3
"Malam ka kasa ganewa ne, wallahi gaba ɗaya hankalina iya kan Mairamu, ba na so na rasha shi kamar yanda na rasha uwa shi, kuma ga Ibrahimu dai kaga ya isha aure, ya kamata ka shirya muje birnin ayi wacce ja ai" Tani ta zage tana korawa malam bayani.
Jauro da bakin shi ya ƙi rufuwa sabida farin ciki ya kalli Tani yace, " Wallahi Tani na fika matsuwa, sho nake kawai Habubakar ya jo ganin gida, aradun Allah da ya jo ja mu bishi birnin, ya kaimu har gidan shi Shaminun a yi ta ta ƙare, dan jalinshi ashe yaro tun haihuwa an ƙi q shada shi da dangin uwashi, sho shuke shuce shun riƙe mairamun ma gaba ɗaya mu mu rasha uwarshi sannan mu rasha shi".
Jauro yana kaiwa nan ya miƙe, tare da ɗaukan sandar shibya kama hanyar fita daga gidan yana ƙwana kiran Ibrahimu...
Sati biyu kenan yanzu ta saba indai ba su yi waya dashi ba duk se ta jibranta babu daɗi, wani irin sirri ne a tattare da shi wanda ta kasa tantance asalinsa. Yau tunda ta tashi ba su yi waya ba, bini bini take duba wayarta ko za ta ga kiransa amma babu, har ta haƙura ta ajiye wayar ta nufi hanyar fita daga ɗakin sai ga wayar na ringing. Da sauri ta koma ɗakin tana jin wani irin nishaɗi har da lumshe idanuwa.
Gabaɗaya farin cikin dake a zalzalar ruhinta ya tsaya cak ta kafe screen ɗin wayar da idanu, kamar ta ɗaga wayar ta buga da ƙasa dan takaici. Sunan Dr. Hafiz ta gani yana yawo akan screen ɗin, ba ta mance sanda tayi masa warning kan ya dena kiranta ba, "mtssssss!!!" ta saki dogon tsaki tare da datse kiran.
Tun kafin ta matsa wani kiran ya sake shigowa, har za ta sake yanke shi sai kuma ta ɗaga, ba ta jira cewar sa ba ta fara zazzaga masifa.
"Wannan wane irin abu ne Hafiz? Ka kira na yi rejecting but you're still calling, dan Allah kar ka ƙarar min da chargy i have an important call to answer" Ƙit ta kashe wayar ba tare da ta jira amsar sa ba, dan 30% ne kawai ya rage mata a wayar ba tayi chargy ba, ta kuma rasa wanda ya ɗaukar mata charger bare ta sa chargy.
Har bayan Magriba Sadiq bai kira ba hakan ya sa ta fara tunanin ko dai ba lafiya. Tana kwance a kan gadon ta ta daure ta yi dialing contact ɗin sa, ringing biyu uku ya ɗaga.
"Assalamu alaikum warahmatullah" sautin muryar sa da yai sallamar da shi ya sanya ta sakin wata bayyananbiyar ajiyar zuciya. Ba tare da ta yi magana ba ya sake cewa, "Ina fata sarauniyata tana cikin ƙoshin lafiya, ina fata ta tuna dani ko da sau biyu ne a cikin yinin yau ɗinnan, kuma ina fata tana cikin walwala da farin ciki, uhmmm?"
Sai da ta wani jujjuya idanunta ta lumshe su sai kuma ta tamke fuska ta cuno baki kamar da tana gabansa tace.
"Bayan yau gabaɗaya ƙin kira na kayi, bayan kai baka tuna da ni ba sai nice na tuna ka ma da kiranka, ni gaskiya nayi fishi kawai".
Da sauri ya tare numfashinta yace. "A'uzu billah, kiyi wa Allah da girmansa ki janye wannan ƙaulin naki, so kike kwarankwatsa ta faɗo ta sani na narke? Saddiqu ba mutuwa yake tsoro ba abinda zai raba shi da Arfan sa yake gudu.
Kin san ma mai yasa ban kira ki ba?" ta girgiza kai a hankali tana murmushi kamar tana gabansa. Idan da sabo ya saba shima yana murmushin yace. "Yau Allah yayi da kwana na a gaba, kiji in faɗa miki wasu mata na ɗauka a adaidaita sahu, suka sani nai ta shiga dasu surƙuƙufi, sabida sun yanka min kuɗi da yawa, ƙarshe haka na gudo ba tare da na karɓibkuɗin ba".
Tana shirin tambayarsa taji ana knocking, kamin tayi wani motsi Ammi ta shigo ɗakin hakan ya sa ta datse kiran kawai ta juya gareta....