1
Tana tafiya murmushi na kuɓuce mata, ba ta san sanda yake zuwar mata ba. Ita kanta idan aka ritsa ta aka ce ta faɗi murmushin me take yi ma, ba ta san me za ta ce ba. Illa iyaka tace tana jin wani farin ciki na ratsa mata ƙirji. A haka ta cigaba da tafiya har ta isa kan kwanar da za ta sha ta isa layinsu, babu zato babu tsammani se ga Sadiq a gabanta.
"Ranki ya daɗe irin wannan sauri haka, ina ta bin ki, kina daɗa yi mini nisa. Kin ga mantuwa kikayi, zuciyata taji baza ta iya haƙura ba, se ta kaiwa wannan zinariya abinda yake nata kuma mallakinta." Ya miƙa mata takardun hannunsa dake cikin envelope fuskarsa ƙayace da murmushi mai daɗin kallo.
Wani sanyi na ratsa zuciyar ta, take kallonsa har ya kammala magana, wushiryar dake bakinsa, ns ƙara kyawun zancen sa, ga sajen da ke gefen fuskarsa, se ƙallin baƙi suke yi, gaba ɗaya kyawun sa ya maƙale a idaniyan ta.
Da ƙyar ta sami courage ta buɗa fatar laɓɓan ta, tamkar ba ma ta son yin magana, tayi murmushi, wanda da ganinsa ka san daga zuciya yske, tace dashi.
"Ya salam, ni kuwa garin ya haka? Na sa ka wahala wallahi, ka yi haƙuri nagode" ta miƙa hannu ta karɓa tana murmushi.
Ya kalleta still smiling yana yace " hajjaju makkatu, dama anan haka kike? Afwan na tsayar dake a titi, bye ki gaida gida" ya juya ya bar wajen ba tare da ya jira amsoshin tambayoyin da yayi ba.
Kan ta yi wani yunƙuri ta ga har ya ɓacewa ganinta, ta shiga tunani, ko ya ma yace mata sunansa? Ta kasa tunawa, a ranta kawai tace, i will be maintaining to call him My ƙani, shiɗin yaron kirki ne, ga kwarjini, ta cigaba da tafiya har ta isa gida.
Tun kan ta ƙarasa gidan ta hango Khaleel, tayi murmushi tace " yaya kenan, yanzu zai fara tambaye tambayensa, ina kika tsaya? me kika tsaya yi?" ta nufe shi tana murmushi.
"Arfa, wane yaro ne wancan? Ki ka rasa inda zaki tsaya da shi se titi."
Tayi shuru tana kallon sa.
Hakan yasa yace, "na fiye takura ko Arfa?"
Nan da nan ta zaro idanunta kamar zasu fito tace
"Kaiiii yaya, na shiga uku ni Maryam, kaji tsoron Allah Yaya. Yanzu tsakani da Allah yaushe nace ka fiye takura, ni bance ba wallahi" Ta turɓune fuska.
Se kuma ta nuna masa file ɗin hannunta, tace "Ka ga fa Yaya, caffée fa na je ashe nayi mantuwa, shine yaron shagon ya biyo ni da shi, yaron yana da hankali, yasan ya ake bawa manya girmansu, zan raka ka wajensu ko kaima se ka riƙa kai aiki wajensu".
Kallon ta kawai ya tsaya yana yi.
Ta tamke fuska tace "mene haka wai yaya? ina ta magana kamin shuru, ni kazo muje na nuna maka ko akwai gyaran da za ka sake yi min" ta ƙarashe tana shigewa cikin gidan nasu.
Yana murmushi shima ya bi ta, ya girgiza kai yace "Arfa sarkin tsiwa".
Ganin tana neman hawa dasu sama yasa ya tsaya, ya ce da ita, "Arfa wai a ina zan duba miki aikin ne? Naga kin kama hanyar sama, fita fa zanyi nima".
Kamar wata munafuka ta dawo da baya a hankali, sai da ta zo dab da shi sannan ta kara bakinta a saitin kunnensa tace, "shhhhhhh, yi shuru yaya karka jazamin. Bana so Yaya Umar yasan ina gidannan, aiki ya sani ban yi ba, yanzu zai ishe ni da tambayoyi kamar wani ɗan jarida".
Ya bita kaman yanda tace har parlon sama, yana mai jaddada rigimarta a ransa, haka rannan fa tace masa wai da kaɗan Umar ɗin ma ya girme ta, kuma ko kare ne ya cije ta bara ta iya faɗa a gabansa ba, mutumin da a ƙalla ya bata good 7 years.
binded papers ɗin dake hannunta ya karɓa, ya shiga dubawa a hankali daya bayan ɗaya, ko three over four of it bai kai ba ta zame ta ɗora kanta a cinyarsa wai ta gaji, bai hana ta ba ya cigaba da abinda yake yi.
Can bayan ya gama ya buɗo wuraren da tayi mistakes da wajen reference ya kirata yace, " Mimi, see this" yaji shuru. Ya sake kiran sunanta but still shuru, hakan sa ya mayar da dubansa gareta.
Ganin yanda take baccinta hankali kwance yasa ya girgiza kai, shi ta hana shi fita tace aiki za suyi ita kuma tazo tana baccin ta, wata rigimar se Arfefen Abba.
Ya zame kanta a hankali, yai mata matashi da pillon kujera, ya fice cike da tabbacin zai sha mita bayan ta farka...