Idan nai kuskure ku yafe min, idan na faranta muku kuyi min addu'a
by @umaimah2024
KUKAN KURCIYA
BY OUM AHMAD
UMAIMAH ADO GAYA
( MRS.NAZEE)
zinariyar taskira 🔷
page 17
... ***...
KARKASHIN JAGORANCIN
💪📚📚
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
****
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda Allah ya bawa ita. da hikimar mu muke Alfahari_
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
Bismillahirrahmanirrahim
MOMMY: Da tsananin tashin hankali take kallon likitan haka nan kunnuwanta sun kasa gaskata abinda suka saurara daga bakin sa, ya buɗe baki domin cigaba da bayanin ta katse shi da faɗin wai doctor akan wa kake magana ne? Ni fa mahaifiyar wannan yaro Lateef ce dake kwance a wancan gadon ta ƙarasa maganar tana mai nuni da inda Lateef ke kwance akan gadon, sauke ajiyar zuciya likitan yai cike da tausayin Mommy yake faɗin hajiya ki yi haƙuri amma ina miki magana ne akan shi dama, furzar da iska Mommy tai daga bakin ta kana tana zamewa a hankali ta zauna dirshen akan tiles ɗin ɗakin cikin murya mai cike da rikici take furta har yaushe Lateef yake shiga cikin mutane da har zai shiga wannan sabgar, bashi da abokai balle nace yawan kula kulen abokansa ne ya samo masu wannan halayyar, kaico na ni Rakiya dana kasance uwa mara kula da rayuwar yaran ta, kaico na da na kasance uwa mai rashin kula da lafiyar yaron ta, kaico na da na kasance uwa mara maida hankali akan tarbiyyar yaranta da addinin su, yau gashi Allah ya nuna mini mugun abu akan yaro na kuma duk dalilin sakaci ne da nai da tarbiyyar su, likitan ya sunkuya ganin babbar mace don aƙalla mommy zata iya yin ƙani da shi na biyar yace " kiyi haƙuri hajiya amma yanzu aikin gama ya riga da ya gama sai dai mu maida hankali gurin ganin ya samu lafiya, goge hawayen fuskar ta mommy tai tana faɗin yanzu me ake ciki likita? Sai da ya sunkuyar da kansa kana ya sauke nannauyar ajiyar zuciya kafin yace a halin da ake ciki dai fatar gaban sa ta samu matsala don kwailewar da tai ba kaɗan bane don har tsokar ciki ana gani sai dai muna kan yi masa magani gurin kuma Alhamdulillah ya fara kamewa sai dai bamu da tabbacin ko zai ƙara muruwa, sannan tsutsar dake fita daga jikin sa munyi ƙoƙarin ganin mun magance matsalar ta hanyar yi masa wata allura da akewa masu irin wannan sana'ar kuma suke son dainawa don matuƙar tsutsar na jikin sa ba zai taɓa dainawa ba sai dai kasancewar ya daɗe a harkar ya sanya dole sai an masa aiki an cire su gaba ɗaya sannan an duba idan basu lahanta masa wani abin ba, sai kuma ƙurjin da ya fito masa wanda na sanar dake cancer ne wanda a halin da ake ciki yanzu muna kan binciken maganin da zai dace dashi sai dai ina ganin gaskiya sai an fitar dashi waje domin yanzu haka da nake miki magana tsawon sati ukun nan bai san inda kansa yake ba sakamakon ƙwayar da ya sha tafi ƙarfin sa kuma ta taɓa kwakwalwar sa, tsabar firgici mommy suma tai sai da doctor ya kira nurses aka bata taimakon gaggawa sannan ta farko, lokaci ɗaya ta zabge ta rame tai zuru zuru, tana kuka ta kira daddy ta sanar masa Lateef na kwance a asibiti bai san inda kansa yake ba, cikin rikici daddy yake faɗin mene? Me ya same shi ? cikin kuka mommy tace Alhaji kawai ka taho ko kuma ka shirya mana viza don likitan yace sai an fitar dashi waje .....
NAFERSAT : Tsawon lokaci tana cikin wannen yanayin na ƙunci da kaɗaici kafin ta fara dawowa daidai saboda ganin gaba ɗaya yadda Nuraddeen ya susuce saboda yanayin da take ciki, gaba ɗaya ya rame ya fita hayyacin sa saboda gani yake tamkar shine silar halin da take ciki, ga iyayen ta da ƴan uwanta suma duk sun shiga damuwa saboda sun kasa gane kanta, ita kuma tana jin bazata iya sanar dasu halin da take ciki ba sabida hankalin su zai fi tashi fiye da yadda ya tashi yanzu,
Zaune take kan kujerar falo sanye cikin doguwar rigar abaya wadda tai mata yawa sakamakon ramar da tai, gaba ɗaya tai fayau fuskar ta tai fafat ta ɗashe, cikin sanyin jiki da murya Nuraddeen ya shigo falon shima ya koɗe ya jeme ya tara uban gashi na kai da ƙasumba, tun da yake a rayuwar sa bai taɓa tunanin zai shiga irin halin da ya shiga saboda mace ba,
Da sauri Nafeesat ta nufe shi ta rungume shi tana faɗin am really sorry my man ka yafe min halin da na sanya ka ciki, kalli yadda ka koma duk saboda ni baka cancanci wannan daga gare ni ba, ƙara ruƙunƙumeta yai a jikin sa yana faɗin Alhamdulillah Allah na gode maka da ka amsa addu'a ta cikin sauri, Nafeesat! I missed you, your sweet voice, your eyes your lips in fact i missed all of you, kuka ta sanya sannan ta riƙo fuskar sa tana kallon cikin idanuwansa ta furta, ina matuƙar ƙaunar ka mijina, ina matuƙar son ka mijina, haƙiƙa nayi soyayya a baya amma sai da na sanka sannan na fahimci ainihin ma'anar so da ƙauna, kai ne farin ciki na noor kai ne muraɗin zuciya ta, ina jin bazan iya rayuwa ba tare da kai a gefe na ba, ina jin rayuwa ta ba komai bace idan har ba kai a cikin ta ba, ina son ka noor fiye da yadda zan iya kwatanta maka, misilta irin yadda nake son ka tamkar ƙasƙantar da so da ƙaunar ka ne a gare ni, dan Allah kar ka rabu da ni duk wuya duk rintsi, ka yarda da ni domin bana jin zan iya cutar da kai ka tausayawa rayuwa ta kada ka rabu da ni dan Allah! Kuka yaci ƙarfin ta ta riƙe gaban rigar sa tana rerawa, sai da tai kuka sosai tana riƙe a hannun Nuraddeen kafin ya ja ta zuwa kan kujera yana lallashin ta, ba tare da ya furta komai ba sai buga bayan ta da yake yana hura mata iskar bakin sa gami da shafa gashin kanta,
Sai da shiru tana sauke ajiyar zuciya kafin ya ɗago fuskar ta yana kallon ƙwayar idanun ta da sukai jajir sukai luhu luhu cikin murya mai sanyi ya furta trust me hubby bazan iya rayuwa ba tare da ke ba,ko da kinyi min laifi mai tsanani zan iya jurewa na zauna dake saboda irin tsananin so da ƙaunar da nake miki, ki nutsu ki kwantar da hankalin ki ki sanar da ni abinda yake faruwa da ke we will fight togther Nafeesat matsalar ki matsala tace amma kike ɓoye min please karki sake, bance dole sai kin sanar dani yanzu ba amma ina son ki zauna ki nutsu ki yi tunani kafin ki sanar da ni a shirye nake na saurari dukkan damuwar ki a koda yaushe, kaɗa kai tayi ta buɗe baki za tai magana kira ya shigo wayar sa, kamar ba zai ɗaga ba sai kuma ya janyo wayar ya ɗaga shiru yai yana sauraron mai maganar kafin yace okay sannan ya katse wayar kana ya buɗe data ya shiga watsapp, dumm! Ƙirjin su ya buga a tare sakamakon ganin hoto da vedion da aka turo masa, jiki na rawa Nuraddeen ya shiga photon, zaro idanu sukai a tare sannan suka kalli juna ganin abinda yake jiki, kafin vedion ya shigo tsananin rawa da jikin Nafeesat ke yi ya sanya shi sakin wayar ta faɗi ƙasa ya riƙo ta sai dai kafin wani lokaci zazzaɓi mai zafi ya rufe ta wanda a take ta fara jijjiga dafara na fitowa daga bakin ta.....
Meet in the next page.....
***