ALLON ƘADDARA

48

by @oumfatima33

✨✨✨✨✨✨✨✨  

 _*ALLON ƘADDARA*_

        _*By*_

   *_OUM FATIMA_* 

_*(Hakimar D. A. W. A)*_

✨✨✨✨✨✨✨✨ 


     _*DASHEN🌲ALLAH*_ 

_*WRITER'S📚ASSOCIATION*_


            _*TEAM*_

_*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*_





 *PAGE 48* 


_*بسم الله الر حمن الر حيم*_




***** A hankali kwanaki suka riƙa shuɗewa suna zama satika yayinda satika ke zama watanni zuwa shekara, sai gashi na cika shekara biyu a Gidan Hammah Jabeer. Babu abinda zance sai godiyar Allah a tsayin shekara biyu da nayi tare da shi mun gudanar da daddaɗar rayuwar farin cikin da bazan taɓa mantawa ba tare da Hammahnah da kuma ƴata da ta girma abinta, idan har nace muku bana son Hammah Jabeer to nayi ƙarya don kuwa bai barni ba sai da ya tabbatar da ya dasa tsaftatacciyar soyayyarsa a zuciyata da bazan taɓa iya barinsa ba.


Ni a karan kaina har mamaki nake yanda nake jinsa a zuciyata nake kishinsa abin har tsoro yake bani, a da in aka ce min zan so wani wanin ma Hamma Jabeer da kwata-kwata bama jituwa, zan so shi fiye da yanda naso Ya Nabeel kai tsaye zan ƙaryata. Kai ko a mafarki na gani sai nayi sadaka, amma sai gani a cikin soyayyah dumu-dumu, lallai babu abinda yafi ƙarfin Allah kuma ba yanda Allah baya lamarinsa sai dai muce Alhamdulillah a komai da ya tsara cikin rayuwarmu.



Anyi rikici sosai da dangin Aunty Kalisat akan riƙon Little sai da Hammah ya fito musu a mutum ya taka musu birki kafin suka haƙura, amma kuma sai suka koma yunƙurin lika masa Fa'iza ya aura. Ba wanda ya iya tunkararsa da zancen sai dai su dami Hajiya Mama da tace baza ta masa dole ba.


Hakan sai ya fara haifar da saɓanin a tsakaninsu, tattara su tayi ta ƙyale suke ta surutu da ƙananan magana ta zaɓi bare akan tata. Duk wannan abin wanda ake yi a kan nasa bai sani ba sabo da ba mai ƙwarin gwiwar iya yi a gabansa, don daya sani da tuni ya takawa abin birki sabo da zai iya ɓatawa da kowa a kan Mahaifiyarsa don bai haɗata da kowa ba.


Da suka ga ba nasara a wannan hanyar sai suka yi amfani da rashin haihuwar da Hanan bata yiba suka riƙa muzguna mata idan ta shiga cikin su ta hanyar mata gorin haihuwar da bata yi ba suna cewa wai ai dama irin tsiya ce don Uwarta ita kaɗai take da ko ta haifa mutuwa suke, don haka dole Jabeer ya auri irin haihuwa.


Abin na matuƙar damuna a rai domin kuwa ni kaina na fara tunanin ko bana haihuwa ne, gashi Allah ya jarabceni da son yara. Sai dai ko na damu in naga Little sai in ji sanyi a raina ko ba komai ina da ita, don haihuwarta ce kaiɗai ban yiba amma yanda nake jinta a raina soyayyar da nake mata ba kaɗan bace.


Ammy kanta jin shiru har yanzu ban samu ciki ba ga kuma ƙananan maganar dake yawo a dangin Hammah na wurin uwa akan bana haihuwa abin na damuta sai dai ta barwa Allah komai tana yi min addu'a ba dare ba rana.


Hammah kuwa duk sanda yaga na shiga damuwa akan hakan kwantar min da hankali yake akan duka ma yaushe aka yi auren da zan tada hankalina.


"Kar ki sake ki saka maganar mutane a ranki ta dame ki Sofyna, su mutane duk abinda zasu yi don hanaka kwanciyar hankali shi suke nema don haka ki manta ki maida hankali a kan abinda ya shafeki ba magan-ganun mutane ba kin ji ko". Wannan shine abinda yake faɗa min duk lokacin da yaga na shiga damuwa.


Ganin dai kamar ban sake ba sosai yanda yake so ya shirya mana tafiya zuwa Los Angeles muje mu ɗan huta daga nan kuma zamu wuce China zaiyi odar wasu kaya da Companynsa ke buƙata sai mu wuce umara.


Sosai nayi farin ciki da ya sanar da ni wanda hakan ya masa daɗi sosai domin ko kaɗan baya son ganina cikin damuwa, zuwa yanzu na gama tabbatar da irin soyayyar da Hamma Jabeer yake min duk da kuwa bai faɗa da bakinsa ba amma ayyukansa da irin tsananin kulawar da yake bani sun tabbatar min da hakan, wata soyayyar girmanta yafi ƙarfin baki ya iya bayyana ta.


Nayi tunananin da Little zamu tafi amma yace a'a Hajiya Mama za'a barwa, ban masa musu ba amma nasan zan yi kewar yarinyata sosai itama haka domin ba ƙaramar shaƙuwa ke a tsakaninmu ba.


Nan da sati ɗaya ne tafiyar don haka muka fara shirye-shirye tafiyar




🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂





A cikin shekara biyu da ta wuce Alhaji Bilal ya samu sauyi sosai a Gidansa ta ɓangaren Samha, domin kuwa dagewa tayi ta riƙa bashi duk irin kulawar data dace. Sannan ta jawo yaransa a jiki take kula dasu tamkar ita ta haifesu wannan yasa shaƙuwa a tsakaninsu da yaran suke sonta da mata kallon Uwa.


Sannan ta ɓangaren danginsa tana kyautata musu wannan yasa Mahaifiyarsa take ƙaunarta danginsa ma da suka fara taya Aliya kishi suka watsar suke zamansu lafiya cikin girmama juna. Yanzu haka tsohon ciki gareta haihuwa yau ko gobe.


Sosai suke zumuncinsu tsakanin ta da Hanan sabo da basu da ƙawayen da suka fi juna, duk wacce ke da matsala suna tattaunawa su bawa juna shawarar da zata taimake su. Tana daga cikin masu kwantar mata da hankali akan rashin samun rabon da bata yi ba, duk da a farko abin baya damuna abinda su Hajiya Asabe ke min ne yasa na fara damuwa har nasa abin a raina.



A ɓangaren Aliya kuma maimakon ta tsaya ta maida hankali ta gyara kusa kurenta ta fuskanci Mijinta su dai-daita a'a sai ma abin nata ya daɗa haukata zuwa matakin gaba, kwata-kwata yanzu babu girmamawa a tsakaninsu. Bata jin nauyin ta buɗe baki ta zagesa ta kirashi mugu munafuki ko a gaban yaransu ne.


Sau tari sai yayi yunƙurin ɗaukar mataki amma ya danne zuciyarsa ya haƙura ko don Iyayensu, sai dai yana zuwa wurin Samha zata yi duk yanda zata sa ya manta da damuwar da yake ciki.


A halin yanzu soyayyarta mai ƙarfi yake ji sabo da kyautata masa da take shida yaransa, shi yasa yake girmamata kuma baya wasa da bukatunta.




 *Aliya*


Duk irin yanda tayi don ganin tasa ya saki Matarsa abin ya gagara, taje tayiwa Hajiya Asma'u kuka da barazana ta ɗaga mata hankali ta kira Bilal tasa shi ya saketa.


Kai tsaye yace mata ba zai saki Matarsa ba idan zata zauna ta zauna idan bazata iya zama ba zata iya tafiya.


Wannan maganar ba ƙaramin rikici ta haifar ba domin kuwa kuka Hajiya Asma'u ta saka ta kira ƴa'ƴanta ta faɗa musu abinda yayi mata, haƙuri suka bata da ƙyar aka kashe maganar.


Aliya kuma Babanta ya mata ƙwaƙwƙwaran kashedi akan kar ta ƙara zuwa ta tadawa Mahaifiyarsu hankali idan kuma ba haka ba shi da kansa zai sa Bilal ya saketa tazo Gidan ta zauna.


Jin hakan yasa bata ƙara zuwa ba sabo da tana son Mijinta bazata iya rabuwa da shi ba, sai dai baza ta iya zama bautar Gida da yaraba da shi kanshi Mijin tunda ba baiwa bace kuma tana da nata ayyukan gaskiya.


Neman shawara ta fara gurin ƙawayenta wasu suka bata shawarar zuwa murin Malamai, wasu kuma makirci suka koya mata. Tace bata da lokancin ɓatawa a wurin Malamai sai dai zata gwada mataakircin .


Shima tana farawa baije ko ina ba sabo da ya san halinta kuma ita a karan kanta ba jure iya zaman Gidan take ba, don haka ta watsar ta koma yawon Kasuwancinta wanda abin yafi da ta barwa amarya ragamar kula da Miji da yaranta baki ɗaya sai baƙin kishin tsiya. 


(Wasu Matan tamkar rako Mata duniya suka yi, Allah ya kyauta).




♦️♦️♦️♦️♦️♦️♦️♦️




Komai na tafiyarmu ya kammala dama nice akayi wa passport da da sauran shiri, yau saura kwana biyu mu tashi don haka ya kaimu Gida muyi sallama da su.


A can muka yini cikin farin ciki tare da Ammyna data ƙara kwantar min da hankali ta bani shawarwari masu amfani, naje shashen Momy na gaisheta a amsa min ba yabo ba fallasa.


Ban zauna ba na shiga ko wane sashe muka gaisa a ƙarshe na yada zango a part ɗin Hajjo muka sha hira.


Da zamu tafi muka bar Little anan har da ɗan kuka na, itama kuka da tasa bazata zauna ba sai da aka lallameta sannan. Ta girma sosai tayi wayo duka shekararta uku amma ba abinda bata faɗa don Hammah yace muna dawowa zai sakata Makaranta.


Muna tafiya cikin Mota jikina a sanyayen da barinta da muka yi ya kalleni yace "Meke damun farin cikin Jabeer uhm?".


"Hammanah yarinyata!". Na faɗa ina kwaɓe fuska.


"Kiyi haƙuri kin ji, zamu dawo ki ɗauko abarki ko?". 

Kai na gyaɗa masa da haka muka ƙara sa Gida yana yi min hira....



Assalamu alaikum barkammu da wannan lokacin kuyi min afuwa jiya nace zan yi ban samu dama ba sakamakon jikin Fatima da ba daɗi. Na gode ƙwarai da addu'oinku Allah ya saka da alkairi.



 *Oum Fatima*