KUKAN KURCIYA masu iya magana suka ce jawabi ne, kuma gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah, labari ne da ke 茩unshe da gwagwarmaya, soyayya, cin amana, rudin she蓷an da dai sauran su , ku dai ku biyo ni umaimah ado gaya don jin me ya 茩unsa?

Ga mai 茩orafi ko shawara message gayaumaimahado@gmail.com/ 09070127320

by @umaimah2024

02

 

KUKAN KURCIYA 




 BY OUM AHMAD 



     UMAIMAH ADO GAYA

( MRS.NAZEE)


zinariyar taskira 馃敺


page 15



... ***...




KARKASHIN JAGORANCIN 



馃挭馃摎馃摎

*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* 


       {T.W.A}


****

_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda Allah ya bawa ita. da hikimar mu muke Alfahari_

       

*A茩alaminmu 拼ancinmu馃挭*




Bismillahirrahmanirrahim




  NAFEESAT : Abu kamar wasa 茩aramar magana ta zama babba don dai sosai Nafeesat ta fita hayyacinta, jinin ta yai matu茩ar hawa har bata gane wanda ke kanta ga miscarrige da tai, sosai hankalin nuraddeen ya tashi ganin lokaci guda Nafeesat ta galabaita ta rame ta shiga wani hali mai wahalar fassarawa, sai da tai tsawon sati a wannan halin kafin ta fara gane mutane, lokacin gaba 蓷aya nuraddeen ya susuce ya fita hayyacinsa gashi har zuwa lokacin ya rasa abinda ya 蓷aga mata hankali har haka, sai da ta 茩ara sati guda sannan aka sallame ta, duk da bata gama dawowa dai dai ba, gashi nuraddeen ya kasa gane mata don kullum cikin kuka take, bata um bata um'um, sai dai ta saka shi gaba tana kallo tana hawaye, sosai abin ya ta蓳a shi shima don gaba 蓷aya ya rasa walwala da kuma farin cikin sa, kwana biyu dasallamo ta suka koma Nigeria ba tare da nisha蓷i ko 蓷aya ba, 


   Dawowar su Nigeria yayi tunanin zata sanya ta dawo cikin walwalar ta sai dai sam hakan bata faru ba don kullum tana 蓷aki ta rufe kanta banda aikin kuka ba abinda take, Abinci wannan rabonta da shi tun suna hongkong sai dai idan taji yunwa zata kashe ta tasha ruwan tea ta sake kulle kanta, banda salla ba abinda yake 蓷aga ta daga kan gado, wasa wasa abin har tsawon watanni biyu amma ba canji, dole nuraddeen ya kira khadeeja ya sanar da ita ko zata zo ta lallashe ta sannan ta tambaye ta abinda ke damun ta, haka akai kuwa domin khadija shiryawa tai takanas tazo amma duk yadda take ganin abin 茩arami ne sai ya gagare ta domin kuwa Nafeesat ta kasa gayawa kowa damuwar ta, idan suka matsa mata kuma sai ta sanya musu kuka, ita ka蓷ai ta san abinda ke damun ta ta 蓳oyewa kowa matsalar ta, har Ammi sai da ta zo da kanta amma Nafeesat tai birsisi ta qi sanar mata, tun tana bawa kowa tausayi har suka fara gajiya da halin ta suka fara jin haushi banda Nuraddeen da har cikin zuciyarsa yake jin yanayin da take ciki.




HASEEB : Tun a ranar ya ha蓷a su yai musu nasiha tare da fatan zasu girmama juna sannan su ha蓷a kawunan su guri guda domin samun nutsuwar sa, kuma kowaccen su tai fatan hakan sai dai rayuwar da suke ta ba ruwan kowa da 蓷an uwan sa ne, kwanan Lateefa biyu tai tsarki kuma a ranar Haseeb bai barta sai da ya maida ta cikakkiyar matar aure sai dai yaji banbanci da Haseeya nesa ba kusa ba, duk da cewar Lateefa budurwa ce sai dai ba kulawa sa蓳anin Haseeya da ta taso tare da mahaifiyarta wadda tasan darajar gyaran jikin mace, sosai darajar Haseeya ta 茩ara ginuwa a zuciyar sa, kana ya 蓷okantu ya kammala ranakunsa a 蓷akin Lateefa ya koma gurin Haseeya wadda ke can tana 茩ara shirin tarbarsa duk da tsananin kishin sa da take, 

   Sosai Lateefa taga canjin rawar 茩afar Haseeb akan ta sai dai kunya ta hana ta tambaya to wai ma mai zata ce masa? Tace meyasa ka daina rawar 茩afa akai na tunda kasanni sau 蓷aya? Kai ina? wannan rashin kunyar ba da ita ba, haka nan shima Haseeb ya kasa sanar da ita matsalar ta ballantana ta gyara, abubuwa da yawa ya saba da su gurin haseeya wanda ya raina salon Lateefa domin ita bata san komai a wannan fannin ba sa蓳anin Haseeya da idanun ta suka gama bu蓷ewa ta wannan fannin, eh tana shagwaba sosai domin Lateefa shagwa蓳a蓳蓳iya ce ta 茩in 茩arawa amma bata iya jan hankalin namiji zuwa gare ta ba, bata san yadda zata ja ra'ayin sa ba, sannan bata san abubuwan da ya kamata tai masa a gado ba, ita dai kawai ta bashi wu茩a da nama yai duk yadda yaso, 

  Da Haseeb yai tunani sai yaga tabbas farkon auren su da Haseeya itama tai wannan alkunyar kafin ta ware rass don haka sai yai mata uzuri ya cigaba da koya mata abubuwa a hikimance da tunanin itama zata waye kamar Haseeya har ya kammala mata kwanan ta bakwai, tun safe ta fuskanci yana rawar 茩afar ya koma gurin matar sa sosai abin ya ta蓳a zuciyar ta duk da ta tabbatar da so gami da 茩aunar da Haseeb yake mata sai dai ta lura sam matsayin Haseeya daban yake a gurin sa baya ha蓷a ta da komai, domin kullum ta duniya idan ya fita da Asuba yaje masallaci baya dawowa part 蓷in ta har sai ya taya Haseeya ta shirya breakfast sannan zai dawo yai wanka sannan suje cin abinci part 蓷in Haseeyar.



  HASEEYA: Tsaf ta karanci zumu蓷in Haseeb akan ta hakan ko yai mata da蓷i kuma ya 茩ara mata 茩warin gwiwar 茩ara gyara kanta kamin zuwa ranar duk da duk lokacin da ya shigo sai sunyi romancing junan su kamar ba gobe, ranar da Lateefa take da kwana shida a gidan taje akai mata lalle na fitar hayyaci ja da ba茩i, bayan an she茩a mata gyaran jiki na musamman, tai gyaran kai da kitso sannan ta dawo gida, washe gari tun da safe ta fara kiciniyar shirin tarbar Haseeb inda la'asar ta kammala komai ta gyara gidn fes kana ta ci ado na ban mamaki kamar dai yadda ta saba, ranar kam duk kawaici da danne kishin Lateefa sai da tai zuciya ta bar musu sashen gaba 蓷aya kana duk yadda Haseeb yaso zuwa ya lallashe ta Haseeya ta hana shi da salon makircin ta, sosai kam Lateefa ta sha kuka a ranar don bacci duk iya satar shi da 茩yar ya sace ta gabanin asuba ta sha kuka iya kuka ta rasa wanda zata fa蓷awa damuwar ta gashi ba ta da ilimin da zata kai kukan ta ga mahaliccin ta, 


  Bangaren Haseeya da mijin ta kam an sha bidiri domin kam Haseeya ta dage gurin ganin ta mantar da Haseeb kowace mace bare kuma Lateefa da ta fuskanci sakarar mace ce ita, bata iya kula da miji ba sam, sallar asuba ma Haseeb bai samu ba sai jam'i sukai shi da Haseeya, kana suka kwanta ramuwar baccin da basu samu ba, tun da Lateefa ta tashi take saka idanun ganin haseeb musamman da ya kasance yau zai koma bakin aiki amma shiru har takwas bashi ba alamun sa, sai around 8:30 sannan ya shigo cikin shirin fita banda 茩amshin sa har na Haseeya yake wanda hakan ya 茩ara taba zuciyar Lateefa sai dai ta danne ta gaida shi ya amsa yana mai 蓷ago fuskar ta da ta kumbura yana fa蓷in subhanallah! Love mai ya same ki? Fashewa tai da wani irin kukan takaici wai love? Love uwar wa? Bayan duk rashin mutuncin da ya tata mata saboda matar sa, share mata hawayen yai yana lallashin ta kafin yace ya isa haka please love kina sawa zuciya ta tana zafi ki gaya min mai ya faru? Girgiza kai tai tana fa蓷in ba komai dama jira nake ka fito naji yaushe zan koma school? kaga karatu yana wuce ni dan ma an kai report, dafe kai yai yana fa蓷in am so sorry dear ki shirya gobe insha Allah sai na kaiki ko? gya蓷a kai tai tana fa蓷in to ngd, masu aiki fa? Gaji har yanzu shiru banga kowa ba, shiru Haseeb yai kafin ya nisa yace ki yi ha茩uri Lateefa ni sam bana da wasu masu aiki sabida bana ra'ayin masu aiki kwata kwata, idanun ta ya kawo ruwa kafin tace amma aikin ya min yawa ban iyawa fa! Gyada kai yai yana fa蓷in ki daure a haka zaki iya ai, ta 茩ara marairaicewa kafin tace to abinci fa ban iya ba fa! Ya furzar da iskar bakinsa sannan yace zanyiwa Haseeya magana sai ta koya miki ko? Ta girgiza kai tana fa蓷in baza ta ji haushi ba? Shiru yai baice komai ba na tsawon lokaci kafin ya mi茩e yana fa蓷in bari na tafi kar na makara Abba yana jira na, Allah ya tsare tace daga zaune shi kuma ya sunkuyo yai mata peak a kumatu, goshi da lips 蓷inta yana fa蓷in sai na dawo,



  Haka rayuwa take garawa a gidan Haseeb ko da yaiwa Haseeya magana akan ta koyawa Lateefa abinci cewa tai akwai catering school ya biya a koya mata amma ita bata san ta yadda zata koya mata ba, cikin sati ko ya samo mata makarantar da ake koyar da abinci kala kala ya kawo mata ta cike sannan ta shiga, wata uku ake yi sai dai kasancewar ita per time take ya sanya sai tayi wata shida sannan zata kammala, kwance tashe a sarar mai rai tun Lateefa tana gwada girki yana 茩in ciyuwa har ta fara yi ana ci da 茩yar kafin ta fara yi yana yi ba yabo ba fallasa sai dai kamin ta kammala catering school 蓷inta ta kware sosai a girki sai dai ta rame sosai saboda rashin hutu kullum tana hanyar makaranta daga nursing zuwa catering school har ta samu ta kammala catering school 蓷in lokacin suna da wata shida da sati biyu da aure kuma a school 蓷in ne ta ha蓷u da wata friend Aysher wadda jinin su ya ha蓷u sosai, yanayin da Lateefa kan shiga wasu lokutan da kuma yanayin yadda take yi idan tana bata labarin rayuwar gidan ta ya sanya ta fuskanci Lateefa na da 茩arancin wayewa a rayuwar aure dama rashin sanin yadda zata gyara jikin ta hakan ya sanya ta 茩uduri aniyar ganin ta gyara mata rayuwarta.



  Meet in the next page 




 Note: Zaku ga na dawo da posting da wuri bayan nace zan tsaya editin SAR茦A茦IYA to hakan ya faru ne sakamakon samun wadda zatai min editing 蓷in shi don haka naga ya dace na cigaba da typing 蓷in KUKAN KURCIYA ina son sanin mene ra'ayin ku akan wannan littafin,shin me kuke hasashe a game da littafin ? Mene ne ilimin dake cikin littafin? Shin littafin yana da ma'ana ko kuma kawai nisha蓷i ne a cikin sa? ya kuka 蓷auke shi a gurin ku? Please ku taimaka ku sanar dani domin na san ta yadda zan bullowa lamarin nagde taku umaimah ado gaya 


  Ga duk mai buqatar fa蓷ar ra始ayinsa sai yai magana a group din mu na comment room


Follow this link to join my WhatsApp group: ***


GA DUK WANDA YASAN ZAI COMMENT DA SHARING AKAN LITTATTAFAI NA TO YAI JOINING.