HURAYYAH (New edition)

HURAYYAH (New edition) Chapter 5

by @ayshadansabo

HURAYYAH

 New edition...


 _Free pages_ 



     Chapter 5







Cikin sauri Hajiya Maryama suka kutsa kai cikin gidan,Mallam Ilu suka hanga a zaune bisa kan ruwan cikin ƙaramar Yarinya yana jibga tamkar ya samu jaka.Gefe guda kuma Inna Habeeba ce ke durƙushe tana kuka tamkar ranta zai fita,salatin da Hajiya Maryama ta saka tana tafa hannaye ne ya janyo hankalin Mallam Ilu da Inna Habeeba waɗanda sam da basu ji shigowar baƙi cikin gidan ba.


Cikin sauri Mallam Ilu ya ɗaga Yarinyar wacce tayi lamo tamkar matacciya sabida tsabar wahalan da take ciki,da gudu Inna Habeeba ta runtuma a guje ta ƙanƙame Hajiya Maryama tare da sake fashewa da matsanancin kuka.


Faɗi take,"Ina cikin masifa Inna,wallahi Mallam watarana shi zai zamo ajalin HURAYYAH,na rasa meyasa ya tsaneta a cikin zuciyarsa."


Hajiya sam bata iya yin magana ba illah kama hannuwan Inna Habeeba da tayi suka isa ga inda HURAYYAH ke kwance da alamu ma ta sume gau ne a wajen,cikin masifar tashin hankali Inna Habeeba ke faɗin, "Shikenan yau ma sumar da ita kayi Mallam?Allah yana kallon irin zalincin da kake mana kuma shi ne zai yi mana sakayya." Takai ƙarshen kalamanta tana tashi domin ɗebo ruwa ta kwarawa HURAYYAH.


Hajiya Maryama ce ta dubi mallam Ilu wanda gabaki ɗaya ya rasa inda zai tsoma ransa sabida tsananin kunya da takaicin halin abinda su Hajiya suka riskeshi yana aikatawa,cikin harshen fulatanci Hajiya ke magana tana faɗin, "Ashe baka da mutunci Mallam Ilu,har yanzu baka canza munanan halayenka akan Habeeba ba?Sai yaushe ne za ka san ka girma har kasan annabi ya faku?Tir da halin baƙin zalincinka Ilu,shashasha! Wanda baisan inda kansa ke masa ciwo ba."

Ta ƙare maganar cikin tsananin ɓacin rai da takaici.

Ta maida dubanta bisa kan Habeeba da HURAYYAH cike da tausayin yadda duk suka fita a hayyacinsu,sabida tsabar azabar irin halin ƙunci na rayuwa da suke ciki.


Aliyu da Iya kuwa tsaye suke sun kasa yin koda ƙwaƙwƙwaran motsi,banda ido da Aliyu ya tsurawa ƙaramar kyakykyawar Yarinyar dake kwance cikin ƙasa bayi ko ƙyaftawa.Tsananin tausayi da takaicin Mallam Ilu sun gama cika zuciyarsa tab,yana mamakin Shi ko Mallam Ilu wani irin azzalumin bawa ne da zai iya hawa kan ruwan cikin ƙaramar Yarinya kamar HURAYYAH yana jibga har ya sumar da ita.


Wani irin doguwar ajiyar zuciya ne ya ƙwacewa HURAYYAH wacce ta samu farfaɗowa daga suman da tayi bayan Inna Habeeba ta kwara mata ruwa,kukan da ya ƙwacewa HURAYYAH ne ya sanya su ƙarisawa baki ɗayansu zuwa inda Inna Habeeba ke cigaba da shafa mata ruwa a fuskarta zuwa ƙirjinta. 



Hajiya Maryama ta durƙushe a gabansu tana faɗin, "Sannu HURAYYAH kinji."


HURAYYAH ko tunda ta jita a jikin Innarta ta sake ƙankameta tana cigaba da rusa kuka, faɗi take "Inna ƙirjina,zan mutu,Mallam zai kasheni Inna,meyasa baya sona?Ya ƙara tsanata ne tunda aka ce na makance....wayyo ni Hurray..."


Ta kasa cigaba da furta kalaman sai kuka,Inna Habeeba kanta ta kasa tsaida hawayenta ga zuciyarta dake tsananin zafi tamkar ya faso kirjinta.Dukkaninsu kalaman Yarinyar ya girgiza zukatansu gami da jefa tsananin tausayinta,Hajiya ko sake nanata kalmar makanta take a cikin zuciyarta tana fatan kada hakan ya kasance ya tabbata.


A hankali Inna Habeeba ta kama hannun HURAYYAH suka nufi ɗakinta,ta kwantar da HURAYYAH Ƴar Kimani shekaru sha biyu a duniya bisa kan gadon baccinta.Fitowa waje gurinsu Hajiya Maryama da suka kasa binta ɗaki tayi,gabaki ɗaya bata cikin nutsuwarta sabida tsabar duhun da zuciyarta tayi."Inna marabanku da zuwa,kuyi haƙuri daga zuwa kun tadda abin tashin hankali,maraba da Aliyu ka zama bature abinka." Ta furta kalaman cikin ƙarfin hali tana ƙaƙaro murmushi,ita kanta ba wani isashshiyar lafiya ne da ita ba ƙarfin hali kawai take.


"Ba komi Habeeba mu ƙarisa daga ciki kema na lura ba wani lafiya ne dake ba." Hajiya ta faɗi hakan tamkar hawaye za su zobo mata.Har zuwa lokacin Mallam Ilu na tsaye yana raba idanu,sam ya kasa koda iya buɗan baki ya gaida Hajiya Maryama.


Duka suka isa zuwa ɗakin Inna Habeeba wanda ba laifi a tsaftace yake sosai,sabuwar ledar tsakar ɗakin da Hajiya Maryama tasa mata yana nan tsaf dashi.


Gadon ma a gyare yake tas dashi,anan Hajiya Maryama ta zauna kusa da HURAYYAH wacce ke kwance har yanzu ruwan hawaye ne ke zubowa daga cikin idanunta


Aliyu aka shinfiɗa ma babbar sallaya ya zauna akai,Iya kuma na bisa kan kujera ƙwaya ɗaya tal dake ɗakin.


A ƙasa Inna Habeeba ta zauna ana gaisawa cikin sakin fuska,Aliyu ta duba tana faɗin "Gadanga ina ka baro matar taka,dafatan duk kuna lafiya? Shekaru da yawa rabanku da garin Dukku, ai ina ga tun haihuwar HURAYYAH sau ɗaya ka dawo a lokacin da kazo tare da Amaryarka taka ko? "


Gyaɗa kai Aliyu yayi yana faɗin,"Hakane Inna Habeeba,kinsan yanayin aiki,gashi nimai yawan tafiye-tafiye ne,yau dai gashi Allah ya nufa na sake dawowa,Samha kuma tana lafiya lau tana gaidaku."


Hajiya Maryama ce ta dubi Inna Habeeba tana faɗin, "Habeeba har yanzu irin wannan zaman kuke da ilu?Har sai yaushe ne zai fara sanin darajarki?Gabaki ɗaya ya kashe miki rayuwa,yanzu kuma har wannan ɗiyar ƙwara ɗaya tal da Allah ya baki yana son sai yaga bayanku gaba ɗaya,wannan wace iriyar rayuwace?Waima miye tayi masa haka da zafi da har yake mata irin wannan bugun ke kuma kina durkushe tamkar gunki kina kuka a gabansa? Na gaji da ganinki a cikin ƙunci Habeeba,ni ina can cikin daula da wadatan rayuwa,ke kaɗai nake gani in ji daɗi in tuna da Yaya Magajiya,amma ke kuma kinƙi bani haɗin kan da za a ƙwatar miki ƴancinki a rabaki da wannan azzalumin,wace iriyar soyayya kike ma ilu da ba za ki iya yakicesa cikin rayuwarki ba Habeeba? 


Hajiya Maryama ta kai ƙarshen kalamanta tana duban Inna Habeeba dake faman zubda ruwan hawaye sosai,cikin rauni da sanyin murya Inna Habeeba ta fara faɗin,"Inna kiyi haƙuri wallahi ni kaina a yanzu zama da Ilu ya isheni,sam bana tsintar komi a zama dashi face baƙin zalinci daga garesa,ban sake jin aurensa ya fita a raina ba sai daya ɗauki karan tsana ya ɗaura akan wannan ɗiyar,sam bayi sonta Inna,matarsa ta dasa masa tsanarta a ransa,tana cewa wai an haifo masa mai kama da aljanu,a yanzu da lalurar makanta ya samu HURAYYAH kuwa sai ya sake riɓanya tsanar da yayi mata,suka haɗa kai da Sahura suka sanya mu a gaba da tsangwama." Inna Habeeba ta kai ƙarshen kalamanta hawaye na wanke fuskarta.(Sahura uwargida ce ga Inna Habeeba wacce ta mallake Mallam Ilu tsaf,baya jin maganar kowa sai nata)


Cikin tsananin razana Hajiya Maryama ta dubi Inna Habeeba tana faɗin,"Innalillahi wa'inna'ilaihirraju'un! Makanta Habeeba? Yaushe HURAYYAH ta haɗu da wannan iftila'in ni Mero?"


Wasu hawayen masu zafi Inna Habeeba ta sake sharewa kafin ta bai wa Hajiya Maryama amsar tambayarta tana faɗin, "Shekara ɗaya kenan Inna Mero,bayan zuwanki garin nan bada jimawa ba,sun fita da Yara wasa aka dawo min da ita wai an watsa mata wani abu a idanun,haka muka kwana ba bacci,a washegari muka tashi HURAYYAH na faɗin cewa bata gani,mafarin lalurar kenan Inna,munyi maganin gargajiyan har mun gaji, Mallam kuma yaƙi yarda a kaita asibiti wai bazai iya salwantar da kuɗinsa a kanta ba,mu rabu da ita haka Allah yaso ya ganta."

Cikin tsananin tausayi Hajiya Maryama ta ɗago HURAYYAH dake kwance tana sauraron dukkanin abinda ake faɗi,tana son tayi magana ta gaida su Hajiya domin zuwa lokacin ta gane Inna Mero ce tazo dubasu,wacce idan tazo take kawo musu kayan daɗi,bata manceta ba tana kallonta a cikin zuciyarta tar. 


"Sannu HURAYYAH In Sha Allah za ki warke kinji?Za ki yi karatu ki zama abin alfahari a garin Dukku baki ɗaya." Ta ƙare maganar cikin rawar murya sakamakon yadda tausayin Yarinyar ya mamaye zuciyarta.Ita ko HURAYYAH kwantar da kanta tayi a jikin Hajiyar tana faman sauke numfashi, jikinta yayi zafi sosai da kyar ta iya yin magana a hankali ta ce,"Kece Inna Mero,Innar Innata ko? Ina yini,don Allah ki tafi dani gurinki Inna inba haka ba Mallam zai kasheni wallahi,sam bana sonsa,yana dukan Inna da ni,duka bayi sonmu sai Babah Sahura dasu Falalu,ni baya sona yana cemin aljana makauniya,bayan kuma Mallam Bala ya ce dukkanin halitta na Allah ne,ina son inyi karatu sosai Inna mero,tun kafin in zama bana gani nake son zuwa boko irin yadda Dijama ke zuwa,amma Mallam ya ce ba zanyi ba."

Ta kai ƙarshen maganarta tana kuka sosai.Daga Iya har Aliyu babu wanda tausayin HURAYYAH baiyi tasiri a cikin ransa ba,kallonta Kawai Aliyu yake yana Ƙarawa. 


Shi har yanzu ya kasa yadda Yarinyar bata gani,domin ga ido har ido tar dasu babu alamun nakasa amma ace wai bata gani? Kai anya? Haka yake ta ayyanawa a cikin ransa,yana jin cewa ayau basai gobe ba zai raba wannan kyakykyawar Yarinyar da garin Dukku domin ya ceto rayuwarta daga faɗawa wani hali. 


Inna Habeeba ce ta miƙe tana fadin "Oh! Ni Habeeba ko ruwa ban kawo muku ba,bari ku gani." Daga haka ta fice daga ɗakin bayan ta ja mayafinta dake jikin ƙofa."


Maƙota ta shiga wajen aminiyarta Huraira,ta shaida mata cewa Inna mero ce tazo,don haka ta taimaketa tayi musu girki mai kyau.


Ruwan sha pure water ta amsa da lemukan kwalba da Huraira ke siyarwa,duk zagayan ita ce mai fridge tana sana'ar saida su ruwan sanyi da lemukan kwalba.


Koda ta dawo ta tadda Hajiya ta tasa HURAYYAH a gaba suna hira,HURAYYAH nata bata labarin Irin wahalar da Mallam ke basu.


Aliyu ya tsura musu idanu bakin HURAYYAH kawai yake kallo,ɗan ƙarami dashi tamkar ba daga bankinta maganar da take cikin hausarta irin na wacce harshenta ya gama karyewa da fulatanci ke fita ba,ko kaɗan ita bata san ma Aliyu na dubanta ba hirarta kawai take zubawa Hajiya Maryama cike da nishaɗi.


Ruwa da lemukan Inna Habeeba ta aje musu tana mai basu hakury akan rashin sanin zuwansu da bata yiba,ruwan kawai Aliyu ya iya sha kasancewar sun sha tsaftatacciyar fura a gidansu Mallam Kalla.Daga haka aka shiga hira tsakanin Inna Habeeba da Hajiya Maryama,inda duk rabin hirar sam ba mai daɗi bane,akan irin zaman ƙuncin da suke fuskantane ita da HURAYYAH a gidan.Inda a yanzu Inna Habeebar ke Jin zaman gidan Mallam Ilu ya fice daga ranta,burinta bai wuce ta tseratar da rayuwar HURAYYAH ba,Domin tana so taga cewa HURAYYAH ta sami ingantacciyar rayuwa.......✍🏻