KUNDIN CINIKAYYA BY A'ISHA M.B

45&46

by @aishamb

***


Domin cigaba da karanta wa ka shiga Wannan link👆👆👆



*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part of the world)*🪐🌎🪐.

Daji 🌲

Magarƙama🏢 da kuma 

Birni🏙️


WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞

(Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu)



***

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

(J.W.A) 

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


 *DIAMOND 💎 STAR⭐* 

   *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️*

  (We stand together)

      🤝🤝🤝


بسم الله الرحمن الرحيم 

*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*

Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!


*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 4️⃣5️⃣▶️4️⃣6️⃣

*___________________________________________*

Haka Zahra ta shiga ɗura wa kowanensu abinci har saita da ta kai kan Sooraj.



Tsayawa ta yi tare da zuba masa idanuwa sannan ta ce. "Kaine babba ko?, harda wani cewa, kiyi maza-maza ki kije ki girka abincin nan, sannan na gama ka ce wani a kaiwa karnuka saboda ka raina min hankali, to kai ma saikaci domin naka ma yafi yawa ka ganshi ko, ta faɗa tana mai nuna ƙaton kula wanda ya cika da abinci. Maida kallonta ta yi kansa ta ce. "To sai ka cinye abincin nan tass in faɗa maka gaskiya". Ta faɗa tana mai ɗaukar chokali sannan ta ɗibi abincin ta kai bakin sa. Ganin ya matse bakinsa yaƙi buɗe wa ya sanya ta kama fuskarsa tare da buɗe bakin nasa da ƙarfi sannan ta cusa chokalin ciki. Haka ta shiga ɗura mai abinci har na kulan ya ƙare.




Tashi tsaye Zahra ta yi tare da karkaɗe jikinta ta ce. "Ƴan banza kawai wato ku nan ƴan sarauta ko?, ko banza dai kunci abincin". Ta faɗa daidai lokacin da Mami ke fitowa daga ɗakin ta.



"Ya subha'anallahi!". Kalmar da ta fara zuwa bakin Mami kenen.



Kallon Zahra Mami ta yi ta ce. "Zahra wane ne ya yi musu haka?, ji fa yadda aka ɗaɗɗaure su kamar wasu akuyoyi, mene ne abin da ya faru?".



Kallon Mami Zahra ta yi ta ce. "Yauwa Mami barka da ƙarasowa". Ta faɗa tana mai zuwa kusa da Mami sannan ta kalleta ta ce. "Kin san mene ne suka aikata?".



Girgiza kai Mami ta yi alamun A'a.



Maida kallonta Zahra ta yi kan su sannan ta ce. "Kina ji ba, Yarima Sooraj ba ya ce saina ƙara girka wannan abincin da na cinye ba, to wai bayan na gama ɓata lokaci na nasha wahala sannan na kawo musu, wai da suka zo wai yarima Sooraj ya ce wai a kaiwa karnuka su cinye. Ni kuma na ce idan na yarda mai tatsine ya dawo duniya, na ce suci suka ce ba za su ci ba. Ni kuma da naga aka na je na ɗauko wani turare na kashe jiki a ɗaki nima ban san turaren na mene ne ba, na fesa musu sannan na ɗaɗɗaure su kana na basu abincin da kaina, shi ke nen fa".



Salati Mami ta rafta tana mai faɗin. "Zahra kin kashe ni, Sooraj fa yana da cutar Asma kuma chronic ne, bai kamata a ce kinyi musu haka ba, domin kuwa ke ƴar aiki ce kawai, ya kamata a ce kina iya sarrafa fushin ki a wasu lokuta".




Ƙunce su Mami ta fara yi yayin da ita ma Zahra ta saka hannu suka kunce su tare.



Saida suka shafe kusan hawa guda ba tare da wani a cikin su ya dawo cikin hayyacin sa ba. Bayan wasu mintuna suka fara dawo wa cikin hayyacin su , yayin da suka shiga amai. 



Gaba ɗaya babu wanda bai farfaɗo ba sai dai Sooraj wanda har izuwa wannan lokacin bai farfaɗo ba.



Hankalin Mami ba ƙaramin tashi ya yi ba ganin Sooraj bai farfaɗo ba. Ɓangaren Zahra ma gaba ɗaya hankalinta ya tashi yayin da take tsoron kada ta je ta kashe ɗan mutane.






******

Bayan Umar yaji labarin cewa Amrah ta tafi ya sa hankalin shi ya tashi. Yayin da suka bazama nemanta amma hakan ya cutura.



A sa'inda Umar ya kira jami'ansa domin su zagaye gaba ɗaya garin Kano dan a nemo ta.





Ɓangaren Amrah kuwa, bayan fitar ta daga ciki gidan ta fara tafiya ba tare da ta san inda take sanya kafafuwanta ba. Babu zato ta ga wasu motoci sun zagaye ta. Nan wasu mutane suka fito fuskokin su rufe da mask. Ba ta yi aune ba ta ji sun shaƙa mata wani abu. Take jiri ya ɗibe ta yayin da bacci mai nauyi ya kwashe ta.



Shigar da ita suka yi cikin motan sannan suka bar harabar wajan da ita.









*******

Tun ana ɓoye wa har labari ya garzayo kunnen sarki. Nan haka wuce da Sooraj asibiti yayin da aka shiga bashi taimakon gaggawa.



Gaba ki ɗaya hankalin Sarki da na Mami ya tashi. Yayin da ɓangaren Zahra take ta faman addu'a Allah ya sa bai mutu ba.



Nan dai likitoci suka yi nasarar dawo da numfashin sa, saida Sooraj ya kwashe kwana biyu a asibiti ana duban lafiyar sa. Kafin daga bisani aka sallamo shi daga asibiti.



Gaba ki ɗaya jikin ƴan gidan ya mutu yayin da suka kasa furta komai, tare da ganin duk laifin Zahra ne da a ce ba ta yi abin da ta yi ba da hakan ba ta faru da shi ba.



Zama gaba ɗaya suka yi a parlour, yayin da Zahra durƙushe gwiwowinta a ƙasa ta duƙar da kai ƙasa.



Kallonta Gimbiya Talatu ta yi ta ce. "Kinga abin da ki ka aikata ko?, yanzu da a ce daga nan ya mutu mene ne za ki ce?, kin san da a ce ya mutu kema rataye ki za'a yi?, wannan wane irin shashanci ne da almubazarancu".




Kallon Sooraj Zahra ta yi nan take taji nadamar abinda ta aikata. Duƙar da kai ƙasa ta yi ta ce. "Ina mai baku haƙuri gaba ɗaya, banyi hakan ba dan wata manufa a zuciyata ba, nayi hakan ne dan kawai na saku kuci wannan abincin amma bawai nayi hakan ba da nufi cutarwa. Idan duk na ɓata muku rai kuyi haƙuri ba zan sake ba".



"Babu wani ba za ki sake ba, kawai mafita shi ne ki tattara komai naki ki bar wannan masarautar". Cewar Gimbiya Saratu.



Ɗaga musu hannu Sooraj ya yi ya ce. "A'a, ba zata je ko ina ba, bazan bari ta tafi haka nan ba, dole ita ma ta ɗanɗana kuɗarta, tunda harta iys ɗora hannayenta a kanmu to ba zata tafi kuma a ƙyale ta ba".




Kallonsa Mami ta yi ta ce. "Amma Sooraj ya kamata kayi nazari, ta riga ta baku haƙuri, ni kawai zan sallame ta tafi".



Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "A'a Mami, da a ce na mutu haka za ki ce a rabu da ita?, bazan bar abinda ta aikata ba, wallahi saina gana mata azaba a masarautar nan, saina sa ta gwammaci mutuwa da rayuwa". Ya ƙarashe maganar tare miƙe wa tsaye sannan ya nufi part ɗin sa.




Maida kallonta Mami ta yi kan Zahra ta ce. "Zahra tashi ki shiga ɗaki kinji".




Girgiza kai kawai Zahra ta yi sannan ta miƙe tsaye tare da nufar ɗakinta. Binta kawai su Samira suka yi da kallo, yayin da suke hayyana irin muguntar da za su yi mata.



Zahra na shiga ɗaki kuwa ta faɗa kan gadonta tana mai sauke ajiyan zuciya sannan ta miƙe zaune ta ce. "Wai me yake nufi?, yana nufin zai azabtar da ni?, dan ma ya samu na bashi haƙuri shi ne zai dinga fadar waɗan nan maganganun, to wallahi daidai da kai aikin banza kawai". Ta faɗa tana mai buga tsaki.





*****

"Hello Please am I talking to Safira Ibrahim?".



Girgiza kai Safira ta yi kamar tana gaban mai maganar a waya sannan ta ce. "Yes of course, please how may I help you?".


Daga ɗayan ɓangaren aka ce."The law school you applied to has accepted you, now you just need to start, but before that, today we need you to come in for signing so that we can verify your details. They will come to pick you up at home, and don't worry about receiving a visa or passport because everything has been completed. We are just waiting for you."



Miƙe wa zumbur Safira ta yi cike da farin ciki ta ce". Wow!, thank you so much, I can't even describe how happy I am. Very soon, I'll be heading to America." Ta faɗa tana mai katse wayar.




Da sauri ta fita parlour ciki sa'a ta tarar da su Mom a parlour, nan ta sanar musu abin da ya faru. Babu wanda bai yi farin ciki ba amma Mom samm ba ta so hakan ba domin ba ta som ta yi nisa da ƴarta.



A gurguje Safira ta koma ɗaki kana ta shirya kanta da kayanta. Bayan ta gama shirya kayanta a travelling box. Ta saka kaya masu kyau riga da wando sannan ta saka ɗan ƙaramin veil sannan ta ɗora kimono a kan riga da wandon.



Fitowa ta yi da box ɗin sannan ta nufi hanyar waje. Bakwana suka yi da kowa na gidan yayin da Daddy ya shiga saka mata albarka. Mom kuwa shiru ta yi domin gaba ɗaya hankalinta ba'a kwance yake ba, ji take kamar wani abu na shirin faruwa da ƴarta.



Kallon Safira ta yi ta ce. "Safira, ni da za ki ji ta baki na kiyi zamanki kawai, idan ya so idan za mu koma America sai kiyi komai, wallahi hankali na ya kasa kwanciya, tsoro na shi ne kada wani abu ya same ki".



Murmushi Safira ta yi ta ce. "Kada ki damu Mom babu abin da zai same ni da izinin Allah".



Daidai lokacin suka jiyo horn ɗin mota a waje. Bye-bye tayi musu kana daga bisani ta fice daga gidan. Fitowa driver ɗin motan ya yi sannan ya karɓi box ɗin kayanta tare da saka su a bayan mota. Shiga cikin motan ta yi kana daga bisani driver ya ja mota suka bar wajan.




Sosai Safira ke farin ciki yayin da take gani kamar cewa ta riga ta zama lawyer.



Kallon driver ɗin ta yi ta ce. "Yanzu hanyar airport zamu wuce ko?".



Shiru driver ɗin ya yi mata bai ko tanka mata ba.


Mamaki ne ya kamata ganin bai amsa ba, hakan ya sa ta yi tunanin ko bai ji ba ne.



Hankalinta bai tashi ba sai sanda ta ga anyi wani kwana da ita ana shiga cikin dajin.



Nan take gabanta ya tsananta faɗuwa. Kallon driver ɗin ta yi ta ce. "Kai driver ina ka ke ƙoƙarin kai ni?, ba airport ka ce zamu je ba, ni ka ga just take me back home please".



Ganin ko kulata bai yi ba ya sa hankalinta ya ƙara tashi.



Addu'a ta shiga yi tana mai neman kariyar Ubangiji. Yayin da hawaye ya fara sauka kan ƙuncinta tana mai nadama kan me ya sa ta biyo wanda ba ta sani ba, kuma saida Mom ta faɗa mata cewa kada taje ta bari idan za su koma America. 



Saida suka je chan cikin tsakiyar daji. Sannan driver ɗin ya tsagaita da tafiya. Parking ya yi kusa da sauran kidnapper's ɗin sannan ya fito daga mota. Buɗe mata ƙofa ya yi kana ya dube ta ya ce. "Duk abinda haka faɗa miki a waya to ƙarya ne. A halin yanzu dai kina ƙarƙashin mu ne, kuma idan muka gadama za mu kashe ki har lahira, ina son ki bamu haɗin kai idan ba haka ba ki mutu".



Faɗuwa gaban Safira ta yi sannan ta ce. "Dan Allah ku faɗa min mene ne na aikata muku?, sannan wane ne ya turo ku sace ni?".




Murmushi mutumin ya saki sannan ya ce. "Kina son sanin wane ne?".



Girgiza kai Safira ta yi alamun eh.


Amsa mutumin ya bata da cewa. "To Aliyu ne".



Rass! gabanta ya buga da mugun ƙarfi. Kallon mutumin ta yi ta ce. Wane Aliyu?, Aliyu wanda zan aura?".



Amsa suka bata da cewa. "Ƙwarai kuwa da gaske".



Kallon su Safira ta yi cikin rashin yarda ta ce. "Ƙarya ku ke, samm Aliyu ba zai sa a sace ni ba, saboda me zai yi hakan?, ni ce fa wacce zai aura. Kunga ku faɗa min gaskiyar cewa ba Aliyu ba ne, domin na yarda da shi ba zai taɓa sace ni ba, kuma mene ne ribarsa ma idan ya sace ni?, me zai samu?".




Dariya gaba ɗaya suka kwashe da shi sannan suka ce. "Kina son sanin me zai samu?. To ki baza kunnuwanki kiji, zai samu kuɗaɗe ne, dubbunan kuɗaɗe, Aliyu samm ba sanki yake ba illa dukiyar ki, kuma dai Aliyu shi ne ba wani ba. Idan baki yarda ba duba nan ki gani".



Mutumin ya faɗa yana mai nuna mata wayarsa. Nan ta ga Aliyu tare da mutanen wajan suna raba kuɗi a tsakanin su, yayin da suke maganar yadda suka sace Amrah, gashi za su sace Safira.





Jikin Safira ne ya mutu, yayin da takaici ya ana ta kasa cewa ƙala. Hawaye ne ya fara gangaro wa bisa ƙuncinta. Ta ce. "Ban taɓa tunanin haka daga gare ka ba Aliyu, me ya sa zai aikata min haka?, da na yanke cewa zan amince na aure sa domin ya nuna min cewa yana so na sannan kuma yana da nutsuwa da sanin ya kamata, ashe duk ƙarya ne". Ta ƙarashe maganar tana mai fashe wa da kuka.










**********

Zahra na zaune ta ga ƴar aiki ta shigo sallama riƙe a bakin ta. Amsa sallamar Zahra ta yi ta ce. "Mene ne ya faru?".



Amsa ƴar aiki ta bata da cewa. "Yarima Sooraj ne ya ce na kira wo masa ke, kuma ya ce ki zo cikin gaggawa".



Taɓe baki Zahra ta yi ta ce. "Allah ko?". Sannan ya ƙara da cewa. "To ki koma ki gaya masa cewa ba zan zo ɗin ba, idan zai iya zuwa ya tafi da ni chan ya zo ya ɗauke ni, sannan kice mai tunda shi ne yake buƙata ya zo da ƙafarsa amma ba dai ni na je ba, ni Mami kawai nake yi wa aiki bawai shi ba, ita kaɗai ce za ta sani aiki nayi ki gaya masa hakan". Ta faɗa tana mai koma wa tare da kwanciya.




Fita ƴar aikin ta yi sannan ta nufi part ɗin Sooraj ta zayyane masa duk abin da Zahra ta faɗa. Nan take ran Sooraj ya ƙara ɓaci. "Ni ce zan kira ta tace wai ba zata zo ba sai dai ni da kaina naje?, za ta gane kuranta". Maida kallonsa ya yi kan ƴar aikin ya ce. "Jeki na san yadda zan yi da ita".


Jin hakan ya sa ƴar aikin ta bar masa part ɗin sa.





******

Zahra na kwance taji an banƙo mata ƙofa. A matuƙar razane ta miƙe tsaye. Su Gimbiya Saratu ne tare da su Fasma.



Rufe ɗakin suka yi sannan suka saka maƙulli suka rufe. 



Murɗa hannayensu suka yi a ƙirji sannan Gimbiya Talatu da su Samira suka fara karkaɗa ɗuwawu.



Kallonta Yusra ta yi ta ce. "Wati ke kin cika ƴar iska da har za ki iya sa mu ci wannan ƙazamin abincin naki".




Murmushi Zahra ta yi sannan ta ce. "Naji ƙazami ne, amma dai koba komai kunci abincin. Tukun na ma me ya kawo ku ɗaki na?".



Amsa Gimbiya Saratu ta bata da cewa. "Munzo mu nakaɗa miki na jaki ne, duka zamu yi miki".





Babu zato Zahra ta kwashe da dariya. Kallon juna su Gimbiya Saratu suka yi ganin tana dariya ya sa abin ya basu mamaki.



Saida Zahra ta yi mai isarta sannan ta ce. "Wai da gaske duka na ku ka zo yi?. To masha Allah maraba da zuwa, me ku ke so na kawo muku, tuwo ko shinkafa?, kun san ana son mutun kafin ya fara dambe ya fara cin abinci mai lafiya ta yadda zai samu ƙarfin yin duka sosai".



Kallon juna suka yi gaba ɗaya suka yi ganin tana neman shashantar da su ya sasu cewa. "Da gaske fa muke ba wasa ba".



Jin hakan ya sa Zahra ta haɗe ranta sannan ta ce. "Zan baku shawara kyauta ba tare da ko sisin ku ba, kuyi wa kanku faɗa ku koma, domin idan na fara dukan ku karku zo kuna bani haƙuri naƙi hakura, ku yanke shawara a tsakanin ku tun kafin a fara".


Kallonta Samira ta yi ta ce. "Kin ɗauka za ki iya dukan mu ne?, ko kin manta cewa sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi?, to ba za mu fita ɗin ba kiyi abin da ki ke ganin za ki yi" .



Jin hakan ya sa Zahra miƙe wa sannan ta nufi hanyar waje ta ƙara rufe ƙofar sosai sannan ta cire ki ɗin tare da saka wa a ciki kayanta wanda yake doguwar riga atamfa mai aljihu.




Koma wa ta yi ta zauna kan gado ta ce. "Ta kan wa za'a fara?, ku gimbiyoyi ku koma ku zauna ku ga idan yaranku suna da ƙarfi ko basu da shi".



Kamar yadda ta faɗa aka gimbiya Saratu da Talatu suka koma suka zauna, yayin da suke jiran kawai suka yaran nasu sun fara jibgar Zahra.




Take Samira ta kaiwa Zahra naushi a fuska. Da sauri Zahra ta kawar da kai sannan ta kama kan Samira da Fasma ta gwara su guri ɗaya.




Nan take suka saki wata iriyar azababbiyar ƙara!. Ƙaran da suka saki ya janyo hankulan su Junaid da na so Sooraj ɗakin. Da sauri suka nufi hanyar ɗakin Zahra tare da bubbuga ƙofan.



Ɓangare Zahra kuwa ɗaukar dorina ta yi ta fata shauɗa musu babu gaggauta wa. Ihuu suke suna neman a kawo musu agaji . Ganin ba za su iya cigaba da jure wa ganin Zahra na dukan musu yara ba ya sa su miƙe wa suka fara rirriƙe hannun Zahra. 



Ɗaga hannu Zahra ta yi zata zuba wa wanda ya riƙe ta dorina. Chak da dakata ganin su Gimbiya Saratu ne. Wafce jikinta ta yi daga nasu ta ce. "Ba zan iya dukan ku ba, domin kuwa kuma a matsayin iyaye na ku ke, dan haka ba zan taɓa iya ɗora hannu na a kanku ba". Ta faɗa tare da koma wa ta zauna.




Miƙe wa su Samira suka yi suna hawaye, yayin da su Gimbiya Saratu suka shiga rarrashin su gani yadda jikinsu ya yi jajir yayin da satin bulalan Zahra duk ya fito jikinsu.




Kallon Zahra Gimbiya Talatu ta yi ta ce. "Ki bamu maƙulli mu fita".



Kallonsu Zahra ta yi mamaki bayyane kan fuskarta ta ce. "Ku fa ku ka ce ba za ku taɓa fita daga ɗakin nan ba har sai kun dake ni, to a kan me ya sa za ku fita bayan baku dake ni ba?, to ku sani cewa muddin baku dake ni ba bazan baku maƙullin ɗakin nan domin ku fita ba".



Roƙan Zahra gaba ɗaya suka fara yi. Yayin da suka ce ba za su sake irin wannan gangancin ba.



Saidai Zahra ko sauraren su ba ta yi ba illa ca da ta yi cewa. "Wallahi ba zan bari ku fita ba muddin baku dake ni, maza-maza ku tawo ɗaya bayan ɗaya ku dake ni kunji ko, kunce za ku dake ni kafin ku fita kuma baku dake ni ba. To ku sani cewa ko wane ne zai zo bai isa ya sani na baku maƙulli domin ku fita ba har sai kun dake ni kamar yadda ku ka furta, ba saida na faɗa muku kuyi wa kanku faɗa ba?, na baku shawara na ce ku tafi amma ku ka yi kunnen ƙashi, kuma na riga na faɗa muku idan na fara jibgar mutum idan wani ya roƙe ni na buɗe ƙofa ba zan buɗe ba, dan aka a yanzu mun sa ƙafar wando ɗaya da ku, sai dai ku dauwama a cikin ɗakin nan muddin baku zo kun taɓa ni ba".








*KAI ZAHRA AKWAI ƘARFIN HALI😹😹😹, KI ƘYALE SU AJEBUTTERS SU FITA😂🤣*





ALƘALAMIN ✍️ 

A'ISHA M.B💞💞💞

(ZINARIYAR JAJIRTATTU)