KUNDIN CINIKAYYA BY A'ISHA M.B

9&10

by @aishamb


*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐.

Daji 🌲

Magarƙama🏢 da kuma 

Birni🏙️


WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞

(Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu)



***

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

(J.W.A) 

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


 *DIAMOND 💎 STAR⭐* 

   *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️*

 *(We stand together)*

      🤝🤝🤝


بسم الله الرحمن الرحيم 

*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*

Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!


*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 9️⃣▶️🔟

*_________________________________________________*

Ba bu abin da jaririyar ke ta faman yi sai kuka, yayin da namun jejin suka bita da kallo. Nan take wasu daga birrirukan suka fara arewa kan bishiya yayin da suka nufi gidan zuma tare da ɗaukar kashin zuma suka nufi inda jaririyar take. 



Suna isa suka saka mata a baki, nan take ta fara tsotsan zuman tana yi tana kuka. Ɗaukar ta gwagon biri ya yi tare da ɗora ta kan cinyarsa, a yayin da ya yi mata lulluɓi da ganye sannan ya fara bata zuman da kansa.



Nan da nan gaba ɗaya namun daji suka tsaya tare da zagaye su. Nan take jaririyar ta kalle su tare da sakin murmushi.



**Saka shi suka yi a cikin cell yayin da suka fara jibgarsa ta ko ina, saida suka tabbatar ya jigata sannan suka ƙyalesa. Zama DPO ya yi yana kallonsa ya ce. 



"Shin wane ne ya tura ka don ka taimaki Mrs Laila?, ba za ka faɗa ba ko sai an ƙara maka duka?".


Ɗago da rinannu isanuwansa ɗan sandan ya yi sannan ya ce. "Ni ɗin jami'i ne, kuma doka bata yarda jami'i ya daki jami'i ba tare da wani ƙwaƙwaran hujja hakan abin da ya aikata ba, sannan kotu bata baka damar yin hakan ba, mundin kotu ta gano to tabbas sai an cika tarar maƙudan kuɗaɗe sannan kuma a dakatar da kai daga aiki".


Baki sake DPO ke kallon ɗan sandan sannan ya ce. "Ni tun da nake ban taɓa ganinka a cikin rukunin ƴan sanda ba, ƙarya ka ke kai ɗin ba ɗan sanda bane, so dai ka ke ka faɗi abin da za ka kare kanka da shi, to ni kuma ba zan bar hakan ta faru ba, mundin ina nan saina tabbatar da cewa kotu ta hukunta ka bisa ƙwaƙwaran hujjoji da nake dasu a kanka. Don haka ka faɗa min gaskiya domin a sassauta maka hukunci da za'a yanke maka".


Murmushi ɗan sandan ya yi sannan ya ce. "Ko za ka kai gobe kana duka na tare da tambaya na ba zan taɓa faɗa maka ba, sai dai kayi duk abin da ka e ganin za ka yi".



Tashi tsaye DPO ya yi sannan ya ce. "Ohh haka kace?, nayi duk abin da nake ganin zan yi ko?, shi kenen za ka ga aiki da cikawa".


Yana kaiwa nan ya ƙwallah jami'ai kira. Nan da nan jami'ai suka hallara a ciki cell ɗin, yayin da ya ce da ɗaya daga cikin jami'ai da ya ɗauko masa iron. Nan da nan jami'in ya ɗauko masa dutsen guga kamar yadda ya buƙata.



Saka iron ɗin ya yi a jikin socket wanda ke kunne, yayin da ya saka suka tuɓe masa kaya. Ɗaukar iron ɗin ya yi wanda ke fitar da tiriri saboda zafi sannan ya kalli jami'in ya ce.



"Zan ƙara tambayar ka a karo na ƙarshe, idan har baka bani amsar da nake buƙata ba, zan ɗora maka wannan iron ɗin a jikin ka".



Cikin rashin tsoro ko fargaba ɗan sandan ya kalle shi sanann ya ce. "Me ka ke jira?, maza ka aiwatar da abin da ka ke niyar yi, kada kayi tunanin za ka tsorota ni da wannan dutsen guga, idan wahala ne jiki na ya saba da wahala, dana faɗa maka gaskiya na gwammace na fuskanci kowace tsanani ko duka da zata fito daga gare ku. Don haka maza ka fara".



Kallon jami'an DPO ya yi, yayin da ya sa suka kwantar da ɗan sandan. DPO bai yi wata-wata ba ya ɗora iron mai zafi a jikin ɗan sandan.




**"Haba Zainab, kina magana kamar wacce bata san ƙaddara ba, haihuwa fa na Allah ne, na san mundin lokacin mu ya yi za'a ƙwanƙwaso mana ƙofar alkhairy ne. Don haka dan Allah ki daina kuka, likita ya ce idan kina shan maganin ki a kan lokaci za'a samu sauƙi". Dattijon ya faɗa yana mai ci-gaba da tuƙi.



Matar dake kusa da shi ce ta ɗago da jajayen idanuwanta tare da ɗora wa a kansa sannan ta ce. "Mai gida me ka ke so nayi to?, yanzu kimanin shekaru goma kenen muna ta fafutuka wajan neman haihuwa, ta ya ya ka ke tunanin ba zan yi kuka ba?, ƴan uwanka da mahaifiyar ka gaba ɗaya sun sa min ido. Kuma nima ban taɓa ganin laifin su ba, saboda ba bu wata uwa da zata so ta bar duniya ba tare da ta ga jikanta ba?, ni kawai ka barni na ci-gaba da kuka na ko zan ɗan samu sassauci a cikin zuciyata"



Girgiza kai mutumin ya yi sannan ya ce. "Karki damu Zainab, Allah yana sane damu, in sha Allahu next week zamu je America domin a duba ki kinji. Kuma da yardar Allah komai zai yi dai......

Da wani irin sauri yaja wani mugun birki.


Saurin ɗago da kai Zainab ta yi ta ce. "Me ya faru mai gida?". 


Fita daga cikin motan mutumin ya yi, yayin da ita ma matar ta fito waje. 



Kallon akwatin mutumin ya yi sannan ya ce. "Kinga wani akwati ina tunanin mutum ne ya manta shi s wajan".



Kasa kunne matar ta yi jikin akwatin. Zaro ido waje ta yi sannan ta ce. "Kamar fa naji motsin wani abu a ciki, dan Allah ka zo mu tafi kada wani abu ya cutar damu, yanzu fa dare ya yi sosai ya kamata mu bar nan wajan".



"Ki tsaya Zainab, zanje na ɗauki akwatin kedai ki zuba ido ki gani". Ya faɗa tare da nufar inda akwatin take. Addu'a ya yi yayin da ya yi bissmillahi sannan ya ɗauki akwatin.


Jin da nauyi ya sa ya kuma tabbatar da cewa akwai wani abu s ciki. Zuwa ya yi har gaban motar sa sannan ya ajiye akwatin. 


Dafa kafaɗar shi matar ta yi cikin tsoro, sannan ta ce. "Dan Allah kada ka buɗe inajin tsoro".


"Dan Allah Zainab kiyi haƙuri ki barni na buɗe akwatin nan in ba haka ba hankalina ba zai kwanta ba". Ya faɗa yana mai zuge akwatin.


Saidai ya zuge akwatin gaba ki ɗaya sannan ya yi bissmillahi tare da buɗe murfin akwatin. Zaro idanuwa waje gaba ki dayansu suka yi. A yayin da zuciyoyinsu ya fara dukan uku-uku.


Baki na rawa matar ta ce. "Me nake gani haka?, jaririya ce da suka saka ta a akwati, wane mara imanin ne ya aikata miki haka?".


Fiddo jaririyar mutumin ya yi sannan ya ce. "Yanzu ba lokacin magana bane, mu fara kaita gida in yaso gobe mu kaita police station ko gidan radio domin bincikar inda iyayenta suke".


Karɓe jaririyar matar ta yi sannan ta ce. "A'a, ba bu inda za'a kaita, zata zauna tare da mu har tsawon ƙarshen rayuwar ta, me ya sa iyayenta zasu watsar da ita su barta a cikin wannan mawuyacin hali. Yanzu da a ce bamu zo ba da wuri da tuni ta rasa rayuwarta saboda rashin iska. Tun da har waɗan da suka haife ta basua sonta ni ina sonta kuma zan riƙe ta tamkar ƴar cikina, ina sonta kuma ina ƙaunar ta. Don haka kamar yadda ka faɗa next week zamu bar ƙasar nan baki ɗaya domin muje mu gina sabuwar rayuwa tare da yarinyar mu". Ta faɗa tana mai rungume jaririyar kan kirjinta. 









*BAYAN SHEKARU*.

      *GOMA*

Kwance take kan bench na ajin, yayin da ayaniyar yara ya cika ajin baki ɗaya.


Ɗago da rinannun brown eyes ɗinta ta yi, tare da ɗora wa kan yaran dake ta faman wasa a cikin ajin.


A hankali ta ɗago da fuskarta gaba ɗaya. Masha Allah baki na ya iya furta wa lokacin da nayi gamo da cute and pretty face ɗin ta mai matuƙar kyau. Lumshe idanuwanta ta yi wanda suka kunkumbura saboda kuka sannan ta buɗe su baki ɗaya. 



Miƙe wa tsaye ta yi tare da nufar inda sauran ɗalibai na ajin suke. Suna ganin ta iso wajan su, gaba ɗaya suka yi saurin barin wajan.


Kallonsu ta yi cikin shesheƙar kuka ta ce. "Wai me ya sa a koda yaushe ku ke gudu na idan ba tunkari inda ku ke?, ban san mena yi muku ba, nima ina son kasancewa tare da ku, ina son na yi wasa sannan muyi karatu tare, bana jin daɗin zama ni kaɗai a cikin wannan makarantar". Ta faɗa tana mai fashe wa da kuka.



Kallonta ɗaya daga cikin yaran ya yi sannan ya ce. "Kinga Zahra Mu ba zamu iya zama da ƴar magarƙama ba, an ce Mamanki sheɗaniya ce tana kashe yara, kuma kema a cikin magarƙama ki ka taso, yayin da ita kanta wacce ta riƙe ki ƴar magarƙama ce. An ce gaba ɗaya ahalin ki rabuwa suka yi dake saboda ba zasu iya riƙe ki ba. muma kuma ba zamu iya zama ko muyi tarayya dake ba, saboda muma kada muje ki kashe mu".


Wata a cikin ɗaliban ce ta ce. "Nima mahaifiyata ta faɗa min cewa kada na kuskure na haɗa ƙawance dake ko na zauna dake. In ba haka ba zata dake ni. Don haka dan Allah ki rabu damu, mu ba zamu zauna da ƴar makashiya ba".


Kallonsu Zahra ta yi sannan ta ce. "Ƙarya ku ke, Mamata ba muguwa bace ba, Idan ku ka ƙara cewa Mamata wai muguwa ce, saina kai ƙarar ku wajan shugaban makaranta.


Ɗaukar jakarta ɗaliban suka yi tare da jefa mata a jiki. 



Hana haka malami ya shigo cikin ajin. Nan take kowanensu ya koma wajen zamansa. Banda Zahra wanda ke a tsaye sai faman kuka take.


Kallonta malamin ya yi sannan ya ce. "Zahra me haka yi miki ki ke kuka?".



Kallonsa ta yi cikin shesheƙar kuka ta ce. "Malam zagin Mama ta suke yi, kuma wai suna ce min ƴar magarƙama".



Taɓe baki malamin ya yi sannan ya ce. "To ai da gaskiyar su, in da mahafiyar ki mutumiyar kirki ce bata damfari al'umma ba da ba za'a dinga yi miki wannan kallon banzan ba, don haka duk abin da haka yi miki to ki ƙaddara cewa Mamar ki ce ta jawo miki. Dani ne ma shugaban makarantar nan da ba zan karɓe ki a makarantar nan ba wallahi".


Durƙusawa Zahra ta yi kan gwiwowinta tana mai fashe wa da kuka. Nan take ɗaliban ajin suka fara mata dariya, tare da fara tsokanarta, yayin da suka fara jifarta da littafi.


Miƙe wa ta yi da sauri sannan ta fice daga cikin ajin. Nufar inda warders wanda ke mata rakiya izuwa makarantar ta yi, yayin da ta kalle su sannan ta ce. "Ina son ku maida ni gida yanzu nan". Ta faɗa tare da shige wa cikin mota.


Kamar yadda ta faɗa haka suka ja mota suka bar harabar wajan. Bai fi lokaci ƙalilan ba, suka isa cikin magarƙama. 


Fitowa ta yi daga cikin mota tare da rugawa a guje ta nufo inda Hajiya Binta ke da zama.


Binta da kallo mutanen dake cikin magarƙamar suka yi, ganin yadda idanuwanta suka kunkumbura ya sa hankalin kowanensu ya tashi, Da sauri sauran mutanen dake cikin magarƙamar suka nufi inda take.


Shiga cikin ɗakin da Hajiya Binta take ta yi. Tana mai fuskantarta ta ce. "Shin laifi ne dan na kasance ƴar magarƙama?, kowane yaro farin ciki yake, amma ni a koda yaushe ba bu abin da nake fuskanta sai baƙin ciki da ƙyama. Kuma na san duk abubuwan nan na faruwa ne saboda Mamata, da a ce bata tafi ta barni ba, da hakan ba zata faru ba. Na tsane ta, bana sonta, me ya sa da zata tafi bata kashe ni ba?, amma ta barni cikin kaɗai ci". Ta ƙarashe maganar tare da fashe wa da kuka.



Da sauri Hajiya Binta ta isa gare ta tare da rungume ta . "A'a ƴata, mahafiyar ki ba muguwa bace, bada son ranta ta tafi ta barki ba. Mamanki tana sonki sosai, kuma karki damu, nan gaba mutane za su daina tsokanarki kuma su daina gudunki kunji".


"Shi kenen Aunty, kiyi min alƙawarin cewa za su daina tsokana ta". 


Murmushi Hajiya Binta ta yi sannan ta ce. "Nayi miki alƙawarin cewa ba bu wanda zai ƙara tsokanarki Zahra". 


Murmushi jin daɗi Zahra ta yi sannan ta miƙe tsaye tare da fice wa waje domin yin wasa.





*BAYAN WASU SHEKARU GOMA*


   *AMERICA*

Ba bu abin da ke tashi a cikin mashayar nan in banda haka. Yayin da ba bu abin da ka ke gani sai mata da maza, yayin da matan ke sanye da ɗingilallen skirt da shi gwanda ba bu. Chan na hangi wata matashiyar budurwa wacce ba zata wuce shekaru ashirin ba a duniya sai tiƙan rawa take yi. Yayin da gaba ɗaya turawan wajan idanuwansu a kanta.


Ɗaya daga cikin mutanen wajan ne naji ya ce. "Diana".

Juyowa ta yi tare da baje gashin ta, masha Allah na furta lokacin da nayi kicibus da haɗaddiyar fuskantar wanda ke ɗauke da light makeup. 


Kallonsa ta yi cikin cool voice ɗinta ta ce da shi. "How are you John?". Ta faɗa da yaren turanci na ƴan ƙasar America. 



Amsa wa John ya yi da cewa. "Am good baby". Ya faɗa yana mai ƙoƙarin shafa jikinta. Nan take budurwar ta ɗago da blue eyes ɗin ta tare da ɗaga hannunta ta kwashe shi da mari.



Nan take mai Dj ya kashe waƙar dake tashi, yayin da gaba ɗaya idanuwan jama'ar wajan ya karkata izuwa kansu. Nuna shi ta yi da ɗan yatsarta cikin ɓacin rai ta ce. "How dare you John?, are you mad or something?. Idan har ka ƙara yi min wannan shashanci saina yi maka abin da yafi hakan". Diana ta ƙarashe maganar tare da ɗaukar car key ɗin ta sannan ta fita daga cikin club ɗin.



Da sauri ƙawayenta suka bi bayanta. 


Nausar iska John ya yi yayin da ɗayan hannunshi ke dafe da ƙuncin shi.


"Diana! Diana! Diana". Haka ƙawayenta suka shiga ƙwalla kiran sunanta, amma ko juyowa bata yi ba ta saurare su, haka ta shige cikin mota tare da jan motan ta bar harabar wajan.



Girgiza kai ƙawayenta suka yi yayin da suka koma cikin club ɗin. 



Tafiya mai nisa ta yi kafin daga bisani ta isa gida. Parking ta yi tare da fitowa daga cikin mota. Ta fara takawa da takalmin ta mai tsini ji ka ke ƙwass! Ƙwas! Ƙwass.



Shiga cikin faɗeɗen palourn su ta yi a tsorace. Cire takalman ƙafarta ta yi sannan ta fara sanɗa tana tafiya. Saida taje daff da zata hau kan upstairs ta ji muryar mahaifiyarta.


Da gudu ta haye kan upstairs tare da shige wa cikin ɗakin ta.




      *NIGEIRA*.

  "Wannan wane irin shirme ne Aliyu?, sama da yara amsin nasa haka yi safaransu izuwa kasashen waje, amma yanzu sai kace min wai wani ɓoyayyen jami'i ya sake su sun tafi, ta ya ya hakan zata faru?. Nafi sama da shekaru talatin ina wannan aikin nawa a ɓoye, kuma yanzu rana tsaka kace min wai yaran da na aika duk jami'ai sun karɓe su sannan suka mai da su gidajen su. Kasan dai wannan abun zai iya taɓa siyasa ta ko? Gashi zaɓe ya kusa, idan har mutane suka gane abin da nake aikata wa ta ya ya za su yarda su zaɓe ni a matsayin govnor. Ya zama dole kasa a rufe wannan abun, in ba haka ba saina sa an ɓatar min da kai daga cikin wannan duniya.



Ɗago da fararen isanuwansa masu kyau da ɗaukar ido ya yi yayin da ya furzar da iska mai zafi waje cikin jin haushi da takaicin abin da ɗan majalisan yake aikata wa ya dube shi ya ce. "Kada ka damu yallaɓai, ko ta halin ƙaƙa ba zan bari komai ya fita ba, nayi maka alƙawarin hakan. Yanzu zanje na samu Mk ne a magarƙama. Na san yana da cikakken bayani game da wanda ya kunce yaran. Mundin ya faɗa min, in sha Allahu zan zo na sanar da kai". Yana kaiwa nan ya fice daga cikin office ɗin ƴan majalisa yayin da ya nufi inda motarsa take kai tsaye. Shiga cikin motan ya yi tare da jan motan ya nufi hanyar magarƙama.



Isarsa magarƙama keda wuya, ya tarar da wasu mata suna buga ƙwallon ƙafa.


Tafiya ya soma yi yayin da jami'ai suka tare shi. Nan take ya nuna musu ID card ɗin sa. Ganin shima jami'i ne ya sa suka barsa ya shiga. 



Sanye matashiyar take da kayan magarƙama yayin da take sarrafa ƙwallon cikin ƙware wa, a yayin da fuskarta ke ɗauke da farin ciki da annashuwa. Buga ball ɗin ta yi da ƙafarta na dama. Cikin rashin sa'a kuwa ball ɗin ya bugi Aliyu.


Zaro idanuwa gaba ɗaya mutanen wajan suka yi tare da bin budurwar da Aliyu da kallo.


Cike da ɓacin rai Aliyu ya ɗaga dara-daran idanuwansa tare da ɗora wa a kan ball ɗin. Cikin ɓacin rai ya ce. "Wace banzar ce ta cilla min ball a jiki?".



Amsa wa budurwar ta yi da cewa. "Nice nan na wurgo ball ɗin". Ta faɗa tana mai juyo da kyakkyawar fuskarta.






💃💃💃💃💃💃💃💃💃

MANAGE PAGE

COMMENTS & SHARE FISABILILLAHI 🥰🙏🥰


ALƘALAMIN ✍️ 

AISHA M.B💞💞💞

(Zinariyar Jajirtattu)