SHU'UMAR MASARAUTA 2

6

by @ameeraadam

*SHU'UMAR MASARAUTA*

        *BOOK 2*

      ©AMEERA ADAM


 *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

  (_Home of qualities and trusted writers of the nation_)


Tsokaci: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a wata kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.

  

 SHAFI NA SHIDA


 Kalaman da ya ji sun daki kunnuwansa ne suka saka shi ɗagowa a firgice, fat! Fat! Fat! Zuciyarsa ta shiga bugawa da ƙarfi tamkar tana yunƙurin yin tsutsuwa ta faɗo daga ƙirjinsa.


 "Ba zan iya cin amanar Yarima ba, haƙiƙa Yarima mutum ne har da rabin mutum. Ya ba ni farinciki a lokacin da duhun ɓacin rai ya dakushe rayuwata, wannan zalinci ne abin da..." 

 Kalaman Bawa Iro suke katse sakamakon dukan da wani matashi da ke gefe ya kai masa. Bakin ne ya fashe nan take jini ya fara fita daga bakinsa, duk da yana jin raɗaɗin ciwon hakan bai hana shi kallon Waziri ya ce.


 "Waziri dama haka kake ban sani ba?" 

Murmushin ƙeta Waziri ya yi yana faɗin.


 "Kai yaro dube ni da kyau, sama ta yi wa yaro nisa sai gani sai hange daga nesa. Ni da kake gani na wuce duk inda kake tsammani, kuma kamar yadda na sa aka ɗauko ka aka kawo ka cikin dajin gidan nan ba tare da wani ya gani ba. Wallahi tsaf zan sa a datse numfashinka a wurgar da gawarka ba tare fa wani ya ji labari ba." Tsoron Waziri ya bayyana ƙarara a fuskarsa, yana nan tsaye ya ji Waziri ya buga masa tsawa.


 "Za ka ba ni haɗin kai, ko ba za ka bayar ba?" 

 Bawa Iro ya girgiza kai ya ce. "Ba zan iya cin amanar Yarima ba." 

 Lokaci ɗaya Waziri da yaransa suka ƙyaƙyace da wata irin dariyar shakiyanci. Waziri ya bi Bawa Iro da kallon wulaƙanci kamar ya ga kashi ya ce.


 "Na saye Bayi sama da goma a cikin masarautar nan, kuma gabaɗayansu mun yi alƙawari da yarjejeniyar za su ba ni haɗin kai." 

Waziri ya tsahirta sannan ya fara zagaye Bawa Iro ya ce.

 "Dama akwai matsiyatan da har su mutu a tsiya za su ƙare, dube ka a wahalce ana son gatata rayuwarka kana ƙi." Shiru Bawa Iro ya yi ƙirjinsa yana bugawa. Waziru ya matsa kusa da shi murya a kausashe ya cigaba.


"Rantse da girman Allah, matuƙar maganar nan ta fita sai na jefa ka a tekun bala'in da har ka mutu ba za taɓa ninkaya da iyo a cikin ruwa da shi." Gyaɗa kai Bawa Iro ya yi jiki na karkarwa, Waziru ya dubi samarin gefensa ya furta.


 "Ku yi masa kashedi." Ko rufe baki bai yi ba suka rufe Bawa Iro da duka sai da jikinsa ya yi tsami sannan Waziri ya ce su dakata.


 Tun bayan tattaunawar da ya gama yi da mahaifinsa yake saƙa da warwarar a kan kalaman da suka tattauna, ajiyar zuciya sarki Abdallah ya sauke. Zuciya a cunkushe ya ɗauki waya ya latsa lambar amininsa Waziri, bugu biyu ta yi daga can ɓangaren ya ji an ɗauka.


 "Indai mulki da sarauta ce to a ƙare ta a msarautar Huddam kowacce iri ce. Allah Ya taimaki Takawa." Waziri ya furta cikin sigar zolaya. Murmushi Sarki Abdallah ya yi ya furta, "Ba ma son shakiyanci Waziri, yanzu dai akwai muhimmiyar maganar da muke son mu tattauna idan ba ku da wani uzurin." Zuciyarsa Waziri fes da ya ji haka don ya tabbata ba a rasa nono a riga, idan haka ne kuwa shi gaba da ta kai shi gobarar titi a Jos.


 "Ba ni da wani uzurin bari na ƙaraso ranka shi daɗe." 

 Waziri ya furta a gaugauce, babbar rigarsa ya saka yana fitowa a falon Adda ya ci karo da Yarima Ramadan zaune suna gaisawa da Adda uwargidan Waziri.


 'Musakin banza da wofi, nan da gobe idan Allah ya kai mu, wani zancen ake ba wannan ba.'

 Waziri ya furta a ransa yana bin Ramadan da kallon tsana. A fili ya faɗaɗa fara'arsa yana faɗin.


 "Yariman gobe!" 

 Jin muryar Waziri ya sa Yarima ya russuna har ƙasa cikin girmamawa ya ce. 

 "Barka da hutawa Baba Yarima." 


 "Barka dai Yarima! Ni bari na ƙarasa wurin Mai martaba." Waziri ya faɗa yana bin hanyar fita, Ramadan ya amsa masa.


 Adda ita ce matar Waziri, mace ce mai kirki da mutumci. Tun Yarima yana ƙarami yake zuwa wurinta shan fura da daddare, har kawo wannan lokacin da ya zama saurayi. Takanas take aikawa a kai masa fura har ɗaki, wani lokacin kuma idan ya yi niyya ya taka har ɗakinta ya zauna ya sha suna hira. Duk furar da Yarima zai sha ba ya taɓa jin daɗinta, matuƙar ba ta Adda ba. Don haka suka shaƙu sosai, har ta ce duk abin da Adda ta ɗauka ta ba shi kai tsaye yake ci domin ya ɗauke ta tamkar uwa a wurinsa.


"Waziri!"

 Sarki Abdallah ya furta yana kallonsa.

 "Ko bakinka bai furta ba, yanayinka ya gama warware mini saƙon zuciyarka ranka shi daɗe. Allah Ya taimake ka me yake damunka!" 

 Waziri ya yi maganar cikin nuna tsantsar damuwa da tashin hankali.

 "Allah Ya sani, duk cikin 'ya'yanmu mun fi ƙaunar Yarima, kuma mun fi son ya kasance wanda zai gaji buzunmu. Sai dai kashi! Mai martaba ya zo mana da saɓanin muradin ranmu." 

 Sarki Abdallah ya yi maganar cikin ɗacin zuciya, jin haka ya sa Waziri ya ɗago a hargitse ya furta.

 "Amma ba ka ganin Mai martaba ko akwai abin da ya hanga kafin zartar da wannan hukuncin, duba da irin lalurar da Yarima yake fama da ita?" 

Ajiyar zuciya Sarki Abdallah ya sauke ya ce.

 

 "Mun yi tunanin haka, amma me ya sa Takawa bai hangi qualities ɗin da Ramadan yake da shi ba? Abin da ba ku sani ba, duk wata kadara da dukiyarmu babu wacce Yarima bai san da ita ba. Kai akwai dukiyoyin da Ramadan yana yin signing sun fita kenan, amma yaron nan ko ficika bai taɓa taɓawa a ciki ba." 

Ya ƙarasa maganar wani hawaye mai ɗumi yana bin fuskarsa.


 Kusan sakan biyar Waziri ya ɗauka yana kallon Sarki Abdallah, a ransa ya furta.

 'Tabbas wannan shi ne mutuwar wani tashin wallahi, ai kuwa dole na sanar da Fulani mu san abin yi.'

 A fili sai ya ce.


 "Amma ina fatan shi Yarima bai san da haka ba?" 

Sarki Abdallah ya jingina da bango ya ce.

 "Mu da shi da Takawa muka fara magana, daga baya Mai martaba ya sa aka kira iyayensu Mata aka sanar da su." 


 Jin daɗin kalaman Sarki Abdallah ya sa murmushi ya suɓuce wa Waziri, domin har ya gano hanyar da zai bi ya ƙala wa Yarima sharri a ruwan sanyi. Amma daga baya sai ya wayance da cewa.

 

 "Ni a fahimtata wannan ba abin ɗaga hankali ba ne ranka shi daɗe, ina ganin hakan ne zai bayar da damar da za a ci gaba da nemawa Yarima maganin lalurarsa. Idan ya so koda a nan gaba ne, sai a sa sabon sarki ya yi murabus." 

 Ajiyar zuciya a fili Sarki Abdallah ya sauke ya ce.


 "Allah Ya sa haka ne ya fi zama alheri, amma muna fatan wannan maganar ta zama sirri tsakaninmu da ku Waziri. Hatta iyalainmu mun gargaɗe su a kan haka, domin ba ma fatan masarauta ta ji wannan labarin tun a yanzu." 

 Da hannu Waziri ya yi wa Takawa jinjina sannan ya ce.


 "Idan har mamacin da ke ƙarƙashin ƙasa zai dawo duniya, na tabbata wannan maganar za ta fito daga bakina."

 Kai kawai Takawai ya gyaɗa masa, sannan suka ci gaba da tattauna muhimman maganganu da suka shafi sarauta da sirrikansa. Bayan da Waziri ya fito daga sashen Takawa sai da ya shiga sashen tsohon Sarki Kamalu ya kwashi gaisuwa a wurinsa, sannan ya yi masa sallama ya wuce gida zuciyarsa cike da saƙa da warwarar a kan ɗanyen aikin da zai aikata.


Fuska ɗauke da damuwa Jadda ta dubi tsohon Sarki Kamalu ta ce. 

 "Allah Ya taimake ka na gagara runtsawa a kan wannan hukuncin da ka yanke, ina ganin duk wanda za a ɗora a kan karagar nan ba zai kama ƙafar Yarima ba." 

 Murmushi Sarki Kamalu ya yi, ya ɗauki ruwan inbin da ke cikin kofi ya kurɓa sannan ya ce.


 "Jawahiruna! Har yanzu kamar ba ki fahimci gidan sarauta ba. Wannan hukuncin da na zartar ba a banza na zartar da shi ba, akwai ƙulallan ɗaurin da na san da shi wanda ba ki sani ba. Lokaci ne zai nuna mana haka." Cike da gamsuwa ta furta.


 "Na aminta da kai ranka shi daɗe, amma wa za a ɗora a kan karagar?" 

 Girgiza kai ya yi ya ce.


 "Karagar masarauta ai ta mai rabo ce, koma wane ne fatan dai Allah Ya ba shi ikon sauke nauyin da yake kansa." 

Jadda ta amsa jiki a sanyaye, don har lokacin zuciyarta babu daɗi.


  Lokacin da Umaima ta farfaɗo ji ta yi jikinta ya sauya gabaɗaya, wani irin abu take ji mai nauyi kamar an danne ƙirjinta da ƙaton dutse. A hankali ta ja jiki ta zauna tana ƙarewa jikinta kallo, ƙarfi da yaji take son tuno wani abu da ya faru a rayuwarta amma ta gagara tunawa. A kan dole ta watsar ta haƙura, tunanin ɗanta Basiru ne ya bijiro mata, da ta so tambayar Bamaguje sai ta ji wata irin faɗuwar gaba ta mamaye ta. Tana son tambayarsa, tana jin shakku da tsoronsa na hauhawa a birnin zuciyarta. 

  Kwana biyu a tsakani ta warke garau, tsutsotsin da ke fita a jikinta suka daina. Sai dai har kawo lokacin ruwa mai ɗoyi bai daina yin sintiri a ƙasanta ba, duk tsafi da sihirin Bamaguje ya yi bakin ƙoƙarinsa amma haƙonsa ya gagara cim ma ruwa. A kan dole ya ɗauke ta takanas, har zuwa fadar Boka Jassu domin ya nema mata magani. 

  Tun da Umaima ta shiga wurin Boka Jassu yake bin ta da mayataccan kallo, lokaci-lokaci yake haɗiyar yaw saboda yadda ransa ya biya a kanta. Ganin irin kallon zargij da Bamaguje yake yi masa ya shi wayancewa, ya ɗauko ƙullin magani ya damƙa mata haɗe da yi mata sigina. Umaima ta yi biris kamar ba ta fahimci abin da yake nufi ba, bayan sun tafi Boka Jassu ya shiga lashe baki, lokacin da ya tuna irin surkullen da ya yi wa Basiru ya fili ya saki murmushi ya ce.


 "Idan aure bai kawo ba, shika zai kawo ki. Ina zaune a nan za ki dawo ƙafarki da kanki." 

 Yana gama maganar ya bushe da dariyar rashin imani.


           ***

 Tun ranar da Rawiya ta ziyarci ƙungiya walwalarta ta sauya, duk da dama can ita ba mai hatsaniya ba ce. Tun Mami na gani tana ɗauke kai har abin ya fara damunta, ita kanta Safina da suke kwana a ɗaki ɗaya sauyin 'yar uwartaa ba ƙaramin damunta yake ba. Saboda sau tari ba ta da aiki sai tagumi da tunani, idan aka matsa mata da tambaya sai dai ta rushe da kuka. Mami ta yi tambayar duniya amma amsa ɗaya take ba ta, wato abu abin da yake damunta. Da abin ya damu Mami ta samu Papa ta sanar da shi, hankali Papa ba ƙaramin tashi ya yi ba. Domin Rawiya da 'yar uwarta su biyu kaɗai ya mallaka, kuma yana matuƙar ƙaunarsu kamar tsoka ɗaya a miya. Dalilin haka ya sa bayan sun gama tattaunawa da Mami ya saci jiki ya shiga ɗakinsa, sannan ya wuce wurin Shugaba domin ya ba shi sani a game da matsalar da Rawiya take ciki.


 "Yarka Rawiya babu wata matsala da take damunta, wannan baƙon yanayin da ke tattare da ita rashin sabo da ƙungiya." 

 Shugaba ya furta yana kallon Papa, a fili ya sauke ajiyar zuciya yana shirin yin godiya Shugaba ya katse shi.


 "Sai dai har kawo yanzu, ruhin 'yarka bai karɓi ƙungiya yadda ya kamata ba. A don haka nake shawartarka da ka nemi jini ka zubar mata domin, sannan har kawo yanzu ba ka wanzar da tukwicin ƙungiya a kan samun matsayin da ka yi ba." 

 Shiru Papa ya yi yana nazari, haka kawai ya ji a wannan karon zuciyarsa babu daɗi.


 "Shugaba kenan dole sai na bada jini? Ina fatan jinin ba daga cikin zuri'ata za a zubar da shi ba?" 


 "Ba kisa za ka yi ba Kabiru!" 


 Jin haka ya sa Papa ya sauke ajiyar zuciya a fili, Shugaba ya ci gaba da cewa.

 "Tsaface shi ko ita za ka yi! Ina nufin Madogara za ta ba ka maganin da za ka shafa a al'aurarka, za ka nemi namiji ta baya ka yi mu'amala da shi. Idan kuma mace ce ita ma mu'amala za ka yi da ita amma ta gaba, domin ana saka ran ta zame maka tamkar taki a gona. Saboda killace ta za ka yi idan har ka yi dace ta samu rabo da kai, to ƙungiya za ta mori jinin ɗan cikinta kuma kai ma haka. Akwai ragowar bayanan da Madogara za ta yi maka su ba ni ba, don a yanzu haka Patrick da kuka samu matsayi tare ya gama tsaface karuwarsa har ya samu rabo da ita. Shi kuma Sani wani matashi ya samu, zancen da nake yi maka bayansa har ya fara fitar da tutsa, ɗazu ya gama sanar da Madogara tarin alkairan da ya fara samu." 

 Shiru Papa ya yi tamkar ruwa ya cinye shi, ya haɗiyi yawu cikin damuwa ya ce.


 "Zan yi bakin ƙoƙarina don ganin na cika umarnin ƙungiya." 

 Shugaba da Papa sun jima suna tattaunawa sannan ya yi masa sallama, sai dai duka tattaunawar ta su ta tafi a kan ƙara wa Papa ƙwarin gwiwa cikin rashin imani.


 Koda Papa ya koma gida sukuku ya fara jin sa kamar marar lafiya, shawarar da ta zo zuciyarsa yake neman zille mata a kan dole ya tsaya mata.


  "Nafi!" 

Ya furta a fili yana kai kawo a cikin ɗakin.

 "Da ke zan gudanar da aikina, idan har ba na fatan asirina ya tonu, tun da babu yadda za a yi na samu mace a daren nan." 

 Kai tsaye ɓoyayyen ɗakinsa ya shiga ya ɗauko wani baƙin garin magani mai haɗe da jini ban da wari babu abin da yake yi. Can falonsa na ƙasa ya kai ya adana, don ya ci alwashin gari ba zai waye ba sai ya yi amfani da Nafi.


Tsakar Dare

   Tun farkon dare Papa ya lura Mami na son yin mu'amala da shi, don haka ya nuna mata ba shi da lafiya, ba don komai ba. Sai don sabuwar matsalar da yake fuskanta ta rashin kuzari, sakamakon a kullum ƙarfinsa sake yin ƙasa yake yi. Hakan ne ya sa Mami ta yi masa sannu, sannan ta yi kwanciyarta babu jimawa bacci ya yi awon gaba da ita.

 Papa yana ankare da Mami ta yi bacci ya lalaɓa saɗaf-saɗaf, kamar sabon munafiki ya fice daga ɗakin. Ta windon baya ya zagaya ɗakin da Nafi take, ta cikin window ya zuge ya hura mata wani garin magani sannan ya koma ta koma ya tura ƙofar ɗakin ya shiga.


 Sai da Papa ya rufe ɗakin sosai sannan ya tuɓe kayansa ya mulke jikinsa da sihirtaccan maganin, da yake Nafi ba ta da girma da hannu ɗaya ya birkito ta ya yana zuwa ƙasanta ya ga fashin sallar da take yi. Kamar zai ƙyale ta sai kuma ya tuna wani abu, don haka ya fara ƙoƙarin kusantarta. Kasancewar Nafi cikakkiyar budurwa ya sa Papa ya jima sannan ya biya buƙatarsa, gefe ya koma yana kallonta yana jin wani baƙon yanayi a game da ita. Ya yi matuƙar mamaki, don bai taɓa tsammanin zai samu yadda yake so daga wurinta ba har ya manta da saduwar tsafi ya zo yi ya ɓige da nazari a kanta. 

 Sai da Papa ya gyara komai sannan ya fice daga ɗakin, ya faɗa toilet ɗin falonsa na ƙasa ya yi wanka.


 Nafi tana kwance ta hangi wani garsamemen baƙin kumurcin maciji ya shigo cikin ɗakinta, duk yadda ta yi da son guduwa domin ceton ranta sai ta ji tamkar an liƙe ta da ƙasa. Tana ji tana gani macijin ya saɗaɗa ta tsakankanin ƙafafuwanta ya shiga cikin al'aurarta, wani irin zafi da zugi take ji a cikin jikinta.


 A firgici Nafi ta farka daga mafarkin da take yu bayan wani lokaci ta haɗa gumi sosai, zafin da ta ji a ƙasanta ya sa ta yi yunƙurin miƙewa a hankali. Cikin galabaita ta fara dafa bango ta shiga banɗaki, har lokacin mamakin jin zafin jikinta da kuma canjin da ta gani a jikinta take. Duk da ta san tana fashin sallah, amma ba ta taɓa jin azaba irin ta wannan lokacin ba.


        ***

Shiru ne ya ratsa na 'yan sakanni a cikin falon, Yarima Ramadan zaune yake a falon mahaifiyarsa shi da ragowar 'yan uwansa. Fulani Kubra sai da ta kalle su ɗaya bayan ɗaya sannan ya dire a kan Yarima ta ɗora da cewa.


 "Na tara ku a nan ne domin yin wata magana, duk da kai Yarima ka san da ita. Amma 'yan uwanka ba su san da ita ba, ina son ku saurari jawabina sosai." Yarima ya jinjina kai cikin girmamawa.


 "Yau kwana biyu kenan da kakanku ya zartar da hukunci, umarni ne ya ba wa mahaifinku da kada a naɗa Yarima a matsayin sarkin garin nan." A razane su Jannat da Faruk suka ɗago, Fulani Kubra ta sauke ajiyar zuciya cikin damuwa ta ɗora da cewa.

 "Sai dai har kawo yanzu bai zartar da sarkin da yake muradin a ɗora ba. Yarima! Duk da tun kana ƙarami na lura mulki ba ya gabanka, amma na san ko yaya dole zaciyarka za ta sosu. Ina fatan ba za ka buɗa wa maƙiyanka hanyar da za su samu damar yin dariya ba, duk da ko ya ka yi musu ba za ka tsira ba. Ba na son koda wasa ka nuna ɓacin ranka a kan wannan maganar, ko ka ƙullaci kakanka da wani tunani. Ina fatan hakan ya zama mafi alkairi a gare ka da mu ba ki ɗaya." Mahaifiyar Yarima Ramadan tana gama magana jiki a sanyaye suka amsa da Amin.

 

 "Allah Ya taimake ki idan har ni ne ba za ka taɓa jin wata ɓaraka daga gare ni ba, ban taɓa kawowa watarana zan zama sarkin garin nan ba duba da halin da nake ciki. Allah Ya zaɓa mana abin da ya fi zama alheri." 


 Yarima ya jima shi da mahaifiyarsa da 'yan uwansa suna tattaunawa, daga ƙarshe ta gargaɗi kunnuwansu da ko kaɗan kada su fitar da wannan maganar.


 Tun bayan da su Fulani Karime suka fito daga sashen Takawa wani irin farinciki ya lulluɓe ta, tun da ta zo duniya za ta iya lissafa abubuwan da suka daɗaɗa ranta. To da a ciki za ta iya saka wannan ranar a matsayin rana mai muhimmanci a wurinta, dalilin haka ya sa ta tara duka 'y'a'yanta suka fara tattauna maganar hana Yarima Ramadan mulki. A cikin zuciyarta tana sake ayyana ƙudurinta a kan iyalan Fulani Kubra, domin duk cikin mata da 'ya'yan Takawa babu waɗanda take jin tsana da haushi kamar su musamman ma Yarima.


 Da daddare


 Yarima yana kwance a ɗakinsa dare har ya fara yi kimanin ƙarfe ɗaya saura na dare ya ji wayarsa tana ƙara. Da hannu ya laluba ya ɗauka, yana karawa a kunne ya ji muryar Kakansa tsohon Sarki Kamalu.


 "Tsoho mai ran ƙarfe kai ne da daren nan?" 

Yarima ya furta yana tashi zaune.

"Ni ne Ramadana, don Allah ka zo yanzu ina son ganinka." 

 Ramadan ya yi mamaki a ransa, amma a fili ya amsa masa sannan ya tashi ya janyo jallabiyyarsa ya saka. Yana fitowa harabar sashensa ya ji kamar motsin an shiga ɗakinsa, yana shirin yin magana ya ji Bawa Sallau ya ce.


 "Allah Ya taimake Ya ƙarama maka lafiya, ina za ka je da daren nan? Amma a gafarce ni ranka shi daɗe." 

 Kamar Yarima zai faɗa masa wurin da za shi, sai kuma ya tuna wataƙila ko tattaunawar sirri kakan nasa yake son yi da shi don haka ma bai neme shi ido yana ganin ido ba.


 "Yanzu zan dawo!" 

 Yarima ya furta yana yin gaba, shiru gidan yake sai kukan tsintsaye da yake tashi. A haka har ya ƙarasa sashen Sarki Kamalu, ƙofar sashen a buɗe ya same ta don haka ya tura ƙofar kai tsaye ya wuce cikin falon tsohon Sarki Kamalu bakinsa ɗauke da sallama.

 Shiru ya ji sai can ƙasa-ƙasa yake jin numfarfashi da gurnani a uwar ɗakinsa, da sauri Ramadan ya shiga yana kiran sunansa. Daga saman gado ya ji muryar Sarki Kamalu a can ƙasa yana faɗin.

 

 "Ka... tafi... ka... koma.... yarima..."

 Da hannu Yarima ya fara laluba saman gadon, nan take ya ji ya tsoma hannunsa caɓal a cikin jinin da ke ƙirjin tsohon Sarki. Hankali a tashe cikin ƙaraji ya ce.


 "Ranka shi daɗe, waye ya yi maka haka?"


 Daga can waje ya ji yo ihun Dogarawa, suna faɗin.

 "Ka tabbata shi ne dai?"


 Dogari Isa da jini ke fita daga gefen cikinsa ya ce. 

 "Wallahi Yarima ne ya kashe shi, na tabbata ba gizo idanuna suke yi mini ba." 

 A daidai lokacin suka shiga cikin ɗakin suka samu Ramadan tsaye a kan Sarki Kamalu, hannunwansa kace-kace da jini ga wuƙar da aka caccaka masa a hannun Yarima na hagu.



***

Ummou Aslam Bint Adam🌚