KUNDIN CINIKAYYA BY A'ISHA M.B

19&20

by @aishamb

***


🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐.

Daji 🌲

Magarƙama🏢 da kuma 

Birni🏙️


WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞

(Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu)



***

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

(J.W.A) 

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


 *DIAMOND 💎 STAR⭐* 

   *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️*

 *(We stand together)*

      🤝🤝🤝


بسم الله الرحمن الرحيم 

*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*

Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!


*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 1️⃣9️⃣▶️2️⃣0️⃣

*_________________________________________________*

Mom ta faɗa damuwa bayyane kan fuskarta yayin da ta riƙe Safeera ƙamm jikinta.



"Wallahi Allah masani, hanya yarinyar nan ba ta da aljanu kuwa?". Aliyu ya faɗa.



Kallonsa Daddy ya yi ya ce. "Gaskiya bana tunanin tana da aljanu saboda a wannan ƙasar babu aljanu balle maye, kuma ba ta taɓa zuwa Nigeria ba balle na ce a chan ta ɗebo aljanu".



Kallon baka da hankali Aliyu ya bishi da shi sannan ya ce. "Okay wato a iya Nigeria ne kaɗai ake samun aljanu ko?, gaskiya Daddy ya kamata ka koma islamiyya ko ka dinga shiga YouTube ko chrome kana koyan abubuwan da ya daganci addinin musulunci, don naga kamar har yanzu da sauran ka".



Kallonsa Daddy ya yi sannan ya ce. "Na je islamiyya mana kuma har ma nayi sauka sai dai ba'a ƙasar Nigeria na ta so ba a wannan ƙasar America na ta so".



Kallonsu gaba ɗaya Mom ta yi ta ce. "Yanzu ba irin wannan magana ya kamata kuyi ba yanzu, ya kamata a ce ku san abin yi domin ta farfaɗo, tun ɗazu nake jijjigata har yanzu ba ta numfashi. Dan Allah ku taimaka bana son na rasa ƴata ɗaya tilo".



Kallonta Aliyu ya yi cikin tausayawa ya ce. "Na fahimci yadda ki ke ji Mom, yanzu mafita ɗaya muke da shi, dole ne muje Nigeria domin yi mata maganin gargajiya. Idan muka ce zamu yi a nan sanadin hakan ƴan sanda za su iya kama mu, domin za su ɗauka cutar da ita zamu yi hakan na iya sawa su kai mu magarƙama ma. Yanzu mafita ɗaya ce shi ne muje Nigeria domin wannan maganin gargajiya ne kawai zai yi aiki.



Kallonsa Daddy ya yi ya ce. "maganin gargajiya kuma?, gaskiya ba za'a bawa ƴata irin wannan ƙazaman maganin ba, saboda ni duk ban yarda da ire-iren waɗan nan magungunan ba".



Girgiza kai Aliyu ya yi sannan ya ce. "Ko ka yarda ko karka yarda dole ne muje Nigeria domin yi mata maganin, in ba aka ba za ku rasa ta".



Jin an ambato batun za'a rasa ta, ya sanya Mom ta miƙe zumbur tare da nufa part ɗin ta. Saida ta ɗau lokaci kafin ta fito daga cikin ɗakin ta. Fitowa ta yi sanye da hijabi yayin da hijabi ɗaya na hannunta. Ƙarasowa wajan ta yi tare da ɗurƙusawa ta sanya wa Safeera hijabin a jikin ta".


Miƙe wa ta yi tsaye sannan ta ce. "Yanzu me ya rage, maza ku shirya mu tafi".



Kallonta Aliyu ya yi ya ce. "Ai kuma bamu haɗa kayayyakin da zamu tafi Nigeria da su ba". 



Kallonsa Daddy ya yi ya ce. "Kada ka damu da wannan zan saka ƴan aiki na su aiko mana su". 


"Amma ka san da cewa bamu da visa, kuma kuɗaɗe basua aiki a wannan ƙasar domin idan ka ce za ka basu kuɗi za su kama mutum ne, sannan kuma ta ya ya zamu je filin jirgi da ita a haka?, domin fa kwata-kwata ba ta numfashi, ba kayi tunanin cewa ƴan sanda za su yi zargin cewa ko sace ta muka yi. Yanzu dai dole ne muna iya ba da shaida takardun aure, takaddun Haihuwar Ma'aurata da masu dogara, hotunan da ke nuna kyakkyawar alaƙa da dangi da abokai". Cewar Aliyu.



Kallon Daddy Mom ta yi sannan ta ce. "Yanzu mene ne abin yi?". Ta tambayi Daddy.



Amsa Daddy ya ba ta da cewa. "Ina da aboki ɗan sanda a chan airport sannan kuma ina da wani ma wanda na san idan na roƙe shi zai bamu visa tun da gaba ɗaya muna da password. Yanzu kawai abin da zamu yi muje chan ɗin, na san da cewa idan suka ganta za su gane ta domin sun san ta sosai ko a cikin office ɗina suna zuwa su ga photon ta a ajiye kan table, so za su gane 

cewar ƴata ce".



"Tom shi ke nen, yanzu waye zai ɗauke ta?". Mom ta tambaya. 



Amsa Aliyu ya bata da cewa. "Kada ki damu, ni zan ɗauke ta". Yana kaiwa nan ya shiga cikin room ɗin sa. Saida ya ɗau kusan rabin hour bai fito ba, sannan daga bisani ya fito cikin ƙananun kaya wanda suka yi matuƙar karɓar jikin sa. Nufar in da suke ya yi sannan ya sa hannu tare da ɗaukar Safeera sannan ya yi hanyar waje da ita.



Ganin hakan ya sa su Daddy suka mara masa baya bayan sun ɗauki muƙulli.



Kai tsaye in da motocin gidan suke Aliyu ya nufa. Danna muƙullin motan Daddy ya yi. Nan take motar ta buɗe da kanta. 



Ganin hakan ya sa Aliyu saka Safeera cikin motan yayin da gaba ɗaya su Daddy suma suka shiga cikin motar. Tada motar Aliyu ya yi. Yayin da gate man ya buɗe musi ƙofa daga bisani suka fice daga cikin gidan baki ɗaya.


Basu nufi ko ina ba sai hanyar airport.




************************

 *Nigeria*


"Mene ne ka aikata haka officer?, me ya sa za ka harbi yarinyar nan bayan da cewa Gov. Musa Muhammad ya ce baya son ɗansa ya san da cewa munzo mun kori dabbobin da ke cikin daji nan".



Officer da haka faɗa wa hakan ya ce. "To baka ga yadda take tsalle kan bishiyoyi ba kamar biri, na san ba zamu iya kamata ba idan muka ce zamu kamata za ta illatar da mu ne. Bani da wani zaɓin ne shi ya sa na harbe ta a ƙafa".



"Wannan laifin ka ne, yanzu idan Sir Umar ya sani na san tamu ta ƙare". 



Wayarsa ya ji tana ringing. Ɗauko wayar ya yi daga cikin aljihun sa sannan ya ɗaga kiran tare da karawa a kunnen sa ya ce. "Hello".



Daga ɗayan ɓangaren haka ce. "Maza-maza ka ce da sauran jami'an wajan nan su bar wajan, domin kuwa Sir Umar ya nufo hanyar wajan yanzu".



Zari ido jami'in ya yi tare da katse wayar sannan ya kalli sauran jami'an ya ce. "An kira yanzu an ce mu bar nan domin sir Umar yana tawo wa nan". 



Da sauri suka matsar da Amrah wanda ke yashe kafarta sai fidda jini yake gefe. Sannan cikin ƙware wa suka fara shiga cikin motocin. Tare da tada mota suka bar harabar wajan.



Bai ɗauki Umar lokaci ba ya ƙaraso wajan. Guri ya samu a cikin dajin sannan ya yi parking.


Fitowa ya yi ciki cikin izza. Sannan ya rufe ƙofar motan. Dafe zuciyarsa ya yi ciki ranshi ya ce. "ban san dalilin da ya sa zuciyata take ta buga wa da ƙarfi-ƙarfi ba, amma yanzu tun da na zo , na san hankali na zai kwanta". Ya faɗa tare da fara tafiya.



Sai da ya yi tafiya mai nisan gaske kafin ya isa wajan kogin dake cikin dajin. Tsayawa ya yi jin yadda dajin ya ɗauki shiru. Mamaki ne ya kama shi jin babu ko da kururwan wani dabba a cikin dajin sai dai tsuntsaye wanda suke ta kai kawo a sama.


Ƙatasawa in da kogin yake ya yi. Take idanuwansa ya sauka a kan dutsen da ke kusa da kogin. Daff da dutsen ya je ganin kamar abi rubuce a jiki. 



Durƙusawa ya yi tare da shafa sunan dake jikin dutsen ya yi. Murmushi ya yi sannan ya ce. "Kenen sunanta Amrah, nice name".



Miƙe wa ya yi tsaye sannan ya bar wajan. 


Tafiya ya soma yi yayin da ya fara arangama da dabbobin da ke yashe a ƙasa.



Mamaki ne ya kama shi ganin dabbobin da ke daji yashe a ƙasa cikin jini.



Daga nesa ya hangi Amrah dake kwance kusa da jikin bishiya. Zaro idanuwa ya yi waje yayin da ya tafi da gudu tare isa in da take.



Yana zuwa ya durƙusawa tare da aza kanta a kan cinyarsa. Tattaɓa fuskar ta ya soma yi. "Amrah me ya sa me ki?, wane ne ya yi miki haka?". Ɗaukar ta ya yi chakk tare da nufar in da motar shi yake da ita.




Saka ta ya yi cikin mota sannan shima ya shiga tare da tuƙa motan sannan ya bar harabar wajan.

 Kai tsaye asibiti ya nufa da Amrah.



****************

Ɓangaren su Zahra kuwa suna isa Kano basu nufi ko ina ba sai asibiti suka nufa. Nan take nurse's suka saka ta a gadon marasa lafiya tare da shigar da ita cikin ɗaki. Nan take suka fara mata aiki ta yadda numfashinta zai dawo. Saka mata oxygen suka yi tare da bata allura. 



Cikin ƙanƙanin lokaci numfashinta ya dawo. 

Allurar bacci suka bata tasha ta yi bacci. 



Fita likitocin suka yi suka bar Zahra kaɗai a ɗakin.

Miƙe wa DPO ya yi sannan ya dubi ɗaya daga cikin likitocin ya ce. "Me yake faruwa ne?, ya jikin nata?".



Amsa likitan ya ba shi da cewa. "Lafiya ƙalau munyi nasaran cetan ta domin kuwa yanzu harta samu bacci. Hamdala DPO ya yi sannan ya ce. "Yanzu zamu iya shiga mu ganta?".


"Eh za ku iya, amma dan Allah banda hayaniya". Yana kaiwa nan ya bar wajan.



Shiga ciki gaba ki ɗaya suka yi, yayin da suka tarar ba ta kan gadon. Zaro ido gaba ɗaya suka yi ganin ba ta kan gadon. Kallon jami'an DPO ya yi ya ce. "Me ya sa muka yi sakaci har ta fece daga nan".



Daga sana suka ji muryarta na cewa. "Yallaɓai DPO gani fa a ta nan". Zahra ta faɗa tana mai sakin murmushi.


Kallon ko ina suka yi basu ganta ba. Nan take suka maida kansu kan gado. 


Kallonta DPO ya yi ya ce. "Ta ya ya kuma ki ka dawo kan gado bayan bakya nan?".


Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Ta ya kuma, kune dai baku duba ba da kyau amma ni dai ina nan banje ko ina ba".



Ajiyan zuciya DPO ya sauke sannan ya ce. "Shi ke nen ta so mu ta fi tun da kin samu lafiya".



Murguɗa baki Zahra ta yi sannan ta ce. "Ku fita to zan yi wani abu".



Duk abin da za ki yi kiyi babu in da zamu je, wato so ki ke ki gudu ko?".



Haɗe rai Zahra ta yi ta ce. "Idan na gudu ina zanje?, wa na sani a wannan garin?, zan yi turoso ne shi ya sa".



"Shashasha kawai". DPO ya faɗa tare da fita daga cikin ɗakin. Fice wa sauran ƴan sandan suma suka yi daga cikin ɗakin.



Tsaki Zahra ta ja ta ce. "tsohon banza kawai, idan an girma a san an girma. Ya tsaya yana biye wa sa'anin ƴaƴan sa. Guduwa ce kuma ya zama dole, domin tabbas saina gudu, haka kurun za'a kaini wani gidan gyaran hali sai ka ce wacce take rashin ɗa'a".

 


Ta faɗa tana mai waige-waige. Nan take wani dabara ya faɗo mata. Tashi ta yi tsaye tare da nufar ƙofar window sannan ta buɗe tare da fita ta wajan.



"Yess". Ta faɗa cike da farin ciki". Sauri-sauri take domin ta fice daga cikin asibitin. Babu zato ta ji an rungumeta ta baya. 



Zaro ido waje ta yi tare da juyawa. Nan take gabanta ya yi mummunar faɗuwa?, yayin da zuciyarta ya fara dukan uku-uku. Take ta tsinci kanta cikin baƙon yanayi. 



Sakinta matar wacce ta yi burzuzu da gashin kanta tamkar mahaukaciya ta yi. Kallonta matar ta yi ta ce. "Ki fitar da ni daga nan ni ba mahaukaciya ba ce kinji, ina so na koma ga ahali na, ina son na ga yarana".



Nan take jikin Zahra ya yi sanyi dubar matar ta yi ta ce. "Kiyi haƙuri ki koma, magani suke miki fa". Ta faɗa tana mai ƙoƙarin barin wajan. 



Da sauri likitoci suka ƙaraso wajan suna mai rirriƙe matar. Kallon Zahra suka yi sannan suka ce kiyi tafiyar ki yarinya, ita ɗin mara lafiya ce, kada ki damu da duk abin da za ta faɗa miki".



Girgiza kai Zahra ta yi tare da fice wa daga cikin asibitin. Ta rasa me ya sa tun da ta ga wannan matar hankalinta ya kasa kwanciya. 



Zama ta yi a bakin titi tana mai hasko matar a cikin idanuwanta. "To wannan matar wace ce?". Ta tambayi kanta. Basar wa ta yi sannan ta ce. "To koma wace ce ina ruwanki zahra, kiyi abin da zai finshe ki kawai".



Dafe cikinta ta yi jin yadda yake murɗawa saboda yunwa. Daga nesa ta hangi shopping mall. Da sauri ta miƙe tsaye sannan ta ce. "Dole na je na ci wani abun don ba zan zauna da yunwa ba".


 

Ta faɗa tare da nufar wajan. Nan take ta ga fadawa da securities na fito wa daga cikin wajan. Yayin da ta ga mutanen wajan gaba ɗaya sun ɗuƙa ƙasa. 


Shiga cikin wajan ta yi yayin da ta ga kowa gwiwar sa a ƙasa. Sakin baki ta yi tana kallonsu. "To me ya mi waɗan nan mutanen kuma na ga kowa a durƙushe. Koda yake wannan ba damuwar ki ba ce ba". Ta faɗa tana mai ƙara shige wa cikin wajan.



Chan ta hangi ma'aikacin wajan a durƙushe a ƙasa. Ƙarasawa ta yi wajan sannan ta ce. "Ina son a bani snacks ko lemo duk abin da ku ke da shi wanda zai ƙosar da ni".



Alamu mutumin ya yi mata da ta yi shiru. Hangame baki Zahra ta yi ta ce. "Bangane ba, na ce ka zo ka saida min da abu ka ce nay shiru, saboda me?, ko kyauta ku ke bayar da kayan naku ne?". Ta faɗa cikin ɗaga murya.




Daga sama ta ji an ce. "Wane ne yake mana wannan tsawan?". Nan take mutanen wajan suka sha jinin jikin su.



Juyawa ta yi da zimmar zuwa ta ɗauki abin da ranta yake so. Nan take idanuwanta ya sauka kan wani handsome mature guy mai jini a jiƙa.



Kallonta ya yi da idanuwansa masu matuƙar rikitarwa sannan ya ce. "Me ya sa ke baki tsungunna ba bayan kowa dake cikin nan ya durƙusa min, kin san wane ne ni?".



Sakin baki Zahra ta yi tana mai bin shi da kallon rainin wayo. Kallon sama da ƙasa ta yi mishi sannan ta ce. "First of all matsa min daga hanya". Ta faɗa ranta a matuƙar ɓace.



Ƙara tunkaro in da take ya yi sannan ya ce. "Idan na ƙi fa?, kin san waye ni? , ni ɗin yarima ne understood?".



Dariya Zahra ta kwashe da shi sannan ta ce"au haba da gaske?, amma sam baka yi zubin ƴan sarauta ba, ka san da irin su wa ka ke kama a jigawa?, kana kama ne da ƴan daƙo, domin kuwa wannan kayan da ke sanye a jikin ka su ƴan daƙon jigawa suke sawa".

Ta faɗa tana mai kuma fashe wa da dariya a karo na biyu. 



A fusa ce. "Yariman ya ce. "Za ki san ni ki ka gaya wa wannan maganar".



Nan take yanayin Zahra suka sauya izuwa ɓacin rai sannan ta dube su baki ɗaya ta ce. "Idan kun isa ku tunkaro in da nake".



**************************

Umar na isa asibiti, likitoci suka saka Amrah kan gado yayin da suka shiga yi mata aiki domin cire bullet ɗin da ke ƙafarta.


Fita ya yi tare da koma wa cikin mota sannan ya nufi hanyar gida. Da mugun gudu yake tuƙa motan yayin da yake ji kamar ya tashi sama domin zuwa in da mahaifinsa yake. Mintuna ƙalilan ya yi masa a gida. Ko gama parking bai yi ba ya fito daga cikin motan tare da nufar hanyar gida. Ƙafar sa na dama ya sa tare da ɓalla ƙofar parlourn.



Nan take mahaifinsa tare da jami'an dake cikin wajan suka miƙe tsaye.



Kallonsu gaba ɗaya Umar ya yi sannan ya ce. "Me ya sa ku ka je ku ka kashe kowane halitta a cikin wannan dajin?, ba na ce bana buƙatar wajan nan ba?, to me ya sa za ku kuma koma wa wajan?, why Abba?".



Ajiyan zuciya Gov. Musa Muhammad ya sauke sannan ya ce. "Nayi hakan ne saboda farin cikin ka son".



Girgiza kai Umar ya yi ya ce. "Farin ciki na?, kayi hakan ne saboda farin cikin ɗanka, baka ji kunyar abin da ya fito daga bakin ka ba, ka tsayar da fari cikin wasu domin samar min da gurɓatacciyar fari ciki mara ɗore wa, kuma a hakan ka ke kiran kanka ɗan siyasa?, shin dama haka shugabanni suke wa waɗan da basu ji ba basu gani ba?".



"To gaba ɗaya ku saurare ni kuji, muddin wannan yarinyar ta mutu ba zan ƙyale kowane mutum daga cikin ku ba hatta kai Abba, kuma sannan wannan farin cikin da ka ke faɗa to za ka rasa shi na har abada ne, domin kuwa ba za ka sake sanya idanuwanka a kaina ba".




"A'a Umar, kada ka yi haka, in sha Allahu babu abin da zai same ta kaji, kada ka nesanta kanka da ni Please".



Murmushi wanda ya fi kuka ciwo Umar ya yi sannan ya ce. "Saboda gudun abin da zai bata min rai hakan ya sa na koma london da zama, kuma duk saboda kai, me ya sa ka ke ƙoƙarin cusa min tsanar ka a cikin zuciyata Abba?. To zan faɗa zan ƙara maimaita wa muddin yarinyar chan ta mutu saikun gane kuranku baki ɗaya. Kuma sannan shi companin ma bana da buƙata, domin bana son koda naira goma daga cikin dukiyar ka, bana so".



Yana kaiwa nan ya fice daga cikin ɗakin. 



Kallon jami'an Gov. Musa Muhammad ya yi sannan ya ce. "Shashashan banza ku sani cewa muddin ɗana ya yi nesa da ni saina ga bayan ku, maza ku ɓace min daga gani".



Fita jami'an gaba ɗaya suka yi. Wayarsa ya ji tana ringing.



Ɗaukar wayar ya yi yayin da ya ga private number bayyane kan screen ɗin. Ɗaga kiran ya yi tare da karawa a kunnensa.



Daga ɗayan ɓangare haka ce. "Barkan ka dai govnor Musa Muhammad. Na san za ka yi mamaki to ni ne, ban mutu ba ina raye. Na kira ka ne domin sanar maka da bad news a gare ka, mrs Laila wacce kayi sanadin rugujewar rayuwarta har izuwa yanzu tana raye".



Zumbur gov. Musa Muhammad ya miƙe tsaye. Yayin da zufa ya fara ƙeto masa ta kowane sashi na jikinsa. Duda iskan AC da ke kaɗawa a cikin parlourn hakan bai hana shi yin zufa ba.



Cikin rawar jiki Gov. Musa Muhammad ya ce. "Waye kai?".


Amsa mutumin ya ba shi da cewa. "Ni ne ɗan sanda wanda ku ka saka haka rufe tsawon shekaru, ni ne MK wato Mubarak. Ka ɗauka ban san duk wani shirin ka ba?, na san da cewa ka aiki ɗaya daga cikin masu ta ya ka aikata miyagun laifuka domin ya yi magana da ni a cikin magarƙama domin neman in da yarinyar Mrs Laila take. Amma sai dai kafin ya zo waje na wata ta dakatar da shi. Ka san wace ce?, to ƴar Mrs Laila ce".



Jiki na rawa Gov. Musa Muhammad ya ce. "Tana ina?, ina da buƙatar thumbprint ɗin ta domin buɗe wannan ma'ajiyarta, ka gaya min in da ƴar tata take".




Murmushi MK ya yi sannan ya ce. "Idan na gaya maka, saka wa za ka yi a kamata?, daga nan kuma fa?, ka saka yaranka su kashe ta?, ko da yake safara mata ita ce aikin ka ko?. To ka sani cewa ƙarshen ka ya kusan zuwa, domin kuwa ba yarinya ɗaya Laila Abdullahi ta haifa ba, su uku ne, blue, green and brown, ƴan uku daga gurare da ban- da ban . Su ne za su yi nasarar kawo ƙarshen ka sannan su wanke mahaifiyarsu daga zargin da kotu da jama'ar gari keyi mata. Sannan kuma su ja ka a kan titi, kamar yadda ka sanya ta gudu a kan titi, haka suma yaranta za su saka ka kayi gudu a titi yayin da jama'a za su yi ta jifar ka da duwatsuna, kana ihuuu kana neman taimako, amma babu wanda zai zo domin ya agaza maka. Ka jira ka gani, domin kuwa ranar tana nan zuwa. Saina tabbatar da ka gurbi abin da ka shuka. Ƴar daji, ƴar magarƙama, da kuma ƴar birni. Gaba ɗaya suna nan zuwa domin ɗaukar fansar abin da ka aikata wa mahaifiyarsu, ka jira ka ga sakamakon abin da ka aikata".







💃💃💃💃💃💃💃💃

*HANA WATA GA WAYA*. *WAI SHIN DAMA MRS LAILA BA TA MUTU BA TANA RAYE?, KENEN ƊAN SANDAN DA YA CECI MRS LAILA NA RAYE?, MENE NE HAƊIN MAHAIFIN UMAR DA MRS LAILA?, MUJE DAI ZUWA DOMIN JIN YACCE ZATA KAYA*


*KADA KU MANTA DA LIKING, COMMENTS, DA KUMA SHARING*💃💃🥰🥰🥰😍.




ALƘALAMIN ✍️

A'ISHA M.B 💞💞💞

(ZINARIYA JAJIRTATTU)