KUKAN KURCIYA masu iya magana suka ce jawabi ne, kuma gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah, labari ne da ke 茩unshe da gwagwarmaya, soyayya, cin amana, rudin she蓷an da dai sauran su , ku dai ku biyo ni umaimah ado gaya don jin me ya 茩unsa?

Follow Gaya Umaimah Ado at facebook

by @umaimah2024

KUKAN KURCIYA 




 BY OUM AHMAD 



     UMAIMAH ADO GAYA

( MRS.NAZEE)


zinariyar taskira 馃敺


page 19



... ***...




KARKASHIN JAGORANCIN 



馃挭馃摎馃摎

*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* 


       {T.W.A}


****

_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda Allah ya bawa ita. da hikimar mu muke Alfahari_

       

*A茩alaminmu 拼ancinmu馃挭*




Bismillahirrahmanirrahim

 


NAFEESAT: Ganin Akram ya turowa Nuraddeen photos 蓷in ya sanya ta tabbatar da cewar ya shirya tozarta ta a idon duniya hakan ba 茩aramin 蓷aga mata hankali yai ba wanda lokaci guda wani azababben zazza蓳i ya rufe ta kuma a take ta fara jijjiga wanda kafin su 茩arasa hospital ta shiga doguwar suma, don da fari ma Nuraddeen yayi tunanin ma ko zuciyar ta ce ta buga, duk dauriyar da maza ke da ita wani lokacin soyaya takan maida su ragwaye ko da ko soja ne dake fita filin daaga, kamar haka ne ga Nuraddeen Allah ya jarabce shi da matu茩ar 茩aunar Nafeesat wanda har wata rana yake tunanin tsananin son da yake mata zai iya silar zuwan sa lahira tsabar shau茩i, in ta茩aice muku labari dai Nuraddeen ya sha kuka sosai kafin daga 茩arshe shima aka bashi gado saboda fa蓷uwar da yayi tsabar yadda jinin shi yai tsananin hawa, to abu ne goma da ashirin ga 蓳acin ran ganin wani 茩ato a tare da matar sa a yanayin da shi ka蓷ai ya dace ya shiga tare da ita ga kuma halin da Nafeesar ke ciki, kasancewar lokacin da zasu fito Feenat na harabar gidan ya sanya ita tai driving 蓷in su zuwa asibitin hakan ba 茩aramin 蓷aga mata hankali yai ba ganin za'i 拼a kwance uwa kwance, sai da Nuraddeen ya samu hutun awa biyar lokacin jinin na sa ya 蓷an sauka kafin ya farka da sunan Allah a bakinsa yana 茩ara nanata innalillahi wa'inna ilihirraji'un ( kamar yadda yazo cikin littafin Allah mai tsarki cewa idan muka jarabce ku da wata musiba sai ku ce innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ) cikin ikon mai kowa mai komai Allah ubangijin mutane da duwatsu mai sama mai 茩asa mai amsa addu'ar bayin sa kamar yadda yai al茩awari ya amsa ro茩on Nuraddeen yaji sau茩i a zuciyar sa, dole ba dan yaso ba sai don ya zama dole ya kira su Ammi ya sanar dasu halin da suke ciki, sosai hankalin Ammi,Abba da ma sauran 拼an uwanta suka tashi kana lokaci guda duk wanda ke cikin garin kano ya rankayo zuwa AKTH domin ganin halin da suke ciki, ganin yadda lokaci 蓷aya Nuraddeen da Feenat sukai zuru zuru ya sanya Abba da Ammi suka danne tashin hankalin su suka shiga rarrashin su da kwantar musu da hankali, inda a nan ma sai da Nuraddeen yai kuka wanda hakan ya 茩ara tsinkawa su Abba zuciya suna masu tasbihi da baiwar ubangiji da ya ke sanya soyayya a zu茩atan bayin sa, ganin duk yadda tabon Nafeesat ke 茩o茩arin bayyana ga duniya amma Nuraddeen bai ji wani 蓷igo na son Nafeesat ya ragu a zuciyar sa ba,


   Tsawon sati biyu da kwanaki Nafeesat bata farka ba wanda hakan ya 茩ara 蓷aga hankalin su dama na likitocin domin kuwa hakan ka iya janyo matsala ga rayuwar ta, kamar gogewar wasu tunanikan abinda ke 茩wa茩walwarta,koma tai loosing memory gaba 蓷aya, cikin ikon Allah a ranar da ta cika sati uku cif ta fara motsa hannun ta, inda kamin 24hours ta fara bu蓷e idanu sai dai bata magana sai bin kowa da take a kallo duk ko mai za'a ce mata ko kuma kowaye zai fa蓷a 蓷in.hankalin su ya tashi da tunanin ko ta samu matsala ne? Amma sai likitoci suka tabbatar musu da cewar ba lallai ta samu matsala ba sai a hankali tukunna komai na ta zai zama dai dai, aikam a kwana na hu蓷u da farkawar ta Nuraddeen na zaune akan kujerar dake gaban gadon su Ammi sunje gida su yi wanka su dawo yana ri茩e da hannuwanta yana kallon fuskarta cikin zuciyarsa addu'a yake mata akan Allah ya bata lafiya kamar da wasa yaji ta 茩ara ri茩e hannayen sa cikin murya irin ta marasa lafiya ko wanda ya da蓷e bai magana ba yaji ta kira sunan sa a hankali, da farko yai tunanin ko gizau muryar ke masa don idanun ta a rufe suke, sai kuma ya ga ta bu蓷e idanun ta tana kallon cikin idanun sa take fa蓷in Noor! Bu蓷e idanun sa yai sosai bakin sa na washewa cikin 茩in茩ina saboda rikicewa ya amsa da fa蓷in Nafeesah? Are you talking? Masha Allah! Masha Allah! Alhamdulillahi ! Oh my god! My feesat ! Alhamdulillah! Murmushi ne ya su蓳uce mata ganin gaba 蓷aya ya rikice ya rasa ma abin fa蓷i ta sake ri茩e shi sosai tana fa蓷in I LOVE YOU NOOR! I LOVE YOU MORE NAFEESAT! Shima yai saurin bata amsa, hawaye ya ziraro daga idanun ta cikin murya mai rauni ta cigaba da fa蓷in kai 蓷in masoyi ne na gaskiya wanda yake tare da abin son sa duk wuya da rintsi, nagodewa Allah da ya bani kai a matsayin miji na mai share kuka na amma ina son ka sauwa茩e mun domin bana son zunubin da na aikata ya shafe ka, kana da kima da mutunci a idanun jama'a da yawa bana son sanadiyar tabo da ya zube please! Girgiza kai Nuradden yai cikin tattausar murya wadda zata iya fahimtar sa ya furta, tun daga ranar da kika tare a gida na kika zama ni na zama ke farincikin ki, damuwar ki da matsalar ki duk nawa ne, mene amfanin barin ki ki fuskanci matsalar ki ke 蓷aya? Rashin ki a kusa da ni yafi min illa fiye da abinda kike gudu ballantana kuma ma abinda kike tunani bazai ta蓳a faruwa ba domin na kai 茩ara CID kuma yanzu haka anyi tracking number an gano inda yake kuma an sanya jami'ai su kamo shi, so we must fight together and win together okay? Lumshe idanu tai ta bu蓷e tana fa蓷in what kind of man are you? You a such a man like no other ina fatan ubangiji ya bani ikon faranta maka kuma ina fata ya saka maka da mafificin alkhairi ya ji 茩an mahaifan ka, yana murmushi yake fa蓷in baki biyun ba? 茒age gira tai alamun tambaya , shi kuma ya amsa da fa蓷in Allah ya barni da Nafeesat mana kuma ya bamu yara masu albarka, ya 茩arashe da kashe mata ido guda.......




   AFTER SOME MONTH 



LATEEF: Alhamdulillah yana samun kulawa daga 茩wararrun likitoci a 茩asar America kuma yana samun sau茩i sosai don zuwa yanzu 茩urjin dake gaban sa ya warke sai dai abinda ba'a rasa ba haka nan anyi treating kwailewar da ya samu, sai dai fa 茩wayoyin sun ta蓳a masa 茩wa茩walwa inda akai masa aiki aka cire jinin da ya ha蓷u da sinadarun dake cikin 茩wayoyin suka toshe masa jijiyar kansa wanda hakan ya janyo masa loosing memory, zuwa lokacin kuma Lateefa ta samu labari har daddy yai mata viza taje dubo shi, yanzu haka shigowar ta hospital 蓷in kenan daga gidan Daddy sanye take da dogon wando falazu da rigarsa wadda ta sauko mata zuwa cinya farare tas sai jacket da veil da tai rolling black colour kamar dai takalmi da jakar hannunta, da sallama a bakin ta ta shiga 蓷akin mommy da daddy da zuwa yanzu suka maida hankali sosai akan yaran nasu yanzu suke basu kulawa sosai, sun nemi gafar Allah akan rashin kulawa da amanar da ya basu, sannan sun nemi gafarar yaran su duk da Lateefa baya hayyacinsa, suka amsa sallamar da murmushi akan fuskar su, daddy yace yauwa daughter gara da kika zo Kinga wannan yayan naki ya茩i kar蓳ar Abinci sai Lateefah yake cewa, da hanzarin ta ta 茩arasa tana fa蓷in Allah sarki yaya na wato ka gane me baka abinci ko? Murmushi Lateef yai yana mi茩a mata hannu yana kiran sunan ta, hawaye ne suka ciko idanun ta, ta ri茩e hannunsa tana murmushi sai kuma ta fashe da kuka tana fa蓷in Allah ya baka lafiya yaya, Allah ya dawo maka da tunanin ka, mommy rungume ta itama tana kuka shima daddy duk dauriyar sa yau sai da yai kuka yana Allah wadai da irin son duniya irin tashi da ta matar sa wanda ta kai su ta baro, Allah yai musu kyautar yara abu mai daraja wanda wasu da dama suke nema inda za'a ce su bada duk abinda suka mallaka domin a basu yara da sunyi, amma su da suka samu suka watsar da su da kulawa da tarbiyyar su har 蓷aya cikin yaran nasu ya fa蓷a babbar halaka na tsawon shekaru a ce matsayin su na iyaye basu sani ba, Allah astagfirullah! Allah astagfirullah, a 蓳angaren mommy itama abinda ya sanya ta kuka kenan tana takaicin son duniyar ta fiye ma da mijinta, me yasa duk da bata rasa komi daga mijin ta ba amma ta kasa zama tare da yaran ta ta basu kulawa? Duk da ita a nata tunanin rashin mijin ta a kusa da ita zai fi damun ta idan ta zauna a gida amma idan tai keeping kanta very busy ba zai dame ta sosai ba, wani 蓳angaren na zuciyar ta kuma yana tuhumar ta akan rashin zama tare da su idan ta dawo daga aikin, wanda hakan ya samo asali ne da yawan gajiya da take 蓷ebowa tana bu茩atar shiru domin ta huta, Amma daga yanzu tayi alwashin bazata 茩ara zuwa wani aiki ba ko da hakan na nufin 茩arewar duk wani Abu da ta tara,Lateefa kam tana kuka ne saboda ganin yayan ta wanda ya raine ta tun tana jaririya yai 蓷awainiya da ita ya bata kulawar da uwa da uba suka kasa bata, ya bata abinci, yai mata wanka, ya kaita makaranta har ta girma amma yanzu shine ya koma tamkar wani 茩aramin yaro, tabbas babu da bara babu 茩arfi sai da Allah, shine yake yin abinda ya so a kuma sanda ya so, zai bar mutum yai ta aikata sa蓳o ya kuma bashi damar tuba idan kuma ya 茩i? Ya hukunta shi dai dai da abinda ya aika ta, ya Allah ka gafartawa wannan bawan naka badan komai da kowa na sa ba, sai don darajar ka da soyyyar ka da bayin ka, 


   Daddy ne ya fara 茩arfin halin goge hawayen sa ganin shima Lateef yana kuka ganin yadda kowa yake kuka, ya dafa kafa蓷ar mommy da Lateefa yana fa蓷in is okay please kun ga kunsa my boy kuka ko? Suma ganin Lateef yana kukan ya sanya sukai shiru Lateefa ta shafa kansa tare da jan kumatun sa tana fa蓷in daddy始s boy sorry kaji kai shiru mun daina, 蓷aga kai yai kawai yana kallon su ganin suna masa murmushi wanda a gurin su na ya茩e ne ya sanya shima yai shirun, abincin da hospital 蓷in ke bawa patient 蓷in nasu ta sake zubawa ta dawo ta zauna zata bashi sai dai tunda ta fara zubawa zuciyar ta ke tsananin tashi ta daure dai tana mamakin abinda zai kawo mata tashin zuciya wanda in dai ba period 蓷in ta ne zai zo ba sam ba ta yi, period! Kalmar ta maimaitu a zuciyar ta tunawa da tsawon lokaci bai zo ba kuma sam hankali ta bai kawo kai ba, ta bashi cokali biyu a na ukun wani 茩a茩茩arfan amai ya taho mata ta tashi da gudu da niyyar shiga ban蓷akin dake cikin 蓷akin amma ya 茩wace mata kafin ta shiga ta dur茩ushe ta fara zubo shi ta baki ta hanci ga wani sarawa da kanta ya 蓷auka lokaci guda, haka nan cikin nata ya fara hautsinawa, gaba 蓷aya suka rikice suka rasa yadda zasu yi, kafin mommy ta dur茩usa ta ri茩e ta ganin tana layi daga dur茩ushen shi kuma daddy ya danna 茩ararawar kiran nurses, wanda in less than minuet wata gajeriyar baturiyar nurse ta shigo, kai tsaye da Lateefa ta fara cin karo hakan yasa tai kanta ta taimaka mata har ta gama sannan ta shigar da ita toilet ta 蓷auraye jikin ta, ta sanar da su mommy dole sai dai a bata nata 蓷akin daban don haka daddy yace mommy taje ta zauna da ita shi zai kula da Lateef 蓷in wanda yake kuka ganin halin da Lateefa ta shiga, haka kam akai aka kai ta wani 蓷akin daban sannan aka 蓷ibi jinin ta don testes bayan doctor ya duba ta ya mata tambayoyi,sannan akai mata allura aka sanya mata drip don ta samu kwari da bacci don ba 茩aramin galabaita aman ya sanya ta ba, cikin 茩an茩anin lokaci nurse ta dawo da result inda ya nuna Lateefa na 蓷auke da ciki har na tsawon wata biyu, sosai mommy da daddy sukai murna har da Lateef da bai san murnar me ake ba.




NAFEEST: Bangaren su Nafeesat ma kam sai dai mu ce masha Allah! Domin ko zuwa yanzu ta warke sumul kuma basu da kowacce irin damuwa sai ciwon zuciya da ya kamata a wancan lokacin kuma likitoci sun 蓷ora ta akan magani, yayin da Nuraddeen da Feenat suka dage gurin kulawa da ita da kare dokokin maganin ta, haka nan duk wasu dangi da masoyan ta suna 茩o茩arin ganin sun faranta mata, sai dai zuwa yanzu duniya ta san dacewar twins yaran Lateefa ne da akai mata fya蓷e ta haife su don sai da aka shigar da 茩arar Akram zuwa kotun musulunci bisa zargin yin fya蓷e tare da 蓷aukan hoton tsaraici yana barazana dashi, inda kotu ta yanke masa hukucin 蓷aurin rai da rai a gidan gyaran hali tare da horo mai tsanani sannan cikin ku蓷in da ya tara kotu ta mallakawa su twins kaso 蓷aya cikin uku na dukiyarsa ,


  Zaune suke gaba 蓷aya akan kujera suna fira, kamar yadda hakan ya zamar musu 蓷abi'a tun bayan daidaituwar lamura, Nuraddeen ya kalli Nafeesat yana fa蓷in " baeby ki taya ni da yiwa bestie magana akan bawa wani dama cikin wa蓷anda suke zuwa neman soyayyar ta dama itama tai aure, murmushi Nafeesat tai tana kallon Feenat da ta turo baki tana hararar Nurddeen ta gefen ido tana fa蓷in to kin dai ji bestie, Lah baeby wai iya abinda zaki ce mata kenan? Nuraddeen yai saurin katse maganar da Feenat ke shirin yi, dariya suka saka gaba 蓷aya kafin Nafeesat tace Noor shi fa aure lokaci ne idan lokacin sa yai dole a yi shi, sai dai abinda ka fa蓷a gaskiya ne, don masu iya magana na cewa alamar 茩arfi yana ga mai 茩iba, alamun auren shine ta saurari wani su fahimci juna, sai dai nasan tunanin da take tana ganin kamar duk wani wanda zai zo cikin rayuwar ta kamar dai tsohon mijin ta ne, wanda ya nuna mata tsananin soyayya kafin aure yayin da akai aure kuma ya shuka mata 蓳acin rai wanda har zuwa yanzu bai goge a zuciyarta ba, so please kowa cikin ku yayi ha茩uri kai kar ka matsa mata ke kuma ki yi 茩o茩ari ki bu蓷e zuciyar ki ki kuma nemi taimakon Allah insha Allah zai taimaka miki kuma cikin ikon sa abinda kike gudu bazai faru ba, ka蓷a kai Feenat tai tana fa蓷in insha Allah bestie matar bestie zan yi abinda kika ce Allah ya tsare ni ya kuma kare ni daga sharrin maza irin su suhail, gaba 蓷aya suka amsa da Ameen, Nuraddeen ya mi茩e yana fa蓷in bari na shiga cikin gari zuwa jimawa ka蓷an zan dawo babe ki tanadar min something special , murmushi kawai tai tare da mi茩ewa itama don tai masa rakiya yayin da ita kuma Feenat tai masa addu'ar dawowa lafiya daga nan, sai da suka je corridor ya janyo ta zuwa jikin sa yana fa蓷in babe zanyi kewar ki , nima zanyi kewar ka fiye da yadda zaka yi kewa ta, sannan bana son ka ji ko ka ga duk wata mace a waje bayan ni ka dai gane ai, ta karasa maganar tana 蓷age masa gira, yai saurin cafewa da fa蓷in " ni ko na gane domin ko yadda kike bani soyayya da kulawa ya sanya duk wasu sauran mata idan na gansu suke koma min tamkar namiji kinga ko namiji mai zai yi da namiji, dariya ta sanya tana fa蓷in un un fa Noor kar naje fa ni ka maida namijin yanzu ma gurin yar wata shawalwalar zaka, ya wani waro idanu yana fa蓷in haram! Wallahi haram ina ni ina maida ke namijin bayan duk abinda kike bani kin manta yanzu ma cewa nai ki tanadar min something special? To idan namiji ne ina ni ina sanar mi shi? No ba wannan maganar ke ni sai na fasa fitar ma wallahi mu wuce 蓷aki kawai kema dai kin san don kin hana nai wani 茩wa茩waran motsi ne gaban Feenat wallahi da tuni na sa蓳e ki a kafa蓷a mun wuce, zaro idanu tai tana fa蓷in no tafi kawai Allah ya tsare ka gaida 拼an gari, ri茩o hannun ta yai yana fa蓷in ai ko wallahi baki isa ba ko 蓷an kiss ai kin bani ko?..........



 Meet in the next story 


***