KUNDIN CINIKAYYA BY A'ISHA M.B
37&38
by @aishamb
Follow the 🌺🌎A'ISHA M.B🌹 HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: ***
*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Thre siblings from different part of the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️
WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)
***
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
(We stand together)
🤝🤝🤝
بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!
*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 3️⃣7️⃣▶️3️⃣8️⃣
*___________________________________________*
Jiki a muce Zahra ta ɗauki kayan da ta zube a ƙasa sannan ta fara ƙoƙarin wuce wa ta gefen Sooraj, a sa'inda zuciyarta ke dukan uku-uku!.
Daga sama ta ji muryarsa. "Dakata!". Ta ji Sooraj ya furta.
Tsaya wa chak Zahra ta yi yayin da ta kasa motsa ko da ɗan yatsarta ne saboda tsananin tsoron da ta shiga.
Zagayowa Yarima Sooraj ya yi har gabanta sannan ya tsaya yana mai fuskantar ta. Yayin da ɓangaren guda idanuwan jama'a a kansu.
Ƙura mata idanuwansa ya yi masu matuƙar ɗaukar hankali sannan ya ce. "wace ce ke?".
Jin tambayar da ya yi mata, hakan ya sa Zahra ta bashi amsa da cewa. "Ni mutum ce mana".
Kallonta ya yi cike da mamaki ganin yadda babu wata alama na nuna jin tsoronsa a tattare da ita, hakan ya ƙara bashi aushi. "Ke haka na ce wace ce ke, me ya kawo ki wannan masarautar?, sannan daga ina ki ka fito?, da me ki ke takama?, sannan tambaya ta ƙarshen ta ya ya ki ka iya buɗe ɗakin ajiyana bayan ni kaɗai ne na san maƙullin sirrin buɗe wannan ɗakin?".
Zololo Zahra ta yi tana kallon shi. "Kai kuwa Yarima irin wannan tambayoyi haka sai ka ce google ake tambaya, ai sai kayi min tambayar ɗaya bayan ɗaya. To farko dai ni sunana Fatima ana kira na da Zahra, na rasa mahaifiya ta ne tun kafin na san ciwon kaina, yanzu haka bani da kowa sai iya Aunty Binta wacce ke kula da ni. Sannan batun me ya kawo ni masarautar nan babu ita domin ba ni ce na kawo kaina ba Mami ce ta buƙaci na zo nayi aiki domin tara kuɗin motan da zan koma garin mu Jigawa. Sannan ka ce da me nake takama, to ni dai babu wanda nake takama da shi sai mahallici na bayan shi kuma babu, sannan sanin ta yadda na iya buɗe wannan ɗakin abu mai sauƙi ne domin wani suna kawai na danna ya buɗe, shi ke nen".
Ajiyan zuciya Sooraj ya sauke!, sannan ya ce. "Har yanzu baki bani amsa gamsashiya ba. zan ƙara tambayar ki a karo na uku ko. Wace ce ke?".
Furzar da iska mai zafi Zahra ta yi kana ta ce. "Kamar yadda na faɗa maka tun fari, sunana Zahra, ni ɗin na taso ni cikin magarƙama tsakiyar masu laifi, hatta daga yin wayo na har izuwa girma na a magarƙama nayi".
Zaro idanuwa waje gaba ki ɗaya al'ummar masarautar suka yi.
Murmushi Sooraj ya yi sannan ya ce. "Kenen dai ke ɗin babbar mai laifi ce ko?".
Sauke ajiyan zuciya Zahra ta yi!, sannan ta ce. "A'a, mahaifiyata ce haka yi mata sharri shi ne aka kaita magarƙama bayan ta haife ni ne ta rasu, kuma ƴan uwanta suka ƙi ƙarɓa ta shi ne Hajiya Binta ta raine ni". Ta ƙarashe maganar zuciyarta nayi mata zafi da ƙuna.
Murmushin mugunta Sooraj ya saki kana ya ce. "Kenen dai mamarki ita ce muguwa ko?, ita ce babbar mai laifi har aka kaita magarƙama. Ai dole ma ƴan uwanta su yi rejecting ɗin ki saboda kar su zo suna dana sanin karɓar ki, sai kuma gashi kema kin yo halin uwar taki".
Danne fushin da ke ƙoƙarin bayyana kan fuskar ta Zahra ta yi tare da kawar da kanta gefe sannan ta ce. "Yarima ka san me za ka faɗa dan Allah, ka iya sarrafa harshen ka".
"Ba zan sarrafa harshen nawa ba". Sooraj ya faɗa a matuƙar tsawa ce.
Nuna Zahra ta yi da yatsarsa sannan ya ce. "Na tabbatar da cewa ke ƴar leƙen asiri ce, kuma idan ki ka kuskure na gano ko asalin wace ce ke to ba za ki sha ba". Yana kaiwa nan ya shige cikin fada sannan ya nufi part ɗin ta.
Sallamar kowa Junaid ya yi, yayin da jama'a suka watse saura mutanen cikin masarautar.
Kallon Zahra Mami ta yi sannan ta ce. "Zahra tawo mu shiga daga ciki".
Murmushi wanda ya fi kuka ciwo Zahra ta yi ta ce. "Wallahi Mami nayi duba da irin mutunci da kuma kima da ki ke da shi ne a waje na. Hakan ya sa na rabu da yarima Sooraj, amma da ba dan haka ba wallahi sai ya san cewa Allah ɗaya ne, ba zan ji daɗin a zagar wa wani mahaifiyarsa ba, haka zalika nima ba zan ji daɗin a zagar min tawa mahaifiyar ba, da ka zagin uwa ta na gwammace ka kwana kana zagi na".
Tana kaiwa nan ta shige cikin fadan sannan ta shiga ɗakin kwanan ta wanda haka ware mata a matsayin ƴar aiki.
Kallon Juna Gimbiya Saratu da Talatu suka yi tare da bushe wa da dariya yayin da suka riƙe hannun juna sannan suka shige part ɗin su.
Girgiza kai kawai Mami ta yi sannan ta ce. "Allah ya ganar da ku gaskiya". Ta faɗa tare da shige wa part ɗin ta.
Rakiya Junaid ya yi wa mai martaba izuwa fadar sa. Gaba ɗaya gidan ya koma kaman gidan makoki. Babu wani hayaniya ko surutu. Abincin ma da aka jera kan dining babu wanda ya bi ta kansu.
Zahra na shiga ɗaki kuwa ta kwanta kan gado. Yayin da fuskar Sooraj ya fara yi mata gizo. Lokaci ɗaya ta ji tsanar sa ya mamaye zuciyar ta. "Aikin banza kawai, dan kawai yana matsayin ɗan gidan sarauta shi ne zai zo ya dinga raina wa mutane hankali, ni Allah ya bani kuɗi ma ni na haɗa kuɗin mota na tafi, na san kuɗin motan ba za ta wuce dubu biyu zuwa dubu uku ba". Dafa cikinta ta yi jin yadda yake murɗa mata alamun yunwa take ji.
"Kambala'i, ashe fa ban ci abincin safe ba na fita, chab Zahra me ki ke jira maza-maza tashi kije ki cika cikin ki". Ta faɗa tana mai miƙe wa tsaye sannan ta nufo hanyar ƙofar ɗakinta ta murɗa handle ɗin ƙofar ta fita.
_________________________
"Dan Allah Amrah ki nutsu, ko daina kuka kinji, munyi miki alƙawarin duk in da ƴan uwanki suke zamu kai ki wajan su". Ramlat ta faɗa damuwa bayyane kan fuskarta.
Girgiza kai Amrah ta yi cikin ƙaramin muryarta ta ce. "Ni A'a, ku maida ni inda ku ka ɗauko ni, ina son ganin ƴan uwana". Ta ƙarashe maganar tana mai rushe wa da kuka.
Dai-dai lokacin Umar ke ƙaraso wa wajan. Su Khairiya kuwa, ganin Umar ya ƙaraso ya sa su sakin ajiyan zuciya sannan suka ce. "Yauwa yahya barka da dawo wa, ka ga Amrah tun ɗazu take kuka wai ita a mayar da ita in da aka ɗauko ta".
Furzar da iska Umar ya yi waje sannan ya nufi in da Amrah take zaune karƙashin bishiya ta yi ruff da ciki. Ƙarasawa ya yi wajan da take sannan ya dube ta ya ce. "Amrah, me ki ke so?".
Ɗago da rinannun idanuwanta Amrah ta yi ta ce. "Ina son ganin ƴan uwa na".
Kallonta Umar ya yi a karo na biyu ya ce. "Shi ke nen, idan ki ka ga ƴan uwan naki komai zai dawo dai-dai?".
Girgiza kai Amrah ta yi alamun eh.
Miƙe wa tsaye Umar ya yi ya ce. "Shi ke nen, zamu kaiki wajan na su".
Kallon Umar Usman ya yi ya ce. "Yahya me ka ke cewa haka?, ta ina zamu samo su?, basun riga sun mut......
"Shshiiiiiii!". Umar ya yi alama da hannu da ya yi shiru.
Shiru Usman ya yi yana mai jiran furucin da zai fito da baki yayan nasa.
Kallon Umar Khairiya ta yi ta ce. "To yahya a ina za'a samo su?".
Amsa Umar ya ba ta da cewa. "Wallahi nima ban sani ba, lokacin da Abba ya je ya saka mutanen sa suka je suna kashe dabbobin dajin ban sani ba sai daga baya naje na tarar da sun kashe duk dabbobin dajin. Ni yanzu ban san ya zan yi ba".
Kallon su Ramlat ta yi ta ce. "Yahya ina da shawara".
"Mene ne?". Suka furta a tare.
"Ku matso ku ji". Ramlat ta faɗa. Matso wa suka yi kusa da ita tare da kasa kunnen su in da take.
Shiru ta yi kana daga bisani ta ce. "Me zai ana muje gidan Zoo na san dai akwai dabbobi a chan, mybe idan muka kaita ta ga dabbobin cikin wajan za ta yi farin ciki. Amma ya ku ka gani?".
Murmushi Khairiya ta yi ta ce. "Wow wannan shawara ce mai matuƙar kyau".
Shiru Umar ya yi na ɗan wasu lokaci sannan ya ce. "Kuma ganin wannan shawarar za ta yi aiki kuwa?".
"Me zai ana?, zai yi aiki mana, suma ai dabbobi ne a chan na san idan ta gansu za ta yi farin ciki".
Cewar Usman. Sannan ya ƙara da cewa. "Amma kamar babu gidan zoo a nan dutse ko?, ni dai ban sani ba ko akwai ko babu".
Kallonsa Umar ya yi ya ce. "Ko akwai ma, ba na wannan zamu je ba, ina son muje Kano daga nan zan yi bincike na a kan wanda nake nema mai safaran miyagun hayyuka".
"Shi ke nen bara muje mu haɗa wasu kayan mu da wanda Amrah za ta saka". Khairiya ta faɗa suna mai shige wa ciki. Lokaci ƙalilan ya ɗauke su suka gama shirya wa sannan Umar ya kalli Amrah ya ce .
"Tashi muje zamu kaiki in da ƴan uwanki suke". Jin abin da Umar ya faɗa, hakan ya sa Amrah saurin miƙe wa tare da sakin murmushi. Juyawa suka yi gaba ɗaya suka nufi wajan parking space, ganin hakan ya sa Amrah ta yi saurin bin bayansu. Shiga cikin motan ɗaya Usman da su Khairiya yayin da Usman ya tada mota, tare da fice wa daga gidan. Buɗe wa Amrah ƙofa Umar ya yi ta shiga sannan ya sauke mata glass ɗin motan ƙasa. Sannan ya tada motan tare da barin harabar gidan.
Daga bisani suka nufi hanyar garin Kano.
*To kafin mu cigaba dai muna son sani wane ne asalin Umar? sanann wane ne asalin gov. Musa Muhammad*.
Alhaji Muhammad shi ne asalin mahaifin Musa Muhammad. Alhaji Muhammad ya kasance mutum tawakali da kuma sanin ya kamata, ya kasance mutum bai bin ƙa'ida. Matar sa Halima ta rasu ne a lokacin da take naƙudan ƴar su ta biyu wacce ta ci suna A'isha. Musa ya kasance ɗa na fari a wajan mahaifin sa sai kuma A'isha. Musa ya taso tun yana ƙarami da burin zama ɗan siyasa domin shi gaba ɗaya a tunanin shi babu komai a cikin yin harkar siyasa sai kuɗi. Hakan ya sa ya ƙudiri niyar zama ɗan siyasa. Alhaji Muhammad ya tura musa karatu domin ya yi karatun Engineering, sai dai kuma abin da bai sani ba shi ne Musa ya chanza course ɗin da mahaifin nasa ya zaɓa masa izuwa Political science. Musa ya gama diploma sa ne yana da shekaru talatin shif. A wannan lokacin A'isha ta kammala HND ɗin ta. yayin da ta fito da wanda take so wato ɗan sarkin garin Kano. Bayan an ɗaura musu aure shima Musa ya auri matarsa Khadija wanda suka haɗu da ita a University ɗin da ya yi.
Haka ya cigaba da sha'awar zama ɗan siyasa ba tare da mahaifin ko matar sa ta sani ba.
Khadija ta kasance mace mai riƙo da addini, tana ƙoƙarin gujewa duk abin da zai ɓata wa mijin ta rai. Bayan shekara ɗaya ta haifo santalelen ɗanta wanda ya ci suna Umar.
Farin ciki wajan waɗan nan ma'auratan ba zai misaltu ba.
Ana tsaka da aka, Musa ya je ya bayyana wa mahaifin sa abin da ya karanta a jami'a. Hakan ya sa ran mahaifin sa ya yi matuƙar ɓaci. Yayin da mahaifin sa ya ƙudiri niyar cewa muddin yana da rai ba zai bari ya zama ɗan siyasa ba. Jin furucin da ya fito daga bakin mahaifin nasa ya sa Musa ya tunzura sannan ya yi tafiyarsa sai bayan wasu lokaci ya dawo wajan mahaifin sa, sai dai a wannan karan bai dawo domin neman yafiyar mahaifin sa ba, ya dawi ne domin ya ɗauki ran mahaifin sa.
Bayan isarsa chan ne ya tara ƴan daba suka zagaye gidan a yayin da ya sa a ɗaukar masa video ta yadda zai kashe mahaifin na shi. Alhaji Muhammad na kwance cikin jinya da tsananin ciwo Musa ya shiga ɗakin nasa. Ganin yana kwance ya sa shi sakin murmushi ba tare da imani ko tausayawa ba ya samu pillow ya danne fuskar mahaifin nasa da shi. Haka Alhaji Muhammad ya dinga kuruwa har rai ya fita daga jikin shi. Musa bai sake shi ba saida ya tabbatar da baya da sauran numfashi. Hakan ya sa shi farin ciki a sa'inda ya dinga ganin kansa matsayin govnor domin kuwa tunda mahaifin nasa ya mutu babu wanda zai ana shi zama govnor.
Jama'a sun yi kuka na rashin Alhaji Muhammad da suka yi, yayin da ita ma Khadija ta ci kukan ta har ta gode wa Allah.
Musa ya fara neman takara shida babban Abokin sa wato Abdullahi wanda suka taso tun suna ƙanana har izuwa girmansu tare suke. Hakan ya sa kowanensu yake da burin zama ɗan siyasa. amma sai dai shi musa bai yi nasara ba domin babu wanda ya karɓe sa hannu biyu. A yayin da Abdullahi ya zama babban ɗan siyasa ya yi alƙawarin gyara ƙasar sa da mutanen cikin ta. Musa ya ji aushi sosai ganin abokin saya samu takara shi bai samu ba, hakan ya sa ya ɗora tsanar duniya a kan abokin nasa, a yayin da yake zuwa wajan Abdullahi da fuska biyu na kirki da kuma na mugunta.
Umar yana da shekaru biyar a duniya Khadija ta kuma haifo santalelen ɗanta saidai yaron bai zo da rai ba. Bayan wasu shekaru Khadija ta sake haifo namiji wanda ya ci suna Usman, Sannan Ramlat sai kuma ta ƙarshe Khairiya wanda su ukun gaba ɗaya shekara ɗaɗɗaya ne a tsakani.
Haka rayuwa ta cigaba wataran da dad'i wataran kuma godiyar Allah. Ana tsaka da haka wata rana Khadija na gyara ɗakin Mijin ta, nan ta tarar da wani caset. Ɗaukar caset ɗin ta yi sannan zuciyar ta tace da ita ta saka caset ɗin a tv ta ga ko film ne. Bayan ta saka caset ɗin ne a tv ta ga abin da ya yi matuƙar firgita tunaninta. Mijinta ta gani ya kashe mahaifin sa da hannunsa . Hakan ya sa ta ji dana sanin auran sa. A dai-dai wannan lokacin kuma Musa ya shigo ya tarar da ita a ɗakin tana kuka. Nan dai ya gano cewa ta gano shi ne wanda ya kashe mahaifin sa. Ganin hakan ya sa Musa ya fara roƙon matar sa da ta rufa masa asiri. Amma ita kuma Khadija taƙi amincewa sannan ta ce dole ta sanar da ƴan sanda ko wane ne mijinta domin ba za ta iya take gaskiya ba. Ganin dai taƙi bashi haɗin kai ne ya sa ya ɗauki glass cup sannan ya rotsa wa kanta. Nan take kanta ya fara fidda jini yayin da ta faɗi ƙasa mutacciya. A dai-dai wannan lokacin Umar ya dawo daga makaranta sannan ya shiga cikin ɗakin nan ya tarar da gawar mahaifiyarsa a kwance. Hakan ya sashi sakin ƙara yayin da ya faɗi ƙasa sumamme.
Ganin hakan ya sa Musa ya goge kowane sheda da ƴan sanda za su bi domin gano makashin.
Bayan nan ne ƴan sanda suka zo suka yi ƙaraci binciken su basu samu komai ba. Hakan ya sa haka rufe case ɗin.
Bayan wasu kwanaki ne Umar ya dawo cikin hayyacinsa a yayin da yake mafarkin mahaifiyar sa sannan ya ƙudiri niyar dole ya zamo jami'i, domin ya san wanda ya kashe mahaifiyar sa sannan kuma ya kare ƙasar sa daga sheɗanun mutane irin mahaifinsa. Umar ya fara jin tsanar mahaifinsa ne tun lokacin ya ga mahaifin sa da wasu karuwai a gidan su. Daga wannan rana Umar ya tsani mahaifin sa.
Bayan Umar ya yi karatun sa na boko da na addini ne ya shiga training school na jami'ai. Hakan ya sa ya fara gudanar da al'amuran sa shi ɗaya. A sa'inda duk abin da ƙanensa suke da buƙata shi yake musu. Kan kace me Umar ya zama babban jami'i wanda gaba ɗaya ƙasa ke magana kan ƙwarewarsa domin kuwa duk wani mai laifi idan ya yi musu wahalan kama wa Umar shi ne wanda ake bawa wannan aikin kuma duk in da wannan mai laifi yake zai nemo shi sannan ya tabbatar da an hukunta shi. Aka ya cigaba da bincike domin gano makashin mahaifiyar sa, sai dai har izuwa wannan lokacin bai gano ko wane ne ba kuma bai san irin aikin mahaifin sa ba.
A ɓangare guda kuma shima Musa ya zama ɗan siyasa ba tare da an san ta wace hanya ya bi ya samu wannan takara ba.
*Amma idan ta yi tsami zamu ji ta yadda ya samu takara shiga siyasa*
Haka su Khairiya suma suka taso cike da ƙaunar juna. Yanzu dai Usman ya gama karatun sa yana aiki a office. Sai kuma Ramlat wacce ke University level 300 tana karatun Optometrist. Da kuma Khairiya wacce ke 100 level tana karatun biology.
*Wannan dai shi ne takamaiman tarihin Umar*
___________________
Shigowa da motoci masu tsaron govnor Musa suka yi. Fitowa Gov. Musa ya yi daga cikin mota ganin babu motoci guda biyu a gidan hakan ya nuna masa alamun cewa tabbas Umar ya fita.
Kallon masu tsaron gidan ya yi ya ce. "Where's Umar?".
Amsa ɗaya daga cikin masu gadin ya bashi da cewa. "Yanzu suka fita".
Girgiza kai Gov. Musa ya yi ya ce. "Kun san in da suka je?".
Amsa suka ba shi da cewa. "A'a, amma mun ji kamar suna zancen za su je Kano".
"Kano!". Gov. Musa ya maimaita sunan. "Shi ke nen". Kawai ya ce sannan ya shiga part ɗin shi. Yana shiga ya yi saurin ɗaukar wayarsa sannan ya lalubo number Aliyu tare da danna mai kira.
______
Aliyu da ke zaune sai faman kallon Safira yake yana murmushi ne ya ji wayar sa na ruri. Maida kallonsa ya yi kan wayar. Ganin sunan wanda ke bayyane kan screen ɗin ne ya sa shi miƙe wa sannan ya bar cikin parlour ɗin daba bisani ya ɗaga kiran. Ya ce. "Salamu alaikum".
Daga ɗayan ɓangaren Gov. Musa ya amsa sallamar sannan ya ce. "Aliyu ina da buƙatar taimakon ka yanzu dan Allah, ɗa na da ƙannensa su tafi hanyar Kano, yanzu haka na san sun kusa isa chan, ina son ka bibiyar mun su bana son ya gano gaskiyar ko ni wane ne, sannan kuma bayan nan akwai yarinyar Mrs Laila a Kano ina son ka bincika min duk in da take ka sa a sace ta. Dan Allah ba dan ni ba Please, zan tura maka duk kuɗin da ka ke da buƙata".
Ɗan jimm Aliyu ya yi sannan ya ce. "Shi ke nen naji, million goma shi ne kuɗin aiki na, kuma cash nake so ba transfer ba".
"Shi ke nen Aliyu, ni zan ma ƙara maka ya zama twenty ni dai kawai buri na shi ne ka dakatar da su sannan ka nemo in da yarinyar Lailah take".
"Kada ka samu damuwa wannan abu ne mai sauƙi, nan da sati ɗaya zan nemo duk in da take, kai dai kawai ka shirya min kuɗaɗe na". Cewar Aliyu.
"Angama". Gov. Musa ya faɗa tare da katse wayar yana mai maida numfashi.
Sauke ajiyan zuciya Aliyu ya yi sannan ya shiga ɗakin sa tare da haɗa kayan sa cikin travel box. Bayan ya gama saka kayansa ne ya nufi ɗakin su Grandpa sannan ya sanar da su yana son yin tafiya sainan da sati zai dawo. Addu'a suka yi mai. Daga bisani ya saka kayansa cikin mota. Babu abin da Safira kai ta faman yi sai satar kallonsa.
Babu zato suka haɗa ido da Safira, saurin kawar da kanta Safira ta yi gefe. Murmushi Aliyu ya yi ya ce. "Kodai za ki je ne?".
Taɓe baki Safira ta y ta ce. "Nop, ni kam babu in da zani". Ta faɗa tare da shige wa ciki gidan.
Girgiza kai kawai Aliyu ya yi tare da tada mota sannan suka yi sallama da mutanen gidan gaba ɗaya daga bisani ya fice daga gidan. Bai zarce ko ina ba sai hanyar Kano.
_________________________
Zahra na fita ta hangi kuloli a jere kan dining hakan ya sa ta haɗiye yawu. Da sauri ta je ta zauna kan table ganin zaman kujera ba zai finshe ta ba, ya sa ta kwashe gaba daya kulolin ta jera a ƙasa sannan ta zauna a ƙasa ta fara buɗe kulolin. Take wani irin ƙamshi ya bugi hancin ta hakan ya sa lumshe idanuwanta sannan ta sake buɗe su. Tuwon shinkafa ne miyan taushe ya ji naman turkey yayin da bangare ɗaya kuma fried rice ne ya ji coslow da naman kaza. Sai ɓangare ɗaya kuma kunun aya cikin jug da kuma lemo mai sanyi tare da Fruit salad.
Ganin ba za ta iya ɗauke ido kan wannan abinci ba, ya sa ta cire duka chokulan kan trey ɗin abincin ta zubar a ƙasa. Hakan ya sa ƙaran chokulan suka bada wani irin ƙara.
Jin ƙara daga parlour ya sa su Gimbiya Saratu da Talatu tare da ƴaƴanta fitowa. Yayin da ita ma a dai-dai lokacin Mami ta fito daga cikin ɗakin ta domin ganin meke faruwa. Dai-dai lokacin kuma Junaid ke dawo wa daga fadan mai martaba.
Fitowa Sooraj ya yi daga cikin ɗakin sa. Tare da nufar hanyar parlour. Tsaya wa chakk gaba ɗaya suka yi ganin yadda Zahra ke ɗura wa ciki ta abinci. Cin abinci ta take hankali kwance ba tare da tsoro ko wani tunani ba. Sai loma take ta kwara abincin da lemo tare da kunjn aya. Haka ta cigaba da cin abinta ba tare da ta kula da zuwansu Sooraj wajan ba.
Baki sake gaba ɗaya suke kallonta. Zahra kuwa sai da ta cinye Tuwon shinkafan tass sannan ta koma kan fried rice. Haka ta na ci tana sumbatu. "Wayyo dad'i kashe ni, da wahala gwanda dad'i ka kashe ni, dad'i kashe ni, da wahala gwanda dad'i ka kashe ni"
Sannan ta ƙara da cewa. "Gaskiya kuɗi duniya ne, Allah kayi mu yadda muke so. Yoo ƴan banza ba dole su dinga tumbi ba suna cin abinci mai daɗi da gina jiki. Daɗin ta ma ba za su ci ba, kinga kenen zanci sosai na ƙoshi, naci na ci na bar na bari. Shi ya sa wannan Gimbiya Talatun bakinta yake wangalele kamar na akuya tunda tana cin abinci mai daɗi dole, sai kuma waɗan nan ƙwalaye ukun nan su Samira ko, dole su dinga yadda suka gadama tun da suna cin kayan dad'i. Yanzu ni duk ba wannan ba hanyar da zanbi na koya wa wannan mai ƙaton kai hankali nake Sooraj yake ko, saina koya mai hankali, ba an ce ni ce zan dinga kula da shi ba, kawai idan Mami ta bani abinci shi na cinye sai in kai mai ragowa ya ci". Ta ƙarashe tana mai bushe wa da dariya.
Duk abin da take a gaban idanunsa. A sa'inda ɓangare ɗaya Gimbiya Talatu ta yi mugun ƙulu wa. Jin abin da Zahra ta faɗa game da halittar bakinta. Sooraj kuwa mamaki kawai ya shiga yi ganin yadda take ta sumbatu tana cin abinci duk ba ga san suna tsaye a wajan ba.
Saida ta gama da komai da cikin kulan tass sannan ta kora da kunun aya da fruit salad. Ji ta yi cikin ta ya yi mugum cika. Gatsa ta yi ta ce. "Ya kamata ki kwanta Zahra domin abincin da ki ka ci su zazzage". Ta faɗa tana mai kwanciya a ƙasan wajan tana mai fuskantar saman silin. Gabanta ne ya bada wani rass!, yayin da zuciyarta ya fara dukan uku-uku ganin gaba ki ɗaya ƴan gidan tsaye a kanta.
Zumbur ta miƙe tsaye tare da karkaɗe jikin ta.
Kallonta Sooraj ya yi tare da kallon kulolin da ta cinye abincin ciki sannan ya girgiza kai ya ce. "Sannunki da aiki, yanzu mutum in banda dabba waye zai iya cinye uban abincin nan, to ki sani cewa baki ci a banza ba domin kuwa sai kin koma kasuwa kim siyo duk abin da ki ka ci sannan kin sake dafa irin shi komai da komai".
Rai a ɓace Gimbiya Talatu ta ce. "In banda iskanci ƴar talakawa har ta samu matsayin da za ta ci abinci a kulan da muke cin abinci. Sannan kuma har ta samu damar ta ce wai ni mai wangalellen baki. Lallai kam wuyarki ya isa yanka".
"Madam za ki iya mana shiru a nan". Cewar Sooraj. Tsaki Gimbiya Talatu ta ja tare da wuce wa part ɗin ta ganin hakan ya sa Saratu ta bi bayanta. Sannan sauran ma suka watse ya rage Sooraj, Mami, da kuma Zahra.
Kallonsa Zahra ta yi bakin ta duk maiƙon kaza ta ce. "Yarima wallahi ban iya girki ba, ban taɓa yi ba, ta ya zan iya yin mai daɗin wannan?, kayi haƙuri dan Allah".
Gyara tsayuwar sa Sooraj ya yi ya ce. "My wish is my command, dole ki sake girka irin wannan kuma taste ɗin dole ya zama iri ɗaya.
Zaro idanuwa waje Zahra ta yi jin kalmarsa ta ƙarshe. "Ni na san ma sai dai nayi muku jagwab ɗin abinci don ban iya ba".
Bai ƙara cewa komai ba ya koma part ɗin sa.
Kallonta Mami ta yi ta ce. "Zahra kiyi abin da ya ce karki damu da wajan nan da ki ka ɓata zan sa ƴan aiki su gyara, maza kije ki siyo ingredient ɗin, domin ya ce ba za'a taɓa na gida ba".
"Shi ke nen". Zahra ta faɗa tare da shiga ɗaki ta saka saka hijabi. Fitowa ta yi yayin da Mami ta ba ta isashun kuɗaɗe domin siyan kayan abincin da ta ci. Bayan ta ba ta kuɗin ne fita daga cikin harabar masarautar tare da tarar mai napep ya kaita kasuwa.
Bayan Aliyu ya isa Kano ne ya samu wani guri kusa da kasuwar kwari ya yi parking. Sannan ya fara waige-waige. Chan ya hango mai tallan tsire. Hakan ya sa ya tare shi tare da siyan na dubu ɗaya domin rage yunwar da take damun shi.
Zahra kuwa saida mai napep ɗin ya yi tafiya mai nisa sosai kafin nan ya isa kasuwar kwari. Chan ta hango tsayuwar Aliyu jikin motarsa. Tunani ta shiga yi kamar ta san wannan mutumin. "Wannan kamar wannan ɗan sandan da ya so raina min hankali a magarƙama ne ko?". Ƙara kura masa idanu ta yi. "Laa babu tantama kuwa shi ne". Dakatar da mai napep ɗin ta yi da ya tsaya. Ba tare da ta tsaya biyan mai napep kuɗin sa ba ta tsallaka titi da gudu tare da nufar in da Aliyu yake tana mai faɗin. "Malam ɗan sanda mai ɗagaggen wando kaine a garin Kano?".
Juyawa Aliyu ya yi ganin waye wannan mai furta wannan kalma. Nan take ya haɗa ido da Zahra. Take gabansa ya yi mummunar faɗuwa!. Nuna ta ya yi ya ce. "Safira!".
Kallonsa Zahra ta yi ta ce. "Wace ce kuma haka?, wai Safira, kai ni ce fa baka gane ni ba a magarƙama da ka zagar min uwa na so nayi maka duka ka tuna?. Ba kai ne wannan ɗan sandan mai ɗagaggen wando ba?".
Dafe kansa Aliyu ya yi jin yadda kansa ke ƙoƙarin sara masa. Riƙe kansa sosai ya yi domin yin tunanin a ina ya santa. Ɗaga kansa ya yi ya kalle ta ya ce. "Kenen ba ke ba ce Safira ba?".
Haɗe giran ta Zahra ta yi tare da turnuƙe fuska ta ce. "Wace ce kuma Safira?, ni fa malam sunana Zahra ba Safira ba".
"I am totally confused, what's going on?". Aliyu ya tambayi kansa. Nan take ya fara tuna wan can ta magarƙamar. Rass gabansa ya faɗi. Cikin ransa ya ce. "Tabbas wannan ita ce wanda na gani a magarƙama kwanaki mai brown eyes, sannan Safira ma tana kama da ita, ga kuma ranar nan na ga wata mai kama da Safira mai grey eyes. Kenen hakan yana nufin su uku ne?, idan kuwa hakan ta kasance to tabbas hasashen Mom gaskiya ne, kenen hakan yana nufin yaran Mrs Laila ne?!".
COMMENTS & SHARE FISABILILLAHI 🙏 🙏
ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(Zinariyar Jajirtattu)