Page 9
by @zahraroyal
*RAYUWAR MAKARANTA*
*©Zahra Royal Star*
Page 9
*No. 14 Audu Bako Way, Nassarawa GRA, Kano Nigeria*
A gajiye suka shigo gidan, dan haka suna shiga Parlon gidan, Nahna tayi saurin haurawa sama dan ko kallon inda Hauwa take batai ba.
Momy ta kalli Hauwa ta ce.
"Hauwa ki haura sama kema ki d'an watsa ruwa, kamin a fito cin abincin dare"
D'an yamutse fuska Hauwa tayi tana cewa.
"Nifa Momy dama Abba baiyi mana d'aki d'aya da Nahna ba wallahi, bana son abunda zai b'ata min rai"
D'an murmushi ta saki tana matsuwa kusa da Hauwa ta d'an dafa kafad'ar ta ta ce.
"Abunda yasa Abbanku ya had'a maku d'aki d'aya shine, tun kuna Yara dama ra'ayinku ba d'aya bane, Nahna ta cika rawar kai da yawa, ke kuwa kin cika rashin ji, halinku kwata-kwata bai zo d'aya ba, bama ku zama waje d'aya bakuyi fad'a ba, shine mu kuma nida Abbanku muka yanke hukuncin a had'a maku d'aki d'aya kowacce da gadonta, ko mun samu ku d'an had'a kanku, amma duk laifin na wajan Nahna, idan bata daina halin nan nata ba wallahi zan d'au mummunan mataki ne a kanta"
Da sauri Hauwa ta girgiza kai ta ce.
"Ko kad'an Momy karma kiyi mata komai, wata rana k'ila ta gane abunda take ba dai-dai bane, zan zauna a d'akin namu, amma....
Sai kuma tayi shuru.
D'an k'aramin murmushi Momy ta saki, tana cewa.
"Amma idan tayi miki ki rama, karma kiji kunyarta, ni na saki tunda ta riga ta zubar da girmanta, amma Hauwa kuyi k'ok'ari ku so junanku ke kuma idan tayi miki wani abun ki rink'a hakuri da ita kinji D'iyar albarka?"
Murmushi Hauwa ta saki itama ta haura saman tana d'aga kanta alamar taji kawai.
Momy ta bita da kallon tausayi, ita yarinyar tausayi ma take bata.
Abba daya dad'e a tsaye daga sama, ya sakko ta b'an garansu ya ce.
"Momyn Yara ko dai zan sa a raba masu d'aki ne?"
"No Karka raba masu please, nafi so su fahimci juna, su so junansu, bana jin dad'in rashin jituwarsu fa sosai"
Momy ta k'are maganar fuskarta ba walwala ko kad'an.
D'an murmushi ya saki yana kallonta ya ce.
"Ki daina damuwa kinji, ai Yara ne har yanzu, duka suka wuce shekara goma Sha hud'u, to nan gaba zasu daina ne insha Allahu"
D'an murmushin itama ta sakar masa ta ce.
"Hmm Yara fa ka ce?, shekara sha hud'u sune Yaran?, dama dai y'an shekara goma ne, sai na ce masu yarinta ke damunsu, idan basuyi hankali a yanzu ba sai yaushe?"
"Momyn Yara kenan, wallahi har yanzu Yara ne, yanzu fa suke shirin shiga JS3 fa karatun naso da saura ma, kofa secondry yanzu suka soma ta, ki bari kiga sadda Hauwa zata tare a gidan D'anki lokacin Zaki gane sun girma amma ba yanzu ba"
Da sauri Momy ta rok'o hannun Abba taja shi suka zauna akan kujerar parlo. D'an murza hannunsa tayi cikin hannunta tana kallonsa, kamin tayi magana ya rigata cewa.
"Ya dai Matar Abba?"
Ya fad'a da murmushi kwance akan fuskarsa, domin yasan abunda zata ce masa.
D'an turo baki tayi domin ita Momy indai a gaban Abba ne ji take kamar Yara suke har yanzun.
Murmushi ya k'ara fad'ad'a akan fuskar Abba yasa hannunsa ya d'an ja mata hanci yana cewa.
"Ke matar nan baki tsufa ne wai?, mi ya faru? fad'a min ina jinki"
"Kasan abunda nake so na fad'a ai"
"Noo fad'a min da bakin ki"
Sauk'e ajiyar zuciya tayi kamin ta d'anyi k'asa da muryarta tana cewa.
"Abbansu Hauwa, abunda nake so na ce shine, mi yasa Hauwa idan ta gama secondary bazata tare a gidan mijinta Abdallah ba?, idan yaso a gidan nasa sai tayi karatun na gaba please Abban Yara karka ce a'a"
Ta k'are maganar had'e da d'an k'ara murja y'an yatsun hannunsa dake cikin nata.
D'an sauk'e lumfashi kad'an yayi kamin shima ya ce.
"Ba wai nak'i bane, amma nafi so yarinyata tayi karatu sosai, bana so aje akaita matarsa ta nemi mai da ita shashasha, amma ya kike gani"
D'an murmushi ta sakar masa ta ce.
"Ko kad'an Lubna bata isa mai da Hauwa shashasha ba, shi yasa ma hankali yake kwance domin nasan halin yarinyata, bata barin ta kwana, bana shakkar zamanta tare da Lubna Abban Yara"
"Uhmmm"
Kawai Abba ya ce yana d'an zare hannunsa dake cikin na Momy ya d'an mik'e yana kallon saman silin d'in parlon, kamin ya ce.
"Abunda nake hangowa daban da naki, amma shikenan nima bana jinta, amma fa dole Y'ata ta fara karatu kamin ta tare a gidansa, bana so abunda zai kawo mata cikas akan karatunta. Sai nake ganin kamar karatun zai bata wahala a gidansa, kamar fad'an auran Abdallah a kanta zai iya kawo mata matsala a cikin rayu....
Da sauri Momy ta mik'e had'e da katse sa wajan cewa.
"A'a karka fad'i haka Abban Yara, kayi masu fatan alkhairi kawai Abban Yara, domin ni harga Allah na gaji da jiran gawar shano a wajan Lubna, domin wannan matar bata tsoron Allah, bana jin dan yanzu zata bari ta haihu, idan ka lura so take ma ta fara juya min Yaro, ni kuma wallahi bazan zuba ido na gani na kyale ba, dole ne na nemar masa mafita, hatta Yarinyata Hauwa bazan barta a haka ta shiga gidan Abdallah ba kariyar Allah a jikinta, dole ne nasa a rink'a sadaka a Masallaci ana sauk'e al'qur'ani mai girma, saboda mata na sanmu da zafin kishi, babu abunda wasu daga cikinmu bazasu iya yi ba, saboda kishi. Da zarar an sanar da ita babu haukan da baza tai ba"
Abba ya murmusa, ya fara hawa sama yana cewa.
"Hakane Momyn Yara, ki hawo sama ki d'an watsa ruwa akwai gajiya"
Bin bayansa tayi kamar yadda ya ce.
A b'angaran su Hauwa ko, tana shiga ta iske Nahna na shirya kayanta a cikin waduruf tana yi tana jin wak'a. Ganin ta shigo yasa Nahna tab'e baki tana binta da wani kallo.
Ko inda take Hauwa bata kalla ba bare tasan ma miye take.
A hankali ta matsa inda tata waduruf d'in take, had'e da gadonta dake gefen damarta, zama tayi kansa, kamin ta d'an mik'e da yake tana da kaya a gidan, sai kawai tasa akwatinta a cikin waduruf d'in bata wani fiddo kayan dake ciki ba, sai wadda ya zama dole zatai anfani dashi a yanzun.
Cire hijab d'inta tayi tana niyar tashi ta nufi toilet d'in d'akin nasu, kawai taji an jawota ta baya.
Da sauri take duban Nahna da tai mata aika-aikar.
"Ke kuma lafiya dallah can?"
Cewar Nahna.
Wani kallon uku saura kwata, Hauwa ta jefama Nahna kamin ta ce.
"Ban gane ba Malama, ina ruwanki dani Kuma?, wani abun nayi miki ne?, zaki wani zo da kwasassun k'afafunki ki wani jawo ni"
Wata uwar harara Nahna tayi ma Hauwa tana cewa.
"Gani nayi daga shigowarki, kin wani d'ibi hanyar toilet, kuma na tara ruwan zafi na, zanyi wanka, fatan dai ba Kashi za'a mana a toilet d'in ba ko?, domin dai nasan y'an K'auye ba abunda suka iya sai Kashi da cin tsiyar masifa"
"Hmmm"
Wani murmushin mugunta Hauwa ta saki, shi yasa a shirye tazo dai-dai take da Nahna wannan zuwan wallahi.
D'agowa tayi ta kalleta sama da k'asa tana nunata da yatsa ta ce.
"Au haka?, au ashe fa ku y'an gayu ne bakwa Kashi da fisari da tusa ko?, saboda kune shafaffu da Mai ko?, ki matsa ki ban waje na wuce Nahna"
Rik'e baki Nahna tayi tana cewa
"Keee ni kike kira da sunana gatsal haka kawai?"
"Au so kike na ce Aunty Nahna ko?, to kija girmanki tukunna sai ki dawo na ce miki auntyn, domin yanzu girma ya riga da ya fad'i, shi dama mutumci Madara ne idan ya zube baya kwasuwa"
Zata sake wata maganar Hauwa ta fisge hanunta ta shige toilet d'in, ta kuma rufe k'ofar toilet d'in da k'arfi.
Da sauri Nahna ta matsa bakin k'ofar toilet d'in tana cewa.
"Na rantse da Allah ki fito, karki tab'a min ruwan wanka na Hauwa, zanyi rashin mutumci wallahi"
Ko tak Hauwa bata sake ce mata ba.
Hakan ya k'ara hassala Nahna, sai b'ab'atu take a k'ofar toilet
Sai da Hauwa ta d'au lokaci sosai kamin ta bud'e k'ofar toilet d'in ta fito.
Lokacin da zata fito ran Nahna idan yayi dubu ya gama b'aci.
Bin ta tayi da kallon na tsananin mamaki, tashi tayi tsaye tana nunata da yatsa ta ce.
"Kan Uban nan kayyasa, au wankan kika yi da ruwan zafin da na tara?, ai ko baki isa ba wallahi"
Nan d'in ma ko inda take bata kalla.
Nahna toilet d'in ta shiga, can sai gata ta fito tana sakin tsaki tana cewa.
"Ai na d'auka wankan kike baki taran wani ruwan ba, da na rantse yau sai kin gane shayi ma ruwa ne"
Ta idasa maganar tana shegewa toilet d'in.
Murmushin mugunta Hauwa tayi tana d'an d'aure wani abu a leda tana yi tana cewa.
"Zaki ci ubanki ne yau wallahi, ke ce zaki gane shayin ma ruwa ne yau"
Zama tayi ta shirya a tsana ke ta shafa mai tasa kayan bacci, domin har bakwai na dare tayi da y'an minti na, shinfid'a abun sallah tayi ta gabatar da sallar da ake binta.
Tana sallame sallar taji ihun Nahna daga cikin toilet da sauri ta mik'e ba shiri sai kuma ta tuntsire da dariya tana tafa hannayenta tana cewa.
"Yanzun za'a fara wasan, ai dani kike zancan, duk wadda ya ci tuwo dani to miya yasha"
Tana rufe bakinta taga Nahna ta fito daga toilet da gudu sai soshe-soshe take tana buri a k'asa sai kiran "wayyo Allah na shiga uku na, k'aik'ayi ko ina na jikina, dan Allah ki taimaka ki sosa min wayyo na bani na shiga uku"
Mi Hauwa zatai idan ba dariya ba, harda kwanciya domin ganin yadda Nahna ke kiran ta bani ta sha uku, yadda take wage baki tana ihun azo a taimake ta.
"Wayyo wayyo wayyo Momy kina ina ne?, dan Allah kizo ki sosa min, wayyo k'aik'ayi ko ta ina jikina, ji nake kamar zan mutu, na shiga uku wayyo wayyo All......
Ta kasa k'arasa maganar jin wani mugun k'aik'ayi ata bayanta, da sauri cikin fitar hayyaci tasa hannun nata a baya zata sosa wajan, can taji wuyanta ya d'auka jikinta ya k'ara d'aukar wani mahaukacin k'aik'ayi wadda yafi dana da, da take ji, ihu ta k'ara saki don k'arfinta.
A rud'e kamar da gaske Hauwa ta sauka k'asa bayan ta gama tikar dariyar tata, Nahna na ganin yadda take mata dariya da yadda ta kasa bata taimako tasan ba wadda yayi mata wannan shegiyar muguntar sai Hauwa.
"Momy!! Momy!! Momy!!"
A rud'e Momy ta sakko tana cewa.
"Innallihi Hauwa miye na wannan kiran har kinsa gaba na ya fad'i Fisbilillahi?"
"Momy Ina Abba?"
"Abbanku ya fita Masallaci"
Zata sake magana Momy taji yadda Nahna ke ihun neman taimako.
Da sauri Momy ta zaro ido waje tana dafe k'irjinta ta ce.
"Subhanallahi mi ya faru Hauwa mi ya faru da Nahna?"
Gaba Momy tayi a mugun rud'e domin ihun da Nahna keyi na fitar hankali ne hakan ya k'ara rud'a Momy sosai, dan har tana tun tube wajan shiga d'akin.
Hauwa da ta rufa mata baya, suna shiga d'akin Momy tayi saurin runtse idonta tana cewa.
"Subhanallahi ke Nahna miye haka?, babu fa sutura a jikinki, miya shiga kanki haka ne?"
"Wayyo wayyo Momy ki taimka min ki sosa min, ko ina na jikina k'aik'ayi yake min".
Da sauri Momy ta matsa kusa da ita tana tallafo ta a jikinta ta fara sosa mata ko ina na jikin nata da har yayi jawur tsabar kartarsa da Nahnar keyi.
Momy a rud'e ta ce.
"Wai mi kika shafa ma jikin naki ne?".
"Wallahi Momy ban sani ba, daga watsa ruwa a toilet"
"Innallihi wa'inna alaihir. Hauwa d'akko min wayata na kira doctor yazo"
Da mugun sauri Hauwa ta k'ara sauka k'asa ta d'akko wayar, ko kad'an bata ji wani tausayin Nahna ba, gobe ma ta sake gaya mata maganar banza.
Tana kowawa Momy har hannunta na kyarma wajan danna number doctor.
Ba'a b'ata lokaci ba Doctor ya iso shima hankali a tashe, domin tunda ya taho Momy ke k'ara faman kiransa kamar zata tada gari, sai uban kira take masa.
Da kyar tasa ma Nahna wata riga marar nauyi har yanzu soshe-soshe kawai take harda su kuka yanzu domin yanzu da ta sosa zafi ma take ji, domin duk ta karce jikin nata.
A tare Abba da doctor suka shigo gidan, inda Abba yayi mamakin ganinsa, ya tabbayeshi ko lafiya?, wani ne ya kirasa a gidan, bai da labari.
A tak'aice Doctor yayi masa bayanin da Momy tayi masa shima.
Ai ko hankali a tashe shima Abba ya haura sama wajan d'akin su Nahnar.
Abba na shigowa ya matsa kusa dasu yana cewa.
"Wai mi ya kawo mata wannan susar jikin haka?"
"Abban Yara nima ban sani ba wallahi, haka na zo na tadda ta, nima Hauwa ta kira ni fa na zo na ganta a haka"
Juyawa yayi inda Hauwa take tsaye harda su kukan munafurci take yi da hawaye kamar gaske ya ce.
"Hauwa mi ya sami y'ar uwarki?"
"Abba nima ban sani ba wallahi, kawai ni dai ta zo ta shiga toilet har tana gaya min cewa y'an K'auye k'azamai ne basa wanka, dan taga banyi wanka ba sai ita, shine fa ta shiga da wata bak'ar leda wai ko k'awarta ta bata ko sabolo ne zatai wanka dashi, k'ila shine yasa ta jin k'aik'ayin"
Duk irin halin azabar da Nahna ke ciki hakan baisa ta kasa gane mi ye Hauwa ke shirin k'ulla mata ba, nan ta k'ara tabbatarwa kanta cewa tabbas Hauwa ce silar sata a wannan halin da take ciki, tabbas ta rantse da tsarkin mulkin Allah sai ta rama bazata tab'a barin Hauwa ta ci bulis ba.
Nahna tana kuka tana susar jikinta ta ce.
"Wallahi Abba ba abunda nasa nayi wanka dashi, kawai watsa ruwa nayi, amma ban san miya kawo min k'aik'ayin ba nima".
Ta wutsiyar ido take ma Hauwa kallon zamu had'u ne, itama Hauwar kallon ina jinranki ta aika mata dashi.
Da kyar dai aka samu Doctor yayi mata wata allura tasa ta bacci had'e da kashe k'aik'ayin.
Inda doctor ya k'ara masu jawabin cewa, akwai abunda ya sa mata k'aik'ayin nan, ba wai haka nan kawai ya same ta ba, akwai abunda ta shifa ma jikin nata..........
*Hi Masoya book d'in RAYUWAR MAKARANTA, karku shagala da yawa fa, domin book d'in RAYUWAR MAKARANTA yanzun ne tafiyar tashi ta soma, na kud'i ne akan raina d'ari hud'u ne kacal #400, zaka iya turo kud'in ka ta wannan account number d'in*.
👇
8130479973 Fatima Rabi'u Opay bank.
Sai ka turo shaidar biya ta wannan number d'in👉***