KUKAN KURCIYA masu iya magana suka ce jawabi ne, kuma gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah, labari ne da ke ƙunshe da gwagwarmaya, soyayya, cin amana, rudin sheɗan da dai sauran su , ku dai ku biyo ni umaimah ado gaya don jin me ya ƙunsa?

Second to the last

by @umaimah2024

KUKAN KURCIYA 




 BY OUM AHMAD 



     UMAIMAH ADO GAYA

( MRS.NAZEE)


zinariyar taskira 🔷


page 20

...


... ***...




KARKASHIN JAGORANCIN 



💪📚📚

*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* 


       {T.W.A}


****

_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda Allah ya bawa ita. da hikimar mu muke Alfahari_

       

*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*




Bismillahirrahmanirrahim




HASEEB : Da sassarfa yake saukowa daga stairs yana kwalawa Haseeya waya, Haseeya dake kitchen tana haÉ—a break fast ta fito da hanzari tana faÉ—in honey lafiya kuwa wannan kira haka daga fitar ka? Murmushi mai haÉ—e da dariya yake kafin ya Æ™araso inda take ya sunkuce ta gaba É—aya yana juyi da ita sai ubangiji yakewa tasbihi hakan ya sanya itama take taya shi don ta tabbatar ko menene sai da ya gaji sannan ya sauke ta yana nishi da faÉ—in kai baby kin Æ™ara nauyi wallahi, dariya tai tana faÉ—in kai dai kace mata biyu sun maida kai rago ko? Haba dai ai kema kin san ni ba rago ba ne wallahi idan kuma kin musa..... Nope ban musa ba ma back to abinda ya sanya ka farin ciki, sai da ya Æ™ara sakin murmushi wanda ita kanta Haseeya da suka taso tare bata taÉ“a ganin shi yana yi ba more especially kwana biyu da Æ´ar gwal É—in sa bata nan walwalar sa ta rago kafin maganar sa ta katse mata tunanin da ta lula, guess what? Ta juya idanu tana faÉ—in ko ka samu contract É—in ne? Ya kaÉ—a kai yana faÉ—in but kafin samun contract É—in na fara samun kiran daddyn Lateefah he is telling me that i am going to be a father very soon, wani irin hajijiya taji kanta na yi don sai da tai saurin dafe gini kafin ta fara ambaton Allah cikin ranta, tayi Æ™oÆ™ari matuÆ™a gurin ganin ta É“oye damuwarta maimakon ma haka sai ta bayyana tsantsar farincikin ta tare da faÉ—in Alhamdulillah! Masha Allah! Kace mun kusa mu fara samun iyali Allah ya bada mai albarka ya raba su kuma lafiya, Amin tawan kema nasan kina tunanin matsalar ki ko? Insha Allah ubangiji zai dube mu kema very soon ki samÉ“alo mana babies É—in mu masu kama da ke da wannan hancin naki mai kamar tasa, kai! Yaya tasa kuma? Ta faÉ—a da shagwaÉ“a ya kece da dariya wadda ta san har zuwa yanzu ta farin cikin É—azu ne kafin yace yauwa kar na manta ki shirya nai mana booking flight zamu dubo Yaya Lateef daga nan kema sai ki ga gynaecologiet ko? Wayyo! Yaya are you really sure? Amma nagoÉ—e Allah ya biya ka Allah ya sauki Lateefa lafiya, Ameen matar yaya, bari na koma sama na Æ™arasa miki mopping É—in kamin ki haÉ—a abincin, No yaya ai kawai ma yau ka barshi farin cikin da ka sanya ni ma ji nake kamar naiwa gidan nan wanka tas tun daga sama har Æ™asa, dariya Haseeb ya sanya yana faÉ—in you are not serious madam oya! Kowa ya koma bakin aikin sa......




  FEENAH : Bestie albishirin ka? Sai da Nuraddeen   yai shiru na wasu dakku kafin yace goro, ta mika masa hannu tana fadin wallahi sai ka biya zan fada maka, tsaki ya Dan ja kafin yace to dame zan biya? Da Abu Mai matukar daraja a gurin ka don wallahi albishir din da zan sanar maka ma idan ka ji sai ka Kara min na sani, okay to shikenan na baki gidana na Alaro city, sai da ta É—age gira for some seconds kafin tace okay rufe idanun ka, dafe kai yai yana faÉ—in oh my Allah bestie ki bar ni naje naga matata mana! Turo baki tai tana faÉ—in Allah bestie ko? Sorry, yai saurin faÉ—a kafin ya rufe idanun nasa yana faÉ—in na rufe, takardar dake hannunta ta saka masa a ciki tafin hannun sa, kafin tace oya open your eyes, da sauri ya buÉ—e idanun nasa ganin takarda a naÉ—e ya sanya shi saurin buÉ—ewa, waro idanu yai bayan kammala karanta abinda yake ciki bakin sa ya kasa furta komai haka nan ya kasa rufewa kafin lokaci guda ya zube Æ™asa yana mai sujjada ga ubangijin sa, ba komai takardar ke tattare da shi ba face shaidar scanning da Nafeesat da Feenah suka je Asibiti akai ma Feenan ba wanda ya nuna sabuwar mahaifar da ta tsiro a cikin Feenah ta girma a kowane irin lokaci kuma idan tana da aure zata iya samun ciki, tsananin murnar da Nuraddeen ya nuna ya sanya Feenah ta Æ™ara jin matuÆ™ar Æ™aunar sa, tabbas samun É—an uwa mai kulawa da lamarin Æ´an uwansa yana da wahala a wannan lokacin amma ita kam tai sa'ar samun Nuraddeen a matsayin É—an uwa tana fatan Ubangiji ya bata ikon farantawa rayuwar sa fiye da yadda yake faranta mata, bayan ya É—ago daga sujudush shukur É—in Feenah ta riÆ™o hannun sa tana faÉ—in another albishir É—in ya ware idanu yana sauraron ta a tunanin sa zata ce masa ta samu mijin aure sai yaji tace we are going to be a parent insha Allah nan da wata baÆ™wai, yamutse fuska yai alamun ya shiga confuse ganin haka yasa tace Bestie na da ciki for almost 2months, bayan munje Asibitin wai taji bata son Æ™amshin Asibitin sai ta fara jiri da tashin zuciya kafin mu taho sai da tai amai har sau uku shine muka tsaya aka duba ta unexpectedly kuma sai result ya nuna tana da juna biyu, shine suka saka mata ruwa saboda jikin ta yai weak suka bata magungunan da zasu taimaka mata yanzu ma ta sha bacci take yi, wayyo farin ciki ina zai saka Nuraddeen Albishir da abubuwa masu matuÆ™ar daraja a gurin sa a lokaci É—aya, ya dubi Feenat yana faÉ—in ki faÉ—i duk abinda kike so ni kuma in dai ina da iko akan sa zan miki da yardar ubangiji, murmushi feenat tai tana faÉ—in ba abinda yanzu nake buri face idan har Allah yayi muna da rabon yara a duniya mu sake Æ™ulla zumuncin mu yafi haka Æ™arfi ta hanyar haÉ—a yaran mu aure, what amazing? Feenat kin gama cika min zuciya da farin ciki sai nake jin farin cikin da kika saka ni yaiwa zuciyata yawa kar ta fashe, dariya Feenat tai sannan tace kai ta godiya ga Allah kana masa tasbihi zai dai dai ta maka farin cikin ka da zuciyarka.....


  Digimi: Cikin watanni bakwai da Nafeesat ta Æ™ara kafin Allah ya sauke ta lafiya taga tattali, idan aka ce tattali to tattalin ake magana ba wai muna tattali ba, ba ga Feenah ba haka ba ga Nuraddeeen ba, sosai suke kula da ita musamman da shima wannan cikin yazo mata da laulayi kamar da na su twins har na wannan ya kere na twins, takanas Feenah ta ajiye aikin ta take kula da ita kama daga duk wani abu da zata iya ci, tausa, aikin gida wanda ba ma'aikata ne suke yi ba, da ma duk wani abu da zata buÆ™ata yayin da shi kuma Nuraddeen yake É—orawa daga inda ya tsaya, haka nan su Ammi a rana sai ta kira waya ba adadi don kawai taji lafiyar yainyar tata saboda ganin irin nata laulayin mai wahala ne, soyayyah dai kam ta sha ta har tai mata yawa sam sam Feenah bata gajiyawa da yi mata hidima, ko da cikin ta ya tsufa ta fara masifa haka Feenah ke shanye duk wani abu da Nafeesan za tai mata kafin daga baya tace tayi haÆ™uri bata san me ya hau kanta tai ba, a haka a haka har Allah ya sauke ta lafiya, in da ta sake haifo kyawawan yaran ta biyu suma kuma mace da namiji, a rananr kam Nafeesat ta sha kuka ganin irin yadda new twins suka samu kyakkyawar kulawa fiye da wadda twins suka samu, duk da cewar suma ba'a Æ™yamace su ba amma ba'a nuna tsantsar shauÆ™in samun su ba kamar waÆ´an nan, 


  Nuraddeen kam yai bajin ta domin kam ya zage ya kawo komai da mai jego da babies É—insa zasu buÆ™ata dai dai aljihun sa, kama daga sutura da abinda zasu ci, dama duk wani abu da ya dace ga lafiyar babies da mahaifiyar su, a kuma ranar ne aka raÉ—awa yaran suna da NAFEESAT & NURADDDEEN yayin da Feenah tai musu alkunya da Farha da Farhan, Ranar suna kam anyi bidiri duk da ba kiÉ—a akai ba sai ma walima da akai aka gayyaci malamai sukai wa'azi da nasiha haÉ—i da jan hankali akan tarbiyyar yara, sosai iyaye da dama jikin su yai sanyi da wannan wa'azi inda yawancin su suka É—au É—amarar bawa yaran su tarbiyya iyakar Æ™arfin su, an ci an sha sannan an raba littafin Azkar da kuma littafi mai tsarki wato Al'qur'anil kareem sannan aka baiwa kowa takeway na snacks da key holder, memo da jaka masu É—auke da hotunan twins......





LATEEF : Watannin sa shiÉ—a a asibiti aka sallame shi bayan an masa aikin da aka kashe dukkan tsutsokin da masu homo suke samu wanda suke hana su daina harkar kuma Alhmadullillah anyi nasara sai dai har zuwa yanzu memoryn sa bai dawo ba, amma likitan ya tabbatar musu da cewar ba jimawa zai warke tunda yanzu ma wasu lokutan wasu abubuwan suna faÉ—o masa cikin tunani, kamar yadda Haseeb yace sun zo sun duba Lateef sannan Haseeyah taga gynaeologist inda ya É—ora ta akan magunguna da shawarwari tare da yi mata albishi da cewar matsalar ta ba babba bace musamman da ta tari abin da wuri, tare da Lateefa suka koma gida duk da bata so ba, amma Haseeb ya dage sai sun tafi tare in ba haka ba kuma ya kashe aikin sa ya zauna tare da ita a asibitin, su dai su daddy ganin Haseeb ya dage ya sanya suka goya masa baya ko dan matar sa da Haseeb ba ruwan sa a gaban ta ya tata rashin kunyar sa na dole ya tafi da matar sa ko su zauna gaba É—aya, ita kam Haseeya tasan Haseeb yana son ta sosai amma tabbas son da yakewa Lateefah na daban ne ita ma shaida ce duk da yana faÉ—in shi abu É—aya ya É—auke su, itama sai da ta sanya baki sannan Lateefa ta yarda suka koma gida Nigeria suka cigaba da rainon cikin Lateefan, musamman ma Haseeb da bai haÉ—a cikin nan da komai ba, komai ya kwaso yace baby, hirar sa ta koma ta baby shiga É—ari fita É—ari baby, duk wanda yake tare da Haseeb to har gajiya yake da labarin baby, idan ya fita aiki kam sai ya kira waya yafi sau goma kafin ya dawo idan ko ya kira basu É—aga ba sai ya dawo yaga ko lafiya? Sosai Haseeya tai nadamar da bata da amfanin ganin yadda Haseeb yake son yara amma ta zubar da nata a rariya a banza a wofi wanda hakan ya janyo mata guzurin kishiyar da tafi ta samun gurbi a zuciyar mijin ta haka nan zata haifi yaran da zasu fi nata samun gurbi a zuciyarsa idan ma tana da rabon yaran kenan.....





  BAYAN SHEKARA ÆŠAYA


   FEENAH: É—auke take da farha a hannun ta dama yayin da mai aikin Nafeesat ke É—auke da Farhan bayan su kuma ma'aikatan mall É—in da suka zo siyayya ne, kamar almara tai gamo da wanda tsawon shekara da watanni take riÆ™e da shi a zuciyar ta, duk ko da cewar gani guda sukai wa junan su amma sam ta kasa mantawa dashi a zuciyar ta, kallon kallo sukewa juna kafin ya miÆ™awa Farha hannu yana faÉ—in baby , saurin miÆ™a masa nata hannun tai tana mai gwaranci ai kam ya karÉ“e ta yana biye mata, murmushi Feenah tai tare da buÉ—ewa ma'aikatan motar da suka zo da ita suka saka musu ledojin su, kafin ta maida hankali kan Farha tana faÉ—in oya princess muje ko? Lafewa ta sake yi a jikin Lateef tana faÉ—in a'a dariya ya sanya yana faÉ—in sorry baby kar Abban ki yai fushi da sai na karÉ“e ki na kai mata an jima , murmushi kawai Feenah tai don tasan Lateef yai tunanin ko yaran ta ne, ya Æ™ara da faÉ—in maman baby kice Allah ya cika miki burin ki gashi nan ya baki kyawawan yara masha Allah a Æ™anÆ™an lokaci ina fatan Ubangiji ya sanya ni a danshin ku, dariya Feenah tai wadda ta sake bayyana kyawun ta kafin cikin muryar da bata san tana da ita ba ta furta, Oh sorry Farha da Farhan yaran brother na ne, my twin brother, sauke ajiyar zuciya yai yana faÉ—in Alhamdulillah kice na huta zuwa asibiti domin nai tunanin har kin yi aure kin haihu na rasa ki har na fara tunanin daga nan sai Hospital nace musu su cire min zuciya ta kawai na huta, waro idanu tai tana faÉ—in why? duk da ta fahimci abinda yake nufi haka nan Æ™asan zuciyar ta wani irin farin ciki ne, wayar sa ya zaro tare da miÆ™a mata yana faÉ—in your number please zan sanar miki komai kinga yanzu akwai baby kar na koya mata soyayya da wuri, sunkuyar da kai kawai Feenah tai tare da sanya masa number , ya amsa da godiya sannan yace Lateef shine suna na mark it in your heart please!.......


Umaimah Ado Gaya 



TALLAH!


   NIFA DUK WANDA YAKE SON YA NUNA MIN SOYAYYA TO KAWAI YA SAI ABINDA NAKE SIYARWA, TO EH MANA, INA TA FAMAN ƘOƘARIN NA DAGE GURIN GANIN MATA SUN SAKE HASKAWA SUN ƘARA MAMAYE ZUCIYOYIN MASOYAN SU DAMA ƘARA JIN ARMASHIN RAYUWAR SU AMMA BAKI MALLAKI NAKI BA? 



SHIN KINA IYA JUYI KI SHEWA KI GWALLI GABAN ABOKIYAR ZAMAN KI TARE DA TUTIYAR KIN KERE MATA A GURIN ADO DA KYAUN FATA?DAMA GURIN MAI HOUSE? 


  KINA FAMA DA MATSALAR CIWON SANYI KO KUMA NI'IMA KOMA GABA DAYA? KO BUDEWA CE MAI MIKI YAWA? 


MUNA DA KASAITACCIYAR MACE AKWAI PIECES AKWAI SAITI NA MAGANIN SANYI, NA NI'IMAH, NA MATSI , AKWAI SABULUN TSARKI, AKWAI HADIN MAN HEAD QUATER, AKWAI HADIN SIT BATH DA NA KAMA RUWA, AKWAI ZUMAR MATA MAI KYAU DA GUMBA GA KUMA DAKA DUK A FARASHI MAI RAHUSA.



  INA AMARYAR DAKE SHIRIN SHIGA GIDAN MIJI? KO KUMA UWAR AMARYA? MUNA DA HADIN AMARYA TUN DAGA KAN MAGANIN SANYI HAR NA GYARAN JIKI CIKI DA WAJE, AKWAI HADIN DILKA DA TURARUKAN WUTA NA KECE RAINI,




  INA MAI FAMA DA MATSALAR FATA KAMA DAGA KAN PIMPLES, TABO, BLACK EYES, WASKANE BUSHEWAR FATA DA TSAGEWAR TA? TO KU MATSO SHIMA MUNYI MUKU TANADI NA MUSAMMAN NA KASAITACCIYAR MACE DAGA KAMFANIN YAR GAYA SCENT AND SKIN CARE PRODUCT 


AKWAI : 


1.SABULUN GYARAN FATA

 2. MAN GYARAN FATA

 3. SCRUB NA GYARAN FATA, AKWAI NA MASU KURAJE DABAN AKWAI NA MARASA KURAJE

 4. SHOWER GEL

 5. SHAMPOO

 6. MAN GYARAN GASHI

 7. KWALAKCAM

 8. FARAR HUMRAH

 9. BAKAR HUMRAH DAMA KALOLI DABAN DABAN 

10. TURAREN HAAWII

11. TURAREN KABBASA

12. TURAREN GAFGAF

13. TURAREN HALUT

14. TURAREN SANDAL

15. TURAREN FARCE

16. TURAEN DAMBU

17. HADIN TURAREN TSUGUNO NA MUSAMMAN


AKWAI SIYAN DAI DAI AKWAI NA SARI MUNA MARABA DA KOWA, KINA TARE DA HADIN KASAITACCIYAR MACE NA YAR GAYA SCENT AND SKIN CARE PRODUCT KE ZINARIYA CE 😃