ke masa yawo a ƙirjin sa.

Ajiyar numfashi ya sauke tare da lashen ƙasan lips insa sannan ya ci gaba


"Abubuwa da dama idan na tuna it hurts, Amma ba shine a gabana ba, mutum ke bayyana raunin sa ne a inda aka san muhimmancin sa ake kuma tausayin sa, but karki damu na yi miki Uzuri duba da wacce kike tare da ita, i know komai na zalunci, makirci da Mugunta za ku iya fiye da haka ai zuciyar ku ce haka a kuma haka Allah ya yiku kuma shi kaɗai ne zai yi maganin ku a duk sanda ya so hakan, a yanzu ma ba wai ya barku bane ba, ku jira Ranar sakamako and bana fatan ko kaɗan ki sauya zuwa mutuniyar kirki ko makamancin hakan, dan biki cancanci Yafiyar Ubangiji ta sauƙi haka ba, irinku sai Allah ya fitadda haƙƙin rayukan da kuka cuta kuka zalunta tun a duniya kafin kuje ku haɗu da nashi sakamakon a can" 


Wata iriyar Hamma ta saki tare da faɗin "wash Allah na" cikin Muryar gajiya tare da mirza idon ta guda ɗaya da ɗanyatsa har lokacin kuma ko inda ya ke bata ƙara marmarin kalla ba 


Wani murmushin takaici ya saki tare da jinjina sheɗancin ta a zuciyar sa,  Allah fa yake gaya mata a fakaice but ta nuna bata damu ba 

tsakiyar kansa ya sosa tare da gyara zamansa dan faɗa mata takamaiman abin da ya kawo shi


"An ɗaura min aure da kene bisa wani nufi da ƙuduri da ku kaɗai kuka sanshi sai kuma Allahn da ya halicce ku.

Ban isa na goge ƙaddara ta ba tunda abokan mahaifina da mutane da dama ta ɓangaren mahaifina da kamfanin mahaifina sun sanar kuma sun shaida ɗaurin auren and kuma Duniya ta shaida Kuma ansan ke in matata ce kuma Ni mijinki ne" 

ya dakata ganin yanda yanayin fuskar ta ya fara sauyawa zuwa yanayin da kai tsaye ba zai iya fassara shi ba.


Wani murmushi ya saki sannan ya cigaba


"Ina da daraja da mutumci, so ba zaki ɓarar min da shi ba idan na zo wucewa ana ga matar wannan ko kuma ace ai matar wane ne tayi abu kaza, abu ɗaya zuwa biyu zan gaya miki" ya faɗa yana saita ƙwayar idanun sa cikin nata da ta wani ɗago a hagunce tana kallon sa jin maganar sa ta ƙarshe da kuma dukkan alama tana son ta ji me zai gaya matan


"Fitarki office daga ƙarfe tara zuwa goma ya yi saidai ban yadda ki wuce ƙarfe biyu na rana ba, kuma duk inda zaki je sai kin nemi izni na haka zalika duk abin da za kiyi sai da amincewa ta kuma zuwa kampani ya koma monday- Thursday kawai, kiji, nayi rantsuwa da Allah na sake rantsuwa da Allah na ƙara rantsuwa da Allah a karo na uku Muddin na umarceki da kimin abu a daidai lokacin da na so kika Musa min ina mai tabbatar miki rantsuwar da nayi ban janye ba na yita ne akan hukuncin Allah ya tabbata a kanki irin hujuncin da Allah ya yi rantsuwa mala'iku suka ce Amin ga duk matar da ta sabawa umarni mijinta"


Yana kaiwa nan ya miƙe tare da sa hannu cikin aljihunsa ya zaro mukullin mota haɗi da ɗora mata shi kan table yayi hanyar ƙofa.

Yana daf da ficewa ne ya dakata ba tare da ya juyo ba da faɗin  "umarni na nafarko kenan karki sake ajiye min key in motar da danke aka siye ta, na biyu kar ki sake kiyi gangancin fita office da safe ba tare da Ni na kaiki ba, idan ina da uzurin ƙin fitar ki nemeni zan sanar da ke"





*Comment*

*Vote*

*Share*

*Follow me on *Wattpad@*AuntiMamee*Arewa writters