NIKAAH (Marriage for rent)

13 NIKAAH Rental Marriage

by @hanaady

NIKAAH

    (Marriage for Rent)


            By 

     AUTHOR  HANAADY

    (Rahama Aminu Bala)




 WhatsApp

 ***


Follow me on Whatpad

Rahama000



HE HAD THE COURAGE 

TO REMARRY.

WILL HE FIND THE COURAGE TO

LOVE AGAIN?








Page 13 


________Cikin yanayin kunya tace kana tunanin damuwana akan haihuwar Jummai ne, d'ago fuskar ta yayi sannan yace Karime nayi tunanin damuwar akan babyne . Murmushin takaici tayi sannan tace bashi bane.


Then menene?Ba zan iya cewa ga ainafin damuwana ba .


Shuru yayi na wasu y'an sec,daga bisani gyaran murya yayi sannan yace please kiyi k'okarin cire duk wata damuwa dake damunki, d'an Adam baya ta'ba rayuwa babu problem so please ki manta komai watarana sai labari.


 Kirane ya shugo wayar sa ko kallon wayar baiyi ba hakanne yasa tace ka d'aga mana d'an ta'be baki yayi sannan yace bana son takura Karima , I'm family man da zata kirani at this time, wula'kanci babu kyau Karime ta fad'a tana mai danne abunda take ji cikin ranta ,wani kiranne ya kuma shugowa , picking call d'in yayi tareda saka handsfree, ajiyar zuciya Alia ta saki sannan tace finally ka d'aga kirana ,what do you want Alia murmushi tayi sannan tace just to hear your voice ,ina matuk'ar missing naka Ramadan ,all years da aka dauka a kowane lokaci a kowane rana babu abunda nake sai tunanin ka ,nayi regretting actions d'ina akan rabu dakai but kayi mun uzuri ba komai bane ya haddasa mun hakan ba sai tsananin kishin ka, you are my King ,I will always be your Queen d'an gyran murya yayi sannan yace Alia if you don't mind mu kwana lafiya,saurin katse shi tayi ta hanyar cewa I love you Ramadan , Shuru yayi na wasu y'an da'ki'kai sannan yace good night had'i da katse kiran.Samun mai sonka a duniya dad'ine Karime ta fad'a cikin dauriya,she left me Karima,cikin wani yanayi yayi maganar ,tashi zaune Karime tayi sannan tace ba kaji me tace ba soyayyar da take maka itace ta haddasa mata kishin ka so ni a ganina ta cancanci a mata uzuri and kada ka manta abunda mahaifiyar neke so ,tashi zaune shima yayi yana fuskantar ta,hannunsa ta kama sannan tace kayi k'okarin yin abunda mahaifiyar ka take so idan har bai sabawa shari'ar Allah ba da ido yake binta yasan duk abunda ta fad'a gaskiya ne ,nuna kanta tayi sannan tace kaga mahaifina yayi mun laifi ta hanyar bayar da aurena bisa haya ,idan naso zan iya guduwa daga gidanku Amma ban aikata hakan ba sabida ina son bin umarninsa duk da sam baya nuna mun soyayya ko kauna matsayina na d'iyar sa ta cikinsa idasa maganar tayi da sakin kuka ,kuka take sosai sauke legs d'inta daga saman bed d'in tayi idanuwa ya zuba mata yana mai jin tausayin ta, sauka tayi daga saman bed d'in tareda nufar k'ofar fita ,ina kuma zuwa Karime ?

Saida ta d'an share hawayen fuskar ta sannan tace d'akina acan nake ra'ayin kwanciya,koda ta kai ayar maganar ta gaba tayi abunta.

Ajiyar zuciya Ramadan ya saki tareda saukkowa saman bed d'in,bin bayan ta yayi .

Kwanciya tayi saman bed d'in ko hasken d'akin bata sami kashewa ba ,lumshe idanuwan ta tayi tana mai zubar hawaye, ya dad'e bak'in k'ofar bedroom d'in ta sosai yake jin tausayin Karimatun sa ,takawa yayi zuwa gareta bakin bed d'in yayi knelling tareda shafa bayan ta kasancewar ta juya masa baya, batareda ta juyo ba tace mijin Sa'ada biyo ni kayi ?Laifine dan miji ya biyo matar sa?

Juyowa tayi tana fuskantar sa ,shafa gashin kanta yayi had'i da sakin murmushi, shagwabe fuska tayi sannan tace nidai ka tafi d'akin ka ,nayi laifine matata ake korana ?

Nidai ka tafi ,ya fahimci bata son takura ya sani daurewa kawai take akan abunda ya faru gidan su , mi'kewa yayi tareda nufar k'ofar fita,Mijin Sa'ada ta kira shi saurin juyowa yayi fuska a sake a tunanin sa ko cewa za tayi ya dawo , please ka kashe mun hasken d'akin kafun ka fita , fara'ar fuskar sa sauka tayi kashe hasken yayi tareda ficewa.Ajiyar zuciya tayi tareda lumshe idanuwan ta sam maganganun Maman Jummai basu b'ata mata rai ba idan da sabo ta saba ,zaune ta tashi tareda yin tagumi hannu biyu biyu,tana matuk'ar kaunar Mijin Sa'ada sai dai me har yanzu ta kasa gane inda ya dosa akan me yake sakar mata fuska had'i da janta a jikinsa tasan dai ba maganar soyayyar domin his heart belongs to Sa'ada abu d'aya ne take da confidence akan mijin Sa'ada shine yana tausayin ta akan yanda Mahaifinta ya bayar da ita haya , kwanciya tayi tareda dafe saitin zuciyar ta firarsu da Alia ne ya fad'o mata a rai murmushin takaici tayi sannan tace dole na koyi rayuwa babu shi ,dole na rage shige masa kona samu zuciya ta ta daina sonsa da kaunar sa.


A bangaren Ramadan kuwa sosai yayi mamakin kansa zai iya cewa this is the first time da mace ta koresa kai tsaye ko dai Alia da tak'i amincewa da auresa akan Sa'ada bata ta'ba nuna bata ra'ayin kasancewa dashi ba but look at Karime korar sa tayi and ya kasa jin haushin ta akan hakan sosai yake jin damuwa because baya son ganinta cikin damuwa ko makamancin hakan zama yayi saman sofa tareda rafka tagumi ,ya dad'e zaune daga bisani kitchen ya shiga domin samun abinci ,domin indomie d'in daya dafa musu Hjy Karime ta gama mata aiki.



Saida yayi nafila kafun ya lallaba zuwa d'akin Hajiya Karime, kwanciya yayi gafenta had'i da jawota jikinsa bacci take hankali kwance,kanta babu hula sabida haka gashinkata a bud'e yake shafa gashin nata yayi had'i da sakin d'an siriren murmushi ya rasa gane dalilin da yasa yake masifar kaunar gashin Karime , k'ara phone d'in sa dayi wacce time d'in daya shugo ya ajiye ta saman bedside table slowly ya mi'ka hannun sa domin d'aukar phone d'in baya son mutsinsa ya tayarda ita.

Alia ya furta k'asa k'asa yana mai k'okarin tashi zaune

I've loved you and I'll always love you

Even after death I'll keep loving you.

Na yadda Sa'ada tana cikin kaddarar ka dani kaina but this time around you are mine ,mine alone , your heart, your soul, your smile your pain all of you Ramadan are mine zuciyar ka ta soni and am very confident tana so da kauna ta ,am coming back to take what is rightly mine.

Shuru yayi na wasu y'an sec ba zai iya cewa ga yanayin zuciyar saba domin wani tsalle take masa lumshe idanuwan sa yayi tareda ajiye wayar rungume Karime yayi tareda furta Best what should i do ? Ya sani tun bayan rabuwar su da Alia shine yayi blocking duk wani hanya da zata iya contacting nasa because he was in love with Sa'ada and ya fahimci communicating da Alia a lokacin za yayi hurting Sa'adatun sa and after mutuwar Sa'ada har gaisuwa tazo masa all the way from Egypt,tayi almost 9 month tana jiran sa and shine ya nuna mata zuciyar sa a rufe take he clearly remember lokacin da yake fad'a mata he will never loved again and she begged him to marry her koda baya sonta still ya fad'a mata baya ra'ayin hakan ,and lokacin da Little Sa'ada tayi 7 years Alia tazo birthday nata all the way from Egypt kuma sosai suka shak'u da Little Sa'ada domin tayi almost 8 month kafun ta koma Egypt.And now ta nuna masa da k'arfin ta take tafe domin samun soyayyar sa for the second time.


,For the sake of Momy ya iya cire numbernta daga blacklist shine harta fara cika baki akan she will make him her's.

K'ara shiga jikin Karime yayi , da haka bacci yayi baga dashi.


Sunday 


Around 5:10 ta farka ganin sa manne da jikinta ne yasata sakin murmushi shafa handsome face nasa tayi wani irin farinciki ta tsinci kanta ashe haka mijin Sa'ada ya namu da ita ganin ya d'an motsane yasa tayi saurin janye hannun ta daga saman fuskar sa ,sauka tayi saman bed d'in tareda nufar toilet.

Motsinta ne ya tayar dashi bud'e idanuwan sa yayi had'i da karanto addu'ar tashi daga bacci ,sauka yayi had'i da ficewa zuwa bedroom d'insa,a gurguje yayi wanka domin an fara kiraye kirayen sallah .


Bayan fitowar da daga toilet a gaban mirror taci burki kanta nade yake da towel haka zalika jikinta sosai take faman goge kanta wanda ta wanke sai faman digar ruwa yake.Bayan sun idar da sallah karatun Qur'an mai girma ya shiga yi mutunan naku Sadiq yana idasa sallah ficewa yayi abunsa jin phone d'in sa na vabrating alamun shugowar kira d'an nesa da masallacin ya tsaya anan ya shiga ansa waya wanda wata sabuwar Beb ce ta kirasa,Bayan ya kai aya ayije Qur'an d'in yayi cikin girmamawa,fiewa yayi domin wani irin bacci yake ji duk da ba sararsa bace bacci bayan sallar Sub duba da jiya bai samu yin bacci da wuri ba ,tunda ya fito daga masallacin idanuwan sa su kayi arba da Sadiq ,tsaki yaja tareda k'okarin tafiyarsa ,saurin ri'ko shi Sadiq yayi had'i da cewa don't forget Dady yana gari kallon rashin fahimta Ramadan yayi masa d'an rufe speaker phone d'in sa yayi sannan yace ka fad'a matarka a sashen Momy ake breakfast duk lokacin da Dady yake gari, d'an siririn tsoki Ramadan yaja tareda nufar hanyar gida ,da murmushi Sadiq ya bishi had'i da cigaba da tsara sabuwar Beb d'insa.


Tsaye take gaban mirror ta samu tayi sallah but still gashin kanta bai bushe ba wannan dalilin ne yasa take ta saman goge kan nata ,da sallama ya shugo d'akin,ansa masa tayi ciki ciki tsaye yayi yana mai binta da kallo , doguwar rigar kanti ce a jikinta sosai rigar ta mata kyau duba da yanda gashin kanta ya jiki had'i da sauka saman bayanta ,tunda ya shugo ta tamke fuska domin ta gama shawara da zuciyar ta akan ba zata kuma shige masa ba ko sakin jiki dashi.Takowa yayi zuwa gareta, rungumo ta yayi ta baya tareda rad'a mata good morning Best.


Fuska ba yabo ba fallasa tace morning,zare jikinta tayi tareda zama bakin bed cigaba da goge kanta tayi,bai kawo komai a ransa ba,zama yayi kusa da ita had'i da ansar d'an k'aramin towel d'in hannunta goge mata kan ya shigayi Hjy Karime kuwa sai wani hura hanci take,babu hairdryer cikin kayan ki ,taji shi sarai nunawa tayi bata ji me yace ba tashi yayi tareda nufar wardrobe d'inta kayan lefen nata ya shiga dubawa,kallo d'aya tayi masa kauda kanta tayi daga kallon sa sosai take kaunar sa saidai me dole tasan matsayin ta a yanzu,batan lokacin daya zauna ba , hucin dryer taji saman kanta , d'ago kai tayi tana son kallonsa mayarda fuskar tata tayi tana kallon mirror , tunanin me kike harna zauna baki san na zauna ba d'an kyaran murya tayi sannan tace niba wani tunani nake ba kawai I'm eager naga Babyn Jummai ne d'an murmushi yayi sannan yace wai dama haka kike son yara k'okarin juyo da kanta take hannu yasa ya kuma fuskar ta tana facing mirror waye baya son yara ta bashi ansa ,kuma fa ya fad'a yana mai cigaba da abunda yake. Koda ya kammala rungume ta tayi ta baya ,room d'in ya d'auki shuru bayan wasu y'an minutes k'okarin tashi tayi bai hanata ba , kitchen ta nufa tana mai fara gyran shi sosai ta zage tana kyara gidan bayan ta kammala komai kitchen ta koma tana son dafa indomie domin yunwa take ji , ya dad'e kwance d'akin ta lokacin daya fito living room sosai falon yayi masa kyau, mamakin kansa yayi akan ko kad'an baiji haushin Karime ba dan ta gyara gidan adan ya kanji haushin ta duk lokacin da zata aikata wani abu da Sa'adatun sa take yi ,kaman gyaran gida da makamancin hakan.


 Jin motsinta a kitchen yasa ya nufi inda take rungume ta yayi ta baya tareda rad'a mata girki za'ayi,yunwa nake ji ta bashi ansa kai tsaye, rad'a mata yayi da ba sai kin wahalar da kanki ba domin yau a sashen Momy za muyi breakfast,gabanta faduwa yayi zare jikinta tayi had'ida juyowa yana fuskantar sa ya fahimci ta d'an tsorata ya sani Momy bata yin Karime but dole suje tunda al'adar gidan ce idan har Dady na gari akanyi 3 days ana breakfast duka family a sashen Momy .


Muje ki rakani na shirya matata,kama hannun ta yayi zuwa bedroom d'insa,zaunar da ita yayi saman couch shafa fuskar ta yayi sannan yace ina zuwa towel ya d'auka. , wanka yake son k'ara yi ,zaune tayi kaman status ta saka wannan ta kwance wannan , lokacin daya fito bata San ma ya fito ba Karima ya kirata saurin dadowa tayi daga duniyar tunani saurin kauda kanta tayi domin mijin Sa'ada babu riga a jikinsa iya towel ne a kugunsa, murmushi ya saki sannan yace tunanin me kike , d'an had'e rai tayi sannan tace ka shirya na jira ka a falo ba tareda taji ansar ba ta fice abunta, murmushi ya saki wanda har hakoransa saida suka bayyana .


Yana gaba tana take masa baya suka isa part d'in Momy, zazzaune suke saman dining table kujerar da Mahaifin sa take ya nufa batada za'bi daya wuce tabi bayan sa gaishe da Mahaifin nasu yayi cikin girmamawa itama ta gaisheshi fuska a sake ya ansa musu tambayar Karime yayi akan ya bakunta ansa masa tayi cikin yanayin kunya akan Alhmudulilahi ,da gudu Little tayo kan Karime rungume Karime tayi had'i da cewa Momyna cikin sakin fuska Karime ta kama hannun Little tana mai mata y'an tambayoyi, ganin ya nufi Momy yasa ta mara masa baya, gaishe ta suka yi ,amsawa tayi cikin sakin fuska,kujera ya jamata cikin alamun rashin sabo ta zauna d'an murmushi Dady yayi domin baiyi tunanin hakan ba a wajen Ramadan d'in but yanzu yaji ya d'an sami natsuwa akan cigaban da aka samu ,zama yayi kujerar kusa da ita gaishe da Sadiq tayi had'i da tambayar sa Anty Rumaisa , shugowar Rumaisa falon yasa Sadiq cewa yauwa gatanan isowa ,bayan Rumaisa ta zauna sosai suka shiga gaisawa da Karime , d'an kallon su Ramadan yayi ya fahimci matarsa ta shak'u da Rumaisa,a bangaren matar Khaleel kallon banza ta ri'ka jifar Karime dashi ,da haka suka fara yin breakfast d'in bayan Abba ya umarci Sadiq ya bud'e musu taron da addu'a.

Little Sa'ada kuwa tuni ita da yaron Khaleel sun fice zuwa sashen Dada.


Sosai yake satar kallon matar sa ya fahimci yawunta a tsinke yake but ta kasa sakin jiki ,dole zata kasa sakin jiki dubada yaune ta fara experiencing wani abu makamancin hakan yanda take had'e yawune ya bashi dariya, murmushi ya saki yana mai k'okarin danne dariyarsa yasan yanda matarsa take son cin abincin , a iya zaman dasu kayi ya fahimci Karime bata wasa da cikin ta , d'an matsowa da fuskar yayi murya k'asa k'asa yace kici abinci mana zaro na mujiya tayi sannan tace d'an Allah kadaina mun magana , wallahi ji nake kaman na ruga da gudu ,murmushi Dady yayi had'i da mi'kewa  enjoy your breakfast idasa maganar yayi yana mai barin dining table d'in dama ba wani dad'ewa yake ba , mi'kewa Momy tayi tareda mara masa baya , ajiyar zuciya Karime tayi domin yanzu ta d'an ji dama dama , cheeps Ramadan ya debo tareda nufar bakinta sosai wannan al'amari ya bama Fadila mamaki shagwabe fuska Karime tayi sannan tace nidai zan iyaci da kaina Sadiq kuwa Rumaisa ya rad'a mawa mutunan da da alama ya kamu , murmushi yayi sannan tace nima na fara tunanin hakan .


Mikewa Ramadan yayi tareda kama hannun Karime janta yayi zuwa cikin gidan sosai wani lobby yabi , k'ofa daga ya bud'e tsarin d'akin ya burgeta matuk'a, zaunar da ita yayi saman bed ina zuwa ya furta ,bayan fitarsa idanuwa ta baza tana mai bin d'akin da kallo , a yanda ta fahimta mamallakin d'akin mace ce duba da komai na d'akin kalar pink ne, shugowa yayi d'auke da faranti, breakfast d'inne ya debo mata domin ya fahimci ba zata iya sakin jiki ba ,zama yayi tareda cire mayafin kanta shagwabe fuska tayi sannan tace mijin Sa'ada kada gashi ya fad'a mun a abinci shafa fuskar ta yayi sannan yace i love your hair ,and ina shaawar kallon sa laifine ? Kallon sa tayi shima haka kallon ta yake ,saurin janye idanuwan ta tayi tareda gyaran murya nidai rufe kaina zan yi ri'ke mata hannun yayi zare ribbon d'in kanta yayi had'i da shafa gashin da hannun sa ,you are very beautiful Karima bai san lokacin daya furta hakan ba zun'buro baki tayi tareda fara cin kayan dad'in dake gabanta,saida ta tabbatar data cika cikinta kat kafun tace Masha Allah ,Ramadan wanda ya shagala da kallon ta , murmushi yayi had'i da goge mata wani d'an abu daya tsaya gefen bakinta , can i kiss you please idasa maganar yayi yana mai shafa lips d'inta zara na mujiya ta fara plate d'in gabanta ya d'auka ajiye shi yayi saman bedside table gently ya jawota saman cinyar sa,i want to you to kiss me Karima she is feeling some strange feeling , something like electricity a dukkan jikinta, please ya fad'a yana mai shinshinar wuyanta mosti take da bakinta, ganin yanda ta rikice ne yasa slowly ya matsar da fuskar sa daf da tata hancinsa ya goga saman ta i want to you to kiss me rage fara'ar fuskar ta tayi domin da fuskar ta a sake take tunda ta cika tunbin ta , this time around ina son kiyi kissing d'ina Karime,mijin Sa'ada why kake mun haka ta furta cikin ranta , k'okarin nisantar da kaina nake da kai akan me kuma kake son k'ara kusantata, ganin ta fad'a duniyar tunani yasa Ramadan cewa ashe tsorone dake saurin kallon sa tayi murmushi yayi sannan yace wasa nake miki Karima ,nasan baki iya komai ba videos d'in dana miki downloading duk a banza tunda naga bakya kallon su .


Duka ta kai masa tareda k'okarin sauka daga saman cinyar sa , knocking k'ofar d'akin akayi yes Ramadan ya fad'a ba tareda ya koda motsa ba ,ture shi tayi had'i da saurin sauka daga jikinsa, mayafin ta ta mayar .

Le'kowa Sadiq yayi cikin alamun zolaya yace please two minutes sarkin soyayya, dukar da kanta tayi tana mai jin dad'in furucin Sadiq , ta'be baki Ramadan d'in yayi sannan yace waye sarkin soyayya? Kai ne mana Sadiq ya fad'a kai tsaye, dawa nake soyayyar Ramadan ya fad'a cikin yanayin basarwa ,gata kusada Kai kallonsa ya mayar kanta cikin yanayin ban damu ba yace she is just a friend to me jin abunda Ramadan yace yasa Sadiq cewa please can we talk ,tashi Ramadan d'in yayi kallon Karime yayi tareda cewa ki jirani ina zuwa da kai ta bashi ansa ,hannu yasa tareda bankada Sadiq waje.


Dafe saitin zuciyar ta tayi had'i da sakin wani marayan kuka ba taji dad'in furucin mijin Sa'ada ba ringing wayar mijin Sa'ada ne yasa tayi saurin kallon wayar , takalmi ta saka tareda saurin d'aukar wayar,waje ta fito babu kowa falon muryar Rumaisa ce tasa Karime saurin kallon inda ta jiwo maganar ,kina neman Mijin kine,cikin sakin fuska Rumaisa tayi maganar ,yabar wayar sane shine nake son kai masa domin ana kiransa , suna garden Rumaisa ta bata ansa, tare suka nufi garden d'in daga nesa ta hango su ,su basu gansu ba sabida sun juya musu baya , tsayawa Rumaisa tayi domin kirane ya shugo wayar ta sabida haka cigaba da tafiya Karime tayi,tunda ta dosa inda suke ta fara jin firarsu .


 you are in love Sadiq ya fad'a yana mai kallon Ramadan murmushi yayi a hankali sannan ya furta bangane me kake son cewa ba ina nufin ka da fad'a soyayya dariya Ramadan yayi sannan yace ai dama tuni ina cikin ta ,kaman ya kenan Sadiq ya fad'a cikin son k'arin bayanin my heart beats for Sa'ada siririn tsoki Sadiq yayi sannan yace wannan tsohon zance ne ,mun saba jin hakan daga gareka ,nafi kowa sanin kana matuk'ar kaunar Sa'ada but for now you are in love with Karime , gabanta dukan ukku ukku yake sosai take son jin abunda mijin Sa'ada za yace 


 , lumshe idanuwan sa yayi kafun ya furta ina matuk'ar tausayin Karime nothing else ,kaman yanda for sure ita kanta tausayina take,, na fahimci yanda take tausaya mun akan rashin Sa'ada da nayi . after that bana tunanin akwai wani abu besides,she don't know what love is am very certain all abunda Karime ta sani shine taci abinci da sauran buk'atun ta. Saurin juyawa tayi karo suka ci da Rumaisa saurin boye damuwar ta tayi ta hanyar cewa dan Allah ki taimaka mun wani abu ya fad'a mun a ido saurin juyowa su kayi jin muryar Karime , jikina kyarma ya nufe ta hannunta ya kama tareda nufar wasu jeren kujeru zaunar da ita yayi,hura mata idanuwan ya shiga yi , da sauki ta fad'a tana mai ture hannun sa daga saman fuskar ta , bai lura da hakan ba .

Rumaisa kuwa bayan sun d'an yi magana da Sadiq cikin gida ta koma.


Tashi tsaye tayi tana mai k'okarin tafiya ina zaki ,shashen Dada ta bashi ansa had'i fa fara tafiya, ajiyar zuciya yayi tareda komawa wajen zaman sa ,lafiya Sadiq ya fad'a yana mai k'ara gyara zama, nothing , you are in love Ramadan , hararar Sadiq yayi sannan yace please if you are enjoying this ni banayi so please lets change the topic.

This girl is coming back fa Ramadan ya fad'a yana mai nunawa Sadiq sa'kon Alia ,bayan Sadiq ya gama karanata cewa yayi so kafara shirin samar mata wurin a cikin zuciyar ka kenan ?

Ta'be baki Ramadan yayi sannan yace bana tunanin hakan but i don't know what positions my heart is in ,akan soyayyar Alia cewar Sadiq about this whole thing, shawarar da zan baka shine , in love always listen to your heart, because ita tasan abunda take so my heart beats for Sa'ada, please Ramadan kada ka kawo mana maganar Sa'ada anan domin she is your past , please lets go of past and face the future for Goodness sake. Look at how confident she is akan samun soyayyar ka , yaushe take dawowa anytime zaka iya ganinta , Kace zuciyar ka ta fara tsalle da farinciki akan dawowar Alia , koda baka aureta ba zaku dasa inda kuka tsaya .


I'm grwon up man yanzu Sadiq bana tunanin idan zan iya koda ri'ke hannun macen da ba matata , dariya Sadiq yayi hada ri'ke ciki,harara Ramadan ya shiga banka masa ,dole nayi dariya , you know what duk duniya babu mutunen dake saka ka sabon Allah sai Alia, what do you mean by sabon Allah ?

You know what i meant Ramadan ,surar Alia , beautiful face nata tuni suke rikitaka duk wani ilimi naka b'acewa yake idan kana tareda ita.

Kasa magana Ramadan yayi gaskiya yau d'innan Sadiq ya kaishi karshe.Cikin yanayin dariya Sadiq yace but banga laifin kaba cox Alia is true definition of beauty,Allah yayi mata sura mai kyau wow i just remember her beautiful eyes ,her kissable lips, enough Ramadan yace cikin yanayin hargowa dariya Sadiq ya kuma yi sannan yace are you jealous ,Sadiq don't tell me , kana son Alia ,if kana sonta i promise you zan yiwa Momy magana akan kai kana kaunar Alia kaga shikenan , I'm very sure ita ma Alia zata so hakan duba da me and you look alike.

God forbid na auri Alia wallahi ko mata sun kare bana iya auren ta ,why yanzu ka gama describing surarta , I'm serious if kana sonta yanzu naje wajen Momy , k'okarin tashi Ramadan yake saurin ri'ko shi Sadiq yayi sannan yace. Ramadan hauka nake na auri leftover d'inki, leftover Ramadan ya fad'a yana wani Kankance ido,yes Ramadan menene baku aikata da Alia ba ,kaga kuwa babu aure tsakaninmu ,Hmm Sadiq how many mata kayi dating a rayuwar ka , since muna JSS3 kasan kayi kissing mace but here you kana wani magana akaina listen to me nothing happened between us , it was just a kiss ,hug and some romance ,we never aikata abunda yafi haka so kaga zaka iya aurenta , Allah ya ki yaye wallahi .

Dariya Ramadan yayi sannan yace banyi tunanin womanizers suna da za'bi ba ,sosai Sadiq yaji haushin furucin Ramadan ,nine womanizer? Cikin fushi Sadiq yayi maganar , of course you are Ramadan ya fad'a yana mai tashi ,Sadiq is speechless ,ya dad'e zaune yana juya maganar Ramadan ,daga bisani cikin gida ya nufa .

A bangaren Karime kuwa sosai suka sha fira da Dada ,duk akan y'an biyu ne wato Ramadan da Sadiq , shugowar Dady and Momy sashen Dada yasa tayi mata bankwana tared Little suka fito zuwa part nasu ,daga nesa taji ana kiran sunan ta, Ramadan ne tsaye jikin mota bata ta'ba ganin sa da glasses ba sai yau sosai glass d'in yayi masa kyau k'arasawa tayi, d'an nesa dashi ta tsaya, we are going out ya fad'a yana mai tsare ta da ido zuwa ina ta buk'ata you don't need to know da haka mota ya shige abunsa jiki a mace ta nufi motar hannun ta ri'ke da Little,bayan ta zauna tafiya ya fara ga mamakin ta part d'in Dada ya nufa parking yayi tareda cewa my baby go in side zan siyo miki chocolates, Dady ina son zuwa do as i said ya fad'a cikin yanayin fad'a, fashewa da kuka Sa'ada tayi ganin haka ne yasa Karime rungume ta jikinta dama can saman cinyar ta take , sosai ta shiga lallashin ta bayan ta samu tayi shuru bud'e k'ofar motar tayi tareda kama hannun Little Saida ta tabbatar Little ta shiga cikin gida sannan ta nufo motar ,fuska a had'e ya fara driving.Ita dai Karime sosai tasha jinin jikinta ,ta lura yau ya dawo aina fin Ramadan data sani a baya .

Parking yayi bakin wani sabon building,maikata neke kai da kawowa ,jingina yayi da seat d'in motar had'i da lumshe idanuwan sa, d'an satar kallon sa tayi,me aka masa yake fushi haka , after some minutes ajiyar zuciya yayi had'i da bud'e k'ofar motar, ficewa yayi ba tareda yace mata komai ba .

Sam bata son ganin Mijin Sa'ada cikin damuwa,jin yanda abun ya dameta yasa ta zaro wayar ta daga aljihun gwon d'in ta samun kanta tayi da son kallon video d'in da yayi mata downloading, kallon videos d'in take cikin yanayin kunya,duk da ba wani rashin tarbiyya ake ba ,kiran Rumaisa ne ya shugo, kuna tare da mijin ki ? Eh muna tare ,kin san cewa fad'a su kayi zaro idanuwa waje Karime tayi sannan tace fad'a shidawa dariya Rumaisa tayi sannan tace shida nawa Mjin mana , dama suna fad'a Karime ta buk'ata, gaskiya suna dad'ewa ba suyi fad'a ba aini bai fad'a mun komai ba sai uban fushi yake , ba zai ta'ba fad'a miki cewa sunyi fad'a Dada tace tun suna yara if su kayi fad'a baya ta'ba fad'i cewa sunyi fad'a saidai shi Abban Adel ya fad'a meya had'a su fad'a har haka Karime ta fad'a cikin mamaki?

Alia fad'uwar gaba taji bangane ba cewar Karime,akan Alia su kayi fad'a, bayanin komai Rumaisa tayi mata bayan ta kai aya cewa tayi dawowar matar nan wallahi bana tunanin akwai alkairi a ciki domin Alia shu'umar yarinya ce , Karime dole ki dage wajen jawo hankalin mijin ki , Anty Rumaisa bana tunanin zan iya hakan ,a yanzu na yanke shawarar ajiye duk wasu kayan yak'i akan sa domin hakan shine mafita , kina son ce mun tana dawowa zaki nemi saki kaman yanda suka buk'ata?

Eh in sha Allah hakan zanyi domin hakan shine mafita, haba Karime kina son zama bazawa da kananun shekarun k ,Anty banida wani za'bi daya wuce hakan , Karime kada kiyi giving up da wuri ni a gani akwai hope akan soyayyar ki wajen Ramadan domin akwai abubuwan da yake miki wanda ban ta'ba ganin hakan a gare shi ba ,Anty na hak'ura da komai ,duk wata kyautawa da yake mun ya fad'a da bakinsa tausayina yake ji , yaushe hakan ta faru?

Iya abunda taji a firarsu ta fad'a mata , please Karime naji bayanin ki but kada ki manta Sa'ada ma ba karamar wahala ta sha ba kafun ta sami kansa, ki d'auka wannan jarabawar ki ce please don't give up early ,ki cigaba da fad'a ma Allah in sha Allah komai zai zama tarihi and za kiyi nasara bayan haka duk wani abu da kika san zai ja hankalin sa dole ki koye shi , daga yanzu ki saka masa ido ki gane me yake d'aukar hankali sa a tareda ke ,da hakan in sha Allah watarana sai labari, knocking k'ofar yayi bankwana ta yiwa Rumaisa had'i da fad'a mata Ramadan d'in na knocking k'ofa .

Bud'e k'ofar motar yayi had'i da zaunawa saurin janye idanuwan ta tayi daga kallon sa , furucin sane akan bata san so ba ya dawo mata ,wai babu abunda ta iya sai taci abincin , siririn tsoki taja saurin kallon ta yayi , zaro idanuwa tayi had'i da cewa wallahi ba kad'ai nake ba murtuke fuska yayi sannan yace ina ne gidan yayar taki?

Batagarawa ta bashi ansa shuru yayi na wasu y'an sec, knocking k'ofar motar tasu aka yi wani mutun ne sanye da kayan engineers , cikin girmamawa ya bama Ramadan watsu papers signing yayi sannan yace mu had'u office by 5:00 da haka rufe motar yayi tareda fara driving.


Bakin wani shopping mall yayi parking,an fad'a miki abunda ta haifa ,Aaa ta bashi ansa a takaice, fiewa yayi ba tareda ya kuma cewa komai ba,few minutes later k'ofar baya ya bud'e tareda saka abubuwan daya siyo, bayan ya koma driver seat, driving ya fara fuska a murtuke.

Da taimakon ta suka isa layinsu Jummai,bayan yayj parking , gyaran murya yayi sannan yace zaki dad'e ne , Eh idan ba damuwa ,ina son ganin Sa'ada if babu matsala,ba damuwa barina shiga zan kawo maka ita da haka ficewa tayi ,fitowa yayi tared bud'e k'ofar baya kayan daya siyo ya mi'ka mata,aaa ai daka barsu k'ara tsuke fuskar yayi sannan yace ai bake na siyawa maba ansa tayi tared yi masa godiya. 

Komawa yayi cikin motar yana mai jiran dawowar ta ,da sallama a bakin ta ta shiga gidan ,gidane na rufin asiri domin mijin Jummai yana da rufin asiri,da gudu Sa'ada tayo kanta kya'kyawar yarinya ce y'ar kimanin 9 years ,kusan age mate d'in Little Sa'ada ce, ke dalla sake ni,ki ri'ka abu cikin hankali Karime ta fad'a tana mai ture Sa'ada daga jikinta, abun mamaki cikin sakin fuska had'i da farinciki Jumma tayo kan Karime ita ma Karime mantawa tayi da b'acin ran da mijin Sa'ada ya cusa mata , sosai suke murnar ganin junan su , hannun Karime Jummai taja zuwa falo ,bayan ta zauna kayan hannun ta ta mikawa Jummai da mamaki Jummai tace had'a d'awainiya, ta'be baki Karima tayi sannan tace shine ya siya . Baki Jummai ta washe had'i da zama daf da Karime kallon mamaki Karime tayi mata , Jummai bata daina murmushi ba wai fara'ar me kike Hmm ai tunda akace Baba ya bayar da auren ki haya nansan cewa dole mutanen masu kud'i ne sabida haka wallahi ki kwantar da kai muci arziki, Dan Allah bani baby na gani kafun ki rufe ni da surutu.

Masha Allah Karime ta furta ganin kya'kyawar baby a hannun ta , tunowa da Mijin Sa'ada ne yasa tayi saurin mi'kawa Jummai babyn ina zuwa yana waje fa , wai dama tare kuke ? Eh mana shine ya kawo ni , Sa'ada yake son gani ya santa dama cewar Jummai ?

Ina fa wai sunan matacciyar matarsa ne ,kice ya shugo yaga baby mana ,Allah yasa bai tafiyar saba ,da haka gaba tayi Sa'ada na mara mata baya ,bakin mota suka hango shi fuskar a sake ya kama hannun Sa'ada,baki ya saki yana fira da Sa'ada kaman wata babba ,ganin ba shida niyyar tafiya yasa Karime cewa dama Jummai tace ka shugo kaga baby , siyayyar daya yowa Sa'ada ya d'auka tareda bin bayan Karime da sallama suka shiga gidan ,bayan sun gaisa da Jummai babyn Karime ta mi'ka masa sosai yayiwa yarinyar addu'a,Best zan wuce k'asa k'asa ta jiyo maganar sa ,babyn ta ansa tareda fad'awa Jummai Ramadan d'in zai tafi ,fitowa daga bedroom Jummai tayi cikin sakin fuska su kayi bankwana ,bin bayan Karime tayi ,zan wuce by 8:00 in sha Allah zan dawo d'aukar ki ,so ki zama cikin shiri ,in sha Allah ta furta tana mai kallon wani side domin dai har yanzu fuskar mijin Sa'ada a murtuke take , bud'e k'ofar motar yayi tareda kasa kansa kud'i ya d'auko tareda cewa please ki bama Maman babyn ,Aaa Mijin Sa'ada kayan da ka kawo ma sunyi , hannunta ya kama tareda saka mata kud'in,shigewa mota yayi abunsa had'i da yi mata key.

Baki ta saki tana kallon motar sa harya bace mata da gani, ringing d'in wayarta ne yasa tayi saurin janye idanuwan ta daga hanya picking call d'in tayi ,me kuma kike jira a waje ,kalle kalle ta fara ita dai bata hango koda kurar motarsa bane ,toh ta yaya yasan tana waje.

You should go cikin gida ko kuma yanzu na dawo na mayar dake gida ,ba shiri ta nufi cikin gidan Jummai.

Bayan ta bama Jummai sa'kon Ramadan godiya ta shiga yi , kice shegen son kud'i irinna Baba yayi miki rana cewar Jummai tana mai zama daf da Karime,nidai banga amfanin da hakan ya jawo mun ba , ke yanzu Karima wannan kya'kyawan Mijin naki ,idan ba don san kud'i irin na Baba ba ina zaki sami irin sa , kefa Jummai dadi'na dake bakya gane abubuwa ,kin manta haya ya bar da auren nawa , na sani Karima amma ai yanzu yana sonki ko?


Hmm Jummai kenan gyara zama Karime tayi tareda fayyacewa Jummai komai ,kice yanzu ita budurwar tasa ta kusa dawowa ?

Eh mana and shi a tunanin sa baki san so ba cewar Jummai, iya cin abinci kad'ai na iya Karime ta fad'a cikin yanayin fushi , dariya Jummai tayi sannan tace nasan halinki da abinci hala fiddo da maitarki fili kika yi akan abinci ,Dan Allah Jummai ki rabu dani Sam ni yanzu komai ma ya ficce mun , yanzu kinyi giving up akan wancen handsome man d'in ,eh nayi kawai ina jiran lokaci tana dawowa zan buk'aci saki kaman yanda suka shirya.

Wallahi Karime baki isa ba cewar Jummai, da mamaki Karime ta kalli Jumma tabbas ki kalle ni da kyau waccan kya'kyawar fuskar ta mijinki ,in sha Allah sai mun haifi iri da ita dan haka idan zaki bani had'in kai mu fara shirin saye zuciyar sa kaman yanda nayi nasarar sace zuciyar Jamilu .

Ta yaya za kiyi wasa da damar da Allah ya kawo miki kina son yi mana bakinciki,duk wasu dabiu na Abdulkarem ajiye su zaki dole ki shirya zama Karima domin ta haka ne za muyi nasara ,abun naki hada cin mutunci Karime ta fad'a tana mai hararar Jummai ,ai dole na fad'a miki ,dole ne soyayyar ki tayi wahalar shiga ransa duba da yanda kike alamuran ki kaman ba mace ba ,Allah Jummai kina k'ara ci mun mutunci zan bar miki gidan ki dariya Jummai tayi sannan tace. Ai tunda kika yi nasarar shiga gidan Ramadan toh fa ita ma zuciyar tasa sai kin shigeta in sha Allah. Murmushi Karime tayi sannan tace shi yasa nake matuk'ar kaunar ki , danma Mama tana mana katsalanda , ke rabu da wanan ita kin san bata son zaman lafiya cewar Jummai.


Toh Readers a ana Hanaady zata tsaya .

Mu had'u next page in sha Allah.

Note

NIKAAH(marriage 4 rent) zai ri'ka zo muku every Sunday in sha Allah.



Vote

Comments

And follow the Author.