HURAYYAH (New edition) Chapter 1
HURAYYAH
Dukkanin yabo da kuma godiya sun tabbata ga Ubangijin halitta,wanda ya nufeni da fara gyara wannan labari domin makaranta su amfana da darussan da ke cikinsa.Ina fata makaranta labarin za su yi alfahari dashi fiye dana baya,domin a wannan karon labarin zai ƙayatar fiye dana farkonsa.Labarin zai kasance paid book ne,wanda za ku biya kuɗi ƙalilan domin ku karanta cikakken labarin.Ina ma ƴan arewabook albishir da cewa za su karanta galla-gallan shafuka akan kuɗi ƙalilan,burina shine ku bibiyi labarin HURAYYAH daga farko har ƙarshensa.
Chapter 1
Matashi ne da bazai haura shekaru talatin da bakwai a duniya ba,hakimce a bayan tsaleliyar motarsa driver na jansa a hankali kasancewarsa mutumin da sam bayi ƙaunar gudu a mota.
Shigowarsa garin na Gombe kenan wanda ya kasance mahaifarsa,bayan ya shafe watanni biyu cur bashi cikin ƙasar ma baki daya.Sosai zuciyarsa ke cike da kewar mahaifiyarsa,wacce sam bai haɗa ƙaunarta da ta kowace mace a faɗin duniyar ba.Jaridar dake hannunsa ya aje bayan ya wadata fuskarsa da kyakykyawar murmushi,fuskar Hajiyarsa ke masa gizo yana ayyana yadda zai sameta cikin farin cikin ganinsa.
Tunowa da yayi da matarsa Samha ya sanya dukkanin farin cikinsa dakushewa lokaci guda,a kuma daidai lokacin suka iso tangameman gidan nasa dake federal low-cost Gombe.
Babban gida ne na sosai mai ɗauke da apartment kusan guda uku,banda boysquarters da ke can baya.
Tun shigarsu haraban gidan hadimansa suka lulluɓe bakin motar,suna masa barka da isowa.
Cikin sakin fuska yake amsa musu gaisuwarsu kasancewarsa mutum wanda ya horu da sanin darajar talaka da ma ɗaukacin mutanen dake ƙarƙashinsa baki daya,alkhairinsa da tsananin tausayinsa ga na ƙasa dashi shi ke sake janyo masa wani irin matsanancin so ga ɗaukacin mutanen da yake tarayya dasu.
Jibga-jibgan jakunan da ya zo dasu ake kwashewa ana wucewa dasu zuwa part ɗinsa kamar yadda ya bayar da umurni,yayin da Shi kuma kai tsaye ya tasanma isa hanyar apartment ɗin mahaifiyarsa zuciyarsa cike da zumuɗin son yin tozali da kyakykyawar fuskarta.
Hajiya Maryama dattijiyar mace mai kimanin shekaru hamsin da biyar zuwa da shida,ita ce hakimce cikin ɗaya daga cikin kujerun da sukai ma parlon ƙawanya.Tana sanye cikin riga da zani na atamfar Holland wanda kalar atamfar ya amshi farar fatar jikinta irin na fulanin asali.Sam ko kaɗan idan ka dubeta ba za ka ce ta kai shekaru hamsin ma a duniya ba,saboda tsabar hutu da jin dadi da take cikinsa.
Sallama ya dinga rafsawa cikin tattausar muryarsa mai sanyin amo,Mum ɗin ta amsa sallamar tasa tare da yin gaggawar miƙewa domin taro tilon ɗan nata da Shi kaɗai ya yi Mata saura a duniya.
A corridor ɗin da zai kawosa cikin parlon suka kusa gwabza karo,yayi saurin ja baya idanunsa fes a kanta yana jin wani irin nishaɗi na kewaye zuciyarsa. A hankali ya tako zuwa gareta bai jira komi ba ya rungumeta tsam yana faman sauke ajiyar zuciya,Hajiya ta kai hannu a hankali ta shafa sumar kansa wanda yayi gadon kwantaccen gashi baƙi siɗik irin na fulani mai tsananin laushi da santsi.Cikin sanyin murya ta furta. "Ma Sha Allah Gadanga,ina mai godia ga Allah daya dawo mini da kai lafiya Aliyu Haydar." Aliyu Sai ya sake shigewa cikin jikinta yana mai faɗin. "I miss u so much Mum,wallahi nayi kewarki sosan gaske. "
Hajiya Maryama ta zamesa daga jikinta a hankali tana mai kama hannunsa har zuwa cikin parlon,zaunar dashi tayi tamkar ƙaramin yaro kafin ta nufa wata ƙofa wacce nake tunanin hanyar isa kitchen ce.
Bata ɗauki dogon lokaci ba ta dawo hannunta ɗauke da ƙaramin tray,Wanda aka ɗauro wani kyakykyawar jug cike da damammiyar fura haɗi da goran ruwa mai matsakaicin sanyi. Aliyu na hangota yayi gaggawar tashi ya amshi tray ɗin daga hannunta yana jifanta da murmushi,da Kansa ya zuba furar yana sha a hankali yayin da Hajiya Maryama ke dubansa cike da tarin ƙauna irin ta UWA da Ɗanta,waɗanda sukai wata irin shakuwa ta ban mamaki da juna.
Sai da ya sha kusan cup biyu na furar sannan ya aje cup ɗin tare da yin hamdala,ya ɗauki cup ya zuba ruwan ya sha yayi gyatsa alamun ya ƙoshi.
Cikin nutsuwa ya baro mazauninsa ya sauka ƙasa daidai Inda ƙafafuwan Hajiyar nasa yake,kwantar da kansa yayi bisa kan cinyoyinta ita kuma ta kai hannu ta shafo sumar kansa.
Ya ɗago Yana kallon kyakykyawar fuskarta ya yi murmushi,ga alama abu ne da ya yi sabo dashi tun yana ƙaraminsa.Hajiyar ce ta dubesa tana faɗin.
"To Haydar tunda naga isowarka lafiya sai ka tashi ka isa ga matarka,nasan yanzu tana can ta cika tayi fam da fishin daɗewarka anan."
Ta kai ƙarshen maganarta tana mai son ɓoye damuwarta game da munanan halayyar surikar tata,wacce ko kaɗan ada bata yi zaton kasancewar Samha a hakan ba.
Aliyu nan da nan sai yayi saurin ɓata fuskarsa,ya turo baki tamkar ƙaramin yaro yana faɗin.
"Kai Hajiyata,yanzu har wani daɗewa nayi da za ta yi korafi akai? Kuma ma inda sabo ai ya ci zuwa yanzu ace Samha ta saduda ta gane cewa ni Aliyu Haydar bana haɗa lokacin mahaifiyata da ta kowace mace a duniya." Ya kai ƙarshen maganarsa cikin fushi da jin zafin halayyar Samha.
Ganin ran maza na son ɓaci ya sanya Hajiya Maryam lallaɓasa ya baro part ɗin nata,bayan ta rakasa har bakin ƙofa ta ga fitarsa kafin ta juya.
Tunda ya sanya kansa cikin part ɗin yake jiyo ƙamshi mai tsananin daɗi yana tashi,a hankali ya dinga ratsawa har ya isa zuwa cikin ƙaton parlon bakinsa ɗauke da sallama.Shiru sam babu alamun mutum a cikin falon,illa qamshi da sanyin air condition dake ratsa kowani sassa na cikin parlon.
Kai tsaye hanyar da zai sada shi da bedroom ɗinta ya nufa,cikin muryarsa mai sanyi yake kiran sunanta "Samha! Samha!!"
A haka ya tura kansa cikin bedroom ɗin nata wanda ni mai ɗakko muku rahoto bazan iya kwatanta muku tsananin tsaruwarsa ba,can ya hangeta kwance Daga bakin makeken bed ɗin nata hannunta riƙe da waya tana dannawa.Jiyo muryarsa da tayi ya sanya ta aje wayar tare da tashi ta nufosa da sauri,bata jira komi ba ta shige cikin jikinsa ya rungumeta tsam yana shaƙan qamshinta mai sanyi.Tabbas a matsayinsa na lafiyayyen namiji idan yace bai yi kewarta ba ya yi ƙarya,watanni biyu ba kwana biyu bane.
A hankali ya kai bakinsa yayi kissing wuyarta yana sake shaƙo qamshin turarenta mai ratsa zuciya,yayin da Samha ta kai bakinta kai tsaye ta lalubo harshensa tana masa salon da tasan yana gigitashi.
Sun daɗe a haka kafin ya sassauta rikon da yayi mata,ta ɗago manyan idanunta ta sauke a kansa kafin ta buɗi baki tana fadin. "I miss u so much my darling,sai dai sam baka min adalci ba Aliyu,a ce ka iso a maimakon ka fara isowa zuwa gareni sai kaje can ka rashe ana tsarama maka magana,haba Aliyuna ni yafi dacewa in fara yin tozali da mijina wanda nayi kewarsa tsayin 2 month ba wata can ba."Ta ƙarishe kalamanta cike da nuna jin haushinta a zahiri.
Aliyu ko gaggawar rabata da jikinsa yayi yana tsareta da manyan idanunsa dake rikitata,cikin wani irin yanayi ya soma faɗin "Wai sai yaushe ne Samha za ki gyaru kisan ƙima da darajar Mahaifiyata? So nawa zan faɗa miki bani ƙaunar irin waɗannan mitan da kike akan Hajiyata? Ke wace iriyar wawiyar mace ce wai?Look Samha na gaji,kin fara kaini maƙura akan yadda kike nuna rashin daraja Hajiya har a gaban idanuna,kinfi kowa sanin babu wata macen data isa in haɗa lokacinta dana Hajiya,sannan wannan ya zama karon ƙarshe da zaki sake min hakan kin gane?"
Bai jira komi ba ya fice daga ɗakin yana mai jin zafinta sosai,Samha Sai ta rufa masa baya a guje cikin sassarfa har ta cimmasa domin ba za ta so daga isowarsa ya ɗauki wannan zafin da ita haka ba.
Hannu ta kai ta janyo rigarsa hakan ya sanya shi tsayawa cak ba tare da ya juyo ya dube taba......✍🏻