HAJAR

{78..}

by @feenerhfeeche


Babu wani pleading word da Nurain bai yi amfani dashi ba wajen consoling Hajar amma taƙi shiru, daga ƙarshe ma juya masa baya tayi ta duƙunƙune da duvet ta cigaba da rusa kukanta, bayan jikinta da yake mata ciwo har zuciyarta ma zafi take, Nurain ya tashi ya shiga bathroom, har ya fito bata dena kukan ba, singlet da short nicker kawai ya saka, wurga towel din da yake tsane sumarsa yayi kan couch snn ya nufi gadon, gefenta ya zauna ya bude fuskarta da ta rufe da duvet, ta muskuta da shirin juya masa baya yayi saurin riƙeta, idonta a runtse yake gamm sai jan zuciya take tamkar zata shiɗe, ya kamo hannunta yace "Baby girl..", ta fincike hannunta sai kuma ta mirgina ta koma can ƙarshen gadon, lokaci guda ta sake rushewa da sabon kuka sbd azabar da taji da ta mirgina din, Nurain ya sauke ajiyar zuciya don yasan ba sauraronsa za tayi ba, amma still ya zagaya ta side din da ta koma ya durƙusa yana kallon fuskarta, ya kai hannu ya shafa lallausan gashinta da ya hargitse yace "Baby wife listen to me..", da sauri ta tankwaɓar da hannunsa daga kanta ta wani turo baki, har lokacin idonta a rufe yake, ya cije lower lip dinsa painlessly gami da sauke wani ƙayataccen murmushi mai sauti, lokaci guda ya kware duvet din daga jikinta, ta tsala wani uban ihu ta cure kanta waje guda, tini ya wuce bathroom da ita don ya tara warm water a tub kafin ya fito, yasan she need warm water don she is still tight, yana ganin ko nan da encounter dinsu na biyar ma saida sitz bath, Hajar ta sha azaba don ruwan na yau sai taji kamar na barkono ne, yana ajiyeta kan gado bayan sun fito daga bathroom ta bige hannunsa daga jikinta, haushinsa take ji na gasken gaske shiyasa ma bata so ya taɓata, murmushi yayi ya kalli hannun nasa da ta bige yace "Eh naji... thank you... you make my morning today Baby wife", ya rage murya yace "it is sweeter than day before yesterday's night..", pecking cheek dinta yyi ya tashi ya fita, sai a lokacin Hajar ta buɗe idonta, ta miƙe a hankali ta zauna a ɗofane don bazata iya zama da kyau ba, room dinta take son komawa, ta miƙe tsaye da kyar tana cije lips, walking slowly sai kace mai taka ƙaya ta nufi door ta fita, tana tafiyar tana hutawa a haka har ta kai kanta ɗakinta, ta zube kan gado hawaye masu zafi na sauko mata, Anya kwa zata iya barin lokacin da ta ƙidaye yaxo kafin ta wanzar da ƙudirinta, Eh sbd favor yake mata shiyasa ya rufe ido ya ɗanɗana mata wnn azabar, sbd favor yake mata shiyasa bai saurari magiya da raƙon da ta ringa masa ba, wato ya gama da salon ɗalle mata baki da gaya mata maganganu ynxu ya dawo azabtar da gangar jikinta kuma, wnn tunanin yasa hawaye suka kasa tsaya mata, idanunta har zugi suke gashi kuma sun ƙanƙance, tana ji aka buɗe ƙofa amma taƙi motsawa zafin da zuciyarta take ya ƙaru, walking majestically ya zauna gefenta yace "Baby girl here is your Coffee", banza ta masa ta wani haɗe gira, yace "the Coffee you like wnda kike shanye min fa.." da haka ya ɗagota, afujajan ta fixge jikinta tana jan shessheƙa tace "please leave me alone", ta koma ta kwanta, yayi slight smirk yace "Ohk then get some rest..", da haka ya miƙe ya fita da mug din coffeen, ɓangarensa ya wuce ya zauna palour yana shan Coffeen, time to time sai yayi blushing sai kace zautacce, ji yake kamar an cire masa wani burden da yake damunsa yana jin kansa sakayau ynxu, yana gama sha ya ajiye cup din ya shiga bedroom, wayarsa dake kan bedside ya ɗauka, missed calls ya gani from 2 people, na Ruqayyah wnda daman ya saba ganinsa don kullum saita kirasa sau goma ko sama da haka, sai kuma missed call din Dr Marwan, na Dr Marwan din yabi, wayar almost 5mins sukay da Dr Marwan kafin Nurain ya katse kiran yana sauke ajiyar zuciya, knn yau sai ya shiga hospital, ya dubi makeken wall clock dake tickling yaga ƙarfe takwas da rabi, ƙarfe tara ya fito cikin shirinsa tsaf da car key a hannunsa ya sauka downstairs, Nearby Eatery yaje ya siyo mata breakfast snn ya dawo, da ledar abincin da kuma wcca Mami ta basa jiya tace ya kawo mata ya shiga palour, direct room dinta ya buɗe ya shiga bayan ya haura sama, ido biyu ya tarar da ita saidai a kwance take, suna haɗa ido tayi saurin janye nata, ya ƙarasa kusa da gadon yana kallonta without blinking yace "how are you feeling now...?", ba tayi niyyar amsa masa ba amma tsoronsa da ya shigeta yasa tace "much better", da kyar ma tayi mgnar ta wani sha kunu, duk yana ankare da yanayinta yaga dai har ynxu fushi take dashi bata sauko ba, don dai sauri yake da sai ya sauko da ita snn zai fita, amma dai bari ya dawo tinda ba wani daɗewa zaiyi ba, yace "Good... gashi Mami tace a baki wnn", ta gyaɗa kai a hankali, yace "i bought your breakfast", nan ma ta gyaɗa kai, after a while ya sunkuyo yayi pecking forehead dinta ya juya ya fita, saida taji ƙarar rufe ƙofa snn ta buɗe idonta, ta kai hannu ta goge forehead dinta inda yayi pecking tana turo baki. Nurain na isa hospital ko office dinsa bai shiga ba ya wuce surgery room, bayan ya gama shirin surgery ya saka surgeon gown ya shiga surgery room din, patient din da zai yiwa aiki har ya zama ready, tinda ya shigo surgery room din Ruqayyah ke kallonsa ta wani haɗe gira, position dinta ta tsaya don yau Vital signs zata ringa dubawa, Nurse Amina kuma ta ringa miƙa instruments, Good 3hours surgeryn ya ɗauka kafin aka gama, tini Nurain yayi disposing hand gloves da nose mask ya fita, throughout the surgery tunanin Hajar da ya bari a gida kawai yake, Allah yaso ma surgeryn ba wanda ake buɗa ciki bane da zai iya barin wani small instrument din a cikin patient, Ruqayyah ta bisa da kallo ta gyaɗa kai, ita da Nurse Amina ne suka mayar da patient din ward, da sauri Ruqayyah ta fita daga ward din bayan ta gama checking Vitals din patient din after surgery, direct hanyar office dinsa ta ɗiba, tana isa bakin office din ta tarar da patients wajen su goma, ta zauna kan silver chair tana jiran ya gama attending patients din kafin ta shiga, wayarta ta ciro daga pocket din Scrub dinta ta shiga messages. Nurain dake zaune office dinsa yana duba patient ya kalli wayarsa da tayi haske, ignoring message din da ya shigo yyi ya cigaba da aikinsa, 1hour ya ɗauka kafin ya gama attending ma patients din, har lokacin kuma Ruqayyah na zaune tana jira, last patient na fitowa ta zura wayarta cikin pocket din Scrub ta shiga office din, ko kallon Haleema ba tayi ba ta wuce ciki, ta mayar da ƙofar ta rufe ta jingina da ita, kallonsa ta ringa yi bbu ko ƙiftawa kafin tace "Assalamu alaikum", bai ɗago kansa daga kallon monitor din laptop da yake ba yana imputing data ya amsa sallamar ƙasa ƙasa, after few seconds din da suka kusa jingine 1mins ta ƙarasa shigowa, kan chair dake gaban huge table din ta zauna, a lokacin ya gama shutting down laptop din don ya gama abinda zaiyi, ya miƙe tsaye yana jan rigarsa, Ruqayyah ta ɗaga kai ta kallesa da mamaki ba dai tace komai ba, taga ya ɗauki car key alamar dai tafiya zaiyi, tace "Dr..", ya ɗan kalleta yace "what's up..?", tace "baka ga message dina ba nace zanyi mgana da kai Please", ya girgiza kai yace "ban gani ba... mene ne akan patient ne or something else...?", tace "please we need to talk", yace "Ohk not now, i will give you time next week Monday.." da haka ya zagayo ya nufi door, tini Ruqayyah ta miƙe tabi bayansa tace "why..?, me yasa ba ynxu ba..?", Calmly ya juyo yace "because my wife is waiting for me.. i can't give you even 1sec from her time" da haka ya buɗe ƙofa ya fita ya barta tsaye nan a daskare, shin da gaske ne wai Dearest dinta yayi aure, na farko da ta bisa Eatery yace mata yayi aure wnda sam sam bata yarda ba, ynxu kuma gashi yace mata ai matarsa na jiransa kuma ba taga wasa a yanayinsa ba. Wajen ƙarfe ɗaya da rabi Nurain ya fito daga wani haɗaɗɗen wajen siyar da wayoyi da wata yellow transparent leather a hannunsa, motarsa ya shiga ya bar harabar wajen, after a ride of 15mins ya isa gida, parking motar yayi snn ya buɗe ya fito, ya amsa sannu da zuwan da mai gadi ya masa kafin ya wuce cikin gida, ya buɗe ƙofar palour ya shiga, Hajar da take ƙoƙarin saukowa daga stairs a hankali tayi saurin kallon ƙofar, ai kam sukay ido huɗu zuciyarta ta buga da wni irin speed, ba shiri ta juya ta koma room dinta ta shiga toilet ta saka lock, wani mugun tsoronsa take ji, bayanta yabi ya haura upstairs din shima, a buɗe yaga ƙofar ɗakinta ya shiga bai ganta ba, ya kalli door din bathroom yyi slight smirk don yasan nan ta shige ya juya ya fita, ɓangarensa ya wuce yayi refreshing kansa ya saka ƙananun kaya riga polo da sweat pant. haka nan Hajar ta ringa gudun Nurain sai kace mage da ɓera har dare yayi, ynxu kam ta dena guduwa bathroom room din nata take rufewa da key snn ta bar muƙullin a jiki, wajen ƙarfe takwas Nurain ya dawo daga mosque sallar isha'i, ya kalli ƙofar ɗakinta yayi slight smirk, kafin ya fita saida ya murɗa handle yaji a rufe, tinda yake da ita a gidan wnn shine first time da ta sakawa ɗakinta key, girgiza kai yayi ya zura both hands dinsa a pocket ya wuce part dinsa, inda ya ajiye spare keys din gidan ya nufa, da kyar ya lalubo na room dinta, da key din a hannunsa ya fito corridor, sau uku yayi attempting saka key din a ƙofar amma yaƙi shiga, sosai yayi realizing ai akwai wani key din a jiki shiyasa yaƙi shiga, ajiyar zuciya ya sauke ya fara knocking door din, tini Hajar dake zaune gefen gado ta miƙe zumbur ta ringa kallon ƙofar, ta haɗiyi wani yawu jikinta ya fara rawa don gani take kamar zai shigo ne, Nurain yayi knocking door din da ɗan ƙarfi yace "Hajar..", idonta kamar zai faɗo ta ringa murza fingers dinta, lokaci guda ta afka toilet ta rufe da keys tana turo baki, after 5mins Nurain ya bar wajen ya sauka downstairs, kitchen ya shiga yayi making coffee ya fito ya haura sama. washe gari da sassafe Hajar ta ringa jin yunwa, jiya ba wani abincin arxiƙi taci ba tin breakfast da ya kawo mata ne acikinta sai kuma plain Noodles da ta dafa, A ɗarare tayi unlocking ƙofa ta buɗe ta fita cikin sanɗa ta sauka downstairs, ynxu kam tana iya tafiya ba taji zafi ba cause sau biyu tana yin sitz bath yau da safe da kuma jiya da daddare, kitchen ta shiga zuciyarta na bugawa don a tsorace take gani take kamar zata gansa a nan, sharp sharp ta tafasa ruwan tea ta haɗa shayi mai kauri ta shanye abinta a kitchen din, bata so ta wuce da cup din room dinta don tasan idan ta koma ta rufe ƙofar kuma sai 12 Noon, tana gama sha ta fito zuciyarta wasai ta haura sama ta shiga ɗakinta, still tayi ta ringa kallon jikin ƙofar ganin bbu keys, sosai zuciyarta ta buga don taji scent dinsa a ɗakin, bata gama lissafin da take ba kawai aka turo ƙofar ta waje, saida zuciyarta ta koma stomach after their eye contact, da baya ta koma sai kuma ta juya a miliyan zata shiga toilet, tini ya fixgota tayi landing a ƙirjinsa yace "Ke... ni Masquerade ne da zaki ringa guduna..?", ta yarfe hannu sai kuma ta fashe masa da kuka tace "wayyo Allahna na shiga uku..", jikinta har ya fara karkarwa don da gaske ta tsorata dashi, ya zaunar da ita gefen gado to calm her down ya duƙa gabanta, ya kamo shaking hand dinta ya riƙe a tafukan nasa yace "look at me Baby wife", kaudar da kanta tayi taƙi ta kallesa duk da yacca ya ringa leƙa fuskarta yana so suyi ido huɗu, yace "Hajar..", ta ɗaure fuska samm taƙi ta kallesa, murmushin kan lips yayi yace "wai har ynxu fushi kike Baby wife, After tough punishment din da kike min, you left me yesterday all alone, i couldn't even sleep comfortably..", ita dai ba tace komai ba, yace "sorry bazan sake ba sai kin gama healing Baby girl, i promise...", fashewa tayi da kuka sosai, wani irin sai tayi healing kuma, shi da zaice ya dena gaba ɗaya sai yace sai tayi wani healing, ta fara ƙoƙarin fincike hannunta amma yaƙi sakinta, murmushi mai sauti yayi don ya gane kukan na mene, yasa palm dinsa ya share mata hawayen yace "i promise you this Baby wife", ledar da ya shigo da ita ya dauka ya dora mata kan laps, ta ringa kallon ledar bbu ko ƙiftawa, yace "Open it", a hankali ta ciro kwalin tsaleliyar wayar daga cikin leda, tin daga kwalin ma kasan wayar me tsada ce, yace "you like it...?", ta gyaɗa kai a hankali sai kuma ta ɗago ta ɗan kallesa, saukar da kanta tayi tace "Thank you.." ta ɗanyi jimm kafin tace "Allah ya saka da Alkhairy", ya ringa kallonta yana jin wani abu mara misaltuwa na figarsa, zamm yarinya nan ta juye irin yacca yake mafarkin matarsa ta kasance, ba tin yau ya fara lura da hakan ba, ta ɗago kanta taga har lokacin kallonta yake, suna haɗa ido ta saukar da kanta, ya kamo hannunta yayi pecking for almost 10secs, a hankali ya ringa murza hannun nata yace "you need anything...?", da sauri ta gyaɗa kai, yace "tell me what is it..?", kanta a ƙasa tace "ina so naje gidanmu dan Allah", yayi ajiyar zuciya yace "Is that what you like..?", ta gyaɗa kai, yace "Ohk then insha Allah on Saturday sai nayi dropping dinki kiga Umma ko..?", ta ɗaga kai ta kallesa, ya sakar mata murmushin da tayi nadamar ɗagowa jin wani abu ya cakar mata zuciya, yace "yeah... Umma da ake kira daga anji wuya mna", turo baki tayi, ya ɗauke kwalin wayar daga laps dinta ya miƙe tsaye sai kuma ya riƙe hannunta ya ɗagota, rumgumeta yayi yana sauke ajiyar zuciya yace "missed you soo much yesterday..", a tare suka lumshe ido, ta kwantar da kanta sosai a ƙirjinsa. Sosai Nurain yayi keeping promise dinsa don bai sake taɓata ba, amma kuma bai sake barin sun raba shimfiɗa ba don baya ma iya bacci sai yayi Cuddling abarsa, itama ƴar farkar tafi jin daɗin bacci a jikinsa, kamar yadda ta saba a da yanzu ma haka take zata dafa abinci ta ajiye masa nasa a warmers, sai dai yanxu ba da kansa yake zubawa ba sai ya kirata ta zuba masa, Abu ɗaya ne yake sukar zuciyarta daga ta tuna cewa favor ake mata, wnn abu sosai ya tsaya mata a rai, ranar Saturday kamar zata zuba ruwa a ƙasa tasha don murna yau zata je gida, kafin ƙarfe goma ta gama duk wani aiki da za tayi, tana komawa ɗakinta ta faɗa bathroom ta fesa wanka, kayan da bata taɓa sakawa ba ta saka cikin na fitar bikin Noor da aka ɗinka mata, ta saka ƙaramin hijab dinta wanda yake tsaya mata a guiwa da kuma Charger din sabuwar wayarta a ƙaramar hand bag da ta fitar, sosai tayi kyau kamar a saceta, ta kalli door jin an buɗe, bai shigo ba ya tsaya daga waje ya waro ido yace "Hey ina zaki da sassafen nan", ta marairaice murya tace "yau ne fa zanje gida", yace "Ohk Okay... Amma dai ba ynxu ba", ta langwaɓar da kai tace "toh Ni yaushe zan tafi ƙarfe goma fa ya wuce", Nurain yayi slight smirk yace "where is my breakfast... bring it to my room". haka nan Hajar ta shiga kitchen ta hada masa breakfast sharp sharp ta kai masa ɓangarensa, ita da ta shirya tin goma da wani abun amma basu bar gidan ba sai sha biyu, Alla Alla take taga sun shiga unguwarsu don yau ma sai taga kamar gudun da yake bai wadaceta ba, Saida ya tsaya wani super market yayi shopping snn suka cigaba da tafiya, wani sanyi ne ya ratsa Hajar lokacin da yayi parking a daidai lungun gidansu, da sauri ta fara ƙoƙarin buɗe motar sai ta jita a kullu, ta juya ta kallesa ba tace komai ba, ya ɗauki envelope din daya ajiye kan dashboard ya miƙa mata, ta girgiza kai tace "Akwai tin wnda ka bani ranar nan", bai saurareta ba ya janyo jakarta ya zuge zip ya saka mata ba tare da ya lura da abinda ke cikin jakar ba, yace "idan na dawo zan shigo na gaida Umma", ta gyaɗa kai a hankali, da haka ya buɗe motar ya sauka, itama sauka tayi taga ya buɗe back seat ya fara ciro shopping bags, yara uku ya biya yace su ɗaukar mata kayan, Hajar ta saki baki tana kallonsa don ba tayi zaton gidansu za a kai ba, saida Hajar ta ɓacewa ganinsa snn ya koma mota yabar unguwar. Nabilah dake bakin rariya tana wanke wanke ta dena abinda take tabi yaran da suka shigo da kaya da kallo, Maama da ta fito daga bayi knn itama kallon yaran tayi baki a sake, Umma na zuba ƙullu cikin gwangwanaye Sabrah na shafa mata manja suma suka dubi yaran, duk cikinsu aka rasa wnda zai yi mgana, walking gently Hajar ta shigo tare da yin sallama cikin murya mai sanyi, Umma dai tini ta ɗau muryar ƴarta ta, Sabrah ta micincina ido lokaci guda ta fasa ƙara tace "Addah.." sai kuma ta tashi da gudu taje ta rumgume Hajar, wani kukan farin ciki ne ya tahowa Hajar ta rumgume little sister dinta, Maama ta saki butar hannunta Nabilah kuma ta saki kwanon da take wankewa don sai ynxu suka gane Hajar, da farko sun sha wata balarabiyar ce tayi shigar hausawa, Maama ta dafe ƙirji murya a sama tace "wai Hajara ce", Hajar ko kallon inda take ba tayi ba ta wuce wajen Ummanta ta duƙa ta rungumeta, sai kuma ta fara hawayen farin ciki tace "Umma.. Ummanmu", Umma tayi murmushi tace "Hajara", Hajar na ɗago kai taga Sa'adatu da Maimuna sunyi cirko cirko a bakin ƙofa suna kallonta sai kace tsofaffin mayu sunji yunwa, Maimuna tayi wani baƙi fuska duk ƙuraje sai wata uwar rama da tayi gayau haƙora sun fito sai kace za tayi cixo, tini Umma ta rufe ƙullun alale taja ƴarta sukay ɗaki, gani kake yuuu Maama da ƴaƴanta suka bi Hajar da idanu, Sabrah ce ta ringa kwaso ledojin ta shigar dasu ɗaki, Hajar was more than happy da taga Ummanta, Umma taji daɗin ganin ƴarta ta data canza matuƙa, Hajar dai ta zama wata tauraruwa abar kallo a wajen Maama da ƴaƴanta, da ta fita yin alwala za tayi sallah har saida tayi tuntuɓe tsabar kallo, ita kam ko bi ta kansu ma ba tayi ba don bbu wnda ta kula, da yamma Baba ya shigo gida, Hajar na jin muryarsa ta ji wani mugun dadi, saida ya shiga ɗakinsa snn ta tashi ta fita ta tsaya bakin labule tayi sallama, da sauri Baba ya juya ya kalli labulen don ya gane muryar favorite din ƴar tasa, har ƙasa Hajar ta duƙa ta gaida mahaifinta wnda ya amsa mata gami ta saka mata albarka bayan ya dafa kanta, farin cikin da Hajar tayi a ranar bazai misaltu ba don rabonta da yin farin ciki kamar na yau har ta manta, bayan sallar magrib ne kiran Nurain ya shigo wayarta, dman contact biyu ne a wayar daga tasa wacca ma ko saving ba tayi ba sai na Umma, ita throughout the day ma bata bi takan wayar ba tana wajen Sabrah sai game take, basu wani jima suna wayar ba kawai ce mata yayi yana kan hanya zaizo ya ɗauketa, tace masa toh Allah ya kawosa lfy, after 15mins kam ya sake kira yace mata yaxo yana ƙofar gida, Hajar tayi wani murmushin gefen baki sai kuma ta saka veil dinta ta fita, bata wani jima ba ta dawo, Hajar ta duƙa gaban Umma wacca take zaune kan darduma tana jan carbi tace "Umma yace wai zaku gaisa", daga bakin ƙofar ɗakin Umma Hajar ta shimfiɗa darduma guda biyu, gashi kuma anyi sa'a yau an kyallaro wutar Nepa, Hajar ta fita soro bayan ta gama shimfiɗa darduman, tare suka shigo dashi ya zauna kan ɗaya daga cikin darduman, Umma ta fito suka gaisa kansa a ƙasa, da haka ya tashi ya nufi soro, Maama dai wuyanta kamar zai karye sbd leƙe daga ɗaki, lokaci guda ta koma gefen gado ta zauna sai kuma ta fashe da kukan baƙin ciki. Hajar ta gyara yafen mayafinta tayi hanyar soro, ta tsaya gami da tattaro courage don abinda za tayi sai da courage, ta ajiye numfashi a hankali, walking gently ta ƙarasa inda yake kanta a ƙasa, har ta isa kusa dashi kallonta yake, dukkansu shiru sukay bbu wnda yace komai, shi yayi breaking silence din da faɗin "shall we..?", ta jingina da bango speaking calmly tace "Thank you", ya tattare thick eyebrows dinsa yace "for what..?", ta kallesa a karo na farko tace "for everything... from the beginning till now that is the end", ya gyara tsayuwarsa yana kallonta da kyau, tace "A watanni huɗu da muka zauna tare nasan cewa na maka laifi dan Allah ka yafemin, i know i wronged you many times please forgive me.. however it seems i won't be able to do any of that now, bxn sake zama burden a kanka ba, ngode da favor din da kayimin na good 4months, nsan cewa Babana yamin aure amma ba auren Alfarma ba", Nurain ya tsuke piercing eyes dinsa yace "Hajar", ta haɗiyi wata ball da ta tsaya mata a throat tace "yess, kace zaka nunamin am your wife and you did that, still dai it won't change the fact that you are doing me a favor", kallonta yake bbu ko ƙiftawa, tace "ban san me yasa kake min favor ba ko don sbd ni ba choice dinka bace ko kuma sbd background dina ne i don't know, ngd da ka dawo dani inda ba favor ake min ba...", ta ɗan ja da baya ganin zai riƙo hannunta, ya ajiye numfashi yace "what are you saying Baby wife...?", da kyar tace "Nurain let me go, i will also let you go, from now on we won't own each other anything", tana gama faɗin haka ta juya ta shiga gida.....✍️