KIRJIN MAI HANKALI!!! (AKWATIN SIRRIN SA)
Free page 1
by @mssxoxo
_*KIRJIN MAI HANKALI*_
_(Akwatin sirrin sa)_
_🏘️👩❤️👨🧳_
*_The Vault of his secrets👩❤️👨❣️_*
_NA:_
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
🎗️°🎗️°🎗️°🎗️°🎗️
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
_(Da sunan Allah Mai Rahama... Mai Jin Qai...)_
_Assalamu Alaikum Wa Rahamatullah... zafafa fans barkan mu da sake haduwa a wata sabuwar tafiyar littattafan zafafa biyar.. Domin kasancewa da zafafa don mallakar books din, Sai a duba karshen shafin don duba yadda zaa mallaki littafan wannan tafiyar..._
_*KIRJIN MAI HANKALI(Akwatin sirrin sa)* qirqirarre ne. wasu sunayen da garuruwan ciki dama wasu abubuwan duk qirqirarru ne. Haka zalika wasu abubuwan na ciki gaske ne ko sun faru a gaske... Idan kuma labarin yayi dai dai da rayuwar wani ko wata to akasi aka samu. Adau hakan a rashin sani..... Abunda zan rubuta dai dai Allah ya hadamu a ladan duka, kurakuren dake ciki rabbana ya yafe mana... Allah Kuma yabamu ikon karasawa lafiya kamar yadda muka fara Amin... Allah Kuma ya Kara mana lafiya da abunda lafiyar zata rubuta Amin.._
°°°°
_FREE PAGE: 1/SHAFI DAYA NA KYAUTA_
°°
_KAUYEN BOKEZUWA_
°°°°
Almajirai ne fal a babban gidan ginin kasa na maraya. Gidah ne na manyan mutane. Da suka amsa sunan masu dattako da suka gauraya da ainihin sanin darajta ta dan adam da sanin ya kamata. ...
An nannade saman gidan da babban kwano...yayinda jikin gidan ya sha yabe gwanin shaawa. Daga can gefe akwai dakali da aka dandabe shi ya zauna daram sosai...
Ya yinda akwai tulin yashi a gefen gidan.ym yara nata hawa kai suna tsalle suna wasan su gwanin shaawa..
Mata ne keta shige da fice daga cikin gidan na su Malam Idi bokezuwa.. wasun su da kwanukan abinci sun shiga ciki. Wasu kuma suna fitowa da abinci daga ciki...
Ya yinda daga wajen gidan daga can gefe bayan wata bishiyar darbejiya. Katuwar tabarma ce dauke da dattawan garin a zazzaune. Da Qur'anai a hannun wasun su. Suna karantawa, ya yinda wasu kuma ke karantawa da baki ba qurani a hannuwan su...
Wani kyakkyawan bakin bafulatani ne a zaune a tsakiyar su. Sanye cikin riga da wando manya. Kansa ya saka hular tashi ka fiya naci. Hannunsa dauke da Qur'ani yana karantawa. Da gilashi a idanuwan sa. Da alama na karin ganin idanu ne..
Duk suna zazzaune a gefen sa. Daga hagunsa. Akwai wani da suke matukar kama shima. Sai dai shi idanuwansa babu gilashi. Sannan hannuwansa rike yake da allo yana karantawa..
--------------------------------------
Wata mata ce ta fito daga cikin gidah da sauri tana shewa hadi da tafa hannuwa cike da farin ciki..murya cikin tsananin murna ta karasa inda tabarmar su suke a zaune..
"Malam...."
Baki daya sai suka juya, Jin ta kira sunan da kowanne da shi ake Kiran sa da shi..
Ta dan sunkuyar da kai. Hadi da Saka kasan gyauton (zanin ta) datayi mayafi dashi tache,
"Allah ya sauke su lafiya. Akace a sheda mu ku"
"Alhamdulillah... Alhamdulillah... Alhamdulillah..." Duka suka hada baki wajen yin hamdala ga Allah
Da sauri Kuma suka mike a tare. Malama Idi ya bawa dan uwan sa malam Nata'ala hannu sukayi musabaha cike da farin diki. Kowanne fuskar sa lullube da tarin murnar da ba zata iya fasaltuwa ba.
"Fatan iyayen na su duk suna lafiya?"
"Kalau alhamdulillah"
"To mashaa Allah."
"An samu mata duka malam..... "
"Mashaa Allah allahu.."
Kai tsaye suka shiga cikin gidan bakunan su dauke da sallama. Bayan matar ta shiga ta nemo mu su iso. Duk kuwa da gidan su ne. Amman ko da yaushe sai sun nemi iso. Saboda mata na yawan shiga gidan Wanda suke na aure. Gidan ko yaushe dauke yake dasu. Saboda suna karatun dare inna goge da gwaggo abule. Sune malaman makarantar daren da akeyi acikin gidan na su...
Malam Idi ya dauki yaran daya bayan daya yana duban kowacce tubarkallah mashaa Allah... Kai kache yan biyu ne saboda yadda aka haife su rana daya lokaci kusan daya da mintina kawai daya ta gota daya....
Addu'oi ya musu. Ya Kuma Kira kiran sallah..kana ya mika musu yaran fuskar sa dauke da murmushi ya dubu malam idi kanin sa.
Malam Nata'ala bayan ya musu adduoi shima ya mika Wa su iya su ,yana bawa dan uwan sa hannu suka sake gaysawa yace...
"Allah ya raya mana.... Zaytunah da Rumanah...."
..
_1-KALBIM:MAMUH GEE_
_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_
_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_
_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_
_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_
_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_
_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_
_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga ***_
*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*
****.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*****
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACCOUNT NAME/SUNAN DAKE ASUSUN BANKI: MARYAM SANI GUMMI*