2
Ba ita ta farka ba sai wajen ƙarfe biyu na rana, duk da carpet ɗin da ta kwanta babu laushi hakan bai hana ta sharar baccin ta ba.
Tana tashi ta nufi banɗaki ta ɗauro alwala sannan tayi sallah, babu addu'a babu komai ta miƙe ta koma kan gadon ta ta kuma ja zanin gadon ta rufe jikinta.
Har baccin ya fara nisa taji ana jan abin rufar a hankali, tana buɗe ido taga Meenah, nan da nan ta murtuke fuska, cike da masifa ta hayayyaƙo mata har da kai mata duka, Meenah ta kauce da sauri, ta fice tana ƙwafa.
Lokaci guda ta ji kamar ana nannaɗo ta da ita da abin rufar tata, can ta ji an fincike abin rufar ma baki ɗaya. A razane ta miƙe za tayi masifa sai kuma ta koma ta zauna ganin ba Meenah bace tana zazzare idanuwa.
Umar yana kallon ta yace "Ina aikin da na saki?" Tayi masa shiru.
Ya daka mata tsawa, "ina magana kin yi min shuru, ehh! in ban kakkarya ki ba, 'yar rainin hankali tashi ki fice, "useless".
Yanda ya hayayyaƙo mata yasa ta fice ba shiri tana ƙunƙuni. Har ta shiga kitchen ɗin ta jiyo shi yana faɗa. "Ba ki yi sallar ba za ki fara aikin? Idan kika bari na ƙaraso nan se kamannin fuskarki sun canza, ni wallahi na rasa irin ki Arfa, malalaciyar banza da wofi kawai, wallahi kaf gidannan nine nan zan yi maganinki, kuma wallahi kikai wasa yau sai na ruɗa niki fatar jikin ki."
jikin ta ya fara rawa sosai, Allah ya zuba ma ta tsoron Umar ba kaɗan ba, saboda abu kaɗan ke sawa ya kai mata duka, kamar dai jira yake ko fata ma yake ya ji ta yi laifi, ko kaɗan ba ya raina abin duka.
Tana idar da sallah ta koma kitchen, duk wani abu da ke kitchen ɗin se da ta ɗaga ta goge komi ta gyara. Tana haki ta fito daga kitchen ɗin wujiga- wujiga da ita, dai dai lokacin da ake kiran sallar Magriba....
Suna dinning baki ɗaya iyalan gidan. Arfa ta saka abaya ruwan madara, hankali kwance take cin abincin safe, duk da yadda ta ga Umar ɗin na sauri bai sa ta matsawa kanta da cewa itama saurin za tayi ba.
Umar da har ya kai lomar ƙarshe ya dubi plate ɗin dake gabanta, gani yayi kamar ma da yanga take cin abincin, sanin zata ɓata masa lokaci ne yasa ya kafe ta da idanu, so yake ta ɗago kanta kawai ya aika mata da saƙo dan yasan idan ma yayi magana Abba goya mata baya zai yi amma ta ƙi.
Ganin ta ƙi kallonsa ne ya sa ya miƙe tare da yima su Abba, Ammi da Khaleel sallama zai fice, ya tsaya yana jiran ta tashi su fita tunda Abba yace shi zai riƙa kai ta, Khaleel kuma ya ɗauko ta.
Kamar ba ta san za su fita ba haka ta cigaba da cin abincinta. Khaleel da tun tuni ya gano plan ɗin ta yayi murmushin ƙasan maƙoshi sannan ya matsa kusa da ita a hankali, yanda ita kaɗai za taji abinda yace, yana murmushi yai ƙasa da murya yace, "toh ki yi sauri dai dan Allah Arfa, kinga fa Umar yana jiranki".
Da sauri ta rufe bakinta tana ƙaƙarin amai ta miƙe tayi hanyar corridor, Khaleel ya yi saurin bin bayanta tare da Ammi, Umar ma kamar zai bita sai kuma ya tsaya.
Ta kuskure bakinta bayan ta zubar da abincin da ya maƙale, suka komo tana ta narkewa a jikin Khaleel tana yi masa kukan shagwaɓa. Umar ma dai hankalinsa ya tashi da yaga tayi amai, ya yi mata sannu, sannan ya sa kai ya fice bayan ya sake yi ma su Ammi sallama.
Abba ke tambayar abin da ke damin Arfa, ita kuma sai ce musu take babu komi, ƙarshe dai tace ta warke ta kalli Khaleel tace: "Yaya, ko kai za ka ajiye ni a makarantar?" Sai da ya kusan tuntsura dariya saboda lamarin Arfa, don tuni dama ya gano ta, ba ta son fita da Umar ɗin ne kawai.
Ammi ma tayi dariya tace, "Arfa ai sai yanzu na gano ki, fita ce ba fa ta son yi da Umar, wallahi ki kiyayi wannan yayan naki, ko da yake ai Abba ne ke ɗaure miki gindi Umar ɗin yayi maganinki...