8
by @ameeraadam
*SHU'UMAR MASARAUTA*
*BOOK 2*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
(_Home of qualities and trusted writers of the nation_)
Tsokaci: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a wata kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
SHAFI NA TAKWAS
Kallo ɗaya Shugaba ya yi masa ya ɗauke kansa gefe rai a ɓace, Papa ya sha jinin jikinsa gabansa yana faɗuwa. Yana shirin yin magana Shugaba ya katse shi.
"Ya aka yi ka kawo mini ziyarar bazata, bayan ka san ba ya daga cikin ikon mambobin ƙungiya?"
Cikin matsananciyar damuwa Papa ya ce.
"Shugaba ka yi mini afuwa, wallahi ina cikin tashin hankali. Dalilin da ya sa na zo ban nemi izininka ba."
"Me yake tafe da kai?"
Shugaba ya wurga masa tambaya a daƙile.
"Tun ranar da na kusanci yarinyar gidana na gagara kama kaina a kanta, babban tashin hankalina yanzu ba na iya kataɓus a wurin iyalina. Ka taimaka mini Shugaba, saboda na mayar da yarinyar nan tamkar iyalina. Duk yadda na kai ga son yin yaƙi da zuciya lamarin ya gagara."
Da gama jin kalaman Papa sai Shugaba ya gyara zama har lokacin fuskarsa a turɓune take, ya ce.
"Kabiru ka riga da ka tafi kenan! Ina nufin a wurin iyalinka har abada ba za ka sake kusantarta ba. Ka mayar da hankali a kan 'yar aikinka domin morar arziki mara yankewa kafin yarinyar ta fara ruɓewa."
A razane Papa ya ɗago ya ce.
"Ruɓewa Shugaba?"
Kai kawai Shugaba ya gyaɗa masa ya ci gaba da cewa. "Kamar yadda na faɗa, ka ci gaba da morarta kafin ta fara ruɓewa. Ina nufin gubar da ka saka mata, sannu a hankali za ta fara ruɓar da ita kamar yadda lemon fata yake ruɓewa."
Papa zai sake magana Shugaba ya ɗaga masa hannu tare da sallamarsa.
Fulani Kubra ta jima tana lallashin Yarima, suna cikin magana Jami'an tsaro suka mayar da shi ciki. Fulani Kubra ta juya ta fice zuciyarta fes, tana fita ta kira layin Waziri bugu biyu ya ɗauka. A gurguje Fulani ta sanar da shi wirin da za su haɗu, bayan sun yi sallama ta shiga motarta ta nufi wani babban titi marar cukowar mutane. A motarsa Waziri ya je sai dai fuskarsa a yane take da baƙin ƙyalle, sai da ya fito daga motar ya ƙarasa ta saitin windon motarta. Ya saki murmushi sannan ya ce.
"Tauraruwa mai wutsiya, ganinki bai cika alkairi ba."
Fulani Kubra ta juya idanu tana cije baki ta ce, "Ai ni da kai duka taron kwaram da Hama ne." Waziri ya yi murmushi ya ce.
"Yanzu ya ake ciki? Wanne dalilin ne ya sa kike nema na?"
Ƙura wa titi idanu ta yi tana nazari na ɗan lokaci sannan ta ce.
"A idon duniya ni mahaifyar Yarima ce, wacce take jin ɗaci da turirin da kowacce irin uwa za ta ji a kan ɗanta wanda take da yaƙinin sharri aka yi masa. Amma a baɗini na fi dafin kunama zafi da raɗaɗi a kan sabon gyanbo. Waziri ina gudun kada binciki ya yi zurfi a gano wani abu game da kisan marigayi, Mubarak abokin yarima ka san babban lauya ne, kuma yaron yana da kwanya fiye da tunaninka, sannan kuma shi ne ya tsaya masa."
Waziri ya ɗago kansa haɗe da sakin tsaki ya ce.
"Yanzu a kan wannan kika nemi mu haɗu? Shin kina tantama da shakku a kan ƙullin da na ƙulla masa ne? Yaushe shekara nawa da ɓatan mahaifiyarsa?"
"Sama da shekara ashirin da biyar."
Fulani Kubra ta furta.
"Idan har za ki ba ni aiki kuma ki dinga wasu-wasi zan zame hannuna a ciki. Duk wata turka-turka da muka ƙulla a shekarun baya, babu wacce ta taɓa kuncewa sai wannan, na riga da na gama da Yarina. Na rantse miki da girman Allah matuƙar da hujjoji za a yi amfani babu lauyan da ya isa ya wanke shi."
Sai a lokacin Fulani Kubra ta saki ajiyar zuciya ta ce.
"Abu na gaba dukiyar Takawa da ke adane a wurin Yarima!"
Ɗan jima Waziri ya yi sannan ya ce.
"Wannan kam sai na yi nazari a kanta, kada mu yi gaggawa al'amarin ya kwaɓe mana." Jinjina kai Fulani ta yi sannan suka ci gaba da tattauna yadda za su ɗaure duk wata ɓaraka da za ta tona asirinsu.
***
Bayan Umaima ta koma kogon Bamaguje bin sa ta dinga yi da wani irin kallon cike da tsantsar tsana, haka kawai Bamaguje ya sha jinin jikinsa don haka ya ce mata.
"Shin ko akwai abin da yake dumunki ne Umaima?"
Umaima ta taɓe baki ta ce, "Kawai yau na tashi da kewar 'ya'yana ne musamman ma Basiru."
A hargitse Bamaguje ya dube ta gabansa na faɗuwa, nan take ta karanci yanayinsa ta kuma gasgata duk wani jawabi da Boka Jassu ya yi mata.
"Basirun da yake yunƙurin halaka ki Umaima? Me ya sa ba za ki shafe babinsa daga cikin rayuwarki ba?"
Bamaguje ya yi magana murya na rawa.
"Dalilin da ya hana ba ka shafe ni a doron ƙasa ba, shi ne dai ya sa na gagara mantawa da gudan jinina."
Umaima ta miƙe tsaye cikin sigar cin alwashi ta cigaba.
"Na rantse da kaifin tsafin da na samu horo a kansa, zan fara bincikar halin da yake ciki ko babu komai na san watarana shi zai gaji buzuna saɓanin ahalina da ke Masarautar Huddam."
Kamar sakarai haka Bamaguje ya saki baki yana bin ta da kallo, ya haɗiyi yawu muƙut har lokacin ƙirjinsa bai daina bugawa. Cikin wayancewa ya tashi da sauri ya cukwikwiyo ta yana faɗin.
"Ni kuma matuƙar ina numfashi, ba zan lamumce ki dawo da Basiru cikin rayuwarki har ya halaka mini ke ba." Umaima ta saki murmushin takaici kai tsaye ta ce.
"Idan kuma ba ka numfashi fa?"
Bamaguje ya yi shiru cikin sanyin jiki ya rasa abin da yake yi masa daɗi, ganin bai tanka mata ba ya sa ta faɗa wani rami wanda take gudanar da tsaface-tsafacenta. Abin duniya goma da ashirin ya mamaye Bamaguje, don haka ya yanke shawarar zuwa ya tunkari Boka Jassu domin ya sake ba shi mafita. Saboda bai taɓa tsammanin a kwana kusa Umaima za ta tuno da Basiru ba.
Sai da Boka Jassu ya gama jin jawabinsa a ransa ya ce. 'Bamaguje kenan! A tsamaninka zan yafe cin kashin da ka yi mini a baya ne, ai na faɗa maka duk rintsi duk daren daɗewa Boka Jassu ba mai yafiya ba ne.'
Amma a fili sai ya sauya fuska cikin damuwa ya ce. "Ya zama wajibi na sake nannaɗe zuciyar Umaima a game da yaron nan Bamaguje, kuma wannan mai sauƙi ne a gare ni. Abu ɗaya nake so daga gare ka wato faratan yatsun ƙafarka." Da sauri Bamaguje ya ɗago ya dube shi, don haka kawai ya ji hankalinsa bai kwanta masa da wannan aikin ba. Amma da ya tuna matsayin Boka Jassu a wurinsa sai ya ce. "Idan har wannan ne ba ka da matsala da ni babban boka, matuƙar za a nesanta Umaima da wancan hatsabibin yaron."
Boka Jassu ya saki murmushin cin galaba, Bamaguje ya saka wata tsafaffiyar aska ya yanko zaƙwa-zaƙwan faratansa ya miƙa masa. Boka Jassu yana karɓa ya juya su a hannunsa yana murmushi, ya kafe Bamaguje da kallo har sai da ya tsargu. Ganin sauyin Bamaguje ya sa Boka Jassu ya wayance da cewar.
"Za ka ji saƙo daga gare ni Bamaguje, idan kana da wata buƙatar bayan wannan ka sanar da ni domin ni mai share maka hawaye ne." Jiki a sanyaye Bamaguje ya ce masa babu sannan ya yi masa ban kwana.
Furucin da Jadda ta gama faɗa ne ya sa duka suka zuba mata idanu cikin tsananin mamaki, Galadima ya sauke ajiyar zuciya ya ce.
"Allah Ya taimake ki kada soyayyar da kike yi wa Yarima ta sa ki gagara gane gaskiya..."
"Duk soyayyar da zan yi wa Yarima ba za ta kai rabin ta Takawa ba, sai dai har yanzu ina ji a jikina Yarima ba shi ya kashe Takawa ba."
Jadda ta katse Galadima.
Cikin ƙunan rai Wambai ya ce, "Ranki shi daɗe kowa ya ga Yarima a kan gawar Takawa wacce kariya za ki ba shi? Duk abin da aka ce mutum ya aikata saboda mulki, wallahi ba zan musa ba. Takawa fa da bakinsa ya taɓa ba mu labarin shi fa fitar da shi aka yi daga masarautar ma bakiɗaya, kuma duk sanadin mulki. Ga halin da aka saka ɗan'uwansa, tsawon shekara sama da sittin Baba Abubakar yana fama."
Shiru Jadda ta yi, Sarki Abdallah sai a lokacin ya ɗago zuciyarsa na zafi ya ce.
"Idan duka mun yarda Yarima ba shi ya yi kisan ba shin waye ranki shi daɗe? Wacce hujja za mu ɗaga mu nunawa duniya da za ta wanke shi? Yarima ya cuce mu, ya shafa mana baƙin fantin da har zuri'armu ta shuɗe ba zai taɓa gogewa ba. Ace wai ɗan cikinmu ne ya hallaka mahaifinmu."
Wani abu ya tokare maƙoshin Sarki Abdallah haɗe da yin shiru saboda takaici.
"Atoh magana ɗaya ce, jinin mahaifinmu ba zai tafi a banza ba. Wanda ya kashe a kashe shi wannan shi ne adalci."
Wambai ya furta yana yin hanyar waje.
Tun ranar da Marigayi sarki Kamalu ya rasu sai da ƙyar ake lallaɓa Baba Abubakar ya ci abinci, saboda wunin ranar cewa ya yi ba zai ci abinci ba sai da shi. Da ƙyar aka yi masa dabara ya ci amma washegari fir ƙin cin abinci ya yi, hakan ba ƙaramin ɗaga hankalin iyalan gidan ya yi ba suka yi ta koke-koke yana bin su da kallo.
Idan aka zubo masa abinci sai da ya yi ta kiran ɗan'uwansa cikin gwaranci yana kuka, hakan ya sa lokaci ɗaya ya yi wata irin rama har ya kwanta rashin lafiya. Allurar baccin da ake yi masa bayan likita ya duba shi, ita ta rage masa damuwar da yake ciki. Bayan ya warke cin abincinsa ya ragu sosai, don da ya fara ci idan ya kira sunan ɗan'uwansa sau ɗaya zuwa biyu sai ya tashi daga kan abincin.
A haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har aka shafe kwana bakwai cif da rasuwa, mutanen da suka zo gaisuwa duka suka watse ya rage sai iyalan gidan. A ranar da ya cika kwana goma da rasuwa a ranar ne ya kama ranar da za a fara sauraron ƙarar Yarima, manyan lauyoyi biyu Sarki Abdallah ya ɗauka domin kare ɓangaren masu ƙara. Daga ɓangaren Yarima kuwa babu wanda ya ɗaukar masa lauya, domin ranar da aka yi sadakar bakwai ya tara kafatanin iyalinsa, ya tabbatar musu da duk wanda ya ɗaukar wa Yarima lauya shi da shi har abada. Idan mace ce daga ranar ya gama zaman aure da ita idan kuma 'ya'ya ne daga ranar ya tsame su daga cikin 'ya'yansa. Wannan hukuncin ba ƙaramin daɗi ya yi wa Fulani ba, domin rashin binciken shi ne mafi alkairi a wurinsu. Amma a fili sai kawai ta rushe da kuka, har sai da Takawa ya dakatar da ita.
Kotu
Kotun ta cika maƙil da mutane kasancewar mutane da dama suna bibiyar abin da yake faruwa. Motar gidan yari ce ta faka a cikin harabar kotun, jami'an tsaro suka riƙo Yarima da ke ɗaure da ankwa a hannuwa. Zuciyarsa ba ƙaramin zafi take yi ba, yana bin mutanen wurin da kallon mamakin halin da ya tsinci kansa a ciki. 'Yan jarida na gidajen radio da television ne suka ƙarasa wurinsu da sauri. Ɗaya daga cikinsu ya ce.
"Yallaɓai ga shi dai yau ce rana ta farko da za a fara sauraron ƙarar Yarima, wanda ake zargi da kisan kakansa. Ko akwai wani ɗan bayani da za ka yi wa masu sauraro?"
Ba su tanka masa ba, sai ma gegerewa da suka yi a gaggauce suka shiga da shi ciki.
Tsirarin mutana aka bari suka shiga cikin kotun ciki har da 'yan uwan mahaifinsa da mahaifiyarsa, suna haɗa ido da mahaifinsa ya ga ya ɗauke kai gefe. Ya dubi 'yan uwan mahaifinsa da suke bin sa da kallon tsana. Fuskar mahaifiyarsa ya hango ta yi jigum cikin damuwa da ragowar 'yan'uwansa.
"A yau biyar ga watan Nuwanba, shekara da dubu biyu da goma sha huɗu (5/11/2014) za mu fara sauraron ƙarar da Mai martaba tare da 'yan'uwansa suka shigar, a kan zargin kisan kai da suke yi wa Yarima Ramadan Abdallah." Magatakarda ya yi wa Alƙaliyar bayani tare da miƙa mata file ɗin. Alƙaliyar ta karɓa tana duba file ɗin cikin ƙwarewar aiki. Sannan ta dube su tana cewa.
"Shin duka lauyoyin ɓangarorin sun hallara ne, idan suna kusa su gabatar da kansu."
Lauyan Sarki Abdallah ya miƙe yana gyara zaman rigarsa ya ce.
"Sunana Shu'aibu Nasir, lauya mai zaman kansa mai muƙamin San! Ɗaya daga cikin lauyan masu ƙara, a tare da ni akwai abokiyar aikina."
Lauya Shu'aibu ya koma ya zauna ɗayar lauyar ta tashi.
"Sunana Barister Fahima Muhammad, ɗaya daga cikin lauyar masu ƙara."
Barister Fahima tana gama magana ta zauna, jiki a sanyaye Mubarak ya miƙe ya ce.
"Sunana Barister Mubarak Harun, ni ne lauyan wanda ake ƙara."
Lokaci ɗaya hayaniya ta fara tashi sama-sama a cikin kotun, har sai da alƙaliyar ta bubbuga teburin gabanta. Sannan ta dubi Yarima ta ce, "Muna buƙatar sanin sunanka."
"Asaalamu alaimum, sunana Ramadan Abdallah Kamal."
Yarima ya furta kansa a ƙasa cike da kunyar mahaifinsa da 'yanuwansa.
"Malam Ramadan ka ji ƙunshin tuhumar da ake yi maka na kisan marigayi Sarki Kamalu, ana zarginka da kisan saboda ya ce ba za ka gaji buzun mahaifinka ba. Shin me za ka ce game da haka?"
Idanun duka mutanen wurin suka yi kan Yarima, wasu na bin sa da kallon tausayi suna yi masa fatan alheri. Ya yin da wasu suke tsine masa, da fatan yadda ya kashe kakansa shi ma a yi gaggawar yanke masa hukuncin kisa. Yarima ya sunkuyar da kai ƙasa ya ce.
"Ni na na kashe shi."
Malam Bala ya jima a kanta yana zuba mata ruwan addu'a, tare da tofa mata duk wata addu'a da ta zo bakinsa har ya samu yanayin da take ciki ya lafa. Ta ɗago da jajayen idanunta da suka rine kamar sabon borkono, cikin wata irin murya ta ce.
"Tun ba a kai da nisa ba ina mai ba ka shawara, babu ruwanka Malam!"
Ba Malam Bukar ba hatta Inna da ke tsaye a wurin cikin firgici da mamaki take bin ta da kallo. Kusan sama da shekara ashirin da huɗu suna tare, amma wannan ne karo na farko da suka fara jin sautin furuci daga bakinta.
"Ba zan zuba ido ku halakar da baiwar Allahr da ba ta ji ba, ba ta gani ba. Su waye a tare da ita?"
Malam Bukar ya furta cike da ɗokin jin amsar da za su ba shi, sai dai shiru ta yi ta sunkuyar da kanta ƙasa. Yana shirin sake yin magana ya ga ta yanke jiki ta faɗi gumi ya shiga karyo mata kamar wacce aka kwarawa ruwa. Dafe kansa ya yi cikin damuwa ya dubi Inna ya ce.
"Tabbas akwai al'amarin da ke tattare da Faɗima, amma koma mene ne na tabbata ba zai fi ƙarfin Ubangiji ba."
Inna ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Malam kana nufin ba ita ta yi maganar ba?"
Malam Bukar ya gyaɗa mata kai, Ba Faɗima ba ce. Hasali ma bayan shafar jinnu akwai matsafan da ke bibiyar rayuwarta, idan ba ki manta ba na taɓa faɗa miki da jimawa." Malam ya dafa kai cikin damuwa sannan ya cigaba.
"Idan Allah Ya kai mu gobe ni da Zayyan za mu shiga cikin daji, akwai magungunan da zan haɗo wa Alhajin nan ita ma sai na haɗo mata nata."
Jiki a sanyaye Inna ta amsa masa, ta bi Faɗima da ke kwance da kallon tausayi.
Washegari
Tun a daren ranar Malam Bukar ya sanar da Zayyan batun zuwansu cikin daji domin samo itatuwan magani da saiwoyi. Don haka asubar fari suna idar da sallah Malam Bukar ya rataya jakarsa, shi ma zayyan ya ɗauki na shi kayan aikin suka nausa cikin daji.
Tafiya suka yi mai nisan gaske sannan suka fara cin karo da itatuwan da suke buƙata, ganyan ƙaiƙayi da ganyen biyar rana ne ba su samu da yawa ba kasancewar rani ne itatuwa da dama sun bushe. Wata surƙuƙin hanya suka bi mai matuƙar duhun itatuwa, mafi yawan itacen wuraren na tsamiya da kuka ne. Kallon itatuwan kaɗai ya isa faɗar da gaban mutum, Malam Bukar yana shirin tsoma ƙafarsa Zayyan ya riƙo hannunsa ya ce.
"Malam an ya ma shiga cikin hanyar nan kuwa? Haka kawai nake jin kamar ba kowanne irin daji ba ne."
Malam Bukar ya yi murmushi ya ce, "Za mu shiga da ikon Allah Zayyan, mu shiga da addu'a In Shaa Allahu babu abin da zai faru da mu sai alkairi."
A lokacin Zayyan ya ji ƙwarin gwiwa da kalaman mahaifinsa, suka shiga ciki bakinsu ɗauke da addu'a, babu abin da yake ta shi sai kukan tsuntsaye da dabbobin ƙasa. Ba su yi tafiya mai nisa ba, suka hangi wata ƙatuwar kulɓa ta gifta ta gabansu, cikin ƙarfin hali Malam Bukar ya ɗaga takobin da ke hannunsa yana waige-waige ba tare da ya sake cin karo da komai ba. A can gefen wata ƙorama suka hangi itaciyar ƙaiƙayi suka tsinka da yawa, sannan suka sake nausawa suka tsinko ta biyar rana. Wata ƙorama suka hango da kainuwa a saman ruwanta, Malam Bukar ya tsaya a bakinta ya biya addu'o'in kariya sannan ya shiga bakin ƙoramar ya yaɗo kaɗan daga cikinta. Sannu a hankali suka juyo da zummar nufar hanyar tafiya kamar an ce su waiga ɓangaren damansu, a bakin murgujejiyar bishiyar tsamiya suka ci karo da wani narkeken farin maciji, jikinsa sai sheƙi yake kamar bayan silba. A kanannaɗe yake kamar gammo, sai dai daga saman kansa an ɗora masa wani ƙaton dutsen wuta. A saman dutsen kuma akwai waɗansu layi ƙananu baƙaƙe da farare, tare da wani ɗan ƙanƙanin ƙoƙon kan ƙwarangwal.
Daga Zayyan har Malam Bukar shiru suka yi suna bin sa da kallo, don ba wannan ne karo na farko da suke shiga miyagun daji ba, kuma ba wannan ne karo na farko da suka saba haɗuwa da iska ko abin al'ajabi a cikin dajika ba. Sai dai wannan ne abin al'ajabi na farko da girmama tunaninsu, Zayyan ya dubi Malam ya ce.
"Malam wannan kuwa iska ce?"
Shiru Malam ya yi yana nazari ya ce, "Haka jikina yake ba ni, amma ina ganin mu wuce kawai Zayyan."
Malam ya ƙarasa maganar yana yin gaba.
Shiru Zayyan ya yi yana nazari, haka kawai ya ji zuciyarsa tana raya masa ya tunkarin macijin ya taimaka masa. Ya sake kai idonsa saman dutsen da kayan tarkacen tsafin da suke kai, jikinsa ya sake ba shi ta yuwu wani aka yi wa sihiri kuma idan ya sauke dutsen da ke kan maciji, wanda aka yi wa asirin zai iya samun lafiya. Duba da irin ayyukan sihirin da suke karyawa da laƙaninnika kala-kala.
"Zayyan!"
Ya Malam ya furta a lokacin da ya tunkarin macijin. A hankali ya juyo, Malam ya ce.
"Zayyana ina jin tsoron kada ka taɓa macijin nan tun da ba mu san wanne iri ba ne!"
***
Ummou Aslam Bint Adam