Chapter one
by @zainab17
~~~~👑👑Masarautar Badara 👑👑~~~~~
Written by
(marubuciya🖊️🖊️ ZAIMAR💕💕)
Hatred🖤
Love ♥️
Romance😍
Bismillahi Rahamanin Rahim
Nazo wucewa na hango wasu Yara mata matasa Wanda baza su wuce shekara 15 bah, suna ta wasan a kogi cikin Anna shuwa da nishadi sunata watsa wa gunansu ruwa sai can naji ance "ANISA" 'Ga talatu yar gidan Mai gari ta dauka Miki kwanon tallen ki, Wanda aka Kira da anisa tafito Daga ruwan da gudu taje gurin talatu tana cewa' talatu kiban kwanona tace 'ba zanbayar ba wannan kwana tallen nawa ne, anisa tace' talatu banason haka kiban ke ma kinsan nawa ne, talatu tace' in kinada karfi ki kwata, sai suka fara kokuwa talatu tayi duka wa anisa, kuma ta tafi da kwanon tallen anisan, kawayen anisa sukazo suna Bata hakuri.
Anisa ta koma gida(wato 'fanti' garin ta kenan) ta na kuka bakinta ma ya kumburu tana shiga gida mamanta tace 'Mai yafaru anisa meya sameki a fuska haka, tace' talatu yar gidan Mai gari ne ta mun duka kuma ta tafi da kwanon tallena wai nata ne kuma karya take yi,
Mamanta tace kiyi hakuri Kinji yar auta na.
Wani Dan saurayi na hango cikin kayan sarauta Wanda shekarunsa bazasu wuce 25 bah, ba fari bane haka zalika kuma ba za'a ce mishi baki ba, he is dark in complexion,yanada dogon hanci, karamin baki, kananan ido da gashin ido Mai kauri bakikkirin, da gashin gira Mai kauri, dogo ne Mai faffadan kirji, barina na barku haka Amman kyansa bazai misaltu bah wato 'YARIMA NIMRAN'dan sarkin Badara magajin shi daya tilo.
Ya Fito Da Ga dakin sa ya nufe fada yaje ya tsuguna agaban wani dattijon Wanda yayi shigan Sarauta da rawanin irin na Sarakuna Yana zaune Akan kujeran Sarauta wato 'SARKI UMAR SARKIN BADARA' yace 'abbiey zan je yankari kuma zan bi na duba gari' sarki Umar yace 'Allah ya kiyaye hanya kuma Kar ka wulakanta wani talaka sbd nasan halinka son, yayi mishi nasiha sosai Mai rasa jikin, yace' in sha Allah abbiey Allah ya Kara maka lafiya da Nisan kwana,yace ameen. Yafito ya je yankari yadan huta sai yadawo garin Badara ya Duba garin yaga komai normal sai ya koma gida wato Masarautar Badara yayi sallah suka hadu a babban palour suka Dan yi hira kowa ya wuce part dinshi, yarima nimran yayi magana da abokanan sa na maleysia suka ce zasu kawo masa ziyara next week,zasu sauka a yankari dun sunajin labarin gurin kafi sai suwuce Masarautar su, yace'ai yankari na kusa da garin na ne, sukace toh sukayi sallama sai ya cigaba da damu woyinsa a cikin waya.
Ranan anisa taje talle a yashi garin dake tsakanin fanti da Badara ita da kawayen ta Bayan sun gama sai da abun tallen su Wanda ake Kira 'Mira' tace kizo muje yankari, a'a mamana tace Kar naje ko ina sukace toh shknn inmun dawo zamu baki labarin gurin yaye ke, na koma gida washe Gari su Mira suka bani labarin ruwan yankari suka ce yau ma zasu sake zuwa harga Allah Har cikin zuciya inaso naje Amman sai na tuna da maganar mamana sai nace musu a'a, haka kullum zasu je washe Gari su bani labari.
Wata rana na sai da abun talle na da wuri suka ce mun nazo muje yankari nace a'a, Mira tace yau kin sai da abun tallen ki da wuri kizo muje baza mujima bah Kinga mamanki ma ba zata gane bah tace a'a, toh shknn tunda baza kije ba Har sun fara hanya sai anisa tabiyo su da gudu,tana ce zan biku Amman Kar mujima.
Sun isa yankari suna wasa abun su
Sunata nunnu mata gurare acikin yankarin, kai wannan gurin nada kyau sosai, su Mira suka ce zomu kaiki gurin ruwan nan da muka baki labari Mai ban mamaki Wanda a lokacin sanyi dumi yakeyi a lokacin zafi kuma yayi sanyi, suka nufi hanyar gurin ruwa da gudu suka bige wadansu mutane bada sanin su Har ansa wasu gibga gibgan mutane su bisu su dake su, sai Wanda muka bige din yace a'a abarmu wai mu Yara ne, mu kuwa muka buya, sai kaltume tace'wannan Wanda kukaga yace wa wadannan mutanan su dake mu to ai shine yarima Wanda labarin sa ya baza garin mu, shi ya tsana talaka, sai nace yanda ya tsana talaka haka mu ma muka tsani masu Kudi irinsa ko masu Sarauta, kaltume tace'ke dai Bari kawai Amman wannan yariman daki ke gani yayi abubuwa da yawa wa talakawa na rashin mutuncin Ga wani jijji da kai Amman babansa mutumin kwarai ne wato sarkin Badara ba ruwansa, nace 'kice albasa batayi halin ruwa ba nikam kibar labarin San nan muje gurin ruwan, tsanan shi ne yake karuwa a zuciya na wallahi, suka je wajan ruwan sunata wasa abunsu.