HURAYYAH (New edition) Chapter 4
HURAYYAH
New edition...
Chapter 4
Washegary sam Aliyu bai zauna ba yini yayi yana kai ziyara a garin na Gombe, Shi ne har masarautar Gombe gaida Mai martaba sarki,wanda yake matsayin aminin mahaifinsa kafin ya rasu.
Sai yamma liss misalin 4pm ya koma gida,kai tsaye part ɗinsa ya nufa yayi wanka tare da sauya kaya.Yana shirin fita zuwa sashin Hajiya Samha ta shigo,tun daga nesa da ta hango shigar da Aliyu yayi ya ɗauki hankalinta.Yana sanye ne cikin navy blue shirt da baƙin wando,ya yi kyau sosai tamkar wani saurayi mai shekaru ashirin da biyar.Wani irin sonsa ke sake fisgarta tana jin cewa tabbas ita ɗin mai sa'a ce data mallaki Aliyu amatsayin miji,da wannan tunanin ta ƙarisa zuwa garesa fuskarta ɗauke da murmushi.Shi ma murmushin ya maida mata yana faɗin, "Ma'aikata sai yanzu kike shigowa ƴan mata?"
Dariya tayi kaɗan kafin ta sanya kanta a kafaɗunsa tana faɗin, "Aliyu yau kuma nice na zama hakan?
Hannuwanta ya riƙo tare da kashe mata idanu ya ce,"Yes ko baki dubi shigar dake jikinki bane Samha,wanda yafi dacewa ace budurwace take yinsa ta fita ba matar aure ba,wai sai yaushe ne za ki ji maganata Samha?Na sha faɗa miki bani son irin wannan shigar da kike kina fita da ƙaramin mayafi,koda yake banda darajar da za ki ji maganata shiyasa."
Ya ƙare maganar yana sakin hannuwanta ya nufi ƙofar fita domin zuwa sashin Hajiya,kamar ta wuce abinta zuwa ɗakinta sai kuma ta bishi domin zuwa gaida Hajiyar wanda rabonta da shiga part ɗin zai kai kimanin sati biyu.
A zaune ta samesu tamkar Aliyu zai shige cikin jikin Hajiyar,sallamarta yasa Hajiya Maryama faɗaɗa murmushinta tana faɗin, "Samha ke ce, har an dawo aikin kenan?"
A daƙile Samha ta gaidata ba tare da tabi ta kan maganar Hajiyar ba,duk Aliyu na kula da yanayinta hakan kuma ya sosa ransa matuƙa.Shiru ne ya ratsa na wani lokaci kaɗan kafin Hajiya ta katse shirun ta hanyar faɗin, "Aliyu wai ya ake ciki ne akan maganar zuwa Dukku gobe? Naji baka sake cewa komi ba."
Aliyu a nutse ya kai dubansa kan Hajiyar kafin ya furta, "Maganar na nan Hajiya,nasa a kammala komi na tsaraba kamar yadda aka saba."
Miƙewa samha tayi tana faɗin, "Na barki lafiya Hajiya,Aliyu saika shigo." Daga haka ta fice abinta tana jin haushin wai har da Aliyu ne za a je wani Dukku.
Iya ce ta shigo cikin falon hannunta ɗauke da plate ɗin dambu wanda ta gama yima Hajiya sai qamshi ke tashi,ta dire plate ɗin a gabansu tana fadin "Hajiya ga Dambu ya sauka."
Wani irin daddaɗan qamshi ne ya bugi hancin Aliyu,take yaji yana son cin dambun,hakan ya sanya shi duban Iya yana fadin "to ai Iya nima sai a zubo min nawa dambun ko."
Murmushi Iya tayi tana faɗin "An gama ranka ya daɗe bari a zubo maka."
Hajiya Maryama sai tayi saurin faɗin, "Barshi Iya mu fara cin wannan in yaso saiki ƙaro daga baya." Kamar yadda ta ce ɗin hakan aka yi tare sukaci dambun da Aliyu,wanda keta faman santin daɗin da dambun yayi.Shi ya fara zare hannunsa daga plate ɗin alamun ya ƙoshi,ya bar Hajiya na cigaba dacin abinta.
Saida aka kirayi sallah sannan ya baro part ɗin zuwa masallaci,bayan an ida sallar ma saida ya saurari karatu har aka yi sallar Isha sannan ya shiga sashinsa.
A ƙoshe yake baya buƙatar sake cin wani abu mai nauyi sam,banda lemun coconut da potato balls babu abinda yake son ci.Hakan ya sanya shi ɗaga waya ya kira Samha domin ta samar masa,don ta kware a iya yinsa sosai.Sai dai sam bata damu da yi masaba inba an kai ruwa rana ba,tafi so komi ta bada umurni ai masa.
Bugu biyu wayar tayi ta ɗaga tana faɗin, "Darling ka shigo ne?Zuwana biyu banganka ba." Ta ƙare maganar tana wani narke murya.
"Samha kizo yanzu please!" Aliyu ya faɗi hakan tare da kashe wayarsa ya fara rage kayan jikinsa.
Ko mintuna biyar ba a rufa ba Samha ta shigo zuwa ɗakin nasa,kallonta yayi sama da ƙasa shigar data yi na taɓa zuciyarsa.Sanye take cikin mini skat da wata iriyar top mai hannun suphagetti ,wuyar rigar a buɗe take hakan ya saka albarkacin ƙirjinta suka fito sosai.
Kujerar da yake zaune ta isa ta zauna jikinsu na gugar juna,Aliyu sai yayi saurin janyota zuwa jikinsa gaba ɗaya ya fara kissing ƙirjinta tare da lumshe ido yana shaƙan qamshinta da ke rikita zuciyarsa.Murya can ƙasa ya kai bakinsa bisa kunninta yana fadin "Hey wifey u look so sexy." Samha sake lafewa tayi a jikinsa har saida ya gama abinda yake son yi da albarkatun ƙirjinta,a hankali ya sassauta riƙon da yai mata yana sanya ƙwayar idanunsa cikin nata.Cikin murya ƙasa-ƙasa yake faɗin, "Samha ina buƙatar cin potato balls da coconut juice please,ina fatan zan samu ba tare da an ɓata mini rai har abin ya fice daga kaina ba?"Ya kai ƙarshen kalamansa yana sake tsareta da manyan idanunsa.
Baki Samha ta buɗe tana faɗin,"Karka damu Darling,yanzu Samuel Ko Rebecca za su sarrafa su kawo."
"Look! Samha,dana ambaci son aimun kinji na kira sunan Samuel ko Rebecca ne?" Ya jefa mata tambayar yana sake shigar da idanunsa cikin nata tare da sake tamke fuska alamun sam bai son wani wargi.
Cikin matuƙar takaici Samha ta narke murya tana faɗin, "To amma Aliy...." Bai bary ta ƙarisa furta abinda take son faɗi ba yayi saurin katseta ta hanyar ɗaga mata hannu ya furta, "Kinga Samha,idan ba za ki yi min da kanki ba kina iya tafiya ki bani guri final." Yayi maganar cike da tsawa ransa a matuƙar ɓace.
Miƙewa tayi tsaye tana dubansa yadda yake aika mata wani matsiyacin kallo,ganin yadda ya ɗauki zafi sosai ya sanya ta faɗin,"Ok darling easy please!Bani 30 minutes yanzu zan gama in kawo maka."
Bai sake cewa komi ba illah kayansa daya ɗauka ya fito zuwa falonsa,kallo ya kunna yana kallon news sanyin AC na ratsa fatar jikinsa.
Akan idanunsa Samha ta fice domin zuwa kitchen ta samar masa da abinda ya umurceta,ba a ɗauki wani dogon lokaci ba sai gashi ta shigo hannunta ɗauke da tray ta aje a saman table ɗin dake tsakiyar falon.Murya a narke ta kai dubanta kan Aliyu tana faɗin, "My Aliyu gashi nan na kammala."
Kallon gurin yayi a lalace hancinsa na zuƙo masa wani irin ƙamshi daya cika falon,babu laifi ta wanke zuciyarsa amma sai ya basar ya cigaba da kallonsa tamkar ma bai ji abinda ta faɗi ba.
Ficewa tayi tana faman ƙunƙuni tana faɗin,"Matsalata dakai miskilanci da rainin wayo Aliyu."
Koda ta fita cigaba da kallonsa yayi bayan ya rage volume ɗin TV,sake shigowa Samha tayi wannan karon ta sauya kaya zuwa wasu nighties masu azabar kyau matuƙa.
Riga ce doguwa mai zubin kyallen tatar koko,rigar bata da maraba da babu kalar red mai hannun bra.Duka albarkatun ƙirjinta a waje suke,cikin taku mai cike da ɗaukar hankali ta ƙarisa zuwa garesa tana mai zama kusa dashi ta yadda har jikinta na gugar kafaɗunsa.Kallon fuskarsa tayi tana duban yadda ya wani ɗauke kai,shi a dole an gama ɓata ransa.
Ganin hakan ya sanya ta miƙe a nutse cike da kwarkwasa ta isa wajen table ɗin data aje tray ɗin potato balls ɗin ta ɗakko,a gabansa ta dire tray ɗin tare da yin zaman dirshan a gabansa tana jifansa Da wani narkakken kallo.Cikin nuna kulawa ta kai hannu ta ɗauki potato balls ɗin guda ɗaya takai bakinsa tana faɗin,"Sorry mana darling,ɗan ci kaji ko yayi yadda kake so." Kauda kansa yayi yana jifanta da hararar da ya sanya ta sakin smile,sake komawa tayi ta side ɗin daya maida fuskarsa tana sake faɗin,"Haba mana Aliyu, please open ur mouth ka ji darling."
Wannan karon baiyi musu ba ya buɗe bakinsa ta saka masa potato balls ɗin kafin tayi kissing ɗinsa tana faɗin "Das my darling,i luv u Aliyu."
A haka ta dinga bashi a baki yana faman basar da ita har ya cinye shi tas,lemun kwakwarma a baki ta dinga bashi har ya shanye cikin cup ɗin data zuba masa.Ya sani sarai Samha ba ƙaramin so take masa ba,Amma sai dai sam bata san yadda za ta tafi da son har ya dinga tasiri a cikin zuciyarsa bane,wannan shine damuwarsa da ita.
Miƙewa yayi ya nufi bedroom ɗinsa,direct toilet ya nufa ya kuskuro bakinsa ya fito.Wajen mirrow ya nufa Yana mai ɗaukar kwalbar daddaɗan turarensa ya feshe jikinsa,a nutse ya aje kwalbar turaren ya nufi bed ɗinsa ya haye domin kwanciya.Bai jima da zama a tsakiyar gadon ba Samha ta shigo ɗakin,direct ita ma kan gadon ta hayo tana dubansa a narke tamkar za ta sakin masa kukan shagwaɓa.Kallo ɗaya yayi mata ya miƙa hannuwansa duka biyu ya janyota zuwa jikinsa ya rungumeta,murya can ƙasa ya furta,"Samha gobe Dukku za mu kai ziyara tare da Hajiya,kinga ba don aikinki yafi komi muhimmanci a gareki ba da gobe kaɗai sai ki ɗauki excuse ki bimu mu tafi tare,hakan zai faranta raina matuƙa har ma Da Hajiya na san za ta yi farin ciki." Aliyu ya ƙare maganar yana wasa da suman kanta dake fidda wani irin ƙamshi mai motsa zuciya.
"Ayyah! My darling,ka koga tun aurenmu sau ɗaya kawai naje Dukku,sai dai sam garin bai min ba Aliyu shiyasa sam bani muradin sake zuwansa cikin raina ,ku dai Allah ya kaiku lafiya ya tsaremin kai Aliyu." Samha ta fadi hakan tana sake ƙwaƙumesa tamkar za ta shige cikin cikinsa.
Sam Aliyu bai ji daɗin kalamanta ba,ya rasa meyasa Samha bata iya faɗa ma mutum magana ta sigar da zai masa daɗi ba,abinda ke sake tunzura zuciyarsa a kanta kenan.
Sabida takaici sam bai iya sake cewa komi ba illah juya mata baya da yayi bayan ya tureta daga jikinsa,duk yadda taso ya biye mata ƙi yayi domin da gaske tayi matuƙar ɓata ransa.
Washegari koda za ta fita ko a dawo lafiya ba tace masa ba tasa kai tabar gidan, hakan ko ba ƙaramin zafi yai ma Aliyu ba ya dinga mamakin yadda raini ke son shiga tsakaninsa da Samhar.
Ƙarfe 10am Hajiya Maryama tare da Iya suka fito cikin shiri,daidai lokacin Aliyu shi ma ya fito yana sanye cikin shadda gezna brown color ɗinkin riga da wando.Aka yi sa'a ya sanya hular daya sake fiddo cikar zatinsa yayi matuƙar yin kyau,shigar ya amshesa sosai tare da fiddo asalin kyawunsa da ƙuruciyarsa.Iya kam ta kasa yin shiru saida ta wasashi,yana faman dariya suka nufi wajen ƙatuwar motarsa Range Robber baƙa wuluk.Shi ne ya shiga front seat yayin da Iya da Hajiya Maryama suka shiga gidan baya,driver ya ja motar bayan an tabbatar an shirya komi na tsaraba a cikin boot.
A sukwane suka fice daga gidan Baba Buzu da sauran hadimai na musu fatan dawowa lafiya,a haka suka ɗauki hanyar zuwa garin Dukku wanda yake nan ne mahaifar Hajiya Maryama.Gari ne na fulani usul wanda daidai gwargwado an samu cigaba sosai a garin,tafiya ne suke yinsa cikin jin daɗi suna hirarsu har suka isa garin na Dukku.Aliyu nata faman raba ido yana ganin irin sauye-sauye da dama,domin rabonshi da Dukku yayi shekaru da yawa.
A ƙofar gidan su Hajiya Maryama da suka yi rayuwa suka tsaida motar,babu kowa da ya rage a danginsu dake cikin gidan sai wasu abokanan arziƙin iyayen nasu ke zaune a ciki domin raya muhallin.Hajiya Maryama ce tasa aka maida gidan ginin bulo aka gyareshi sosai,Malam Kalla shi ke zaune tare da iyalinsa Laminde tsawon shekaru a ciki.Su Hajiya Maryama da Iya ne suka shiga cikin gidan suna faman rafsa sallama,Laminde ta fito a guje jin muryar Hajiya Maryama data jima bata shigo garin ba.Nan da nan Laminde suka tarbi su Hajiya Maryama cikin nuna tsananin murna da zuwansu,sun jima sosai a gidan Hajiya ta sanya aka dinga shigo musu da tsaraba.Kama Daga buhun shinkafa har zuwa kan su taliya da mangyaɗa,sai Laminde da aka haɗa mata har da turmin atamfa.Tamkar za su zubda hawayen murna haka suka ji,nan suka dinga sama Hajiya Maryama albarka har suka rakota zuwa wajen mota.
Aliyu ya sanya hannu ya zaro 20k yaba Mallam Kallah,nan Mallam Kallah ya fashe da kukan farin ciki yana ma Aliyu Addu'ar gamawa lafiya.
Daga nan gidan sai suka nufi gidan Mallam Ilu,tun daga nesa Hajiya Maryama ke hangen ginin gidan yadda ta sanshi.Katanga duk ya zube babu wani cigaba da aka samu,saima sake lalacewa da gidan yayi.Sanya kansu DA suka yi cikin soran gidan,yayi daidai da jiyo wani irin ihu da ake zanbaɗawa daga ciki.Jikin Hajiya Maryama har rawa yake sukai saurin isa ciki gidan, zuciyarta na harbawa da ƙarfin gaske.......✍🏻