3
HADARIN GABAS…..👌
3️⃣
(My dear fans, I've received many messages asking if I've stopped posting updates about Hadarin Gabas. I'm sorry to say that I won't be posting this weekend. We haven't even reached the midpoint of the story yet, and I'm already feeling anxious about how it will unfold. Just be patient, all will be revealed soon. Stay tuned, fans! This is just the beginning of the story.)
Da sauri Amani ta ware idonta, Iman ma a firgicen take. Dada kuwa bai wani jira komai ba ya isa gaban mahaifiyarsa Didi da take yashe a k’asa jikinta sai rawa yake cikin matuk’ar tashin hankali Ya d’Agata yana kallon yarda jikinta ke kakkarwa “Iman Go and call the Doctor she is unconscious…” Iman ta janye Amani daga jikinta ta fita da sauri. Safna kuwa wani farin ciki ne ya shiga zuciyarta a take ta fara addu’ar Allah yasa Didin ta mutu ta huta. Dama sosai matar ta tsaya mata a Rai ta hanata rawar gaban hantsi… Don haka a ranta ta dinga furta “Margaya Didi, Allah ka amshi ran baiwarka.” A zahiri kuwa sai ta isa wajen Didin da sauri itama tana furta “Imaam tofa mata addu’a, Allah yasa ba ajalinta ba ne yazo.” Wani irin kallo Imaam Ya jefa mata yana sake jin wata muguwar tsanarta a ransa. Ji yake kamar ya mata saki Uku, sai dai Ya san bai isa ba he is not authorizedto do that..” Ya rungume Didin a jikinsa hankalinsa a tashe yana furta “Ya Allah, kada ka saka Didi ta mutu ta sanadiyyar bak’in cikin da na k’unsa mata, ba zan iya rayuwa ba babu ita ba, Ya rabbi ka bata lafiya…” Ya fa’da manyan idanunsa masu hasken gaske tuni suka riki’de suka koma wasu kalar Brown kamar yarda suke zama a duk sanda yake cikin b’acin rai. Leb’ensa kawai yake fisga da k’arfin gaske bai damu ba koda zasu fashe. Zafin da yake ji na zuciyarsa yafi masa kowane irin ciwo da zai ji ra’da’di.
Amani dai tana zaune her heart filled with pain and sorrow. Tana ta addu’a Allah kada ya amshi ran Didi, don Didi ita ce kwanciyar hankalinsu sai Umma T.
A da kama tana son Dada kamar ta Mutu ganin yarda yake nuna musu kulawa sai dai tun bayan abinda ya faru take jin wata muguwar tsanarsa. She feels intense anger.
Shigowar Doctor ne yasa ta tsagaita daga kukan da take. Tana sauraran bayanin Doctorn da yake bawa Nurses Umarnin su kawo masa wasu allurai. Yana kallon Moddibo Ya ce “Kada ka damu, she will survived In sha Allah, firgita ta yi normally kuma mutum yana shiga irin wannan yanayin a lokacin da Ya shiga firgita ko damuwa ko razana, so that ba wani abu ne she will be there zuwa nan da two days muga abinda Allah zai yi.” Imam ya lumshe ido a hankali yarda leb’ensa ne kawai Ya d’aga ya ce “Allahu Ya sha…” Shi kansa sai ya ji kunyar saka Allah a
Lamarinsa. Anya Allah zai amsa addu’arsa bayan wannan abin kunyar da Ya aikata. Ya sake runtse idonsa yana jin yarda zuciyarsa ke wani irin bugu. He wished ya mutu kawai a lokacin Ya daina kallon Amani yana jin kunyarta. Didi da idanunta ke zubar da hawaye ta saka hannunta da yake rawa ta yafito Imaan. Da sauri Imaan ta isa wajenta a hankali ta kara kunnenta a kusa da bakin Didi. Didin cikin rawar murya ta furta “Ki…..ra….min…Tee…” Sai kuma bakin ya datse. Imaan tsaf ta gane nufinta don haka da sauri ta d’au wayarta zata kira Umma T D’in, da sauri Imaam Ya kalleta cikin dakiyar murya ya furta “Give me your phone Imaan…” Irin Tsawar da Ya daka ne yasa Imaan bata san sanda ta mik’a masa wayar ba hannunta na rawa. Amani ta saki wani malalacin murmushi a ranta take sak’a Lallai Ma Dada, ya aikata abin sannan Ya ce ba ya son a gayawa y’an uwansa, ai ba y’an uwansa ba ma duk duniya sai an ji in dai tana raye, sai ta tona masa asiri mutane sun masa tofin Allah Ya tsine. Don haka ta ji ta samu wani irin courage da sauri ta saka hannu ta d’au wayarta tana hararar Dada da gefen ido. Direct kiran Umma T ta yi. Basu farga ba sai ji suka yi ta rusa kuka ta furta “Umma T. Pls Ki zo Didi ba lafiya” ta fa’di jin abinda ta ce yasa Da wani irin hanzari Ya fisge wayar da take hannunta, yana kallonta cike da mamakin abinda ta aikata. Itama kallonsa take kamar yarda bai rusunar da k’wayar idonsa ba itama k’in rusunar da tata ta yi ta kafe shi da Wild eyes d’inta da take jin kamar suna fitar da turirin hayak’i tsabar kallon tsanar da take masa. “Have you come to your senses? Lets settle this peacefully. Tara mana jama’a kike son yi?” Ta runtse ido tana furta “Yes ba ni da hankali, bani da hankali ka cuce ni ka saka min hauka kuma ba zan tab’a yafe maka ba, sai na saka jama’a Sun maka tofin Allah Ya tsine, I hate you Dada, I am fed up with seeing your face.”
“Ke, Amani ki lura da Wanda yake Miki magana mana, mahaifinki ne fa.” Safna ta furta fuskarta na wani irin blushing sam farin cikinta ya kasa b’uya. Amani da Imani suka mata wani irin kallo kafin Amani ta dartse leb’enta tana jin kamar ta shak’e Mommyn. Tsabar takaici ma kasa furta mata ko kalmar ‘a’ ta yi. Dada ya koma saman kujera ya zube hannunsa cikin tarin sumar gashin kansa ta asalin fulani. Yamutsa gashin yake kamar zai cire shi. Duk duniyar ta masa wani irin duhu. Tsawon lokacin ba wanda ya iya furta komai sai Amani da take ta kuka tana jin kamar zata rasa ranta….
UMMA T…
Tunda Amanin ta kirata ta ji wani irin mummunan fa’duwar gaba ta sameta. Salati ne kawai a bakinta, sai Kalmar Innalillahi da take furtawa a hankali. Ji take kamar Amani ta ce mata Didin ta Mutu. Haulat da take gefe ta dafa ta tana furta “Ammi calm down, bafa mutuwa Didin ta yi ba, mu je asibitin mu gani kada ki tashi hankalinki…” Fatima ta zubawa y’ar tata ido tana fatan abinda Haulat D’in ta fa’da Ya zama haka ne. Allah yasa Didi ba yanzu zata Mutu ba. Suna son Didi suna son kuma rayuwa da ita fiye da komai. Hijab Haulat ta zura mata sannan ta mik’e hannunta cikin na Haulat D’in suka fice daga gidan. Haulat ce take jan motar don duk sun san asibitin tun bayan da Moddibo Ya gina shi har su kansu asibitin suke zuwa.
Tana parking Umma T ta fito da sauri Har tana yin kamar zata kifa. Hakan yasa Haulat D’in furta “Be careful Umma T.” Sannan ta fito ta saka Umman tata a gefen jikinta suka k’arasa cikin asibitin.
Har a lokacin ba Wanda yake magana a cikin d’akin. Kowa da tunanin da yake ransa. Amani idanunta a lumshe, tana tuno wancan bak’in daren da Dada ya rusa mata rayuwarta saboda son zuciya…. Duk da sound D’in bu’de k’ofa da ta ji bai saka ta bu’de lumsassun idanunta ba har sai da ta ji maganar Umma Tee. Tana tambayar Dada me yake faruwa da Didi? “Kiddo ka gaya min mana…” Ta bu’de lumsassun idanunta tana kallon Dadan tana son ta ga reactions D’in fuskarsa. Iska taga ya fesar bai yi magana ba ya jingina da kujerar idanunsa a lumshe. Wani irin fa’duwar gaba yake ji ya rasa da wani irin ido zai kalli Umma T D’in. Fateemah ita ce tasa, ko a cikin siblings d’insu tasu tafi zuwa d’aya. Ita yake tara da dukkan damuwarsa me zai ce mata a yau da komai Ya Riga ya kwab’e, bayan sai da ta dinga masa warning sau tari idan yaje wajenta sai ta garga’de shi…. Umma T. Ta isa wajen gadon Didin ta dafa idanunta a kanta. Tana jin yarda sautin zuciyarta ke k’ara bugu… kafin ta ce komai Didi ta bu’de lumsassun idanunta da suke zubar da hawaye tana kallonta. Cikin rawar murya ta ce “Fad’imatu…maza fita da ni daga asibitin nan na daina ganin Moddibo da ahalinsa…. A yau na yi nadamar d’aukar cikin Moddibo na yi nadamar zamo…..” da sauri Umma T. Ta rufe mata bakinta da tafin hannun ta tana girgiza mata kai gabanta yana tsananta bugu. Ta ce “Yi barci Didi, kada ki masa baki.” Sai kuma ta juya wajen Moddibo da yake tsaye ya yi folding hand d’insa a k’irji jirkitattu kuma birkitattun idanunsa da suka sauya color ya zubawa Didin. Hannunta tasa ta finciki nasa da sauri suka yi hanyar waje, duk jikinta rawa yake tana addu’ar Allah yasa Moddin ba wani abu mai girma ya aikata ba da Ya tashi hankalin Didin. Bata tsayar da shi a ko ina ba sai a cikin motarsa tana kallonsa ta furta “Bu’de min mu shiga ciki ka gaya min menene? Koma me ka aikata lamarin sa na tabbatar ya yi muni Kiddo, tunda har ya zubar da Didi duk jarumar zuciyarta…” Hannu ya saka ya danna remote D’in motar suka shiga… da suka shiga ma kasa mata magana ya yi ya lumshe idonsa yana jin yarda idanunta suka bi suka dabaibayeshi. “Ina jiranka” Umma T ta furta…. Idanunsa a lumshe Ya furta “She is pregnant….” Umma T. Da wani irin tashin hankali ta furta “Who? Kada ka ce min Amani?” Ya ha’diye wani abu da Ya tsaya masa a wuya da k’yar sannan ya d’aga mata kai…. Ko bai yi magana ba ya san ta san me yake nufi. Da k’arfin gaske ta jijjiga shi ta ce “Sai da ka aikata Moddibo? Sai da ka rusawa yarinyar nan rayuwarta? Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna, dole Didi ta firgice dole ta rasa kanta wannan abin k’azantarsa ya munana…” Ta fa’da idanunta suna zubar da wasu irin hawaye. Jikin Moddi Ya yi sanyi don abu ne da bai tab’a ganinsa ba hawayen Tee d’insa, tun yarintarsu har yanzu da suka girma… Ya kama hannunta ya matse da kyau. Kafin ya d’ora fuskarsa a tafin hannunnata yana sakin wani irin kuka da yake bayyana tashin hankalin da zuciyarsa take ciki… Da wani irin zafin nama ta janye hannunta ta kuma kafe shi da idanunta kafin ta furta “To hell with you Moddibo, me zaka ce min sau nawa naja maka kunne akan hakan Amma ka nuna min bakomai… gashi nan abinda ake gudu ya faru… na tabbata ko rantsuwa zan yi ba zan yi kaffara ba k’ungiyar matsafa ka shiga, su suka ‘dora ka akan haka. Ka cuce mu, ka cuci yaranka ka cuci kanka, ka kuma cuci Didi da ta d’au dukkan kulawar ta ta d’ora a kanka, ga sakayyar da ka mata nan na tabbata wannan ne zai zama ajalinta. Zan d’auke Uwata zan bar asibitin nan da ita bana son kuma koda wasa kazo inda take, yaranka kuma ka san yarda zaka yi da su, ga abinda ake gaya maka nan wannan loakcin ake gudu gashi yazo…” Daga haka ta fice daga motar da sauri, kamar zata tashi sama. Zuciyarta wani irin zafi take ga tausayin Amani da take ji a ranta. Me Moddibo ya aikata shikkenan ya rusa rayuwar Amani waye zai aureta da wannan bak’in painting da Ubanta ya shafa mata? Tafiya kawai take bata san inda take saka k’afarta har zuwa sanda ta isa d’akin da aka kwantar da Didin da Amanin. Tana shiga ta kalli Haulat da Iman don bata son yin zancen a gabansu ta ce su tafi waje. Idanunta Ya rufe ta nufi wajen Amanin ta jata da k’arfin gaske ta fara zuba mata dundu tana furta “Hankalinki ya kwanta Ama? Mahaifinki Ya kusanceki ko ga tsarabar sa nan a cikin ki? Sai ki fara shirin abinda zaki fuskanta nan gaba.”
Da sauri Mommy ta isa wajen tana furta “Aa Umma T, kada ki mata lahani, ki bi a hankali duk da an San abin da ciwo Amma ai k’addara ta riga fata…” Wani irin kallo Fateema ta jefa mata tana furta “K’addara? K’addara kike kira Safna?” Sai ta cije bakinta ta isa wajen Didi da ta ji tana nishi da k’yar. Hankalinta a tashe kawai ta zube a wajen tana sakin wani irin kuka. Shigowar Umma D. ne yasa ta ‘d’ago tana kallon Umma D D’in da ta nufi wajen Safna tana furta “Me ya faru ne?” Safna taja ajiyar zuciya kamar gaske ta furta “Wannan tashin hankalin bai kamata ki ji shi ba.” Wani kallo Dijatu ta mata kafin ta isa wajen Didi tana furta “Ya Ilahi wai me ke faruwa ne?” Safna ta jijjiga kai a ranta ta furta “Ai yanzu zan gaya miki asararriya burina yau ya cika…” a fili ta furta “Abin dai ba da’din Ji, Amani ce da cikin mahaifinta a jikinta ……” Dijatu ta juyo da sauri tana zubawa Safna wani gigitaccen Mari kafin ta furta kada ki k’ara gaya min wannan banzar maganar, Har abada Jinin Muhammadu Moddibo ba zamu aikata irin wannan fasadin mara da’din ji ba, ta fa’di dai Uban da ya mata ciki ba Moddibo ba, sau nawa nake fa’da a sakawa yarinyar nan ido rawar kanta tafi k’arfinta, yanzu Fateemah kin yarda da abinda na fa’da, Har kuke jin haushi na da na hana yaron wajena aurenta, yanzu kun ga Hujjata ai dama na fa’da da wata a k’asa gashi kuwa ta fito….” Fateemah ta ‘d’ago a hankali tana kallon Dijatu abin mamaki sai taga kamar Dijatun farin ciki ne a cikin idanunta kamar Moddibon ba D’an uwanta da suke ciki guda ba…. Ba tun yau ta san Dijatu bata son Zuri’ar Moddibo ba ba, ta kuma rasa dalili.. cikin b’acin rai ta furta “Adda D, kamar abinda kike bai kamata ba, ya kamata mu samu mafita ba kuma a samu na Yaya tawa a gari ba…” wata dariya ta yi kafin ta kalleta ta ce “Ai zancen Duniya ba zai tab’a b’uya ba….
JIKAR NASHE★✍️