HURAYYAH(New edition) Chapter 6
HURAYYAH
New edition...
_Free pages_
Chapter 6
Hurairah da kanta ta shiryo abincin data gama dafawa ta kawo gidan Mallam Ilu,gaisuwa ta ban girma da mutuntawa ne ya shiga tsakaninsu dasu Hajiya Maryama,wacce ta jima da sanin irin amincin dake tsakanin Huraira da Inna Habeeba.
Farar shinkaface da miya ta dafo musu,inda aka yanka kaji biyu aka yi amfani dasu cikin miyar.baya gashi sai haɗaɗɗiyar dambun zogale,wanda already Hurairan shi tayi a gidanta dama.
Kusa da HURAYYAH Hurairah ta isa tana faɗin, "Hurryn Inna ya aka yine wai? Banji kin tambayi Dije ba."
HURAYYAH ta saki murmushi ta ce,"Innar Dije ai nasan yanzu tana boko ne,nima Inna Mero tace zanyi karatu har sai ƴan garinnan sunyi alfahari dani."
Yadda tayi maganar bilhakki ya sanya Aliyu dubanta yana jin wani irin abu na taɓa zuciyarsa,tausayin HURAYYAH yake ji nayi ma zuciyarsa dabaibayi farat ɗaya.
Dafa kanta Hurairah tayi tana faɗin,"Ma Sha Allah HURAYYAH,nayi farin ciki sosai,kice za ki gudu cikin garin Gombe ki barmu da kewarki,koya Dije za ta kasance?Nayi miki murna HURAYYAH domin duk wanda yaga irin rayuwar da kike yi anan zai ji miki daɗi sosai idan an rabaki da wannan garin baki ɗaya."
Hurairah ta ƙare maganar tana share hawaye,domin ita kaɗai tasan yadda take jin tausayin HURAYYAH da Inna Habeeba.Barin ma yanzu da lalurar makanta ta sami HURAYYAHN,cike da ɗoki ta dubi Hajiya Maryama ta ce,"Hajiya hala za ki tafi da HURAYYAH cikin gari ne? Amma kin kyauta idan hakan ne,Allah ya biyaki da gidan aljanna."
Murmushi Hajiya Maryama tayi tana faɗin,"Ai ya zama dole Hurairah,domin bazan iya bacci ba yau idan har ban tafi da wannan ɗiyar gabana ba,ai yau nina ga baƙin zalinci ganin idanuna,ace wai Ilu ne zai hau bisa kan ruwan cikin Yarinyarnan yana jibga tamkar ba jininsa ba,tabbas a wannan karon zan bashi mamaki,zai kuma san cewa HURAYYAH ƴace da ya kamata yayi alfahari da ita,makanta kuwa idan har bada shi Allah ya rubuta za ta rayuba to sai ya zama tarihi,matukar arziki za su yi ranarsu." Hajiya ta ƙare maganar tana duban Aliyu,wanda ke faman gyaɗa kai alamun amincewa ga dukkanin zantukan dake fitowa daga bakinta.
A nutse kuma ya buɗe baki ya fara faɗin, "Tabbas Hajiya shawarar da zuciya ta yanke Kenan,na cewa mu tafi da HURAYYAH wajenmu,ni zan zame mata Uba kuma Yaya,sannan zan tsaya tsayin daka domin ganin cewa rayuwarta ta inganta."
Inna Habeeba wacce ta kasa rufe baki sabida tsabar farin ciki,tayi saurin duban Aliyu tana son yin magana amma sai Hajiya ta hanata ta hanyar rigata faɗin,"Tashi maza Habeebah ki kiramin azzalumin mijinki domin ayita ta ƙare,ke ni yau ko ni ko shi ne a garin Dukku,har kema Sai ya bani takardarki mun tafi can ki huta da wannan ƙuncin rayuwar,idan har bazai sauya hali ya zama namiji a gidansa ba."
A tare Inna Habeeba da Huraira suka fice daga ɗakin,cikin sa'a suna fita waje sai ga ɓullowar Mallam Ilu,da alamu daga gidan sahibarsa Sahura yake,kasancewar ba gida ɗaya ya ajesu da Habeeba ba,amma kuma duk da hakan bai hana Inna Habeeba kwankwaɗar takaicin kishiya ba.
Sanar dashi sukai cewa Hajiya Maryama ce ke son ganinsa,jin hakan ya sanya cikinsa murɗawa domin yasan akwai rigima yau.Domin kuwa batun yanzu yasan cewa Hajiya Maryama bata ƙaunar zamansa tare da Habeeba ba,shi kuma Allah ya gani yana son Habeeba sosai,lokuta da yawa yana mamakin kansa yadda yake aikata wani mugun abun a kansu.
Jiki a saluɓe suka jera har zuwa cikin gidan Shi da Inna Habeeba,da sallama suka shiga cikin ɗakin ya sami guri ya zauna.Sam ya kasa haɗa idanunsa da kowa a cikin ɗakin,sabida kunyar abinda suka sameshi yana aikatawa a ɗazu.Da ƙyar ya haɗo kalaman gaisuwa ya jefasu ga Hajiya Maryama,ta amsa a daƙile tana mai ɗaurawa Da faɗin,"Ɗago ka dubeni Ilu,domin yau ko ni ko kaine a garin Dukku,ina so ka buɗe kunnuwarka da kyau ka jini,domin a yau zanbar garin Dukku tare da HURAYYAH,kai da ita sai dai idan ta zo gaidaku lokaci bayan lokaci,shi ma Hakan zai faru ne domin mu fita hakkin musulunci,don haka saika faɗawa matar gwal ɗin taka ta zuba ruwa a ƙasa ta sha,sai magana ta biyu idan har ka gaji da Habeeba a yau nake so ka bani takardarta,ka sakar mini ita in haɗasu in tafi dasu tunda kai an riga an shanyeka,koda yake damacan ba wani mutuncine da kai ba."
Ta ƙare maganar tana tsaresa da idanunta dake nuna zallan ɓacin rai.
Mallam Ilu gabaki ɗaya zufa ne ya fara ketowa daga jikinsa,babu masifan dake ratsashi a Duniya irin a ambaci kalmar rabuwa tsakaninsa da Habeeba.Yana mata wani irin so ne da baki bazai iya kiyasinsa ba,dukkanin abubuwan dake faruwa suna faruwane ba tare da son ransa ba sam.
Cikin rawar baki da tashin hankali yake faɗin,"Aradun Allah Hajiya ba zan iya sakin Habeeba ba nan duniya,domin ina sonta ita ma kuma tana sona,kiyimin rai kada ki rabani da matata."
Wani kallo Hajiya Maryama ta watsamai tana faɗin "Ashe har wani so kasani Ilu?Amma kuma shine kake zalintarsu kana wulaƙantasu?Dubi fa yadda Habeeba ta koma,haka ka aurota? Nace haka muka baka Habeeba?To bari kaji,wallahi idan har Habeeba ta zaɓi rabuwa dakai ina tabbar maka ko kotu za mu tafi saika saketa,shashasha sallamamme kawai." Hajiya ta kai ƙarshen kalamanta tana mayar da dubanta kan Inna Habeeba tace,
"Ke kuma Habeeba kina son zama da shi ko kuwa? " Inna Habeeba sai tayi ƙasa da Kanta tana sharar hawaye,domin tana son mijinta sosai.Baƙin uƙuban da take ci a hannunsane yake sanyawa take jin ya fita a ranta,amma da a ce zai gyara halinsa to za ta zauna da shi tunda gashi za a ɗauke Mata HURAYYAH,wacce halin da take ciki shi yafi komi sake dagula lissafinta.
Ganin taƙi cewa komi ne ya sanya Hajiya fahimtar cewa lallai Inna Habeeba bata son a rabata da mijinta,cikin takaici take faɗin,"To Ai shikenan Habeeba tunda kin zaɓi zama da mugu bazan kashe miki aure ba,amma ki sani,ya zama tilas ki koma gidan gadonmu ku zauna tare da su Mallam Kallah,ɗakunan da nake sauka idan nazo nan za ki yi amfani da guda biyu a barmin ɗaya ya isheni,idan ya biyoki amfaninsa,in bai je ba ki rabu dashi,zan baki jari mai yawa kiyi kasuwanci kina jina ko?"
Gyada kai Inna Habeeba tayi tana mai jin farin ciki da kaunar Hajiya Maryama na sake mamaye zuciyarta,cike da rawar murya ta shiga yiwa Hajiyar godiya tare da yi mata fatan gamawa lafiya.
Mallam ilu kansa wani farin ciki ne ya mamaye zuciyarsa,tabbas wannan tsari yayi masa.Godiya yayi sosai Hajiya na zubamai harara,shi ko Aliyu takaicin Mallam Ilu ne ya gama cika zuciyarsa taf.
Kayan HURAYYAH Hajiya ta saka aka kwaso tana dubawa,sam bata da wasu kayan kirki sai guda biyu da suka fi sauran kyau a ciki.Hakan ya sanya ta cewa Habeeba ta bayar kawai,bayan ta ciri guda biyun da suke sune masu kyau a ciki.
Bayan driver ya gama sauke tulin tsarabar da aka kawo ma Inna Habeeba,sai Hajiyar tace suyi shirin komawa gida. Huraira ce ta sake shigowa domin yin godiyan tsaraba,domin buhun shinkafa da jarkan mai har da sabulai da 5k Hajiya Maryama ta aika mata dashi.Tare da Dije ƙawar HURAYYAH suka shigo,Dije suka rungume juna ita da HURAYYAH suna kuka sosai.HURAYYAH faɗi take "Dijama zan tafi in barki ba don ina so ba,bana son zamana anan domin watarana zan iya mutuwa sabida irin uƙuban da nake sha,ina ma ina gani inga yadda kike zubar da waɗannan hawayen na kewar rabuwa dani."
HURAYYAH ta ƙare maganar cikin muryar kuka sosai.
Kusan kowa saida ya ji tausayin yadda rabuwar HURAYYAH da Dije ya kasance,domin kuwa kullum suna tare da Dijen a ƙauyen Dukku.idan Dije ta dawo daga boko za ta zo taita koyawa HURAYYAH abinda ta koyo,Islamiyar Mallam Bala kuwa ita ke kama hannun HURAYYAH su tafi tare,tana sauraren karatun tare da haddace komi.
Mutane ne suka fito ana tama HURAYYAH a sauka lafiya,Aliyu ya dinga rabon kudi ana sanya masa albarka.
Ƙarfe 6pm da kusan rabi suka baro garin Dukku,da yake duka tafiyar bai wuce 50 minutes zuwa 1 hour ba tsakaninsu da cikin gari.
HURAYYAH tasa hannu tana share hawayen rabuwarta da Innarta,wanda rabon data ga fuskarta a zahiri shekara ɗaya kenan.
Kwantar da kanta tayi a jikin Hajiya Maryama tana kuka a hankali,yayin da Hajiya ke faman rarrashinta da kalamai na kwantar da hankali.
Aliyu na sauraren duk abinda ke faruwa,ana idar da sallar magriba suka shigo cikin garin Gombe.
Koda suka iso gida kowa sashinsa ya nufa,domin Aliyu a gajiye yake liƙis,burinsa kawai ya watsa ruwa ya gabatar da sallah.
Hajiya da Iya tare da HURAYYAH suka nufi part din Hajiyar,koda suka shiga Hajiyar ce ta sanya Iya ta taimakawa HURAYYAH tayi wanka domin ta ji daɗin jikinta.
Sosai Iya ta taimaka mata tayi wanka mai kyau,aka wanke wannan uban gashin kan nata mai cika da tsayi.Gashi ne irin Na fulani mai santsi sosai,Iya sai faman yaba kyawun HURAYYAH take tana hasaso nan gaba kaɗan yadda Yarinyar za ta zama abin rububi ga maza je,domin kuwa za a yi kallon kyawu da cikar halitta a wajennan,sai data gyareta tsaf sannan ta sake mata jagora zuwa ɓangaren Hajiya Maryama.
Ganinsu ya sanya Hajiya Maryama saurin tashi ta kamo hannuna HURAYYAH tare da zaunar da ita kusa da ita tana faɗin,"Yauwa Iya sannu da aiki,HURAYYAH sannu ko,yanzu saura kiyi sallah,ina fata kin iya?" Gyaɗa kai tayi alamun eh! Hajiya ta sanyata ta dinga gaya mata yadda ake yi,tsaf ta faɗa mata sai ɗan gyara kaɗan data yi mata.
Hajiya da kanta ta raka HURAYYAH toilet ɗinta tayo alwala suka fito,sai data ga ta tsayu akan sallaya tsaf sa'annan ta fice daga ɗakin tana faɗa mata idan ta idar ta kira azo ai mata jagora zuwa falo.....✍🏻