RAYUWAR MAKARANTA

Page 8

by @zahraroyal

*RAYUWAR MAKARANTA*





*©Zahra Royal Star*




Page 8



*Government Secondary School Rimaye Katsina State Nigeria*




A hankali Hauwa ta mik'a hannunta ta amshi Report d'inta. A hankali Malamin ya bita da murmushi yana kallon y'an class d'in ya ce



"A first term d'inmu ga wacce tazo ta d'aya a cikin ajin nan, dan haka ku tafa mana please"


Gaba d'aya ajin ne ya d'auki tafi, murmushi mai sanyi kawai Hauwa ta saki tana komawa ta zauna akan kujera.


Tofa tunda Mlm ya fad'i haka, wasu daga cikin y'an class d'in suka fara bin Hauwa da wani kallon uku saura wasu hassada ce cike da cikin nasu.


Duk K'awayen Hauwa sune suke bi mata a report d'in, Atu tayi na biyu, Hadiza na uku, sai Ammama na hud'u Fatee na biyar, sai ko su Asiya da Hafsat dake bin bayansu.


Abunda ya k'ara jan wasu y'an surutai a cikin ajin kenan, wasu ma cewa suke ai Malamin dake basu Report d'in saurayin Hauwa ne, sonka kawai aka nuna ba wai adalci akai ba.


Asiya dake tafiya da Hafsat bayan an sallami kowa an raba report anyi hutun sati uku, kowa na tafiya a k'asa d'alibai cike da farin cikin hutun da akai masu.


Asiya ta kalli Hafsat dake cika tana batsewa ta ce.


"Amma gaskiya an cuce mu wallahi, ace duk class d'inmu a rasa su waye za'a ba na d'aya dana biyu har zuwa na biyar, sai masu biye ma wancan yarinyar mai iskokai a saman ka?, wannan abun da kinji kin san wallahi son kai ne kawai aka nuna mana"



Tsaki Hafsat taja tana cewa.


"Ke nifa na tsane ta wallahi, ta fara tare mana wani abun da mu ya kamata mu fara samunsa ba wai ita ba, da sauran rukuninta, dole ne sai na ja mata kunne, dan naga sai wani shewa suke kamar da gayya ma"


Tana idasa fad'ar haka tayi gaba inda take hango su Hauwa suna tafiya ita dasu Ammama, Asiya na faman kiranta amma ina tayi gaba, idonta ya rufe da masifa.


Su Hauwa suna cikin tafiya kawai suka ga an Sha gabansu.


Da d'an mamaki Fatee ta kalli Hafsat, ta d'an harareta dan itama haushinta take ji ta ce.


"Ke kuma Malama miye haka?, muna tafiya zaki wani zo ki tare mana gaba, bama son k'auyenci fa"


Wani mugun kallo Hafsat ta jefama Fatee tana nunata da yatsa ta ce.


"Keee kinga rufe min bakinki a nan wajan, mai warin baki Kawai, ki daina ganin kunyo na farko a cikin class d'inmu, idan banda wannan shashashar dake d'oraku tana baku satar amsa, ku kun isa ku goga damu ne?"


Hafsat ta k'are maganar had'e da nuna Hauwa tana wani mata kallon banza


Hauwa ta rik'e k'ugunta tana k'arema Hafsat kallo a tsanake, Atu zatai magana Hauwa tayi saurin sa hannunta ta rufe bakin Atu

Tana d'an harararta ta ce.


"Karki sake ki ce komai, dan tsaf na sanki yanzu zaki b'ata mana lamarin"


Ta sake juyowa wajan Hafsat dake tsaye. Zuwa can saiga Asiya ta iso.


Hauwa ta d'an taka ta matsa kusa da Hafsat sosai kamin ta nunata da yatsa ta ce.


"Ya ma sunanki ne baiwar Allah?"


Wata uwar harara Hafsat ta dankara ma Hauwa ta na jan dogon tsaki ta ce.


"Ba'a sani ba, wata k'ila ko sunan Gyatuma ne dani ba..... Bata idasa maganar ba taji wani gigitaccan mari tasssss, wadda ya kusa sa jinta da ganinta daina aiki.


Da mugun sauri Asiya ta nuna Hauwa tana huce ta ce.


"Kutumar uban nan Kaii, shine zaki mare ta?, ke wace ce?"


"Ni uwar da ta haife ta ce, baki ji miye ta ce bane daga k'arshe?"


Hafsat dake rik'e da kuncinta cikin jin rad'ad'in marin da ta ji shi a bazata, take kallon Hauwa da d'unbin mamaki.


A zabure Hafsat ta kai hannunta domin rama marin da Hauwa tayi mata, kamar k'iftawar ido taji an rik'e tsintsiyar hannunta.


Ido cikin ido Hauwa take kallon Hafsat ta ce.


"Ai wallahi Uban kuturu yayi kad'an bare na makaho, ke kin isa na tsaya ki mare ni?"


"Ni kuma kika mare?, ai na rantse da sarkin mulkin Allah yau sai na rama mari na wallahi"


"Hhhh au haka dan Allah?, sai ki mare ni mu gani, ai mari na mare ki, kuma na mari banza, domin da baki tab'a min uwa ba, da bazan mare ki ba, ki sani iyaye ba abin wasa bane, daga yau ki sake tab'a iyayen wasu, wata k'ila ni na miki da sauk'i, akan abunda zaki tarba a gaba, idan kika tab'a Iyayen wasu, ki iya bakin ki Malama, kije gida a koya miki tarbayar iya magana, da alama har yanzu akwai rashin tarbiyya a tare da ke, akwai kuma ciwon hassada dake d'awainiya dake, to shi dai ciwon hassada cinye aiki yake dan haka Malama Hafsa kike ko wacece ma dai sai a taka a sannu"


Tana gama fad'ar haka ta rab'a ta gefanta ta wuce tana ce ma su Atu


"Kai please ku taho mu je, domin kun san ana Jira na a gida yau zamu wuce Kano, ni kad'ai suke jira, karma wannan mugun ya gaji da Jira na naje yayi min wata muguntar tashi"


Bin bayanta sukai suna mamakin Hauwa a yau, domin sun san da y'an jan fad'ar na kai da yau Hafsat ta ci ubanta har da Uwar.


Asiya cike da takaici ta dubi Hafsat dake had'iyar zuciya kamar zata mutu haka take ji tsabar haushin kanta da take ji, da tsanar yarinyar can Hauwa.


"Sai da na ce miki kwata-kwata bai kamata ki tare ta a nan ki ce zaki ci mutumcin ta ba, da kin bini a sannu zan gano mana hanyar da zamuyi maganinta, amma gashi ta baki kunya a gaban jama'ar makarantar nan, kin b'ata abun wallahi".


Kuka kawai Hafsat ta saki tana cewa.


"Ai wallahi bata ci banza ba, na rantse da Allah banzan yarda ba, saina rama wallahi. Amma yanzu mi kike tunanin zamuyi mata ne?"



"Karki damu, daina kukanki kawai ni nasan matakin da zamu d'auka, kawai ki bari a dawo hutu"


"Shikenan Allah ya kaimu a dawon"



Da haka suka ci gaba da tafiya

Suma.


Atu da Ammama ne har suna had'e baki wajan cewa.


"Amma gaskiya yau ba k'aramin birgeni kikai ba Hauwa"


Kallonsu ta d'anyi da mamaki kamin ta ce.


"Tofa yau kuma, to akan mi?"


Atu ce ta amshe da cewa.


"Kawai yau d'in ne kinyi aiki da hankali, bakiyi fad'an naki kamar yadda kika saba ba"


Dariya Hauwa tayi tana cewa


"Ai ko idan haka ne, karma kuyi saurin yanke hukunci, domin ba hankali nayi ba, idan ma shine kuke tunanin nayi, domin wallahi sa'arta d'aya su Momy na Jira na, zamu tafi Kano, amma da babu mai jira na a gida wallahi saina tsaya munci uban juna ni da ita, sai na nuna mata ruwa bafa sa'an gwando bane, har yanzu ina a matsayin Hauwar da kuka sani a'ato ba canzawa nayi ba"


Wani tsaki Atu taja tana tab'e baki ta ce.


"Ai dama ni na sani, ai barin hali sai mutuwa, Allah dai ya shirye ki"


Ammama ta amshe da cewa


"Ke ni fa ta wani b'angaran bana ganin laifin Hauwa, saboda mutane idan kana barinsu suna maka duk abunda suka ga dama, tofa ka bani ka shiga uku, amma idan kaja masu birki dole su ja su tsaya"


Da irin wannan firar suka rabu da juna kowacce tayi hanyar gidansu, suna cewa zasuyi miss d'in juna saboda hutun da akai, da hakan suka rabu.


Atu ce k'arshe zata bi layin gidansu ta d'an tsaya tana ce ma Hauwa.


"Y'an birnin Kano, a dai mana tsaraba please, kar a sake a dawo mana hannu rabbana a'ato"


D'an bugu ta kai mata a hannu tana cewa.


"Ke dai kika sani, tsaraba kuma banyowa"


"Karda Allah yasa kiyo jarababba kawai"


Dariya suka saki a tare cike da kewar juna suka rabu.


Hauwa na sayo kai d'akin Inna taji Y Abdullah na jan wani tsaki yana ce ma Inna.


"Wai Inna wannan yarinyar taki har yanzu bata dawo bane?, anya kwakwalwar yarinyar can ba tab'in hankali kuwa, kwata-kwata bata da natsuwa fa"


Wani kallo Inna take ma Abdallah, hannunta ta ware tana cewa.


"Abdallah Ungo nan, Jikar tawa ce mai tab'in hankali?, ka kiyaye ni Abdallah wallahi, kaga wancan wadda ya fita shin.....


Da sauri Abdallah ya tashi yana matsawa inda Inna take yasa tafin hannunsa yana zaro ido waje ya ce.


"Haba Inna, ya da haka Kuma, yi hakuri ba sai kin idasa ba, haba mai ran k'arfe"


Y'ar dariya ta saki tana harararsa ta ce.


"Ke ni sakar min baki ja'irin yaro kawai, yarinyar da Mat.....


Tashi yayi da sauri ba shiri yana toshe bakinsa yana cewa.


"Ni dai Inna sai had'uwa ta gaba gaskiya, na fita zuwa mota ina waje ina jiransu, idan sun shirya ta dawo, wannan magana da kike ta zarowa Inna, sauran wa'incan Yaran suji, suma raina ni"


Ya k'are maganar had'e da ficewa daga d'akin da sauri.


Inna ta d'aga murna yadda zaiji ta ce


"Da ka tsaya mana d'an rainin wayo"


Yana fitowa ya ci karo da Hauwa da ta gama jin duk abunda suke cewa, taso ace taji abunda Inna zata fad'a daga k'arshe, ta kasa gane ina maganar ta dosa, duk inda ta d'ora ta sai taga batai ba.


Allah ya so wannan karon basu yi k'aro ba, dan basa waje tayi ya wuce yana jefa mata wani kallo, ita dai tunda ta gaida sa bata k'ara gigin masa magana ba.


Nahna ta fito daga uwar d'akin Inna, tana wani lumshe idonta had'e da wani yatsine fuska ta kalli Inna dake dubanta ta ce


"Wai Inna ita wannan yarinyar bata dawowa ne haka, dole ma sai mun tafi da ita ne, a barta inda tafi wayo mana"


"Ke kinci ubanki yanzu nan wallahi, kaga ja'iran Yara, kowa ya taso Hauwa dai Hauwa dai, haba dan Allah ku barta ta huta mana ta shak'ata"


Zata k'ara magana Hauwa ta shigo ko kallon inda Nahna take Hauwa batai ba, sai ma wani siririn tsaki da Hauwar taja mata.


"Yawwa ga y'ar albarkar nan ma ta zo"


Momy da ta idasa sallar k'arfe d'aya saboda da tafiyar da zasuyi tayi sallarta, danta ga har sha biyu da rabi tayi, shi yasa kawai tayi sallar, dan sallar zata iya riskarsu kan hanya ne.


Ta fito daga d'akin tana cewa.


"Kinga NahNah zan sab'a miki, dallah tashi kije kiyi sallah kizo ki shirya muyita tafiya. Y'ata Hauwa kema tashi ki Shirya ko mun d'auki hanya, kar dare yayi mana akan hanya"


Da to Hauwa ta amsa ta tashi, ta shige, uwar d'aki, tana cire kayanta ta shiga toilet na cikin d'akin tayi wanka, tana fitowa ta shirya a gurguje tayi sallah, ta gama dama akwatinta har an kai sa mota. Itama kwata-kwata bata son tafiya tabar Innarta shi yasa yau d'in kwata-kwata bata wani jin dad'in yanayin.


Tana Jin sadda Nahna ta shigo tayi sallar itama, koda ta idar tana d'akin, nan ma ba wata magana sukai ba, ta rasa mi yasa basa jituwa da juna.


Komi Hauwa ta tuna jin muryar Abba ta fito da sauri tana cewa.


"Yawwa Abba, kasan na nawa nayo a school?"


"A'a d'iyata, yanzu nake cewa kina ina ne, dama abunda nake so na tabbaye ki kenan dama. Matso na gani Y'ar tawa na nawa Tayo"


Da saurinta Hauwa ta matsa da zumud'i tana damk'ama Abba report d'in nata.


Nahna da ta fito yanzu ta tsaki wani tsaki can ciki yadda ba wadda yaji ta tana maganar zuci.


"Yo na nawa zatai fa?, idan banda na k'arshen class, karatun k'auye har wani karatu ne"


Kamar Hauwa tasan miye Nahna ke kitsawa ranta. Ta d'an matso saitin da take tana kallon yanayin fuskarta yadda take wani tab'e baki tana b'ata fuska.


Tana jin lokacin da Abba ke cewa.


"Wow wow My daughter, gaskiya dole na baki kyauta domin kinyi k'ok'ari sosai ki ce first class fa mashaa Allah"


Abba ya idasa fad'ar haka cike da tsananin murmushi akan fuskarsa da murna, Momy ma amsa tayi tana yabawa sosai.


Hauwa dake tsaye kusa da Nahna a hankali ta d'an duk'a dai-dai tsawon Nahnar domin Hauwa ta fita tsawon k'afa ta ce


"Ohhh sai gashi kuma nayo abun kirkin da baki so ji ba, karfa kiyi tunanin makarantun k'auye abun banza ne, no ba'a nan take ba Aunty Nahna, idan mutum Allah ne ya basa kwakwalwa, to a ko ina yayi karatu bazai tab'a dakushewa ba, wannan daga Allah"


Da wani mugun sauri NahNah ta waigo tana kallon Hauwa da mugun mamaki. Ubanwa ya gaya mata zancan zucin da take yi ne, ko dai aljanu ne da ita?.


Hijab har k'asa Hauwa tasa tayi mata kyau sosai tasa ruwan k'asa.


Nahna zatai magana taga su Abba sun mik'e sunama Inna sallama gaba d'aya suka fita har Innar domin masu rakiya, har ita Hauwa sai ta take masu baya, dole tasa Nahna yin shuru ba dan ta so ba, itama ta bi bayansu.



Kamar yadda suka zo a mota d'aya haka Abba ya shiga gaba Abdallah na driving, sai Momy a baya da Hauwa da Nahna. Hauwa kamar tayi kukan rabuwa da Inna, amma ta d'an matse hawaye a b'oye ta shige mota, Inna sai tsiya take mata, wai dama so take ta tafi ta barta ne.............