HURAYYAH (New edition) Chapter 8
HURAYYAH
New edition...
_Free pages_
Chapter 8
*_WAIWAYE ADON_* *_TAFIYA..._*
Aliyu Ibrahim shine asalin sunan Aliyu,mahaifinsa Alhaji Ibrahim ɗan asalin garin Gombe ne a ƙaramar hukumar Billiri.
Alhaji Ibrahim wanda aka fi saninsa da mai fata,sananne ne sosai a cikin garin Gombe kuma attajiri,wanda ya tara dukiya a harkan kasuwancinsa na fita da fatu zuwa ƙasashen ƙetare.
Auren saurayi da budurwa suka yi da Hajiya Maryama,waɗanda dukkaninsu fulani ne ziryan.Aure ne aka yishi na soyayya,kasancewar dukkaninsu wayayyu ne,sunyi karatun zamani dana addini.
Lokacin da Alhaji Ibrahim ya auro Maryama,ta shigo gidansa da ƙafar dama domin ko nan da nan al'amuransa suka sake buɗewa,arzikinsa kullum ƙaruwa yake.
Hakan yasa yasa yake jinta a cikin zuciyarsa sosai da sosai,shekarunsu biyu da aure Iyayen Alhaji Ibrahim suka rasu a sakamakon gobarar daya kama rugarsu babu wanda ya tsira.Lamarin ba ƙaramin daga hankalin Alhaji Ibrahim da Maryama yayi ba,ya dawo marayan da bashi da Uwa bashi da Uba sai dangi da matarsa abin ƙaunarsa Maryama.
Bayan rasuwarsu bada jimawa ba Hajiya Maryama ta fara laulayin ciki,murna a gurin Alhaji Ibrahim ba'a cewa komi,sai dai cikin nada watanni hudu suka rasashi.
Haka ta dinga samun ciki yana fita har dai aka samu wani ya tsaya ta haifi ƴa mace,watanni 2 ita ma ta koma zuwa ga Allah.Hakan ya jefa damuwa a zukatansu ba kaɗan ba,daga wannan haihuwar Kuma sai Hajiya Maryama ta sami hutu na kusan shekaru biyu ba tare da ta sake samun wani cikin ba. Kwatsam watarana sai ta tashi da matsanancin ciwo,wanda har ya kaisu ga kwanciya a asibiti.
Binciken farko aka gano ciki ne da ita ɗan wata guda a jikinta,murnan data yi ba wani mai yawa bane domin gani take ko cikin ya tsaya ta haihu ba lallai ne abinda ta haifa ya rayu ba.
Haka suka dinga rainon cikin har watannin haihuwarsa yayi,zuwa lokacin arziƙi ya sake yin zaman dirshan a gurin Alhaji Ibrahim,wanda ya kasance mutum mai tsananin taimakon na ƙasa dashi.Sannan akwai shi da taimakon addini,hakan ya janyo masa farin jini sosan gaske.
Sabon gini yayi a unguwar GRA suka koma,sun tare da sati biyu Hajiya Maryama ta haifo yaronta ƙaton gaske,kyakykyawa dashi duk wanda yazo barka sai ya tanka kyawunsa.
Kan kace kwabo mutanan Dukku garin su Hajiya Maryama suka iso cikin garin Gombe, Yayarta magajiya itace kan gaba a kulawa da ita.Haka aka dinga hidiman arziƙi har zuwa ranan suna yaro yaci suna Aliyu,sunan mahaifin Alhaji Ibrahim kenan da ya rasu.
Rayuwa ya cigaba da tafiya musu cikin jin dadi da wadata,Aliyu na samun tsananin gata da kulawa haɗi da soyayya a gurin mahaifinsa da Hajiya Maryama,sun ɗauki so sun ɗaura masa amma hakan bai hanasu ɗaura shi akan tarbiya ta gari ba.
Sun bashi ilimin addini tun yana ƙaraminsa kafin a saka shi boko,cikin sa a sai ya taso da kaifin ƙwaƙwalwa da baseera,ga kyawunsa da kullum ƙaruwa yake abin sha'awa.
Shekarun Aliyu uku aka sanya shi a primary skull,bayan ya kammala ya wuce secondary skull.Kasancewar Alhaji Ibrahim mai yawan fita ƙasashe ya sanya koda Aliyu ya kammala secondary sai ya wuce dashi zuwa ƙasar london domin hado deegree ɗinsa acan,inda ya fara karantar Public Administration.
Hajiya Maryama tayi kewar rabuwa da tilon ɗanta,amma hakanan ta daure ta kauda kai tana binsa da addu'a kullum akan Allah ya kare mata Aliyu daga sharrin ruɗin zamani.
Duk hutu yake dawowa ƙasarsa ta haihuwa har ya kammala deegree ɗinsa ya dawo,dawowar da bazai taɓa mancesa ba cikin tarihin rayuwarsa ba.Dawowar daya tarwatsa farin cikinsu shida Hajiya Maryama,ya dasa musu mikin da har yau ya kasa gogewa a cikin zukatansu baki ɗaya.
A lokacin da jirgi ya sauke Aliyu a airport ɗin Abuja ne yayi waya da mahaifinsa cewa ya sauka,amma yana so ya sake shigowa wani jirgin daga Abuja zuwa Gombe.Sai Alhaji Ibrahim ya sanar dashi cewa to aishi gashi shi ma a garin Abujan,kuma shi yake jira su wuce Gombe tare amma shi tafiyar mota zai yi bazai hau jirgi ba,kasancewarsa mai son tafiyar mota yana kallon gurare ta yadda zai ga irin cigaban da ake samu a wurare.Haka suka ɗakko hanya driver ɗin Alhaji Ibrahim Mallam Uba shi ke jaye dasu,Aliyu yana tare da mahaifinsa a back seat suna hirarsu yana sake jaddada ma Aliyu muhimmancin taimako da kuma haƙuri Da rayuwa.Yayi ma tilon ɗan nasa maganganu masu tsayawa arai matuƙa,suna daf da shiga garin Gombe suka tafka mummunan haɗari.A nan take kuma Alhaji Ibrahim da Mallam Uba suka amsa kiran Ubangiji,yayin da Aliyu aka wuce dashi asibiti mafi kusa sam baisan ma inda kansa yake ba.
Jami'an ƴan sanda ne sukai amfani da wayar Alhaji Ibrahim suka kirawo mutanan da yayi waya dasu a ƙarshe,ciki kuwa har da Hajiya Maryama wacce ta gama shan ado tare da kammala komi da za ta tarbi mijinta da tilon ɗanta.Ita suka kira kai tsaye, ringing biyu ta amsa kiran da ba za ta taɓa mancewa dashi ba.
Aminin Alhaji Ibrahim a wancan lokacin,mai suna Alhaji Falalu shine ya fara isa asibitin domin ganin gawar aminin nasa.A lokacin Aliyu ya sami farfaɗowa,kuma cikin ikon Allah ko ƙwarzane baiyi ba illah buguwar jiki kaɗai.
A lokacin da Aliyu ya fuskanci cewa mahaifinsa ya rasu nan take ya sake sumewa,har aka amshi gawarsu akai musu sutura Aliyu da Hajiya Maryama wacce ta iso asibitin tana ganin gawar mijinta da amintaccen driver ɗinsa ta zube a gurin ta sume,basu sake sanin inda kansu yake ba.
Sai bayan kwana ɗaya sannan suka fara iya ɗaga ido su kalli mutane,ba tare da suna iya furta ko kalma guda ba.
Tamkar masu taɓin hankali haka suka koma,saida taimakon addu'a da lallashi aka samu har suna iya zubda ruwan hawaye domin samin sassauci.
Kowa yaga halin da suka shiga sai ya tausaya musu,haƙiƙa sunyi rashin bango majinginin da ba za su taɓa maida kamarsa ba.
Yayah Magajiya da mahaifiyar Hajiya Maryama Inna Hure sune suka zauna da ita har akai arba'in,randa akai sadakan arba'in ɗin ne suka koma Garin Dukku domin duka suna da aure babu halin su zauna da ita har ta fita takaba.
A lokacin sai aka samo Iya mai aiki domin su zauna tare,haka rayuwa ta cigaba da tafiya musu cikin juriya da tawakkali har Hajiya Maryama ta gama takaba.
Aliyu ya tattara ya koma ƙasar America domin ya haɗo masters ɗinsa,yayi nesa da 9ja gaba ɗaya domin ya sami sukuni daga alhinin rashin Abbansa da har zuwa lokacin ke dukan zukatansu shi da mahaifiyarsa baki ɗaya.
Sosai Iya ke iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta ɗebe ma Hajiya Maryama kewa,sannan ita ma Yaya Magiya tana yawan zuwa daga Dukku ta ɗan kwana biyu duk don su ɗebe mata kewa.A hankali zuciyar Hajiya Maryama ke samun dangana,har ya kai cewa ta gama sadaƙarwa ta rasa mijinta har abada.Babu abinda yayi saura irin ta tallafi tilon ɗansu ta bashi dukkanin kulawa,ta yadda Hakan zai rage masa raɗaɗin rashin Uba.
Sosai ta duƙufa wajen yima Alhaji Ibrahim addu'a,tana roƙon Allah yasa aljannace makomarsa tare da cigaba da yin duk wasu ayyukan alkhairi da ya saba yi lokacin yana raye.
Maƙociyarta Hajiya Hafsat da ita kaɗai ta saba tun dawowarsu GRA,matar akwai karamci sosai ita da mijinta Alhaji kabeer.
Suna da yara uku biyu maza sai auta mace mai suna Samha,wacce take can Bauchi gurin Yayar Alhaji Kabeer tana zaune gidanta tana zuwa jami'ar Bauchi.Hakan yasa da fari sam Hajiya Maryama bata taɓa sanin cewa Hajiya Hafsat nada budurwar Yarinya mace ba.
A tunaninta Ahmad da Sadeeq sune kaɗai yaranta,tunda akai rasuwar sai Hajiya Hafsat take yawan leƙowa gurin Hajiya Maryama domin ɗebe mata kewa.Hakan kuma ba ƙaramin daɗi yake wa Hajiya Maryama ba,domin suna jimawa ana hirar rayuwa tsawon lokaci.
Watarana Hajiya Hafsat ta shigo wajen Hajiya Maryama suna hira sai ga wayar Samha ya shigo wa Hajiya Hafsat ɗin,sun jima suna magana da juna kafin su kammala.Hajiya Hafsat ta dubi Hajiya Maryama tana faɗin, "Yarinya tace ta kammala karatu za ta dawo gida gobe,shine fa ake ta ɗoki abinki da auta."
Cikin mamaki Hajiya Maryama ke faɗin,"Dama kina da ɗiya mace shine baki taɓa sanar dani ba?" Nan dai suka dinga hirar Samha,har zuwa lokacin da Hajiya Hafsat tayi sallama dasu ta tafi.
Washegary koda Samha ta dawo garin Gombe a ranan da dare suka shigo gidan Hajiya Maryama,domin alqawarine Hajiya Hafsat ta ɗaukarwa Hajiya Maryama na cewar da zarar Samha ta dawo za ta kawota suga juna........✍🏻